2025-08-08@07:10:25 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3063
«Yamma»:
Wa jirgin sama na daukar marasa lafiya ya yi hatsari ya kuma fadi a kan gidajen mutane a kusa da birnin Nairobi babban birnin kasar ta Kenya a jiya Alhamis.AMREF Flaying Doctor, jirgi ne karamin samfurin XLS ya tashi daga tashar jiragen sama na Nairobi da nufin zuwa wasu yankuna a kasar Somaliland ya fadi...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk bayan shekaru hudu, Najeriya na kara yin zabe kuma ko wanne lokaci ‘yan takara kan dauki alkawura. Ko shekaru nawa wadanda ake zabe ke bukata don cika alkawuran da suka dauka? NAJERIYA A YAU: Mummunan Tasirin Rashin Bambance Zazzabin Lassa Kan Lafiyar Al’umma DAGA LARABA: Me Ke...
Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya bayyana cewa yara miliyan 11 da ke ƙasa da shekaru biyar a Najeriya na fama da rashin abinci mai gina jiki, lamarin da ke ƙara yiwuwar wani yanayi mai barazana ga rayuwa saboda rashin kuzari. Shugaban Ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahma Rihood Mohammed Farah,...
Mazauna kauyuka akalla 30 daga Dan-Isa da Kagara dake karamar hukumar Kaura-Namoda a jihar Zamfara, sun mamaye gidan gwamnati dake Gusau babban birnin jihar domin nuna takaicinsu kan yadda rashin tsaro a yankin na su “yaki ci yaki cinyewa” a ranar Alhamis. Masu zanga-zangar da suka hada da mata da kananan yara suna dauke da...
Ya kuma lura da cewa, tattaunawa da ‘yan bindiga a wasu jihohin suka yi ya kara ta’azzara satar shanu, inda ya ce, Sam hakan, ba za a amince da shi ba. Dangane da ta’azzarar rashin tsaro, Gwamna Bago ya ce, za a nemi taimako daga shugaba Bola Tinubu da mai bai wa shugaban kasa...
Manoman gundumar Ɗan Isa da ke Ƙaramar hukumar Kaura Namoda a Jihar Zamfara sun ce ’yan bindiga sun yi musu barazana a wannan damina ta bana. Da yake tabbatar da hakan ga Daily Trust a wata tattaunawa ta wayar tarho, Hakimin unguwar Malam Hassan Yarima, ya ce kowane ƙauyuka 35 da ke ƙarkashin gundumarsa ya...
“An kashe da dama, kuma wasu da yawa sun sami munanan raunuka.” In ji Kaftin Adewusi Bayan farmakin ta sama, sojojin kasa na Birget 1 dake karkashin sashe na 2 na OPFY sun kaddamar da wani samame ta kasa a ranar 5 ga watan Agusta, inda suka yi nasarar dakile wani harin kwantan bauna...
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Injiniya Abdullahi Garba Ramat a matsayin sabon Shugaba kuma Babban Jami’in Gudanarwa (CEO) na Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC). Haka kuma, ya naɗa Abubakar Yusuf a matsayin Kwamishinan Harkokin Abokan Hulɗa, da Dr. Fouad Olayinka Animashun a matsayin Kwamishinan Kudi da Harkokin Gudanarwa. A cikin...
Da yake la’antar kisan a matsayin “mummuna, dabbanci, kuma lamarin da ba za a lamunta ba,” gwamnan ya yi alkawarin tabbatar da adalci. Ya umurci hukumomin tsaro da su dau mataki tare da kama wadanda ke da hannu a kisan nasa nan take. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Ekiti, Joseph Eribo, ya tabbatar da ƙwato jaririn da aka sace a wani asibiti da ke Ado-Ekiti ranar Litinin. An miƙa jaririn ga iyayensa, Mustapha Aliyu mai shekara 29 da kuma Salmatu Lawal mai shekara 22, bayan da jami’an ’yan sanda suka tsananta binciken lamarin. An kashe matafiya biyu da yin...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta biya iyalai 14 da aikin sake gina Babban Masallacin Gumel ya shafa kudaden diyya da suka kai Naira miliyan 277 da dubu 44. An gudanar da bikin bayar da takardun cekin kudin ne a Fadar Mai Martaba Sarkin Gumel, Dr. Ahmad Muhammad Sani, tare da halartar masu rike da sarautu, da...
Hukumar NDLEA ta Nijeriya da takwararta ta Indiya sun amince da yin aiki tare domin daƙile safarar miyagun ƙwayoyi tsakanin ƙasashen biyu. Wannan yarjejeniya ta fito ne daga wata tattaunawa ta kafar intanet tsakanin Shugaban NDLEA na Nijeriya, Janar Buba Marwa (mai ritaya), da shugaban hukumar ta Indiya, Anurag Garg. Shugabannin sun jaddada buƙatar haɗin...
