“Amnesty International”: Korar Falasdinawa Daga Gaza Laifin Yaki Ne
Published: 7th, May 2025 GMT
A yau Laraba kungiyar kare hakkin bil’adama ta “Amnesty Interantional” ta fitar da rahoto da a ciki ta yi kira ga HKI da ta kawo karshen shirinta na korar Falasdinawa daga Gaza da karfi, tare da cewa; Har yanzu Isra’ilan tana ci gaba da tafka laifukan yaki a Gaza da yi wa mutane kisan kiyashi.”
Haka nan kuma kungiyar kare hakkin bil’adaman ta kasa da kasa ta ce; Isra’ilan tana fakewa da batun fursunoni domin halartawa kanta aikata laifukan yaki akan Falasdinawa.
A wani rahoto na sirri da aka yi kwarmatonsa,an nuna yadda gwamnatin HKI ta amince da sake mamaye yankin zirin Gaza baki daya.
Tashar talabijin ta 12, ta ambata cewa Shirin wanda majalisar ministoci ta amince da shi, ya kunshi sake mamaye zirin Gaza daga Arewacinsa zuwa kudancinsa.
A watan Febrairu ne dai shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi Magana akan Shirin fitar da Falasdinawa daga Gaza, da mayar da yankin zama wurin shakatawa.
A wancan lokacin dai kasashen duniya sun yi tir da furucin na Trump daga ciki har da kasashen turai abokan kawancen Amurka.
A halin yanzu dai HKI tana mamaye da kaso 1/3 na yankin Gaza, tare da rufe dukkanin kofofin shigar da tallafin abinci zuwa yankin.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
CMG Ya Watsa Jerin Shirye-Shirye Don Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin CMG Ya Gabatar Da Jerin Rahotannin Talabijin Kan Tunawa Da Cika Shekaru 80 Da Dawowar Yankin Taiwan Kasar Sin November 8, 2025
Daga Birnin Sin Xi Ya Yi Kiran Zurfafa Gyare-gyare Da Bude Kofa A Yayin Rangadin Aiki A Guangdong November 8, 2025
Daga Birnin Sin Kamfanoni Masu Jarin Waje Na Samun Kwarin Gwiwa Daga CIIE November 8, 2025