Sai kaga mutum daga ya samu wata yar dama to do yake ace ya samu wata hanyar wulakanta wannan wanda yayi masa rana kokuma ya wuce shi a matsayi ko wani abin Duniya ba tareda la’akari da cewar wannna wanda ya koya maka to ya fika sanin komai a wannan harkar musamman ma a nan masana’antar Kannywood.

Don haka kamata ya yi ce mutane sun fahimci cewar babu ta yadda za a yi ka ci gaba matukar ka na da wata niyyar cin amanar wanda ya taimake ka ka kai wani matsayi na rayuwa, ni yanzu a matsayina na Ayatullahi Tage na yi biyayya ga maigidana Alhaji Tage wanda ya nuna mani hanya, ya rike ni kamar dan da ya haifa, kuma yake fatan duk wani alheri na Duniya ya same ni.

Ga shi yanzu ina ganin amfanin biyayyar domin kuwa duk wani abin da ake fatan samu na alheri a wannan masana’antar Allah ya nufe ni da samu kama daga mutunci, daukaka da kuma abin Duniya, don haka nike shawartar ‘yan uwa abokan sana’ara da ma sauran mutane da su kasance masu biyayya a duk inda suka samu kansu a rayuwa kuma kada su zamo masu girman kai ko nuna kyashi ga abin da wani ya samu domin kuwa  Allah mai iko ne akan kowa da komai zai iya baiwa wanda bai da shi, ya kuma amshe ga wanda ke da shi idan yaga dama.

Dangane da matsaloli ko kalubale da masana’antar Kannywood ke fuskanta Tage ya ce, ba komai ya janyo hakan ba illa rashin hadin kai a tsakanin masana’antar, duk al’ummar da aka ce babu hadin kai a tsakaninsu to lallai za ka samu wannan al’umma babu wani cigaba da suka samu, to amma matukar muka hada kanmu ya zamana mun zamo tsintsiya madaurinki daya babu wata baraka da za ta iya shigowa a cikinmu ya tabbatar.

Muddin aka ce akwai hassada ko kyashi a tsakaninmu to zai yi wuya mu dinga bai wa junanmu shawarwarin da za su ciyar da masana’antar gaba, sakamakon haka kuwa ba karamar illa zai janyo mana ba, don haka nike kira ga mahukunta da sauran al’umma da ke cikin Kannywood da mu daure mu hada kanmu domin mu kai wannan masana’antar inda ya kamata ta kasance.

Daga karshe ya bukaci mutane da ke furta kalaman tsinuwa ga jaruman fim da suji tsoron Allah su bari, idan kuma ba haka ba to su sani cewa su kansu basu san wadanda za su haifa ba, mai yiwuwa su haifi yaron da zai ji ya na sha’awar  harkar fim kuma ya shigo harkar a dama dashi, to idan haka ta faru wannan tsinuwar da sukayi wa jaruman fim za ta shafi yayansu da suma suka shiga cikin harkar fim din.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Kannywood masana antar

এছাড়াও পড়ুন:

Tottenham Ta Doke Manchester United A Wasan Karshe Na Europa 

 

Duka kungiyoyin biyu sun kasa tabuka abin azo agani a wannan kakar a gasar Firimiya Lig, inda Manchester United ke matsayi na 16 Tottenhma na bi mata, amma wannan nasarar da yaran na Postecoglu suka samu ya sa sun samu gurbi kai tsaye a gasar Zakarun Turai ta badi.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tottenham Ta Doke Manchester United A Wasan Karshe Na Europa 
  • Farar Dabarar Da Tsoffin Masana’antu Ke Yi A Kasar Sin Don Tafiya Da Zamani
  • Raya Kasa Na Bukatar Bin Daidaitacciyar Hanya
  • Yadda aka kashe dan fashi aka kama wasu 7 a Abuja
  • Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ta Iran Ya Ce: Haramtacciyar Kasar Isra’ila Ba Ta Da Alkiblar Siyasa
  • Shugaban Kasar Colombia: Ayyukan Kasar Sin Sun Nuna Wani Sabon Salo Na Ci Gaban Zamantakewar Al’ummar Bil’adama
  • Xi Jinping Ya Ziyarci Birnin Luoyang Na Lardin Henan
  • Kwara Ta Kafa Tutar Hadin Kai Mai Mita 70 A Ilorin
  • Uwargidar Gwamnan Zamfara Ta Sake Jaddada Kudurin Dakile Tu’ammali Da Miyagun Kwayoyi A Jihar
  • Hadin Gwiwa Bisa Daidaito Da Girmama Juna Tsakanin Sin Da Amurka Zai Samar Da Moriyar Juna