An kama mutum 6 da ake zargi kan garkuwa da mutane
Published: 8th, May 2025 GMT
Rundunar ’yan sandan Jihar Akwa Ibom ta ce, ta kama wasu mutum shida da ake zargi da yin garkuwa da wasu mutane a jihar kwanan nan.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan, DSP Timfon John ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya sanarwa manema labarai a ranar Alhamis a garin Uyo, inda ya ce an kama su ne biyo bayan sahihan bayanai game da shirin yin garkuwa da mutane a ƙaramar hukumar Eket.
John wanda ya bayyana cewa mace ɗaya tilo a cikin waɗanda ake zargin ba ’yar Najeriya ba ce, ya bayyana cewa an ƙwato wata mota ƙirar leɗus da wayoyin hannu guda biyar daga hannun waɗanda ake zargin.
“A bisa wannan bayanin, jami’an rundunar sun tattara kadarori, inda suka kama wani mutum mai suna Joseph Alafia, a Garin Oron a ranar 6 ga Mayu, 2025. Wannan kamun na farko ya ƙara kai samame wurare biyu a Afia Nsit Eket.
“Waɗannan ayyuka da rundunar ’yan sandan ta gudanar tare da haɗin guiwa sun yi nasarar cafke wasu mutane kamar haka: Oyibo Ayibakumo Brown, namiji ɗan Jihar Bayelsa, Wisdom Harry, namiji ɗan Jihar Ribas, Afanye Igonikon, namiji dan Jihar Ribas, Dare Olaniyi, namiji ɗan Jihar Ogun, da ke zaune a garin Port Harcourt, Jihar Rivers da kuma Tita Mercy Masume mace ’yar ƙasar Kamaru.
“A yayin samamen, hukumomi sun gano motar Lexus RX 300 mai lamba KMR 491 AE mai launin toka, waɗanda ake zargin ana amfani da su wajen yin garkuwa da mutane, tare da wayoyin hannu guda biyar.
“Waɗanda aka kama ana kyautata zaton suna da alaƙa da sace-sacen da aka yi a Eket na baya-bayan nan, kuma a halin yanzu ana gudanar da bincike mai zurfi.
“Kwamishanan ’Yan sanda, CP Baba Mohammed Azare fsi, ya yaba da yadda jami’an ’yan sandan suka yi taka-tsan-tsan da ɗaukar matakin da suka ɗauka na samun nasarar kamen.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Akwa Ibom Masu Garkuwa da mutane
এছাড়াও পড়ুন:
An gurfanar da mutum 10 kan yi wa nakasasshiya fyaɗe a Kaduna
Wata kotun majistare da ke titin Ibrahim Taiwo a Kaduna ta gurfanar da wasu mutane 10 da suka haɗa da kaka, bisa laifin yi wa wata yarinya ’yar shekara 16 fyaɗe a ƙauyen Likoro da ke ƙaramar hukumar Kudan ta jihar.
An ruwaito cewa wanda ake zargi mutum na 11 na hannu a lokacin da shari’ar ta taso, ranar Alhamis.
An zaɓi Robert Prevost sabon fafaroma Ficewar ’Yan Majalisa 3 a PDP: Raɗɗa ya halarci zauren Majalisar WakilaiWaɗanda ake zargin, a cewar rahoton farko da aka samu, sun ce wacce aka yi wa fyaɗen an yi ta aikat fyaɗen a lokuta daban-daban ta hanyar yaudara da kuma lallashinta ta zuwa wurarensu daban-daban inda suke da masaniya game da ita.
Lamarin ya haifar da samun ciki kuma wadda aka yi fyaɗen ta haifi ɗa namiji watanni huɗu da suka wuce.
Ɗan sanda mai gabatar da ƙara, Insfekta Yakubu I. Lemu, ya ce matakin ya saɓawa sashe na 257 na kundin laifuffuka na Jihar Kaduna.
Ya ce, “A cewar rahoton farko da aka samu a ranar 27 ga watan Oktoba, 2024 da ƙarfe 6:30 na yamma, wani Usman Yusuf ya ruwaito cewa ya gano cewa ƙanwarsa Fatima Maikanti na ɗauke da juna biyu na wata shida, ya ce a lokacin da aka tambaye ta, ta bayyana cewa a wurare daban-daban, a lokuta daban-daban waɗanda ake zargin sun yi ta lalata da ita ne, sun kai ta wurare daban-daban a ƙauyen inda ta samu juna biyu, hakan ya sa ta haifi yaro.