2025-06-24@06:18:18 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2460
«rashin wuta»:
Sai dai babu wani tabbaci daga gwamnatin Iran ko Isra’ila kan cewa sun yarda su dakatar da yaƙin. Trump ya kira rikicin da ake ciki da suna “yaƙin kwana 12,” yana mai cewa wannan rikici da za a iya yin shekaru ana fafatawa da shi bai bazu ba, kuma ba zai bazu ba. Mene ne ke faruwa yanzu? Bayan da Trump ya sanar da cewa an tsagaita wuta, Isra’ila ta ce an kashe mutane uku sakamakon hare-haren da Iran ta kai. Amma ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce babu wata yarjejeniya ta tsagaita wuta. Sai dai ya ce Iran za ta daina kai hari idan Isra’ila ma ta dakatar da nata. Rikicin ya tsananta ne bayan Iran ta...
Shugaban Ƙasar Amurka Donald Trump ya ce an ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta gaba daya a yaƙin da ya ɓarke tsakanin Iran da Isra’ila. Kafar yaɗa labarai ta the Guardian ta ƙasar Birtaniya ta ruwaito cewa Trump ya sanar da haka ne a shafinsa na sadar da zamunta, ’yan sa’o’i bayan hare-haren ramuwar gayya da Iran ta kai a sansanin sojin Amurka da ke ƙasar Qatar da Iran bayan hare-haren da Amirkan ta kai wa Iran. Ya sanar cewa cikin awa shida na farko Iran za ta fara dakatar da kai hare-hare, daga bisani Isra’ila ta dakatar, wanda hakan zai kawo ƙarshen yaƙin ɗungurungum. Sanarwar tasa na zuwa ne bayan tsohon Fira Ministan Rasha, babbar ƙawar Iran, Dimitry Medvedev na cewa...
Gwamnatin Qatar ta yi Allah-wadai da harin da Iran ta kai kan sansanin sojin saman Amurka da ke yankin al-Udeid na kasar. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar, Majed al-Ansari, ya wallafa a shafinsa na X cewa: “Mun ɗauki wannan a matsayin keta haddin Qatar da sararin samaniyarta da dokokin duniya da kuma yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya.” Iran ta ƙaddamar da hare-hare kan sansanonin sojin Amurka Babu dalilin kai wa Iran farmaki — Putin Ya ce na’urorin kakkaɓo makamai na ƙasar sun “samu nasarar daƙile hare-haren na makamai masu linzami” kuma tuni aka janye dakarun Amurka daga sansanin tun kafin harin. Ya ƙara da cewa “an ɗauki duka matakan da suka dace wajen tabbatar da tsaron lafiyar dakarun a sansanin, ciki...
Wani hari da Sojojin Amurka da Isra’ila suka kai kan wuraren Nukiliyar Iran ya kara tsoratar da kasuwar mai, wanda ke nuna cewa farashin na iya haura sama da $80 a kowace gangar mai. Masana sun yi hasashen cewa farashin fetur na iya haura sama da N1,000 a litar cikin ‘yan makonnin nan idan ba a dauki mataki ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rahotanni na cewa ƙasar Iran ta fara abin da ta kira martani mafi girma da nasara kan hare-haren Amurka. Kamfanin Dillancin Labaran Iran na Tasnim, ya ce dakarun juyin juya halin ƙasar sun ƙaddamar da hare-haren makamai masu linzami kan sansanin sojin Amurka da ke Qatar da Iraƙi A halin yanzu ne aka samu labaran jin ƙarar abubuwan fashewar a Qatar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban Ƙasar Rasha, Vladimir Putin, ya ce babu wata hujja ko dalilin kai wa Iran hari. Putin ya yi wannan furuci ne yayin wata tattaunawa da Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Agarachi a fadar Kremlin da ke birnin Moscow. Akwai ƙasashen da ke shirin bai wa Iran makaman nukiliya — Rasha Fararen hula sun yi garkuwa da sojoji 57 a Columbia A jawabin da ya gabatar a farkon tattaunawar wanda aka yada a gidan talabijin na gwamnatin Rasha, shugaba Putin ya ce: “Babu wata hujja ko dalili da zai sa a kai wa Iran farmaki.” Ya ƙara da cewa “na ji daɗin zuwan ka [Agarachi] Moscow a yau. Wannan zai ba mu damar tattauna waɗannan batutuwa masu wahala da kuma...
Wani babban jami’in Rasha, Dmitry Medvedev ya yi iƙirarin cewa akwai wasu ƙasashe da ke shirin bai wa Iran makaman nukiliya domin kare kanta daga abokan gaba. A ranar Lahadi, Dmitry Medvedev wanda tsohon Firaministan Rasha ya yi iƙirarin cewa wasu ƙasashe sun shirya domin bai wa Iran makaman nukiliya kai-tsaye bayan hare-haren Amurka kan tashoshin nukiliyarta. Matashi ya yi wa maraya ɗan shekara 10 kisan gilla a Zariya Amurka ta roƙi China ta sa baki kada Iran ta rufe mashigar tekun Hormuz “Wasu ƙasashe sun shirya domin bai wa Iran makaman nukiliyarsu kai-tsaye,” kamar yadda Medvedev, Mataimakin Majalisar Tsaron Rasha, ya bayyana a wasu jerin saƙonni da ya wallafa a shafin X. Medvedev ya ce da alama wuraren da...
Rahotanni sun bayyana cewa, kasashen Rasha, da Sin da Pakistan, sun gabatar da wani daftarin kudurin kwamitin sulhun MDD, kan halin da ake ciki a Iran. Game da hakan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya shaidawa nuni taron manema labarai da aka saba yi a yau Litinin cewa, harin da Amurka ta kai kan wuraren da kasar Iran ta girke na’urorin nukiliya ya saba wa manufar tsarin dokokin MDD, tare da kara ta’azzara tashin hankali a yankin gabas ta tsakiya, don haka, dole ne kwamitin sulhun ya dauki mataki kan batun. Kakakin ya kara da cewa, kasar Sin na sa ran mambobin kwamitin za su goyi bayan daftarin kudurin, tare da sa kaimin kwamitin ya taka muhimmiyar...
Rundunar Sojin ƙasar Columbia ta tabbatar da cewa fararen hula sun yi garkuwa da dakarunta guda 57. Janar Federico Alberto Mejía na Rundunar ya sanar a ranar Lahadi cewa mutane kimanin 200 sun yi garkuwa da sojojin ne bisa umarnin ’yan tawayen FARC da suka addabi ƙasar. Ta bayyana cewa al’ummar ƙasar suna fuskantar matsin lamba daga ’yan tawayen masu ɗauke da makamai. Sanarwar ta ƙara da cewa an sace sojoji 31 a ranar Asabar, ragowar kuma ranar Lahadi. Erik Rodríguez ya bayyana cewa sace sojojin na da alaƙa da kama wani jagoran ’yan tawayen kungiyar EMC da sojojin suka yi. Ya ce a yayin da suke ƙoƙarin daukar sa a jirgi ne mutanen suka yi musu ƙawanya suka yi...
Allah Ya yi wa mahaifiyar Babban Editan Jaridar Daily Trust, Hamza Idris rasuwa. Kaninsa, mai suna Aminu Idris, ya bayyana cewa a safiyar Litinin ne Allah Ya yi wa mahaifiyar Babban Editan, Hajiya Rabi (Umma) cikawa bayan gajeruwar jinya a Jihar Kano. Za a gudanar da jana’izarta kamar yadda addinin Musulunci ya ranar a Layin Ɗorawar ’Yan Kifi da ke unguwar, Rijiyar Zaki, Kano. Daga nan za a kai ya maƙabartar Walid Mai Zage da ke Kofar Mazugal. Muna roƙon Allah Ya yi mata rahama, Ya ba wa dangi haƙurin rashin da kuma dangana.
Gwamnatin Amurka ta buƙaci ƙasar Sin da ta hana Iran rufe mashigar tekun Hormuz, ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin jigilar kayayyaki a duniya. Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya yi kiran ne bayan da kafar yada labarai ta Iran, Press TV ta ruwaito cewa majalisar dokokin ƙasar ta amince da shirin rufe mashigar. Duk wani cikas ga samar da man fetur zai yi tasiri mai tsanani ga tattalin arzikin duniya. Ƙasar Sin ce babbar mai sayen mai daga Iran kuma tana da kyakkyawar alaka da Tehran. Harin Iran: Amurka ta ɗebo ruwan dafa kanta Koriya ta Arewa za ta taimaka da gyara tashoshin nukiliyan Iran —Masani NAJERIYA A YAU: Matakan daƙile kisan matafiya a hanyoyin Najeriya Farashin man fetur...
Manyan Hafsoshin Tsaro na ƙasar Iran sun sha alwashin mayar wa Amurka da martani mai tsanani wanda sai ta yi da-na-sanin harin da kai wa Iran. Rundunar Tsaro ta Iran ta sanar da haka ne bayan wani zama da Babban Kwamandan Sojojin ƙasar, Amir Hatami, ya yi da wasu manyan kwamandojinsa. Harami ya shaida wa taron tsare-tsaren cewa ya zama tilas Amurka ta girbi abin da ya shuka a Iran a wannan karon. Ya bayyana cewa ko a baya, Iran ta saba koya wa Amurka darasi a duk lokacin da ta takali Iran. Koriya ta Arewa za ta taimaka da gyara tashoshin nukiliyan Iran —Masani NAJERIYA A YAU: Matakan daƙile kisan matafiya a hanyoyin Najeriya Babban Hafsan Tsaron Iran, Abdolrahim...
