HausaTv:
2025-05-23@07:20:55 GMT

Putin ya ba da shawarar tattaunawa kai tsaye da Ukraine a Istanbul

Published: 11th, May 2025 GMT

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ba da shawarar yin  tattaunawa “kai tsaye” ba tare da sharadi ba” tsakanin kasarsa da Ukraine a ranar 15 ga Mayu a Istanbul.

A martanin da ya mayar, shugaban na Ukraine ya ce a shirye ya ke don tattaunawa kai tsaye, amma ya zama dole a tsagaita bude wuta a gabanin haka, yana mai nuni da shawarar da kawayensa na yammacin duniya suka bayar na tsagaita bude wuta na kwanaki 30 ba tare da sharadi ba daga ranar Litinin.

Ba tare da yin tsokaci a kai tsaye kan shawarar kasahen ba, shugaban na Rasha ya caccaki turawan da ya ce sun yi wa Rasha “rashin ladabi da kakkausan lafazi” ya kuma ce ya kamata kafa sulhu ya zama wani bangare na tattaunawa kai tsaye kan rikicin da aka shafe sama da shekaru uku ana yi.

A wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban kasar Rasha Recep Tayyip Erdogan ya yi maraba da shawarar Vladimir Putin na tattaunawa tsakanin Moscow da Kyiv a Istanbul, in ji fadar shugaban kasar Turkiyya.

“A yayin tattaunawar, shugaba Erdogan ya shaidawa shugaba Putin na Rasha cewa, a shirye Turkiyya ta ke ta karbi bakuncin tattaunawar da za ta kai ga cimma matsaya mai dorewa.”

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: da shawarar a kai tsaye

এছাড়াও পড়ুন:

‘Yan Ta’adda Na Amfani Da Sojoji Da ‘Yan Siyasa Wajen Samun Bayanan Sirri – Zulum 

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi ikirarin cewa akwai mutanen da ke aiki a matsayin ‘yan leken asiri ga ‘yan ta’adda da suka hada da Sojoji, ‘yan siyasa da sauran mutanen gari. Da yake jawabi yayin hira da kamfanin labarai na ‘News Central’ a ranar Laraba, gwamnan ya jaddada bukatar sabunta dabarun leken asiri da daukar kwararan matakai don magance matsalar rashin tsaro a yankin. Sara Da Sassaka Ba Ya Hana Gamji Toho Gwamnatin Kano Ta Hana Tallace-tallacen Magungunan Gargajiya A Fina-finai Da Kan Tituna “Akwai wadanda suka yi hadin gwiwa da ‘yan ta’adda daga cikin sojojin Nijeriya, cikin ‘yan siyasa, da kuma cikin mazauna yankunanmu, abin da za mu yi shi ne mu karfafa fasahar leken asirinmu don cafko marasa kishin kasa acikinmu sannan mu yi maganinsu ba tare da wani tausayi ba” in ji Zulum. Ya yi kira da a sauya salon yaki da matsalar tsaro, yana mai yin Allah wadai da irin wannan kwangila da wasu ke amsowa don tada zaune tsaye. A cewarsa, kawar da irin wadannan mutane, na iya maido da zaman lafiya cikin gaggawa.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yadda ‘Yan Majalisa Ke Cusa Ayyuka Marasa Amfani A Kasafin Kuɗi – Rahoto
  • Tottenham Ta Doke Manchester United A Wasan Karshe Na Europa 
  • Za’a Gudanar Da Tattaunawa Zagaye Na 5 Tsakanin Amurka Da Iran A Ranar 23-Afrilu A Roma
  • An Tattauna Hanyar Zamanantar Da Kasa A Dandalin Tattaunawa Na Masanan Sin Da Afirka
  • ‘Yan Ta’adda Na Amfani Da Sojoji Da ‘Yan Siyasa Wajen Samun Bayanan Sirri – Zulum 
  • Sharhin Bayan Labarai: Iran Zata Ci Gaba Da Tashe Uranium Tare Da Yarjeniya Ko Babu Ita
  • Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ta Iran Ya Ce: Haramtacciyar Kasar Isra’ila Ba Ta Da Alkiblar Siyasa
  • ‘Yan Gwagwarmayar Falasdinawa Sun Halaka Sojojin Sahayoniyya Tare Da Jikkata Wasu A Beit Lahiya
  • Shugaban Kasar Colombia: Ayyukan Kasar Sin Sun Nuna Wani Sabon Salo Na Ci Gaban Zamantakewar Al’ummar Bil’adama
  • Rasha Ta Ce Za Ta Tattauna Da Ukraine Don Yin Sulhu Game Da Yaƙin Da Suke Tafkawa