Leadership News Hausa:
2025-08-05@20:00:17 GMT

UEFA: An Kai Ruwa Rana Yayin Da Inter Ta Koro Barcelona Gida

Published: 7th, May 2025 GMT

UEFA: An Kai Ruwa Rana Yayin Da Inter Ta Koro Barcelona Gida

 

Wannan nasara da Inter Milan ta samu ya sa ta kai wasan karshe na gasar Zakarun Turai a karo na biyu cikin shekaru 3, a shekarar 2023 Manchester City ta doke Inter Milan a wasan karshe na gasar, wannan rashin nasara da Barcelona ta yi ya bata mata burinta na lashe gasar a karon farko cikin shekaru 10.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Xi Jinping Ya Ba Da Muhimmin Umarnin Jin Ra’ayoyin Masu Amfani Da Intanet Kan Tsara Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-Biyar Na 15

Babban sakatare na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS, kana shugaban kasar, Xi Jinping ya bayar da muhimmin umarni game da binciken ra’ayoyin jama’a masu amfani da shafukan Intanet kan aikin tsara shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15 a kwanan nan, inda ya ce, ya kamata aikin tattara ra’ayoyin jama’a ta yanar gizo wajen tsara shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 15 ya samu shigar jama’a sosai, kuma ya kasance wani aiki na dimokuradiyya dake shafar dukkan bangarori.

Jama’a sun yi ta ba da shawarwari tare da gabatar da ra’ayoyi masu muhimmanci, wadanda ya kamata sassan da abin ya shafa su yi nazari a hankali tare da shigar da su cikin tsarin. Kuma dole ne kwamitocin JKS da gwamnatoci a dukkannin matakai su bi tsarin da ya shafi al’umma, su gudanar da bincike mai zurfi kan ra’ayoyin jama’a, da sauraron muryoyinsu, da shigar da hikimominsu cikin tsarin, ta yadda za a samar da hadin gwiwa mai karfi don ingnta zamanintarwa irin ta kasar Sin, da ci gaba da tabbatar da cikar burin jama’a na samun ingantacciyar rayuwa.

Daga ranar 20 ga watan Mayu zuwa ranar 20 ga watan Yunin bana, an fara aikin tattara ra’ayoyin jama’a kan tsara shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 15 ta yanar gizo, kuma an bullo da shiri na musamman a shafin intanet na Jaridar People’s Daily, da na kamfanin dillancin labarai na Xinhua, da shafin intanet na babban rukunin gidajen rediyo da talbijin na kasar Sin wato CMG, da kuma kan dandalin “Learning Power”, don neman ra’ayoyin jama’a.

Ya zuwa yanzu, aikin ya sami shawarwarin jama’a masu duba shafin intanet sama da miliyan 3, tare da samar da muhimman bayanai don tsara shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 15. (Safiyah Ma)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Nafisa ta cancanci kyautar Dala 100,000 da gida da OON — Pantami
  • Xizang Ya Cimma Nasarorin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Suka Kafa Tarihi Cikin Shekaru Fiye Da 60
  • Nafisa ta cancaci kyautar Dala 100,000 da gida da OON —Pantami
  • ’Yar shekara 17 daga Yobe ta lashe Gasar Turanci ta Duniya
  • Tinubu ya bai wa ’yan wasan ƙwallon kwandon mata kyautar Dala dubu 100 da gidaje
  • Xi Jinping Ya Ba Da Muhimmin Umarnin Jin Ra’ayoyin Masu Amfani Da Intanet Kan Tsara Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar-Biyar Na 15
  • Ƴan matan Najeriya Sun Lashe Gasar Kwallon Kwando Ta Afirka
  • Son Zai Bar Tottenham Zuwa Amurka Bayan Shafe Shekaru 10 A Ingila
  • Shirin ACRESAL Zai Samar Da Injinan Ban Ruwa Masu Amfani Da Hasken Rana A Jigawa
  • Menene Sirrin Nasarar Ƴan Wasan Nijeriya Mata A Ƙwallon Ƙafa?