Rikicin Isra’ila da Iran ya kara dagula tabarbarewar harkokin man fetur da iskar gas a cikin fargabar barkewar rikicin Gabas ta Tsakiya wacce ta kasance jigo wajen hada-hadar man fetur da iskar gas. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Akwai yiwuwar ƙasar Koriya ta Arewa mai ƙarfin makaman nukiliya za ta taimaka wajen gyara tashoshin nukiliyan Iran da hare-haren Amurka suka lalata da kuma gina sababbin masana’antun ƙera makamai masu linzami masu gudun walƙilya a Iran. Wani masani mai suna Ankit Panda daga cibiyar zaman lafiya ta kasa da kasa ta da ke Amurka, ne ya bayyana hakan, baya Amurka ta kai hare-hare kan tashoshin nukiliya na ƙasar Iran. Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito Ankit Panda, yana bayyana cewa matakin zai kawo ƙarshen irin takura da ƙasashen Yamma ke yi wa Iran. Hakan na zuwa ne bayan da Ma’aikatar Harkokin Wajen Koriya ta Arewa ta yi tir da harin da Amurka ta kai a matsayin keta hurumin...
Batun sauya sheka da ke faruwa a cikin tsarin siyasar Nijeriya, Jega ya kira a hana sauya sheka ga wadanda aka zaba a bangaren zantarwa da kuma ‘yan majalisa. Ya kuma yi kira ga jami’an INEC a matakin tarayya, da na jihohi su shirya gudanar da zaben cike gurbi da zarar an samu labari game da sauya sheka. Ya ba da shawarar cewa ‘yan Nijeriya da ke zaune a kasashen waje su dunga kada kuri’a a zaben shugaban kasa, kuma ya yi kira a tsaurara dokoki kan kudaden kamfen ciki har samar da hukumar da za ta sa ido kan aiwatar da hukunci. Jega ya yi nadama da cewa daya daga cikin manyan kalubalen da Nijeriya take fuskanta shi ne,...
Idi ya kuma yi nazari kan matakin da bangaren kiwon dabbobin kasar yake, inda yawan Shanu suka kai miliyan 20.9, Tumaki miliyan 49.1, Awakai miliyan 88.2, Kajin gidan gona kuma miliyan 258.5. Kazalika, Maiha ya jaddada muhimmancin hadakar ta zuba hannun jari a fannin na kiwon dabbobin, wanda ya sanar da cewa; hakan zai taimaka matuka gaya wajen dakile yaduwar cututtukan da ke yi wa dabbobin illa. A nasa jawabin, Babban Shugaban Kamfanin Ricardo Lacerda ya bayyana cewa; kasar Brazil na shirin samar da wuraren kiwon dabbobi na zamani kimanin guda 200,000 a wasu daga cikin jihohin wannan kasa, musamman don kara samar da isasshen naman Shanu. Ya kara da cewa, kasar za kuma ta tabbatar da kokarin kara habaka...
Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari wasu ƙauyuka biyu da ke Ƙaramar Hukumar Kajuru a Jihar Kaduna. A yayin harin, wata matar aure ta rasu, yayin da wani manomi ya samu rauni. ’Yan bindiga sun sace babban alƙali a Bayelsa Dole a ɗauki mataki kan waɗanda suka kashe ’yan ɗaurin aure a Filato — Uba Sani Harin farko ya faru ne da misalin ƙarfe 2 na daren ranar Asabar, 21 ga watan Yuni, 2025, a ƙauyen Ungwan Sarkin Hausa da ke Rimau. Ana zargin maharan sun gudu da shanun da suka sato daga Ƙaramar Hukumar Kauru. A lokacin harin, sun kashe wata mata mai suna Misis Alheri Danzaria. Sun kuma sace wasu mutum biyu, amma daga...
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya ce Sin ta yi matukar Allah wadai da hare-haren da Amurka ta kai kasar Iran, tare da jefa bama-bamai kan cibiyoyin sarrafa nukiliyar kasar, dake karkashin kulawar hukumar lura da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ko IAEA a takaice. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana hakan ne a Lahadin nan, lokacin da yake tsokaci kan sanarwar da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar, cewa Amurka ta kaddamar da hare-hare kan cibiyoyi uku na nukiliyar kasar Iran. Jami’in ya ce matakin Amurka ya yi matukar keta makasudi, da ka’idojin MDD da dokokin kasa da kasa, ya kuma ruruta yanayin rashin tabbas da ake ciki a yankin Gabas ta...
Trump ya ce hare-haren da Amurka ta kai kan cibiyoyin nukiliyar Iran guda uku, lallai zai kara rura wutar rikici a ci gaba da yakin da ake yi tsakanin Iran da Isra’ila. Sai dai ministan harkokin wajen Iran Seyed Abbas Araghchi ya yi Allah wadai da harin da Amurka ta kai da cewa “abin takaici ne” sannan ya ce Iran ta tanadi “dukkan zabin kare ‘yancinta”, yana mai jaddada cewa Amurka za ta fuskanci “tsauraran sakamako”. Araghchi ya kara da cewa, Amurka ta keta kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya a matsayinta na mamba a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya. Bugu da kari, wani dan Majalisar kasar Iran, ya kara da cewa, “babu wani mummunan lahani...
’Yan tawayen Houthi na Yemen sun yi barazanar cewa Amurka za ta gamu da fushinsu muddin ta kai wa Iran hari a rikicin da ya ɓarke tsakaninta da Isra’ila. ’Yan tawayen sun ce za su kai wa jiragen ruwan Amurka hare-hare a Tekun Bahar Rum, idan har Washington ta yi kuskuren shiga yaƙin da Isra’ila ta ƙaddamar wa Iran, duk kuwa da yarjejeniya tsagaita wuta da aka cimma a baya-bayan nan. Mahaifin Rahama Sadau ya rasu Za mu sake gina kasuwar waya ta Farm Center — Abba A cikin wani faifan bidiyo, kakakin ’yan tawayen Houthi Yahya Saree ya bayyana cewa, muddin Amurka ta kai wa Iran hari ko kuma ta shiga cikin wannan rikici, mayankansu za su ƙaddamar da...
Hukumar kididdigar makamashi ta Amurka US Energy Information Administration (EIA) ta kiyasta cewa a farkon shekarar 2023 an yi dakon kusan ganga miliyan 20 na fetur a a kullum ta tekun. Wannan ke nufin ana kasuwancin kusan dala biliyan 600 na makamashi duk shekara ta tekun. Duk wani tsaiko a tekun zai iya jawo matsala a hada-hadar man fetur a duniya, wanda nan take za a iya gani ta hanyar tashin farashin man. Sai dai masana suna gargadin cewa daukar wannan matakin zai iya zafafa rikicin na Isra’ila da Iran. Wannan kuwa shi ne zai jawo wasu kasashen cikin rikicin, ciki har da Amurka, wadda take ta’allaka da man fetur daga kasashen Larabawa. Yaya girman mashigar Hormuz? Mashigar Hormuz na...
Ya nemi ‘yan jarida da su riƙa amfani da kafafen su wajen haska labarai da ke nuna sauye-sauyen da aka samu a hukumomi, yadda jama’a ke shiga cikin harkokin gwamnati, cigaban ababen more rayuwa da bunƙasar tattalin arziki, a matsayin wani ɓangare na rawar da kafafen ke takawa wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya. “Yayin da muke bikin shekaru 26 na ci gaba da mulkin dimokiraɗiyya a Nijeriya, dole ne kafafen yaɗa labarai su riƙa yaɗa labaran da ke bayyana nasarorin da dimokiraɗiyyar ƙasar nan ta samu, irin su gyaran hukumomi, gina ababen more rayuwa, shiga jama’a cikin harkokin gwamnati, da kuma cigaban tattalin arziki,” inji shi. Idris ya ƙara da cewa yayin da kafafen yaɗa labarai suke haska waɗannan nasarori ta hanya...
Mahaifin fitacciyar jarumar nan a masan’antar Kannywood, Rahama Sadau, ya riga mu gidan gaskiya. Jarumar ta wallafa wani saƙo a shafinta na Facebook tana mai cewa “Allah Ya yi wa mahaifina rasuwa…” sannan ta ɗora wani hoto da aka rubuta Inna lilLahi wa inna ilaiHi raji’un har sau uku a ƙarƙashin saƙon. Shi ma abokin sana’arta, Ali Nuhu, a saƙon da ya wallafa mai ɗauke da hoton Rahama tare da mahaifinta, ya sake tabbatar da rasuwar. Bayanai sun ce Alhaji Ibrahim Sadau ya rasu ne a garin Kaduna, inda nan gaba kaɗan za a yi masa jana’iza.
Firaministan kasar Singapore, Lawrence Wong, ya yi hira da wata wakiliyar CMG a kwanan baya, inda ya ce, yana da cikakken imani kan kasar Sin, saboda jama’ar kasar suna da kwarewar kirkire-kirkiren sabbin fasahohi da hikimar daidaita al’amura. A cewarsa, kokarin neman ci gaban harkoki da jajircewa na al’ummar Sin sun sa shi dakon ganin makomar kasar Sin mai cike da haske. Wong ya kara da cewa, ya taba cudanya da jami’an gwamnatin kasar Sin na matakai daban daban a shekarun baya, wadanda suka nuna kwarewar aiki da hazaka a fannin fahimtar ayyuka. Ban da haka, Wong ya ce, jami’an kasar Sin suna son sauraron ra’ayoyi na bangarori daban daban, da kokarin neman dabara mafi dacewa wajen daidaita matsala. A...
Gwamnan Kano Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi alƙawarin sake gina kasuwar waya ta Farm Center da ta yi gobara a kwanakin baya. Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Asabar. Amurka ta ƙaddamar da hare-hare kan Iran Za mu ci gaba da yi wa Isra’ila luguden wuta — Shugaban Iran Sanarwar ta ce bayan ziyarar gani da ido da gwamnan ya yi a ranar Juma’a, ya ɗauki matakin sake gina kasuwar tare da sabunta ta da zamanantar da ita, aikin da da ya ce “gwamnan zai kashe naira biliyan 2.” “Wannan yunƙuri ba kawai saboda gobarar ba ce, za mu yi amfani da wannan damar ne...
