Dalilan Da Ke Nuna Malaman Makaranta Na Da Muhimmaci (5)
Published: 10th, May 2025 GMT
12.Malaman makaranta suna nuna yadda muhimmnci ilimi yake.
Malaman makaranta suna zama abin yin koyi musamman ma saboda lamarin ilimin da al’umma suke karuwa da shi daga gare su.Yada suka maida hankalinsu kan koyon darussan da za su koyar, hakan ya sa daliban abin ya basu sha’awa har abin ya burge su suka fara gane karfi da darajar ilimi, a rayuwa ta yau da kullum.
13.Malaman makaranta suna karkakawa kan yadda al’umma za su bada gudunmawar ci gaban wuraren da suke
Malaman makaranta suna bada muhimmiyar gudunmawa wajen koyar da yadda su dalibai za su gane cewa suma fa akwai ayyukan da za su yiwa al’ummar domin ci gabansu.In kana koya muhimmancin yi wa al’umma ayyuka, halaye masu kyau, yadda za su kasance cikin kowane aiki na al’umma. Malaman makaranta sune wadanda za su iya daukar nauyin aiwatar da hakan ga ‘yan kasa wadanda suke da sha’awar yin hakan.
Yadda Malamin makaranta zai cimma wannan burin:
Koya darussan da suka shafi gida, kasa, da kuma duniya gaba daya.
Ka ba dalibai kwarin gwiwa na kasancewa cikin ayyukan da suka shafi al’umma, da kuma Kamfen da ya shafe su.
Koya masu muhimmacin jefa kuri’a,aikin sa kai,da kuma da kuma sauran ayyuka masu inganta rayuwar al’umma.
14.Malaman makaranta suna samar da suka kamata ga ci gaban karuwar basira abubuwan ci gaba na al’umma
Malaman makaranta suna samar da wani yanayi inda dalibai za su samu damar koyon sabbin dabaru, su yi tunanin da zai samar da wani sabon abu,dauki wani matakin da ana iya samun matsala da kwakwalwa amma idan aka samu nasara akwai karuwa.Irin wannan bada kwarin gwiwa yana bunkasa kowane dalibi ta yadda kirkirar wani abu da sauki,tare da samar da tunanin da zai bunkasa ci gaban al’umma.
Hanyoyin da Malaman makaranta za su bunkasa iya kirkirar abubuwa:
Samar da wasu ayyuka wadanda za su ba dalibai samun damar yadda za su bayyana abubuwan ta hanyar bada shawarwari.
Ba dalibai kwarin gwiwa inda za su musayar ra’ayi, yin gwaji,da kuma gabatar da shawarwarinsu.
Bada dama yadda za a shigar da yadda za ayi maganin wata matsala da ke nasaba da kirkira a kowane darussan koyarwa na kowace rana.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Kauyuka 30 Sun Yi Zanga-zanga Kan Ta’addancin ‘Yan Bindiga A Zamfara
Mazauna kauyuka akalla 30 daga Dan-Isa da Kagara dake karamar hukumar Kaura-Namoda a jihar Zamfara, sun mamaye gidan gwamnati dake Gusau babban birnin jihar domin nuna takaicinsu kan yadda rashin tsaro a yankin na su “yaki ci yaki cinyewa” a ranar Alhamis. Masu zanga-zangar da suka hada da mata da kananan yara suna dauke da alluna dauke da rubuce-rubuce kamar: “Muna bukatar zaman lafiya a kauyukan Kaura-Namoda,” “Gwamna Dauda Lawal da Matawalle ku kawo mana dauki”, “Ana kashe mu kowace rana,” da dai sauransu. Tsoffin Kansilolin APC Sun Yi Zanga-zangar Nesanta Kansu Da Maganganun Abdullahi Abbas Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Jihohin Makwabta, Ya Kara Ta’azzarar Rashin Tsaro A Neja – Bago Da yake jawabi a gidan gwamnati, jagoran masu zanga-zangar, Lawal Kamilu daga Dan-Isa, ya ce sun gudanar da zanga-zangar ne don nuna takaicinsu kan yadda ’yan bindiga ke addabar kauyukansu tare da kashe mutanensu a koda yaushe. “Dukkanmu mun fito ne daga kauyuka kusan 30 don nuna rashin amincewa da rashin tsaro saboda yawancin mutanenmu ko dai an kashe su ko kuma ‘yan bindiga sun yi garkuwa da su. “Suna bukatar a biya su kudin fansa da ya kai miliyoyin Naira, alhalin ba mu da komai, babu abin da za mu bayar a matsayin kudin fansa, domin duk mun sayar da kadarorinmu da gonakanmu domin biyan kudin fansar ‘ya’yanmu da ‘yan uwanmu da aka yi garkuwa da su a baya,” in ji Kamilu. Masu zanga-zangar sun yi kira ga Ministan Tsaro, Bello Matawalle, da gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Tinubu da su kawo musu dauki, suna masu cewa “Yanzu Zamfara na hannun Ubangiji mai rahama, Madaukakin Sarki”.Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp