Za a faɗaɗa Gasar Kofin Duniya ta Mata zuwa ƙasashe 48 — FIFA
Published: 10th, May 2025 GMT
Hukumar Ƙwallon Kafa ta Duniya, FIFA, ta ce za ta faɗaɗa Gasar Kofin Duniya ta Mata daga tawagogi 32 zuwa 48.
FIFA ta ce sabon tsarin zai fara aiki ne daga gasar 2031, wadda Amurka ce kawai ke neman ɗaukar nauyinta.
Sauya sheƙa bayan cin moriyar jam’iyya butulci ne — Kwankwaso HOTUNA: An ƙaddamar da tashin sahun farko na maniyyatan Nijeriya zuwa SaudiyyaTuni dai FIFA ta faɗaɗa gasar cin Kofin Duniya ta Maza da za a yi nan gaba, zuwa wannan adadi.
FIFA ta ce ta ɗauki matakin ne saboda yadda gasar ke ci gaba da samun karɓuwa da farin jini tsakanin masoya ƙwallon ƙafa a duniya.
Masu suka sun zargi hukumar da fifita kuɗin da za ta samau fiye da la’akari da yawan wasanni da ’yan wasa za su fuskanta.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gasar Kofin Duniya ta Mata
এছাড়াও পড়ুন:
Kakakin majalisar dokokin Ribas da takwarorinsa 16 sun fice daga PDP zuwa APC
Kakakin Majalisar Dokokin jihar Ribas, Martin Amaewhule tare da mambobin majalisar su 15 sun sanar da sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Amaewhule ya bayyana shawarar ’yan majalisar ne a zaman majalisa na ranar Juma’a, inda ya ce akwai abin da ya kira “rarrabuwar kai a fili” a cikin PDP wanda ya sa suka yanke wannan shawara.
Muna tafe da karin bayanai…