Amurka ta sanar da kaddamar da manyan hare-hare kan wasu muhimman cibiyoyin nukiliya a kasar Iran. Shugaban Amurka Donald Trump ya ce an kai hare-hare kan wasu cibiyoyin nukiliya guda uku na Iran, inda ya yi barazanar kai wasu hare-haren idan har Iran ba ta nemi yi sasanci ba. Za mu ci gaba da yi wa Isra’ila luguden wuta — Shugaban Iran Ɗan ƙunar baƙin wake ya kashe mutum 10 da bam a Borno A wata sanarwar da Trump ya fitar a jawabin da ya yi a talabijin yana ikirarin sun tarwatsa cibiyar, ya ce “hare-haren na soji babbar nasara ce.” Trump ya ce Amurka ta kai hare-haren ne a yankunan Natanz and Isfahan na cibiyar nukiliyar Fordo wurin da Iran...
Shugaban Ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya bayyana cewa ƙasarsa za ta ci gaba da mayar da martani kan hare-haren da Isra’ila ke kai mata. Ya bayyana haka ne a lokacin da yake magana da shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ta wayar tarho. Uba Sani ya yi jajen ’yan ɗaurin aure 12 da aka kashe a Filato Ɗan ƙunar baƙin wake ya kashe mutum 10 da bam a Borno Shugaba Pezeshkian ya ce Iran tana da niyyar yin haɗin gwiwa da sauran ƙasashe don amfani da makamashin nukiliya ta hanyar da ba ta da alaƙa da yaƙi, amma hakan ba yana nufin za su dakatar da inganta shirye-shiryensu na nukiliya gaba ɗaya ba. Ya ƙara da cewa hare-haren da Isra’ila ke kai...
Bayan karar, lauyan masu shigar da kara, Abdulhamid L. Tukur, ya kira Nnadikwu Izuchukwu Collins, wani jami’in binciken EFCC, domin ya gabatar da gaskiyar lamarin. Collins ya shaida wa kotun cewa wasu gungun masu zuba jari sun mika koke ga hukumar EFCC a ranar 21 ga Oktoba, 2022, kan FARM360 da MCBHADMOS Trans-Atlantic Trade Limited, bisa zargin cewa kamfanonin sun yaudare su wajen saka hannun jari a harkar noma da kasuwanci tare da “alkwarin mayar da hannun jari.” Ya bayyana cewa kungiyar ta hada baki ta zuba jarin Naira miliyan 93 tare da kamfanonin. “A yayin gudanar da bincike, an aika da wasikun ayyukan bincike zuwa Hukumar Kula da Canje-canje (SEC), Bankuna, Babban Bankin Nijeriya (CBN), da Hukumar Kula da...

Sin A Shirye Take Ta Yi Aiki Da Rasha Don Daukaka Amincewar Juna Ta Fuskar Siyasa Da Karfafa Muradun Juna
Mataimakin firaministan kasar Sin Ding Xuexiang, ya bayyana a jiya Jumma’a cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da kasar Rasha don ci gaba da daukaka amincewa da juna a fannin siyasa da karfafa dankon zumunci na cin moriyar juna. Ding ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin. Mataimakin firaministan ya ce, a yayin da ake fuskantar gagaruman sauye-sauye a yanayin duniya, ya kamata Sin da Rasha su kiyaye cikakken tsarin hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, da kare adalci a matakin kasa da kasa, da tallafa wa tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban na kungiyar WTO, tare da kiyaye gudanar da harkokin tsarin samar da kayayyaki cikin lumana, da zurfafa...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD ya yi kiran hada karfi da karfe a bangaren kasa da kasa don karfafa tattaunawa domin ganin an yayyafa ruwa ga rikicin Isra’ila da Iran. Wakilin, Fu Cong ya ce, yayin da rikicin yake-yaken sojoji na Isra’ila da Iran ya shiga kwana na takwas, abin bakin ciki ne ganin yadda lamarin yake janyo asarar rayukan fararen hula da dama tare da lalata kayayyakin aiki a dukkan bangarorin biyu. Ya kara da cewa, idan har wutar rikicin ta ci gaba da ruruwa, ba kawai bangarorin biyu ne za su tafka babbar asara ba, hatta sauran kasashen yankin lamarin zai yi musu mummunar illa. Fu Cong, ya fada wa wani taron gaggawa na kwamitin sulhun...
’Yan Najeriya mazauna ƙasar Isra’ila sun maƙale bayan ɓarkewar yaƙin Iran da Isra’ila. Sun nemi agajin Gwamnatin Tarayya game da kan halin ƙuncin da suka faɗa tun bayan ɓarkewar yaƙi. Cikin wani rahoto da Jaridar Punch ta wallafa, ’yan Najeriyar sun zargi gwamnati da rashin kai masu ɗauki yadda da ya kamata, inda suka ce tuni sauran ƙasashe suka fara kwashe ’yan ƙasarsu. Rahoton ya bayyana cewa ’yan Najeriyar sun fi yawa a birnin Ƙudus da Tel Aviv, inda Iran ta tsananta kai hare-hare. A halin yanzu, mazauna Isra’ilar sun bayyana cewa suna ɓoye ne a wurare da babu tabbas kuma rayuwarsu na cikin haɗari, a koyaushe komai na iya faruwa da su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wakilin ƙasar Iran ya isa birnin Santanbul na ƙasar Turkiyya domin halartar taron Ƙungiyar Haɗin kan Kasashen Musulmi (OIC) a ranar Asabar. Kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya ruwaito cewa, a yayin taron Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, zai gana da jami’an diflomasiyya na ƙasashen Larabawa don tattauna batun rikicin da ke ƙara ƙamari tsakanin ƙasarsa da Isra’ila. Kimanin jami’an diflomasiyya 40 ne ake sa ran za su halarci taron a daidai lokacin da Isra’ila da Iran ke ci gaba da musayar hare-haren makamai masu linzami. “Ministan harkokin wajen ya isa Istanbul a safiyar yau domin halartar taron ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan Musulunci,” in ji Tasnim. Yadda Iran ta lalata cibiyar kimiyya mafi muhimmanci a Isra’ila Najeriya...
Najeriya ta tura sojojinta 197 domin zuwa aikin tabbatar da tsaro da wanzar da zaman lafiya a kasar Gambia. Dakarun na Najeriya waɗanda tuni suka kammala samun horo, za sai yi aikin wanzar da zaman lafiya a Gambia be a ƙarƙashin rundunar Ƙungiyar Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS) da sunan (ECOMIG). Shugaban Ayyuka na Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya, Manjo-Janar Uwem Bassey, ya buƙaci sojojin da su kasance masu nuna nuna ƙwarewa da jarumta a yayin gudanar da ayyukansu a ƙasar Gambia. Ya yi wannan kira ne a jawabinsa a wurin bikin yaye sojojin a Barikin Sojoji na Jaji da ke Jihar Kaduna, kafin tafiyarsu. Yadda Iran ta lalata cibiyar kimiyya mafi muhimmanci a Isra’ila An sallami ƙarin ma’aikata 639...
Haka zalika, Gwamnatin Jihar Kebbi ba ta bayar da tallafi ga mahajjantanta 3,800 daga jihar ba. Amma a kasar Saudiyya, Gwamnan Nasir Idris ya amince da bayar da Riyal 200 ga kowane alhaji daga jihar. Gwamnatin Jihar Lagos ba ta tallafi ga mahajjatanta a wannan shekara ba, yayin da kowane daga cikin masu aikin hajji 1,315 daga jihar ya biya kimanin naira miliyan 9. Amma kuma, Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya ba kowane daga cikin mahajjatan kyauta Riyal 180, wanda ya kai naira 98,454,050 gaba dayansu. Gwamnatin Jihar Jigawa, wacce ma ba ta bayar da tallafi ga mahajjatanta ba a wannan shekarar, amma ta ba su kyautar Riyal 100 (kimanin naira 43,000) ga kowanne daga cikin mahajjatanta 930. Dukkanin alhazai Jihar...
Iran ta lalata cibiyar binciken kimiyya mafi muhimmanci a Isra’ila, wato cibiyar kimiyya ta Weizmann Institute of Science da ke birnin Tel Aviv. Cibiyar, wadda ke da alaƙa da binciken harkokin sojin Isra’ila, ta sanar da cewa harin da Iran ta kawo ɗin ya yi sanadiyar ɓarnar da ta kai kimanin Dala miliyan 500. Makaman Iran sun lalata gine-gine da dama a cibiyar, lamarin da ya sanya masu bincike faɗi-tashi don ceto samfurin bincike a cikin ɓaraguzan gini, a yayin da gobarar ke ci. Wani makami mai linzami ya tarwatsa wani gini mai ɗauke da ɗakunan gwaje-gwaje na zamani da dama, a yayin harin na ramuwar gayya, bayan da Isra’ila ta kashe masana kimiyyar nukiliya na Iran. 2027: Manyan ’Yan...
Iran ta lalata cibiyar binciken kimiyya mafi muhimmanci a Isra’ila, wato cibiyar kimiyya ta Weizmann Institute of Science da ke birnin Tel Aviv. Cibiyar, wadda ke da alaƙa da binciken harkokin sojin Isra’ila, ta sanar da cewa harin da Iran ta kawo ɗin ya yi sanadiyar ɓarnar da ta kai kimanin Dala miliyan 500. Makaman Iran sun lalata gine-gine da dama a cibiyar, lamarin da ya sanya masu bincike faɗi-tashi don ceto samfurin bincike a cikin ɓaraguzan gini, a yayin da gobarar ke ci. Wani makami mai linzami ya tarwatsa wani gini mai ɗauke da ɗakunan gwaje-gwaje na zamani da dama, a yayin harin na ramuwar gayya, bayan da Isra’ila ta kashe masana kimiyyar nukiliya na Iran. 2027: Manyan ’Yan...
Ƙasar Iran ta bayyana shirinta na shiga tattaunawar sasantawa “idan aka tsagaita hare-hare”, kamar yadda ministan harkokin wajen ƙasar ya bayyana bayan ganawa da takwarorinsa daga Faransa, Burtaniya da Jamus. Yayin da ministocin Turai suka nuna sha’awar ci gaba da tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran, Shugaban Amurka Donald Trump ya nuna shakku kan yiwuwar nasara, yana mai cewa Iran tana son magana kai tsaye da Amurka. Hakan ya faru ne a lokacin da rikici tsakanin Iran da Isra’ila ke ci gaba, inda Isra’ila ta kai hari kan wasu wurare a Tehran, kuma Iran ta mayar da martani da harin makamai. Fadar White House ta bayyana cewa Trump zai yanke shawara cikin makonni biyu kan ko Amurka za ta ɗauki mataki...
Iran ta lalata cibiyar binciken kimiyya mafi muhimmanci a Isra’ila, wato cibiyar kimiyya ta Weizmann Institute of Science da ke birnin Tel Aviv. Cibiyar, wadda ke da alaƙa da binciken harkokin sojin Isra’ila, ta sanar da cewa harin da Iran ta kawo ɗin ya yi sanadiyar ɓarnar da ta kai kimanin Dala miliyan 500. Makaman Iran sun lalata gine-gine da dama a cibiyar, lamarin da ya sanya masu bincike faɗi-tashi don ceto samfurin bincike a cikin ɓaraguzan gini, a yayin da gobarar ke ci. Wani makami mai linzami ya tarwatsa wani gini mai ɗauke da ɗakunan gwaje-gwaje na zamani da dama, a yayin harin na ramuwar gayya, bayan da Isra’ila ta kashe masana kimiyyar nukiliya na Iran. Makamin ya faɗo...

Duk Da Jihohin Nijeriya Sun Fara Biyan Mafi Ƙarancin Albashi Na 70,000, Ana Ci Gaba Da Fuskantar Matsin Rayuwa
Mai bai wa Gwamna Uba Sani shawara kan harkokin kwadago, Adamu Samaila ne ya shaida wa wakilinmu cewa; nan bad a jimawa ba gwamnati za ta karbi rahotan tantance ma’aikatan da kuma yadda za a daidata albashin nasu. Samaila ya kara da cewa, “A mako mai zuwa ne za mu gana da wanda yake kula da aikin tantancewar, domin samun sakamakon rahoton albashin ma’aikatan.” Zamfara: Ba A Aiwatar Da Biyan Dari Bisa Dari Ba A Jihar Zamfara, gwamnati ba ta aiwatar da fara biyan sabon mafi karancin albashin ga ma’aikatanta ba. Guda daga cikin manyan jami’an gwamnatin da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa wakilinmu cewa; mafi karancin albashin, zai fi mayar da hankali ne a kan ma’aikatan...
A cikin takardar, ƙungiyar ta bayyana cewa ta yanke shawarar kafa sabuwar jam’iyya maimakon haɗaka da wasu. Sun bayyana cewa sun zaɓi suna All Democratic Alliance (ADA) kuma taken jam’iyyar shi ne “Justice for All” wato “Adalci ga Kowa.” Sun kuma haɗa da adireshin babban ofishin jam’iyyar a cikin takardar. Sun gabatar da wasu muhimman takardu da suka haɗa da tambarin jam’iyya, tsarin kundin mulki, tutar jam’iyyar, da manufofinta. Tambarin jam’iyyar ya ƙunshi kayan hatsi irin su masara da launuka masu ma’ana. Kundin tsarin mulki kuma ya ƙunshi manufofi, tsari da dokokin jam’iyyar, bisa ga tsarin dokokin Najeriya da ƙa’idar dimokuraɗiyya ta duniya. Takardar ta ƙare da girmamawa, inda ta ke roƙon INEC da ta ɗauki mataki na gaba wajen...
Jagororin jam’iyyun adawa na Najeriya a ƙarƙashin ƙungiyar hadaƙa ta Nigeria National Coalition Group (NNCG) na neman yin rajistar All Democratic Alliance (ADA) domin ta zama sabuwar jam’iyyar da za su yi amfani da ita don tunkarar Jam’iyyar APC a zaɓen 2027. NNCG ta riga ta miƙa takardar neman rajistar jam’iyya ga Hukumar Zaɓe mai zaman kanta INEC a hukumance don babban zaɓe na gaba. Jami’an tsaro sun ƙwato makamai da kama mutane 398 a Kaduna Wani ya kashe mahaifiyarsa mai shekara 71 a Akwa Ibom Takardar wadda suka aika zuwa ga shugaban Hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu a ranar 19 ga watan Yuni, wanda shugaban ADA na ƙasa Cif Akin Ricketts da sakataren riƙo Abdullahi Musa Elayo ne suka...

Jakadan Sin Dake Amurka Ya Yi Jawabi A Gun Liyafar Da Kwamitin Kasa Mai Lura Da Kasuwancin Amurka Da Sin Ya Shirya
Kwamitin kasa mai lura da kasuwancin Amurka da Sin ko USCBC, ya gudanar da liyafar murna ta shekarar 2025, a ranar Laraba 18 ga wata a birnin Washington na Amurka, liyafar da jakadan kasar Sin a Amurka Xie Feng ya halarta tare da gabatar da jawabi. Cikin jawabin nasa jakada Xie ya ce cimma moriya da nasara tare, muhimman ginshikai ne na ci gaba mai dorewa na hadin-gwiwar Sin da Amurka ta fuskar raya tattalin arziki da kasuwanci, inda dukkan bangarorin biyu gami da duniya ke cin gajiya. A halin yanzu, habakar tattalin arzikin duniya na tafiyar hawainiya, kuma kara hada kai ita ce mafita daya tilo ta shawo kan hakan. Ya ce ci gaban kasar Sin zarafi ne ga...
Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta yanke wa wani mai suna Olukoye Olalekan hukuncin daurin shekaru 76 a kukuku saboda yada hotunan tsiraicin yara kanana da kuma aikata damfara. Alkalin kotun, Mai Shari’a Alexander Owoeye, ne ya yanke hukuncin ranar Alhamis, bayan ya samu mutumin da aikata laifukan da aka zarge shi da su. Rikicin Filato: An sake kashe mutum 17 a Mangu da Bokkos 2027: ‘Sai bayan babban taron APC Tinubu zai bayyana wanda za su yi takara tare’ An dai gurfanar da Olukoye ne a gaban kotun ana zarginsa da laifuka 18 da suke da alaka da yada hotunan tsiraicin yara kanana, damfara ta intanet, boye kudaden haram da kuma mallakar kadarori ta haramtacciyar hanya, wanda Hukumar...
Barcelona ta amince da yarjejeniyar ɗaukar ɗan wasan gaba na ƙungiyar Athletic Bilbao Nico Williams, amma kuma har yanzu akwai ƙalubalen da zasu fuskanta kafin ɗan wasan ya samu damar rattaba hannu a ƙungiyar ta Catalonia, ɗan wasan na ƙasar Sifaniya Williams, wanda ya zura ƙwallaye 31 a wasanni 167 da ya buga wa Bilbao, ya janyo hankalin ƙungiyoyin Arsenal da Bayern Munich a bana. Amma ɗan wasan mai shekaru 22 ya amince da kwantiragin shekaru shida a Barcelona, wanda hakan zai sa ya hadu da abokinsa kuma abokin wasansa a matakin ƙasa Lamine Yamal a Nou Camp, Williams ya buƙaci Yamal da ya taimaka masa wajen zuwa Barcelona, bayan kakar da ya yi a Bilbao inda ya taimaka musu...
Sanarwar ta ce: “Ma’aikatar Harkokin Waje na sanar da jama’a cewa, sakamakon rikicin da ke kara kamari tsakanin Isra’ila da Iran, Gwamnatin Tarayya tana shirin karshe na kwaso ‘yan Nijeriya da suka maƙale a wadannan kasashe. “Saboda haka, ana shawartar dukkanin ‘yan Nijeriya da abin ya shafa da su kiyaye matakan tsaro da kuma tuntubar ofishin jakadanci mafi kusa domin yin rijista da samun karin umarni.” Baya ga haka, Gwamnatin Tarayya ta sake kira da a dakatar da fada tsakanin Isra’ila da Iran, tare da bukatar bangarorin su rungumi tattaunawa, su mutunta dokokin kare hakkin dan Adam na duniya, kuma su bai wa rayuwar fararen hula muhimmanci. Ma’aikatar ta jaddada cewa Nijeriya na goyon bayan hanyoyin warware rikici ta hanyar...
Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ce ta bayyana hakan a rahoton ayyukan ta’addanci na watanni 12. Rahoton ya bayyana ayyukan ta’addanci miliyan 51.89 da suka shafi iyalai, satar waya ce mafi yawa a ciki da kaso 13.8 da rahoton satar waya miliyan 25. Rahoton ya nuna akwai layukan waya da ke aiki a wayoyin hannu miliyan 216.66 a Nijeriya haka ma kaso biyu bisa uku a kimanin shekaru 10 da masu yawan shekaru ne ke amfani da wayoyi. A yayin da duniya ke kara komawa a duniyar fasaha, wayoyin hannu na yi wa al’umma amfani fiye da sadarwa domin suna amfani a matsayin wajen neman ilimi, kasuwanci, karamin banki da biyan bukatun yau da kullum, kuma hanyar rayuwar al’umma da...
Shugaban Isra’ila, Isaac Herzog, ya bayyana cewa ƙasarsa za ta iya samun nasara a yaƙin da take yi da Iran ko da kuwa Amurka ba ta shigar mata ba. Sai dai Herzog ya shaida wa ABC News cewa kawar da barazanar nukiliyar Iran yana da muhimmanci ga “duniya mai ’yanci”, ciki har da Amurka. Nan da mako biyu za mu yanke shawara kan shigar wa Isra’ila yaƙi — Trump Muna shawartar Trump kada ya shiga yaƙin Iran da Isra’ila — Birtaniya Da yake amsa tambayar ko me zai ce dangane da yiwuwar shigar wa ƙasarsa yaƙin da take yi da Iran da Shugaba Donald Trump ya yi iƙirari, Herzog ya ce “ina da cikakkiyar yarda a kan duk wani hukunci...
