NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyar ’Ya’yansu
Published: 8th, May 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Duk wanda ya shekara arba’in zuwa sama ya san irin tarbiyyar da ya samu daga wurin iyayensa a da, da irin mu’amalar da ke tsakaninsa da iyaye da kuma irin shaƙuwar da ke tsakanin ’ya’ya da iyaye.
A yanzu kuwa, abubuwa sun canza daga yadda aka san su, inda abubuwa suka rincaɓe suka yi wa iyaye yawa.
Ɗaya daga cikin manyan sauyin da aka samu shi ne aikin gwamnati ko aikin wata da iyaye mata suke yi a wannan zamani wanda a wasu lokuta ke barazana ga irin kulawar da ’ya’ya suke samu.
NAJERIYA A YAU: Me Ya Sa ‘Yan Gwagwarmaya Ke Shiga Tasku A Najeriya? DAGA LARABA: Ɓoyayyun Dalilan Da ke Sa Faɗuwa Jarabawa A NajeriyaShirin Najeriya A Yau zai yi nazari ne kan irin ƙalubalen da iyaye ke fuskanta a wannan zamani wajen tarbiyyar ’ya’yansu.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: ya ya iyaye kulawa Tarbiyya
এছাড়াও পড়ুন:
Sashen Lafiya Zai Fara Amfani Da Sabuwar Fasahar AI Don Inganta Lafiya
Kwalejin Kiwon Lafiya ta Najeriya ta fara taron shekara-shekara karo na 19 na kimiyya da nufin yin amfani da sabbin fasahohi da kirkire-kirkire wajen kawo sauyi a fannin likitanci a kasar.
Da yake yiwa manema labarai jawabi gabanin taron a Sokoto, shugaban kwalejin na kasa, Dokta Peter Ebeigbe ya ce taron zai tattauna hanyoyin da za a bi domin tunkarar manufofi aiwatarwa mai inganci da shigar da kamfanoni masu zaman kansu a fannin ilimin likitanci na gaba da digiri na biyu.
Gidan Rediyon Najeriya dake Sokoto ya ruwaito cewa, ana sa ran taron zai kuma tattauna kan ingancin aikace-aikacen kirkirariyar fasaha ta Artificial Intelligence (AI) da illolinsa na isar da sahihanci mai inganci.
Shugaban na kasa ya kara da cewa ana sa ran masu hannu da shuni hudu ne zasu jagoranci taron.
Nasir Malali