Rukunin farko na maniyyata dari biyar da sittin (560) daga jihar Kwara tare da jami’an hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON su biyu, sun tashi daga Filin Jirgin Sama na na Babatunde Idiagbon da ke Ilori zuwa Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2025.

Yayin da yake jawabi ga maniyyatan kafin tafiyarsu, Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bukace su da su kasance masu kamun kai da kuma wakiltar jihar da kasa Najeriya.

Gwamna AbdulRazaq, wanda mai ba shi shawara ta musamman, Alhaji Saadu Salaudeen, ya wakilta, ya yi kira ga dukkan maniyyata 2,174 daga jihar da su yi addu’a domin zaman lafiya da hadin kai a jihar da kuma kasa baki daya.

Gwamnan ya kuma gargadi maniyyatan da su nisanci duk wani hali da zai iya bata suna ko kimar jihar da kasar nan, tare da jaddada bukatar zaman lafiya da fahimta a tsakanin maniyyatan.

A jawabansu, Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kwara, Farfesa Mashood Mahmood Jimba, da Amirul-Hajj na bana, Olupo na Ajase-Ipo, Oba Ismail Yahaya Alebiosu, sun shawarci maniyyatan da su kasance masu hali na gari a tsawon lokacin aikin hajji.

Shi ma a jawabinsa, Shugaban Hukumar Jin Dadin Maniyyatan Musulmi ta Jihar Kwara, Alhaji Abdulkadir Abdulsalam, ya bayyana cewa za a yi sahu 4 wajen jigilar jimillar maniyyata dubu biyu da dari daya da saba’in da hudu (2,174) a matsayin wani bangare na shirye-shiryen aikin hajjin bana.

Maniyyatan sun tashi ne a jirgin Max Airline da karfe goma sha biyu da minti arba’in (12:40) na rana, zuwa kasa mai tsarki.

 

Ali Muhammad Rabi’u 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Kwara Jihar Kwara jihar Kwara

এছাড়াও পড়ুন:

Tawagar Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Farko Ta Sin Ta Dawo Daga Abyei Cikin Nasara

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaba Tinubu Ya Rantsar Da Sabbin Kwamishinonin Hukumar INEC
  • Falasdinawa 1500 Ne Su Ka Zama Makafi Sanadiyyar Yaki
  • Zamfara Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Kula Da Aikin 2025 Domin Kyautata Jin Dadin Alhazan Jihar 
  • Tsohon Dan Takarar Gwamna A NNPP A Jihar Ondo Ya Yi Murabus Daga Jam’iyyar
  • Tawagar Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Farko Ta Sin Ta Dawo Daga Abyei Cikin Nasara
  • Gidauniya ta yi wa masu cutar gwaiwa dubu 12 tiyata kyauta a Katsina
  • Majalisar Da Take Kula Da Nukiliyar Pakistan Za Su Yi Taron Gaggawa
  • IRGC Ya Kaddamar Da Sabon Sansanin Jiragen Yaki Na Karkashiun Kasa
  • HOTUNA: An ƙaddamar da tashin sahun farko na maniyyatan Nijeriya zuwa Saudiyya