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce sai nan da mako biyu zai yanke shawara kan ko zai shigar wa Isra’ila yaƙin da take yi da Iran ko kuma akasin haka. A wata sanarwa da sakatariyar yaɗa labaran fadar gwamnatin Amurka, Karoline Leavitt ta karanto, Trump ya ce akwai yiwuwar a zauna a teburin sulhu. Waadin yanke shawarar da Trump ya bayar na zuwa ne bayan kwanaki ana rade-radin cewa Amurka za ta shigar wa Isra’ila yaƙin da ta ƙaddamar don ganin ta hana Iran mallakar makaman nukiliya. Trump dai ya shafe makonni yana bibiyar hanyar diflomasiyya don cimma yarjejeniyar nukiliya da Iran wadda ya soma tattaunawa da ita tun a wa’adinsa na farko a shekarar 2018. Sai dai duk da...
A ranar 27 ga Mayu, 2025, Indomie Arewa ta ƙara ɗanɗano da armashi a cikin tasowar yara. Babban kamfanin abincin tana alfaharin ƙaddamar da Indomie AI Career Generator, wata dandalin zamani irinsa na farkon da aka ƙirƙira don nuna irin baiwar da yara ke da ita ta hanyar ba su damar ganin makomarsu ta wata sabuwar hanya. Indomie tun da dadewa tana da kaimin ciyarwa da abincin dake gina jiki da kuma cincidar Mafarkin kowanne yaro. Wannan dandalin na Indomie AI Career Generator ya tunkari wannan manufa, na taimakawa yara su fahimci ƙarfin gwiwarsu, su yi manyan mafarkai, kuma su san cewa makomarsu tana gab da su. “Indomie ta tallafa wa yarada dama wajen girma, koyo, da zama ababen Alfahari. Tare...
Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya buƙaci Donald Trump kada ya ɗauki matakin soji kan Iran, yana mai kiran da a biyo wa lamarin ta hanyar lalama. Mista Starmer ya ce akwai “mummunan hatsarin bazuwar” yaƙin, inda ya yi kira ga duka ɓangarorin sun rungumi sulhu. Ba zai yiwu mu bar Khamenei a raye ba — Isra’ila Hisbah ta lalata katan 243 na barasa da wasu kayan maye a Yobe Ya ƙara da cewa a baya an samu “jerin tattauna masu yawa da Amurka, kuma ina ganin wannan ita ce hanyar warware matsalar.” Kalaman nasa na zuwa ne yayin da sakataren harkokin wajensa, David Lammy ke shirin ganawa da takwaransa na Amurka, Marco Rubio kan yadda za a taƙaita bazuwar yaƙin....
Ministan Tsaron Isra’ila, Israel Katz ya ce ba zai yiwu su bar jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei a raye ba. Israel Katz ya yi barazana ga Ayatollah yana mai cewa ya zama tilas ya ɗauki alhakin hare-hare da makamai masu linzami da Iran ta yi a kan wata cibiyar lafiya da ke kusa da Tel Aviv. Hisbah ta lalata katan 243 na barasa da wasu kayan maye a Yobe Guguwar ruwan sama ta yi ɓarna a Kwalejin Kimiyya da Fasaha a Kogi Kafin harin an yi ƙoƙari kwashe marasa lafiya da dama, saboda a ceto rayukansu. Tuni dai Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ziyarci Cibiyar Lafiya ta Soroka da ke Beersheba da harin makami mai linzami na Iran ya...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta tabbatar da aniyarta na dawo da dukkan Alhazan Najeriya da ke Saudiyya zuwa ranar 28 ga watan Yunin, 2025. Rahotanni daga Hukumar NAHCON da ke birnin Makkah na cewa, alhazan Najeriya 6,528 ne suka dawo Najeriya, yayin da Kamfanin Max Air ya kammala jigilar Alhazai jirgi na 16 a ranar Talata. Kotu ta ba da belin Natasha kan N50m kan zargin bata sunan Akpabio Ba Atiku kaɗai ba ne matsalar PDP — Gwamna Lawal Wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktan yaɗa labarai Fatima Sanda Usara ta fitar ta ce NAHCON tare da hukumar jin daɗin alhazai ta jiha, da kuma masu jigilar jiragen sama na shekarar 2025 suna yin duk abin da za su iya...
Wata kotun shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu a Jihar Kano, ta yanke wa wasu mutum bakwai hukuncin ɗauri, bayan da suka ji wa wani ɗan sanda rauni yayin da ake ƙoƙarin cafke su. Al’ummar unguwannin Tudun Maliki da Sheka ne suka kai rahoton mutanen, inda suka zarge su da sayar da miyagun ƙwayoyi. ’Yan bindiga sun kashe manoma 24 a Katsina Yadda manoma suka yi addu’ar roƙon ruwa a Zamfara A kotun, an gurfanar da su kan laifukan haɗa baki domin tayar da hankali, jikkata mutum, hana ‘yan sanda yin aikinsu yadda ya dace, da kuma ɓoye wanda ake zargi. Lauyan gwamnati, Barrista Aliya Ibrahim Aminu ce, ta karanta musu tuhumar a gaban kotu. Ɗaya daga cikinsu ya musanta...
Ayatollah ya yi gargaɗi cewa, idan Amurka ta shiga cikin rikicin kai-tsaye don taimaka wa Isra’ila, wannan zai jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin matsala babba. Rikicin da ke tsakanin Iran da Isra’ila ya shafe kwanaki shida yanzu, inda mutane da dama suka mutu a ɓangarori biyun, baya ga asarar dukiyoyi da gine-gine. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi kan kada a kuskura a shiga tsakanin yaƙin da Iran da Isra’ila ke fafatawa ta hanyar amfani da ƙarfin soji. Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya yi gargadi kan duk wani “shiga tsakani na soji”, a yankin Gabas ta Tsakiya, inda manyan abokan gaba Isra’ila da Iran ke musayar wuta a rana ta shida. Sojojin Nijeriya sun kashe gomman ’yan ta’adda a Tafkin Chadi Nijeriya za ta fara fitar ta tataccen mai zuwa Asia — Matatar Dangote Ita ma ƙungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta bukaci bangarorin biyu, da su kare fararen hula yayin da adadin mace-mace da jikkata ke ci gaba da karuwa. Babbar sakatariyar ƙungiyar ta kasa da kasa, Agnes...
An cimma jerin yarjejeniyoyin hadin gwiwa a taron koli na biyu na kasar Sin da tsakiyar Asiya da aka gudanar a birnin Astana na kasar Kazakhstan a ranar 17 ga watan nan agogon kasar. Shugabannin kasashen biyar na tsakiyar Asiya sun yaba wa kasar Sin a matsayin babbar abokiyar hadin gwiwa kuma kawa ta gaskiya da kasashen yankin tsakiyar Asiya za su iya amincewa da ita har abada. Ana iya sa ran cewa, hadin gwiwar da Sin za ta yi da tsakiyar Asiya ba wai kawai za ta inganta manyan ayyukan hadin gwiwa ba ne, har ma za ta kara karfafa kokarin “neman sabbin abubuwa masu dadi” da “sabbin kirkire-kirkire”, da sa kaimi ga kasashen shida wajen cimma zamanantarwa tare...
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ya kai ziyara Jihar Benuwe domin jajanta wa mutanen jihar bisa hare-haren da suka faru a wasu ƙauyuka kwanan nan. Ya je ne domin nuna alhininsa ga waɗanda abin ya shafa da kuma tattaunawa da shugabanni don nemo mafita mai ɗorewa. Mun shirya yin sulhu da ’yan bindiga — Gwamnatin Sakkwato Sojoji sun raunata shugaban ISWAP na Najeriya, Albarnawi A yayin ziyarar tasa ta yini guda, Shugaba Tinubu ya fara ne da ziyartar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Benuwe, inda ta duba waɗanda suka jikkata. Shugaban ya shirya ganawa da iyalan waɗanda aka kashe, da waɗanda suka rasa muhallansu, da kuma shugabannin al’umma. Hakazalika, Shugaba Tinubu zai gana da manyan masu ruwa da tsaki s jihar,...
A ci gaba da yakin da suke yi da ’yan ta’adda, sojojin Najeriya sun samu nasarar jikkata jagoran kungiyar ISWAP, Abu Moussab Albarnawi a dajin Sambisa. Bayanai sun nuna sojoji sun sami nasarar ce bayan wani gagarumin harin da suka kai ta sama a wani sabon sansani na ’yan ta’addan da ke dajin Baikee a yankin Sambisa a Jihar Borno. Dakarun rundunar da ke karkashin Operation KALACHEN WUTA, wanda bangare ne na rundunar sojojin saman Najeriya da ke karkashin rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) ne suka kai harin. Litar fetur za ta iya komawa N1,000 a Najeriya saboda yakin Isra’ila-Iran – Masana Majalisa ta aike wa Tinubu kudurorin dokar haraji domin ya rattaba musu hannu Majiyoyin sojojin Najeriya da ke...
Masana sun yi gargadin cewa yakin da ake gwabzawa a tsakanin Isra’ila da Iran zai iya shafar farashin man fetur a duniya kuma hakan zai iya yin illa ga tattalin arzikin Najeriya. Masanan na cibiyar Commercio Partners da ke Legas sun bayyana fargabar ce a cikin wani rahoto da cibiyar ta fitar mai taken: “Farashin kayayyaki ya sauka a Najeriya a watan Mayu, amma akwai matsala a nan gaba” wanda aka wallafa shi ranar 16 ga watan Yunin 2025. A cewar rahoton, rikicin da ake fama da shi a yankin Gabas ta Tsakiya zai iya rage yawan man fetur din da ake samarwa a duniya wanda kuma zai kai ga tashin farashinsa a kasuwanni. Ma’aikatan Kwalejin Ilimi ta jihar Kaduna za...
