HausaTv:
2025-05-12@09:26:24 GMT

Tehran ta bayyana aniyarta na karfafa hadin gwiwar ‘yan sanda da Nijar

Published: 11th, May 2025 GMT

Iran ta bayyana aniyarta ta karfafa hadin guiwar ‘yan sanda da Nijar.

Wanna bayanin ya fito ne a wani bangare na ziyarar da, Birgediya Janar Ahmad-Reza Radan, babban kwamandan rundunar tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya kai ziyara a kasar Nijar a ran gadinsa a Afrika.

A ziyarar tasa ya gana da firaministan Nijar Ali Lamine Zeine, da ministan harkokin wajen kasar Bakary Yaou Sangaré, da ministan harkokin cikin gida Janar Mohammed Tomba, da shugaban ‘yan sandan Nijar Janar Omar Chiyani.

A yayin ganawar, M. Zein ya jaddada karfafa hadin gwiwar ‘yan sanda a tsakanin kasashen biyu inda ya ce: “A shirye muke mu yi amfani da gogewar da ‘yan sandan Jamhuriyar Musulunci ta Iran suke da ita a dukkan fannoni.”

A nasa bangaren Janar Radan ya bayyana aniyar Iran ta mika kwarewar aikin ‘yan sanda zuwa Nijar tare da bayyana fatan kasashen biyu za su iya fadada hadin gwiwarsu a dukkan fannoni da suka hada da yaki da ta’addanci da safarar muggan kwayoyi da manyan laifuka.

A yayin ganawarsa da Mista Sangare, babban jami’in na Iran ya jaddada saukaka hadin gwiwa wajen musayar bayanai tsakanin  kasashen biyu, da mika wadanda ake zargi ta hanyar Interpol.

Tunda farko dama bangarorin sun sanya hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa da fahimtar juna wacce Janar Radan na Iran da Janar Mohammed Tomba, ministan cikin gida na Nijar suka rattabawa hannu

Bangarorin biyu sun jaddada karfafa hadin gwiwar ‘yan sanda, da musayar bayanai da yaki da ta’addanci.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: karfafa hadin

এছাড়াও পড়ুন:

Nijar da Iran sun cimma yarjejeniyar fahimtar juna a tsakaninsu

Kasashen NIjar da Iran sun cimma yarjejeniyar fahimtar juna a tsakaninsu a bangarori da dama.

Bangarorin sun sanya hannu a yarjejeniyar ne a yayin ganawar data wakana tsakanin ministan harkokin cikin gida da tsaron jama’a da wata tawagar Iran karkashin jagorancin babban kwamandan rundunar tsaron kasa Birgediya Janar Ahmad Rezaei RADAN.

A yayin wannan zama Nijar da Iran sun amince da kafa kwamitin kwararru domin yin musayar ra’ayi lokaci-lokaci da karfafa hadin gwiwa.

Nijar da Iran, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da nufin karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, musamman a fagen yaki da ta’addanci, da manyan laifuffukan kasa da kasa, tsaron iyakoki, da kuma shige da fice ba bisa ka’ida ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran Da Amurka Sun Fahinci Juna Sosai A Zagaye Na 4 A Tattaunawa A Mascat
  • Yadda ɓallewar ƙasashen AES ta illata ECOWAS
  •   Iran Ta Yi Maraba Da Tsayar Da Wutar Yaki A Tsakanin Indiya Da Pakistan
  • Iran Ta Bayyana Damuwarsa Da Makaman Nukliyar HKI A Sanda Ake Takura Mata
  • Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Gana Da Tokwaransa Na Kasar Saudiya A Jiya Asabar
  • Shugaban Putin Ya Gana Da Sisi Don Karfafa Harkokin Kasuwanci Tsakanin Kasashen Biyu
  • Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Ce Kafa Hujja Da ‘Yan Tawaye Kan Iran Yankewar Kauna ce Ga Makiyanta
  • Nijar da Iran sun cimma yarjejeniyar fahimtar juna a tsakaninsu
  • Sin Da Rasha Za Su Karfafa Hadin Gwiwa Don Kare Karfin Ikon Dokokin Duniya