Mazauna kauyen Chatta da ke karamar hukumar Hawul a jihar Borno sun fada alhini sakamakon rasuwar wasu mutum hudu ’yan gida daya. Ba a dai tabbatar da ainihin musabbabin rasuwarsu ba, amma mazauna yankin da lamarin ya faru sun ce suna zargin hayakin injin samar da lantarki na janareta ne ya yi ajalin su. An...
Majiyoyi daga cikin jami’an tsaron sun bayyana cewa sojoji da ‘yan sa-kai sun fafata da ‘yan bindigar. Sun kashe ‘yan bindiga da dama, sannan suka ƙwato bindigogi AK-47 guda uku daga hannunsu. ‘Yan bindigar sun gudu, wasu daga cikinsu na da raunuka ko kuma an kashe su, sai dai adadin ba a tabbatar da shi...
Bayan kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin tubabbun ’yan bindiga da jama’ar gari a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna, mazauna yankin sun ce yanzu matsalar tsaron ta dauki sabon salo. A watan Oktoban 2024 ne dai aka kulla yarjejeniyar sulhun tsakanin bangarorin biyu. Yarjejeniyar na zuwa ne bayan shafe sama da shekara 10 ana...
Shugaban Amurka, Donald Trump, yana shirin ƙara tsaurara wa Rasha takunkumi idan har ba a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ba kafin ranar Juma’a, 8 ga watan Agusta. Ko da yake Rasha ita ce ƙasar da aka fi ƙaƙaba wa takunkumi a duniya, har yanzu tana amfani da arziƙin man fetur da iskar gas da ta...
Kwamishinan ya ce tuni ya ba da umarni a fara bincike kan waɗanda ake zargin. Ya kuma tabbatarwa da jama’a cewa duk wanda ya kawo ƙorafi za a saurare shi, ba tare da an tsananta masa ba. A cewar rundunar, an daɗe ana samun ƙorafi cewa wasu ɓata-garin ‘yansanda suna karɓar kuɗi daga masu laifi...
“Su dai kawai abin da suke alfahari da shi, shi ne dukiya, yawan gidaje da jirage. Ba su san cewa mutane na kallonsu a matsayin ɓarayi ba.” Sanusi II, ya ƙara da cewa ba shugaban ƙasa ko gwamna kaɗai ke da laifi ba, hatta shugabannin addini da sarakuna ma sun ɓaci a yanzu. “Yawancin shugabanninmu...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A cewar masana harkar kiwon lafiya, rashin tantancewa balle a bayar da kulawar da ta dace a kan lokaci na cikin dalilan ta’azzarar barazanar da Zazzabin Lassa ke yi ga bangarori da dama na rayuwar al’ummar Najeriya, musamman a yankunan karkara. Wani bincike a kan tasirin Zazzabin Lassa...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A fannin noma ma, watsa shirye-shiryen da Sinanci zai taimaka wajen bayyana burin Nijeriya na fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, musamman yadda take neman aikewa da karin kayayyakin amfanin gona zuwa babbar kasuwar kasar Sin, tare da bai wa masu ruwa da tsaki na kasar Sin damar sanin abubuwan da Nijeriya za ta iya...
Shugaban Kasar Iran ya jaddada cewa; Dole ne kasashen musulmi su hana ci gaba da aikata laifuka a Gaza Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da fira ministan Malaysia Anwar Ibrahim, ya jaddada bukatar kasashen musulmi su dauki matakin hana ci gaba da bala’in jin kai a Gaza ta hanyar...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Taya Ali Larijani Murnar Nada Shi Sakataren Majalisar Kolin Tsaron Kasar Iran
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya taya Larijani murnar nadin da aka yi masa a matsayin sakataren majalisar koli ta tsaron kasa Abbas Araqchi, ministan harkokin wajen kasar Iran, ya taya Ali Larijani murnar nadin da aka yi masa a matsayin sakataren majalisar koli ta tsaron kasar. A cikin sakon taya murna, Araqchi ya taya...
Da safiyar Larabar nan ne kwamitin tsaron MDD ya gudanar da taron tattaunawa game da batun rikicin Isra’ila da Falasdinu, inda a jawabinsa game da aniyar Isra’ila ta tsananta hare-haren soji, da mamaye daukacin zirin Gaza, mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya bayyana matukar damuwa kan hakan, yana mai kira...
Shugaban ya kuma yabawa cibiyoyin koyon ilimi tare da bayyana cewa wadannan nasarorin da aka samu shaida ne na ingancin ilimin Nijeriya wanda ke kekkenshe yara masu basira a duniya. Tinubu ya yi imanin cewa, ilimi muhimmin abu ne ga ci gaban kasa; don haka, babbar hobbasar da gwamnatinsa ta yi a fannin, shi...