Sanarwar ta ƙara da cewa ana aiki tare da hukumomin cikin gida da na ƙasa da ƙasa domin ganin an gudanar da aikin kwasar cikin tsaro. Sanarwar ta ce: “Ma’aikatar Harkokin Waje na sanar da jama’a cewa, sakamakon rikicin da ke ƙara ƙamari tsakanin Isra’ila da Iran, Gwamnatin Tarayya tana shirin ƙarshe na kwaso ‘yan Nijeriya da suka maƙale a waɗannan ƙasashe. “Saboda haka, ana shawartar dukkanin ‘yan Nijeriya da abin ya shafa da su kiyaye matakan tsaro da kuma tuntuɓar ofishin jakadanci mafi kusa domin yin rijista da samun ƙarin umarni.” Baya ga haka, Gwamnatin Tarayya ta sake kira da a dakatar da faɗa tsakanin Isra’ila da Iran, tare da buƙatar ɓangarorin su rungumi tattaunawa, su mutunta dokokin kare...
Majalisar Dokoki ta kasa ta ce ta aike wa Shugaban Kasa Bola Tinubu kudurorin dokar harajin da ta amince da su a hukumance domin ya rattaba musu hannu su zama doka. Shugaban Kwamitin Yada Labarai na Majalisar Dattawa, Sanata Yemi Adaramodu (APC, Ekiti) ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai ranar Talata a Abuja. A bara ne dai Tinubu ya aike wa majalisar kudurorin domin su yi nazarinsu sannan su amince da su a matsayin doka. Ambaliyar Mokwa: Har yanzu muna neman mutum 700 – Gwamnatin Neja DAGA LARABA: Ko Kare Kai Daga Harin ‘Yan Ta’adda Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro? Kudurorin dai a baya sun yamutsa hazo sosai a zaurukan majalisun da ma a fadin kasa, kafin...

Majalisar Wakilai Ta Fara Binciken Yadda Aka Raba Naira Tiriliyan 1.12 Kan Shirin Lamuni Ga Manoma Da Masana’antu
Kwamitin Majalisar wakilai mai kula da samar da abinci mai gina jiki da tattalinsa ya fara bincike kan yadda aka kashe Naira Tiriliyan 1.12 na shirin Ba da Lamuni na Anchors. Har ila yau, binciken ya shafi yadda cibiyar NIRSAL’s ta raba Naira biliyan 215 na ayyukan noma da kuma yadda Bankin Masana’antu (BOI) shi ma ya raba Naira biliyan 3 ga kananan manoma 22, 120 ta shirin AVCF. An Gudanar Da Bikin Mu’amalar Jama’a Da Al’adu A Tsakanin Sin Da Tsakiyar Asiya A Astana Sin Ta Fara Aiwatar Da Matakin Soke Haraji Kan Kayayyakin Kasashen Afirka 53 Da yake jawabi a zaman binciken, shugaban kwamitin Hon. Chike Okafor, ya bayyana damuwarsa cewa, a cikin cibiyoyin hada-hadar kudi 24 da...
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa ya san inda jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei yake “boye”, kuma ya yi gargadi cewa Washington na iya halaka shi, amma za su dakata a halin yanzu. Wannan na zuwa ne yayin da Trump din ya gargadi Iran kan da kada ta kai harin makamai masu linzami kan fararen hula ko kuma sojojin Amurka, yana mai cewa hakurinsu na karewa. Iran ta kai hari hedikwatar hukumar leƙen asirin Isra’ila Rikicin ƙabilanci ya yi ajalin mutum 20 a Chadi A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Truth mintuna kadan bayan wannan sako, Trump ya rubuta cewar Iran din ta mika wuya ba tare da wani sharadi ba kawai. Rahotanni a...
Kafofin yaɗa labarai na cikin gida a Iran sun yi iƙirarin cewa ƙasar ta kai hari kan hedikwatar hukumar leƙen asiri ta ƙasar Isra’ila (Mossad). Kamfanin dillancin labaran Iran (TASNIM) ya ruwaito cewa rundumar juyin juya hali na Iran (IRGC) ce ta kai harin a hedikwatar Mossad da ke Herzliya. Kamfanin ya wallafa wasu jerin hotuna da ya ce suna nuna yadda hedikwatar ta Mossad ke ci da wutan ne bayan harin makamai masu linzami ne da Iran ta kai mata. Kafar yaɗa labarai ta Tehran Times ta ruwaito cewa hare-haren na IRGC sun ƙona wani ɓangare na cibiyar Aman, wanda wani ɓangare ne na ginin hukumar leƙen asirin asirin sojin Isra’ila ta Aman, da ke Glilot. An garzaya da...
Akalla mutane 20 sun mutu yayin da wasu 16 suka jikkata a wani rikicin ƙabilanci da ya auku a wani lardi na gabashin kasar Chadi. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar sadarwa ta ƙasar ta fitar, ta ce fadan ya barke ne daga ranar 10 zuwa 14 ga watan Yuni a yankin Molou na lardin Ouaddai da ke gabashin kasar. An garzaya da ’yan Isra’ila 154 asibiti bayan harin Iran Tankokin Isra’ila sun kashe mutum 51 a wurin karbar abinci a Gaza Wata majiya ta ce rikicin ya samo asali ne bayan da matasan Zaghawa biyu dauke da makamai suka sace babur na wani dan kabilar Ouaddai a ranar Talata, lamarin da ya haddasa kazamin rikici. Bayanai sun ce rikicin...
Isra’ila ta tabbatar cewa an garzaya da ’yan ƙasarta aƙalla 154 asibiti bayan sabbin hare-haren ramuwar gayya da Iran ta kawo mata. Ma’aikatar lafiyar Isra’ila ta ce aƙalla mutum huɗu daga cikin waɗanda aka kai asibitin suna cikin halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai, wasu biyar kuma na samun kulawa ta musamman saboda tsananin tashin hankali. Alkaluman da ma’aikatar ta fitar sun nuna cewa mutum 130 daga cikin majinyatan sun samu raunuka marasa tsanani a sakamakon hare-haren. Wannnan na zuwa ne a yayin da Iran ta ci gaba luguden rokoki a matsayin ramuwar gayya a sassan Isra’ila a a ranar Talata. Isra’ila ta ce Iran ta lashe mata mutane akalla 24. A ɗaya ɓangaren kuma Iran cewa harin tsokana da Isra’ila ta kai mata...
Tankokin yaƙin Isra’ila sun i kashe kimanin mutun 51 a yankin Khan Younis da ke Zirin Gaza, a yayin da mutanen suke tsaka da karbar abincin tallafi. Jami’ain lafiya sun sun ce mutum 51 sun mutu, wasu 200 sun samu raunuka — 20 daga cikinsu suna cikin halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai — bayan harin. Sun bayyana harin a matsayin daya daga cikin mafiya muni da sojojin Isra’ila suka kai a baya-bayan nan a yayain da Falasdinawa ke kokarin samun abinci domin su rayu. Bidiyon lamarin da suka karade kafofin sada zumunta sun nuna wasu gomman gawarwaki da ake zargin tankokin yakin Isra’ila sun mutsuttsuke a kan titi a Khan Younis. Shaidu sun bayyana cewa sai da sojojin Isra’ilan suka sa mutanen suka...
Hukumomin Isra’ila na ci gaba da bincike tare da ɗaukar matakan gaggawa domin daƙile tasirin harin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump ya ce yana neman ganin an kawo karshen rikicin nukiliyar ƙasar Iran gaba ɗaya, a yayin da aka shiga kwana na biyar a yaƙin da ya ɓarke tsakanin Iran da Isra’ila. Trump ya bayyana shirinsa na tura manyan jami’an ƙasarsa zuwa birnin Tehran domin tattaunawa da hukumomin Iran a game da lamarin. Ya bayyana haka ne a yayin da yake hawa jirgi domin barin ƙasar Kanada, inda ya halarci taron ƙasashen G7. A yayin taron, shugabannin ƙasahen sun bayyana Iran a matsayin barazana, da bai kamata a bari ta mallaki makaman nukiliya ba. A ɗaya bangaren kuma sun bayyana ’yancin Isra’ila na kare kanta. Matatar man Isra’ila ta daina aiki bayan harin Iran Sarki ya...
Hukumar gudanarwar matatar man ƙasar Isra’ila da ke yankin Haifa ta sanar cewa matatar ta dakatar da ayyukanta ɗungurungum bayan harin da Iran ta kai mata. Kamfanin Bazan Group da ke kula da matatar ya ce harin na Iran ya tilasta musu tsayar da gaba ɗaya — a yayin da sabon rikicin na yankin Gabas ta Tsakiya ke ɗaukar zafi tsakanin ƙasashen biyu da suka jima suna yi wa juna kallon hadarin kaji. Bazan Group ya bayyana harin rokokin Iran ya lalata tashar wutar lantarki da matatar ke amfani da shi. Harin na Iran ya kuma halaka ma’aikata uku a matatar ta Haifa, kamar yadda hukumomin Isra’ila suka sanar. Wannan na faruwa a ci gaba hare-haren ramuwar gayya da makamai...
Ƴansandan jihar Kogi sun tabbatar da sace wani basarake mai suna Samuel Ajayi Bello yayin da yake aikin gona a gidan gonarsa na Ponyan da ke kan titin Ponyan-Irele, a ƙaramar hukumar Yagba ta Gabas. Mai magana da yawun ‘yansandan jihar, SP William Aya, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da ƙarfe 10 na safe a ranar Litinin. Ya kuma ce Kwamishinan ‘yansandan jihar ya tura rundunar ta musamman don taimakawa wajen gudanar da bincike da kuma ceto wanda aka sace. Ministocin Harkokin Wajen Sin Da Afirka Sun Yi Alkawarin Karfafa Alaka Ƴan Bindiga Sun Kai Farmaki Kwara, Sun Kashe Mutum 1, Sun Ƙona Gidaje Shugaban ƙungiyar ci gaban yankin Ponyan, Hon. Banjo Fabola, ya tabbatar da cewa an...
Wani yaro mai kimanin shekaru goma a duniya ya harbe mahaifinsa wanda jami’in ɗan sanda ne mai mukamin sufeto a Jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Nijeriya. Haka kuma, wakilinmu ya ruwaito cewa yaron ya harbi wani yayansa da bindigar mahaifin nasa ta aiki kirar AK-47. Kashe jagoran addini na Iran zai kawo ƙarshen yaƙi — Netanyahu Mun bankaɗo sabuwar dabarar ’yan siyasa ta satar kuɗi — EFCC Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Anambra, Tochukwu Ikenga ya raba wa manema labarai a ranar Litinin. Kakakin ya ce an gaggauta kai jamin asibiti domin a ceto rayuwarsa amma likitoci suka tabbatar da cewa rai ya riga ya yi halinsa....
Wani yaro mai kimanin shekaru goma a duniya ya harbe mahaifinsa wanda jami’in ɗan sanda ne mai mukamin sufeto a Jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Nijeriya. Haka kuma, wakilinmu ya ruwaito cewa yaron ya harbi wani yayansa da bindigar mahaifin nasa ta aiki kirar AK-47. Kashe jagoran addini na Iran zai kawo ƙarshen yaƙi — Netanyahu Mun bankaɗo sabuwar dabarar ’yan siyasa ta satar kuɗi — EFCC Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Anambra, Tochukwu Ikenga ya raba wa manema labarai a ranar Litinin. Kakakin ya ce an gaggauta kai jamin asibiti domin a ceto rayuwarsa amma likitoci suka tabbatar da cewa rai ya riga ya yi halinsa....
Ƴansandan jihar Kogi sun tabbatar da sace wani basarake mai suna Samuel Ajayi Bello yayin da yake aikin gona a gidan gonarsa na Ponyan da ke kan titin Ponyan-Irele, a ƙaramar hukumar Yagba ta Gabas. Mai magana da yawun ‘yansandan jihar, SP William Aya, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da ƙarfe 10 na safe a ranar Litinin. Ya kuma ce Kwamishinan ‘yansandan jihar ya tura rundunar ta musamman don taimakawa wajen gudanar da bincike da kuma ceto wanda aka sace. Ministocin Harkokin Wajen Sin Da Afirka Sun Yi Alkawarin Karfafa Alaka Ƴan Bindiga Sun Kai Farmaki Kwara, Sun Kashe Mutum 1, Sun Ƙona Gidaje Shugaban ƙungiyar ci gaban yankin Ponyan, Hon. Banjo Fabola, ya tabbatar da cewa an...
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce duk wani shiri na kashe jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei ba zai rura wutar rikicin da ake yi yanzu ba, hasali zai ma kawo ƙarshen rikicin ne. A wata hira ta tsawon minti 20 da tashar talabijin ta ABC ta Amurka ta yi da shi, Netanyahu ya kare matakin farmakin da ƙasarsa ta kai wa Iran, inda ya kwatanta jagoran addini Khamenei a matsayin wani sabon Hitler na wannan zamani. Mun bankaɗo sabuwar dabarar ’yan sisaya ta satar kuɗi — EFCC Tinubu zai je jaje bayan kisan fiye da mutum 100 a Benuwe A yayin hirar, duk wata tambaya da aka yi masa game da ko Shugaban Amurka Donald Trump ya sahale...
Za a gudanar da taron jin ra’ayin jama’a a lokacin ziyarar shugaban ƙasa. Tun da farko, Tinubu ya yi Allah-wadai da rikicin da ke faruwa a Benuwe, inda ya yi kira da a zauna lafiya. Haka kuma, ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu da dukiyoyinsu a sanadin rikicin. Tinubu ya shirya kai ziyara Jihar Kaduna a ranar Laraba domin ƙaddamar da ayyukan gwamnatin jihar, amma yanzu ya ɗage ziyarar zuwa ranar Alhamis, 19 ga watan Yuni, 2025. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
Yau Litinin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Guo Jiakun ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum. Game da halin da ake ciki yanzu a yankin Gabas ta Tsakiya, Guo Jiakun ya ce, ministan wajen Sin Wang Yi ya riga ya tattauna ta waya tare da takwarorinsa na Iran da Isra’ila, inda ya yi kira ga bangarorin biyu su warware rikicin ta hanyar tattaunawa. Ya ce ya kamata bangarorin biyu su dauki matakai nan da nan don hana ruruwar wutar rikicin. Kana Sin za ta ci gaba da yin mu’ammala da bangarorin da abin ya shafa, ta yadda za ta ba da gudunmawa wajen yayyafa ruwa ga rikicin. Game da taron koli na Sin da kasashen yankin tsakiyar...
Iran ta ce ta aiwatar da hukuncin kisa ta hanyar rataya ga mutumin da aka kama yana yi wa Isra’ila leƙen asiri. Mahukunta a bangaren shari’ar sun ce an kama Esmail Fekri a shekarar 2023 yana ƙoƙarin miƙa wa Isra’ila bayanan sirri ne don samun kuɗi. KADSEMA da IOM sun fara tantance ɓarnar da ambaliya ta yi a Kaduna Sabon harin Iran ya hallaka mana mutum 8 – Isra’ila Wannan ne karo na uku a baya-baya nan da Iran ke aiwatar da hukuncin kisa saboda zargin leƙen asiri ga Isra’ila. A ranar Lahadi, Isra’ila ta ce ta kama wasu ’yan ƙasa biyu da ake zargin suna aiki da hukumar leƙen asirin Iran. Babban alƙalin Iran, Gholamhossein Mohseni Ejei, ya bayyana...
FCCPC ta lura cewa, waɗannan sassan dokar suna kare ‘yan Nijeriya daga “rashin adalci, rashin sanin ya kamata, daga kwastomominsu.” A wata wasika mai ɗauke da kwanan watan 13 ga watan Yuni 2025, FCCPC ta yi amfani da sashe na 32 da na 33 na FCCPA, inda ta bukaci kamfanin da ya gurfana a gaban hukumar a hedikwatar ta Abuja a ranar Litinin 23 ga watan Yuni 2025. Hukumar ta yi gargaɗin cewa, rashin bin wannan umarni na iya haifar da tsauraran takunkumai da suka hada da tara da ɗauri kamar yadda aka bayyana a sashe na 33(3) na dokar. Har yanzu Air Peace ba ta amsa sammacin ba har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto. ...

Shugabannin Duniya Za Su Gudanar Da Taron Sanya Hannun Jarin Bunƙasa Ƙudurorin Muradun Ƙarni A Sifaniya
Shirin dai zai kunshi abubuwa masu mahimmanci guda uku; Na farko, Taron Sevilla zai taimaka wajen zaburar da shigowar tallafi zuwa ga kasashen da suka fi bukatarsa. Na biyu, dole ne kasashe su kasance a kan kujerar tattara albarkatun cikin gida ta hanyar karfafa samar da kudaden shiga da magance rashin biyan haraji, hadin gwiwar kasa da kasa. Wannan zai samar da albarkatun da ake bukata sosai domin bayar da fifikon kashe kudade a wuraren da ke da tasiri mafi girma kamar ilimi, kiwon lafiya, ayyuka, kariya ga zamantakewa, samar da abinci, da makamashi irin na zamani. A bangare daya kuma, akwai bukatar bankunan ci gaban kasa, da na shiyya-shiyya da kuma bankunan raya kasa-da-kasa, su hada hannu domin saka...
Dan wasan mai shekaru 27 ya zura kwallaye 20 sannan ya taimaka wajen zura bakwai daga wasanni 40 da ya buga a duk wasannin da ya buga a kakar wasan data gabata, Lookman ya ci kwallaye 17 kuma ya taimaka wajen zura 10 a kakar wasanni ta shekarar 2023/24. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Dakarun kare juyin juya halin Musulunci sun kai hare-hare har sau uku kan cibiyoyin leken asirin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Ma’aikatar hulda da jama’a ta dakarun kare juyin juya halin musulunci ta Iran ta fitar da sanarwa inda ta bayyana harin da aka kai kan cibiyoyin leken asirin haramtacciyar kasar Isra’ila a mataki na uku na hare-haren daukan fansa na “Alkawarin Gaskiya na Uku”. Sanarwar ta kuma bayyana cewa: Hare-haren wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya suke kaiwa kan kasar Iran da jijjifin safiyar yau sun nufi yankunan gidajen jama’a ne. Sannan maharan yahudawan sahayoniyyan sun kashe jami’an leken asirin dakarun kare juyin juya hali uku, shahid Mohammad Kazimi, Hassan Mohaqeq, da Mohsin Baqiri. A ci gaba da mayar...

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Sojojin Isra’ila Sun Kashe Kananan Yara Masu Yawa A Iran
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Yahudawan sahayoniyya sun kashe adadi mai yawa na yaran Iran a cikin ta’addancin da suke yi Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya bayyana cewa: Gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta kashe kananan yara masu yawa na Iran a cikin wannan ta’asa da take gudanarwa kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran. A cikin wani sako da Ismail Baqa’i ya rubuta a ranar Lahadin da ta gabata ya bayyana cewa: “Gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta kashe adadi mai yawa na yara Iraniyawa tare da kai hari kan asibitin yara a tsawon kwanaki uku na hare-haren soji kan Iran. Kamar yadda Ya’ir Golan, tsohon mataimakin hafsan hafsoshin sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila ya amince da cewa: Kashe...
Iran ta zartar da hukuncin kisa kan jami’an leken asirin Hukumar leken asirin yahudawan sahayoniyya “Mossad” a safiyar yau Litinin A wani gagarumin farmaki da aka kai kan cibiyar leken asirin yahudawan sahayoniyya a cikin kasar Iran, an kama wani mutum tare da yi masa shari’a bisa zargin hadin kai da hukumar leken asirin ‘yan sahayoniyya, bisa tuhumarsa a matsayin maci amana da gudanar da barna a kan doron kasa. An zartar da hukuncin ne bayan kammala shari’ar laifuka da kuma tabbatar da hukuncin da kotun koli ta yanke. A cikin wani hadadden aikin fasaha da leken asiri a cikin kasar, an kama Isma’il Fakri a watan Disamban shekara ta 2023 yayin da yake da alaka da hukumar leken asiri...
Jami’an tsaron kan iyakokin Iran sun harbo jiragen saman yaki marasa matuki ciki guda 44 a cikin sa’o’i 48 da suka gabata Kwamandan rundunar tsaron kan iyakokin kasar Iran Birgediya Janar Ahmad Ali Goudarzi ya bayyana cewa: An harbo jiragen sama marasa matuka ciki guda 44 da kananan jiragen saman yakin gwamnatin ‘yan sahayoniyya tare da lalata su a wasu kan iyakokin kasar. Birgediya Janar Goudarzi ya bayyana a ranar Lahadi cewa: “Bayan harin da gwamnatin ‘yan Sahayoniyya ta kaddamar kan Iran, a cikin sa’o’i 48 da suka gabata, jami’an tsaron Iran sunsamu nasarar kakkabo jiragen sama marasa matuka ciki na gwamnatin ‘yan sahayoniyya guda 44 da kananan jiragen sama na wannan muguwar gwamnati, sakamakon Sanya ido kan shige da...
Gwamnatin Amurka ta rufe Ofishin Jakadancinta da ke haramtacciyar kasar Isra’ila Jakadan Amurka a haramtacciyar kasar Isra’ila Mike Huckabee ya sanar a yau Litinin cewa: Wani makami mai linzami na Iran ya fado kusa da ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Tel Aviv, wanda ya yi barna kadan amma ba a samu rauni a tsakanin ma’aikatan ba. A cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce: Daga yau Litinin ofishin jakadancin da sauran ofisoshin Amurka da suke haramtacciyar kasar Isra’ila za su ci gaba da kasancewa a rufe a matsayin matakin riga-kafi. Jakadan ya kara da cewa: Babban abin da ya sa a gaba shi ne kare lafiyar jami’an diflomasiyyar kasarsa, kuma za su ci gaba da sanya ido kan...
Matatar mai ta Dangote ta sanar da fara dakon man fetur da dizal a fadin kasar daga ranar 15 ga Agusta, 2025. A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, matatar ta bayyana cewa shirin zai hada da ‘yan kasuwa, masu gidajen mai, masana’antun, kamfanonin sadarwa, kamfanonin jiragen sama, da sauran manyan masu amfani da man a fadin kasar nan. A wani bangare na dabarun kasuwanci, matatar Dangote za ta yi dakon man kyauta, domin kawar da tsadar sufuri da kuma inganta harkar kasuwancin matatar a duk fadin kasar. Domin saukaka aikin, matatar ta sayo sabbin tankunan dakon man mai amfani da iskar Gas (CNG) 4,000, wadanda za su zama kashin bayan dakon kayan zuwa inda ake bukata....
Isra’ila ta ce mutum takwas sun mutu a daren ranar Litinin sakamakon sabon harin da Iran ta kai a biranen Tel Aviv da Haifa da wasu sassa na ƙasar. Wannan na zuwa ne a matsayin ci gaba daga jerin hare-hare da Iran ke kai wa tun bayan da Isra’ila ta fara kai mata hari makonnin da suka wuce. NAJERIYA A YAU: Dalilan Durƙushewar Sababbin Sana’o’i Tun Ba A Je Ko’ina Ba Iran ta kai sabbin hare-hare birnin Tel Aviv da Haifa Yanzu haka, adadin mutanen da hare-haren Iran suka kashe a Isra’ila ya kai 24, yayin da mutane sa.a da 300 ke kwance a asibitoci saboda raunuka. Isra’ila ta ce a martaninta, jiragen yaƙin ƙasar sun kai hari a birnin...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Sabbin masu sana’oi na tafka kurarai da suka hada da rashin kyakkyawar tsari, karancin jari, rashin shawarwarin kwararru da wasu kalubalen na daban. Sai dai masana suna ganin idan sabbin masu sana’oi za su yi amfani da shawarwarin da suke badawa zai taimaka wajen dorewar sabbin sana’oin su. NAJERIYA A YAU: Rashin Aikin Yi Da Hanyoyin Magance Su A Najeriya DAGA LARABA: Dalilan Rashin Jituwa Tsakanin Marasa Lafiya Da Jami’an Kiwon Lafiya Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan irin wadannan kura-kurai da kuma shawarwarin da masana suka bada don dorewar sabbin sana’oi. Domin sauke shirin, latsa nan
Iran ta kai sabbin hare-hare kan manyan biranen Isra’ila da suka haɗa da Tel Aviv da Haifa, inda ta yi amfani da makaman linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa. A cewar gidan talabijin na Iran, gomman makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa ne suka tashi zuwa Isra’ila, kuma wasu daga cikinsu sun ƙetare garkuwar kariyar iska ta Isra’ila. An tallafa wa mata 250 da abinci da kayan sana’a a Kaduna Yadda wani ɗan sanda ya rasu a hanyar zuwa ɗaurin aurensa Sai dai har yanzu ba a ji wani bayani daga sojojin Isra’ila ba. Faɗan Iran da Isra’ila ya fara ne bayan Isra’ila ta kai hari kan wani sashen ofishin jakadancin Iran da ke birnin Damascus na Siriya, wanda...
Sojojin kasar Iran sun cilla makamai masu linzami da kuma jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa kan HKI a dazuda nan nan, wayo yau lahadi a ci gaba da musayar wauta da suke yi da sojojin HKI kwanaki uku da suka gabata. Kamfanin dillancin labaran kare kai na kasar Iran Tasnim ya nakalto sojojin kasar na cewa sun cilla makamai masu linzami da Drones a karon farko da rana ido na ganin ido a kan HKI kuma tuna makaman sun fada a inda yakamata su fada a cikin haramtacciyar kasar. A safiyar ranar jumma’a ce sojojin HKI suka kai hare-hare kan birnin Tehran inda suka kai manya-manyan jami’an sojojin kasar ga shahada, sannan suka kashe mutane fararen hula wadanda...
Garkuwan sararin samnaiyar kasar Iran a lardin Zanjan ya bada labarin kakkabo jiragen yakin na HKI guda biyi wadanda ake sarrafasu daga nesa a sararin samaniyar. Kamfanin dillancin lbaran Tasnim na sojojin kasar Iran ya nakalto majiyar dakarunn juyin juya halin musulunci na kasar Iran tana fadar haka. Labarin ya kara da cewa rubuce rubucen da aka rubuta a jikin jiragen da aka tarwatsa sun bayyan cewa kirar kasar Amurka ce. Wannan yake tabbatar da irin hannun da Amurka take da shi a cikin yakin da Iran take fafatawa da HKI. A wani labarin kuma yansandar yanar gizo sun kama mutane biyu wadanda suke yada labaran karya dangane da yaki da kuma shuwagabannin kasar. Har’ila yau an kama wasu wadanda...

Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Ce Ba’a Rufe Kofar Diblomasiyya Ba, Matukar HKI Ta Dakatar Da Kaiwa Kasar HKI
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya bayyaana cewa kasarsa bata rufe kofar diblomasiyya dangane da shirinta na makamashin Nukliya ba, matukar HKI zata dakatar da hare-haren da take kaiwa kasar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a yau Lahadi a taron yan jaridun da ya kira a birnin Tehran. Ya kuma kara da cewa Iran tana son ta ci gaba da shirinta na makamashin Nukliya ta zaman lafiya ta hanyar diblomasiyya idan an bata damar yin haka. Ministan ya ce ikidar JMI ne warware dukkan matsaloli da farko ta hanyar Diblomasiyya, da kuma tattaunawa amma ba zamu taba amincewa wani ya hanamu hakkimu na mallakar makamashi nukliya ta zaman lafiya ba....
Babban kwamandan dokarun khatamul Ambiya (s) a nan birnin Tehran ya bayyana cewa sojojinsa zasu ci gaba da fafatawa da HKI har zuwa lokacinda zata dakatar da kawowa Iran yaki, ko kuma ta sami nasara a kansu, Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Janar Ali Shudmoni, yana fadar haka a yau Lahadi bayan da suke cilla makamai masu linzami da kuma jiragen yaki wadanda ake sarrafasu da nesa kan HKI a karon farko na rana, a cikin kwanaki uku da fara yakin. Janar Shodmani ya kara da cewa zasu ci gaba da kaiwa yahudawan hare-hare har zuwa lokacinda zasu yi nadama sun daina yakin. Kwamnatin ya bayyana cewa ya zuwa yanzu sun saminar kasar lalata cibiyoyin da...
Kakakin gwamnatin kasar Iran ta bayyana cewa, kasar Iran ta shiga yaki, kuma don haka dole sai an sami sauyi a rayuwar mutane ba. Fatima Muhajirani ta bayyana cewa daga yau ramukan layin dogo a cikin birnin Tehran wuraren mafaka da muyewa ne na mutanen da suke birnin har’ila yau za’a bude masallatai da makarantu don su zama wuraren samun mafaka. A wani bangare fatimeh Muhajirani ta bayyana cewa an rufe sararin samaniyar kasar Iran, don haka babu jirgi wanda zai tashi a ciki ko wajen kasar har zuwa abinda hali yayi ta kuma kara da cewa a halin yanzu jirgin kasa zai zama hanyarb tafiya mafi sauki a wannan haling a mutane. Tace mahajjan Iran zasu dawo ta hanya...