Sudan ta katse dangantakar diflomasiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa
Published: 7th, May 2025 GMT
Gwamnatin Sudan da ke da goyon bayan sojoji ta katse dangantakar diflomasiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), tana bayyana ƙasar a matsayin mai katsalandan, a cewar Ministan Tsaron Sudan, Yassin Ibrahim.
A cikin jawabin da aka watsa a talabijin ranar Talata, Ibrahim ya bayyana cewa Sudan ta “katse dangantakar diflomasiyya da UAE,” tare da janye jakadanta da rufe ofishin jakadanci da konsulat ɗinta a ƙasar Gulf ɗin.
Ya zargi UAE da take hurumin Sudan ta hanyar “ƙawarta”, wato Rundunar RSF, wacce ke yaƙi da sojojin Sudan tun watan Afrilu 2023.
“Dukkan duniya ta shaida, fiye da shekaru biyu, laifin kai hari kan hurumin Sudan, cikakken yankinta da kuma tsaron ‘yan ƙasarta da UAE ke yi ta hanyar ƙawarta ta cikin gida, wato ƙungiyar ‘yan ta’adda ta RSF,” in ji ministan.
Gwamnatin Sudan ta sha zargin UAE da samar wa RSF makamai — zarge-zargen da Abu Dhabi ya musanta.
Matakin da gwamnatin Sudan ta ɗauka ya biyo bayan harin jirage marasa matuƙa a Port Sudan — wanda yanzu ya zama babban birnin ƙasar na wucin gadi — wanda aka kai har sau uku a jere.
Ibrahim ya ce UAE ta ƙara tsananta shiga cikin rikicin ta hanyar samar wa RSF “makamai masu ci gaba na zamani” bayan nasarorin da sojojin Sudan suka samu a filin daga, inda suka sake karɓe iko da babban birnin Khartoum a watan Maris.
Ya ƙara da cewa Sudan za ta “mayar da martani ga wannan hari ta kowace hanya da ta dace don kare hurumin ƙasar” da kuma “kare fararen hula.”
Yaƙin da ya yi sanadin mace-maceYaƙin da ke gudana a Sudan ya kashe dubban mutane, ya raba mutane miliyan 13 da muhallansu, kuma ya haifar da babbar matsalar gudun hijira da yunwa a duniya.
Rikicin ya raba ƙasar gida biyu, inda sojojin ke iko da arewa, gabas da tsakiyar ƙasar, yayin da RSF ke mamaye mafi yawan yankin Darfur na yamma da wasu sassan kudu.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Zan Ba Ku $1,000 Kyauta In Zaku Koma Garuruwanku – Trump Ga Baƙin Haure
Trump ya bayyana cewa, waɗanda suka zabi barin ƙasar da kansu na iya samun dama ta hanyar doka don dawowa cikin Amurka nan gaba idan suka cika ka’idojin da suka dace.
A cewar rahoton, an riga an sayo tikitin jirgi ga mutum na farko da ya karɓi wannan tayin — daga birnin Chicago zuwa ƙasar Honduras.
Tun bayan da Trump ya sake komawa kan kujerar mulki a watan Janairu, ya gindaya sabbin matakai masu tsauri don hana baƙin haure shiga ƙasar. Wasu daga cikin waɗannan matakan na haifar da ce-ce-ku-ce, musamman ganin yadda ake amfani da tsofaffin dokokin wanda suke da alaka da zamanin yaƙi wajen aiwatar da su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp