HausaTv:
2025-05-07@20:16:37 GMT

Kasar Indiya Ta Yi Luguden Makamai Masu Linzami Kan Kasar Pakistan

Published: 7th, May 2025 GMT

Gwamnatin kasar Indiya ta yi luguden makamai masu linzami kan kasar Pakistan, yayin da Pakistan ta sha alwashin mayar da martani

Gwamnatin Indiya ta kai hare-haren makamai masu linzami kan wasu wurare a kasar Pakistan da yammacin jiya Talata, kuma sojojin Pakistan sun sha alwashin mayar da martini, yayin da ake ci gaba da samun takun saka tsakanin kasashen biyu masu karfin nukiliya.

Gwamnatin Indiya ta kai hare-hare da makamai masu linzami guda uku kan wasu wurare a yankin Kashmir da Punjab na kasar Pakistan, yayin da daya daga cikin makaman ya afkawa tsohon filin jirgin sama na Muzaffarabad a yankin Kashmir da Pakistan ke iko da shi.

A nata bangaren, gwamnatin Indiya ta sanar da cewa ta kaddamar da wani farmaki kan abin da ta kira ababen more rayuwa na ‘yan ta’adda a Pakistan da Jammu da Kashmir, ta kuma ce sojojinta sun kai hare-hare kan wasu wurare 9 na Pakistan.

Indiya ta kara da cewa: Hare-haren sun fi mayar da hankali zuwa wasu wurare da aka tantance, kuma ba tare da nufin janyo wani tashin hankali ba, don haka ba a kai hare-haren kan wasu cibiyoyin sojin Pakistan ba.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: kasar Pakistan kai hare hare wasu wurare

এছাড়াও পড়ুন:

Saudiyya Ta Tanadi Hukunci Mai Tsanani Ga Masu Yin Aikin Hajji Babu Takardun Izini

Wanda ya ba su masauki a otal, gida, ko wani wurin zama shi ma zai fuskanci irin wannan hukunci.

Duk wanda ya je aikin Hajji ba tare da izini ba ko dan ƙasa ne ko wanda ya daɗe fiye da lokacin zama za a kori mutum zuwa ƙasarsa tare da dakatar da shi daga shiga Saudiyya na tsawon shekaru 10.

Hukumomin shari’a za su kuma karɓi motocin da aka yi amfani da su wajen safarar waɗanda ba su da izinin yin aikin Hajji, musamman idan motocin na masu laifin ne.

A wani labari da ya shafi aikin Hajji, Hukumar Hajji ta Ka6sa (NAHCON) ta sanar da cewa jigilar mahajjatan Nijeriya na shekarar 2025 zai fara ne daga ranar 9 ga watan Mayu.

A cewar wata sanarwa da Daraktar Watsa Labarai ta NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta fitar ta ce mahajjata 43,000 ne suka riga suka biya kuɗin Hajji a bana.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Duniya Ta Gano Damammaki Masu Kyau Daga Kasuwar Kasar Sin A Yayin Hutun Ranar Ma’aikata Ta Duniya
  • Kasashen duniya sun damu da rikici tsakanin Indiya da Pakistan
  • Yaƙi ya ɓarke tsakanin Indiya da Pakistan
  • Karuwar Tafiye-Tafiye Yayin Hutun Ranar Ma’aikata A Kasar Sin Ya Bayyana Kuzarin Masu Kashe Kudi
  • Jiragen Yaken HKI Sun Kai Hare-Hare A Kan Tashar Jiragen Sama Na Birnin San’aa Na Kasar Yemen
  • Saudiyya Ta Tanadi Hukunci Mai Tsanani Ga Masu Yin Aikin Hajji Babu Takardun Izini
  • ’Yan bindiga sun kashe matar aure bayan karɓar N10m kuɗin fansa
  •  Sojojin HKI Sun Kai Hare-hare A Sassa Mabanbanta Na Kasar Yemen
  • Kasar Iran Zata Mayar Da Martani Mai Tsanani Kan Duk Wani Hari Da Zata Fuskanta Daga Makiya