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin gaggauta aiwatar da shirin bayar da kulawar lafiya kyauta ga tsofaffin ma’aikata masu ƙaramin albashi da ke ƙarƙashin tsarin fansho na haɗin gwiwa (Contributory Pension Scheme – CPS), yana mai bayyana shirin a matsayin muhimmin bangare da zai taimaka wa rayuwarsu. A wata sanarwa da mai...
Mutum 22 sun gamu da ajalinsu, yayin da wasu 20 suka jikkata, bayan wata babbar mota da ta yi lodin mutane da dabbobi ta yi hatsari a kan hanyar Lambata zuwa Lapai da ke Jihar Neja. Hatsarin ya auku ne da safiyar ranar Litinin. Tinubu ya taya ’yan matan Yobe da suka lashe gasa a...
Malaman jami’o’i sama da 100 daga Isra’ila sun bayyana cewar jan kafar da ƙasar Jamus ke yi wajen ɗaukar matakin matsin lamba ga gwamnatin Isra’ila na iya bai wa ƙasar damar ci gaba da aikata manyan laifuffuka a Gaza. Wata wasika da masanan suka rubuta wa ɗaya daga cikin manyan shugabannin jam’iyyar SPD da ke...
A jawabin da Shugaban Jami’ar ABU, Farfesa Adamu Ahmed, ya yi ta bakin mataimakinsa, Farfesa Sanusi Rafindadi, ya yaba da yadda taron ke taimakawa wajen wayar da kai game da wannan cuta mai hatsari. Ya kuma gode wa Hajiya Fatima bisa amsa gayyatar jagorantar taron. Shugabar Sashen Kula da Mata, Farfesa Rahanatu Lawal, ta jaddada...
Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Zamfara, CP Ibrahim Balarabe Maikaba, ya kawata jami’ai 390 da aka daga matsayinsu zuwa sabon mukami a rundunar. An gudanar da bikin kawata jami’an ne a Hedikwatar Rundunar ‘Yan Sanda da ke Gusau, babban birnin jihar. A cewar sanarwar da mai magana da yawun ‘yan sanda, DSP Yazid Abubakar,...
Kakakin dakarun juyin juya halin musulun a nan Iran ya bayyana cewa nasarar da JMI ta samu na tunkude hare-harenda HKI ta kawowa kasar ya saya abubuwa da dama a bangaren siyasa da wasu al-amura a yankin da kuma duniya gaba daya. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto General Ali Mohammad Naeini...
‘Yansanda a kasar Iran sun bada labarin cewa suna amfani da jiragen leken asiri da wasu kayakin masu aiki da lantarki na zamani don tabbatar da lafiyar masu tattalin 40 zuwa wurare masu tsarki a kasar Iraki. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Brigadier General Ahmad Ali Goodarzi shugaban yansanda a nan...
Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana cikakken goyon bayan rundunar ‘yan sanda ga Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano wajen tabbatar da kiyaye dabi’u da yakar munanan halaye a cikin al’umma. CP Bakori ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar wayar da kai da Sakatare na Hukumar, Abba El-Mustapha,...
Mataimakin shugaban kasar Iran Muhamad Reza Aref ya bayyana cewa kasar Iran tana goyon bayan dukkan shirin zaman lafiya a yankin musamman tsakanin kasashen Armenia da kuma Azarzaijan. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Aref yana fadar haka a lokacin ganawarsa da shugaban kasar Armenia Vahagn Khashaturyan a kasar Tukeministan ake ake...
’Yan bindiga sun sace mutum 150 a mabanbantan hare-haren da suka kai kauyuka daban-daban na jihar Zamfara a cikin kwana hudu. Kakakin Gwamnatin jihar ta Zamfara, Mahmud Mohammed Dantawasa ne ya tabbatar da hakan ga BBC. Sai dai duk da yake bai bayyana hakikanin adadin mutanen da aka sace ba, amma ya ce gwamnatinsu na...
A dai dai lokacinda ake yaki na kwanaki 12 tsakanin Iran da HKI da Amurka, daga ranar 13-24 na watan Yunin da ya gabata, cibiyoyin yakin yanar gizo na kasar Iran sun gwada karfinsu da kuma kwarewansu a wannan fagen fama. Kanfanin dillancin labarai na Tasnim na kuma kasar Iran ya nakalto sharhin wasu kafafen...
Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Ali Namadi, ya ajiye aikinsa bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi rahoton kwamitin bincike da ke duba rawar da ya taka a batun ceto wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu. Wannan matakin na murabus ana kallonsa a matsayin wani muhimmin cigaba da...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wasu matasa sun zabi tallata ‘yan siyasa a kafafen sada zumunta na zamani ta yadda bai kamata ba a wasu lokutan. Tallata ‘yan siyasa da matasan suke yi kan haifar da hatsaniya, ko kiyayya, a intanet ko ma a zahiri a tsakanin su. NAJERIYA A YAU: Yadda...
Gwamnan ya kuma jaddada kudirinsa na ci gaba da tabbatar da adalci, ladabtarwa, da yakar laifukan da suka shafi sha da fataucin miyagun kwayoyi da sauran munanan dabi’u da ke addabar matasa da al’umma jihar Kano. Gwamna ya kuma yi gargaɗi ga duk masu rike da mukaman siyasa da su rika yin taka-tsantsan kan al’amuran...
Ya kuma kara da cewa, a Benuwe, sama da mutane 5,000 ne suka rasa rayukansu a gwamnatin baya. Nuhu ya bayyana cewa, ayyukan da sojoji ke ci gaba da yi a yankin Arewa-maso-Yamma sun kai ga ceto mutane 11,259 da aka yi garkuwa da su a watan Mayun 2025. An kuma kashe wasu manyan...
A cewar mahaifin marigayen, Dankama, ya bayyana cewa ba ya gida lokacin da katangar ta fado, inda ya ce ya kadu da jin labarin. “Wannan lamarin ya faru da kusan mutane goma, amma mutane 6 sun riga mu gidan gaskiya. A yanzu haka, uku suna kwance a asibiti suna karbar magani,” kamar yadda ya...
Sashen cinikayyar samar da hidimomi na Sin ya ci gaba da bunkasa yadda ya kamata cikin watanni shida na farkon shekarar nan ta 2025, inda ya karu da kaso takwas bisa dari kan mizanin shekara. A cewar ma’aikatar cinikayya ta Sin, darajar hidimomin shige da fice a wannan wa’adi ta kai kudin Sin tiriliyan 3.89,...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Haɗin kai tsakanin kafofin watsa labarai, diflomasiyya da fage na tabbatar da ƙarfi da ci gaban ƙasa A jajibirin ranar ‘yan jarida ta kasa, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya ziyarci hukumar kula da harkokin yada labarai ta kasa (NBO) inda ya gana da shugaban kungiyar da...
Sojojin Yemen sun kaddamar da hari kan filin jirgin saman Lod da ke birnin Jaffa a haramtacciyar kasar Isra’ila da makami mai linzami Dakarun sojin Yemen sun sanar a yau cewa: Sun kai hari kan filin jirgin saman Lod da ke birnin Jaffa, domin mayar da martani kan laifukan kisan kiyashi da kakaba masifar yunwa...
Dokta Muhammad Tahir da aka yi wa barazanar kisa ya bayyana abin da ya gani na masifa a Gaza Dr. Muhammad Taher ya dauki kashe-kashe da kakaba yunwa da ke faruwa a Gaza a matsayin abin tunawa da abin da ya faru da Imam Husaini (a.s), kuma Gaza ita ce Karbala ta wannan zamani. A...
An samu bullar sabani da rikici a tsakanin ‘yan sahaypniyya game da mamaye Gaza a daidai lokacin da ake ci gaba da kai hare-hare da kuma rage yawan sojojinsu a yankin Yakin kisan kiyashi yana ci gaba da gudana a Gaza ta hanyar ci gaba da kai hare-hare kan mai uwa da wabi, tare da...
Matar Shugaban Karamar Hukumar Giwa, Hajiya Hadiza Ahmad Sama’ila Yakawada, ta kaddamar da Makon Shayar da Nono na Duniya na bana, tare da kira ga iyaye mata da mazajensu da su ba wa jarirai nono kacokam na tsawon watanni shida na farko. A yayin kaddamarwar, Hajiya Hadiza ta bayyana cewa shayar da jarirai nono na...
Rahotanni sun bayyana cewa, fitaccen kwamandan ‘yan ta’adda Bello Turji ya mika wuya tare da sako wasu mutane 32 da aka yi garkuwa da su, biyo bayan wani shirin zaman lafiya da malaman addinin musulunci suka yi a jihar Zamfara. Wani fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Musa Yusuf, wanda aka fi sani da Asadus-Sunnah ne...
Rundunar ’yan sandan Nijeriya reshen Abuja ta sanar da cafke wasu mata ’yan gida ɗaya da ake zargi da kitsa garkuwar ƙarya da zummar karɓar kuɗin fansa na naira miliyan biyar a wurin mahaifinsu. Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar. Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda...

Xizang Ya Cimma Nasarorin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Suka Kafa Tarihi Cikin Shekaru Fiye Da 60
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp