Ra’ayin Al’umma Game Da Iyaye Masu Furta Muggan Kalamai A Kan ‘Ya’yansu
Published: 10th, May 2025 GMT
Abu ne wanda bai dace ba kuma ya saba ka’ida sai dai mu yi wa irin wadannan iyayan fatan shiriya, munanan kalamai gurbata tarbiyyar ‘ya’ya yake yi sukutum, abun fada shi ne kawai iyaye su kiyaye harsunansu wurin furta munanan kalamai ga yaransu ko sauke takaicinsu a kansu dan hakan kan iya janyo babban matsalar da al’umma za ta yi turrr da halin ‘ya’yan, hakuri za su rika yi su kuma danne zuciyarsu saboda zuciya ba ta da kashi munanan kalamai za su iya fita har wanda kan iya janyo da-na-sani kamar tsinuwa da makanantansu.
Sunana Aminu Adamu Malam Maduri:
To magana ta gaskiya iyayen da suke da irin wannan hali suna jefa rayuwar ‘ya’yansu cikin wani hali sakamakon irin wadanan kalamai domin furta mummunar kalma ga ‘ya’yanka babban kuskure ne. To magana ta gaskiya ya kamata iyayen su fi maida hankali wajen yi wa yaransu addu’ar shiriya akai-akai hakan zai taimaka wajen saukin lalacewar tarayyar yaran. To irin wadanan maganganun suna tasiri sosai wajen lalacewar tarayyar yaro muddun aka cigaba da yi masa su wanda hakan daga karshe zai iya addabar iyayensa dama sauran al’ummar unguwa duk ta dalilin irin wannan munanan maganganu. To shawara ta a nan ita ce ya kamata iyaye su dage wajen yi wa yaransu addu’ar Allah ya shirye su a duk lokaci domin hakan zai taimaka wajen shiriyar su da kuma kaucewa aibata su, daga karshe nake addu’ar Allah ya shirya mana zuri’a bakidaya.
Sunana Jamila Ibrahim Jihar Katsina:
Abin da zan ce game da hakan shi ne ita wannan dabi’ar ta iyaye ba abu ba ce mai kyau ba kuma tana da hatsari sosai a cikin al’ummar musulmi. Sannan yana sa tsoro sosai tsakanin yaran da iyayensu har ma ya sa ba sa iya tunkarar iyayennasu da wata magana. Ni dai a nawa ganin idan uwa na son sarrafa harshenta ita ce su koyi jinkiri kafin su mayar da martani ga ‘ya’yensu, kuma su samu hadin kai a wajen mazajensu dan wadansu mazan ne ko surukai suke kin hukunta ‘ya’yan sai su yaran su yi abin da suke so daga haka sai hakan ya haifar da da mara ido. Illolin da hakan ka iya kawo wa su ne wataran iyaye za su iya furta wata kalmar da za ta iya lallata yaran domin kuwa shi bakin uwa da sauri yake tasiri a kan danta wanda ta haifa kuma daga hakan sai wadansu ta sanadiyyar hakan su zama masu wata muguwar dabi’ar musamman ga maza. Shawarar dai ita ce rashin bam-bamta yaran wajen nuna musu soyayya, rainonsu a inda babu yara ko inda babu yara marasa ji da tarbiyya, nuna musu daidai da ba daidai ba tun suna yara don ice tun yana danye ake tankwara shi.
Sunana Abba Abubakar Yakubu, marubuci kuma dan jarida daga garin Jos:
Salamu Alaikum. Gaskiya kuskure ne babba, iyaye su rika aibata yaransu ko su rika jifansu da munanan kalamai. Addinin Musulunci ya koyar da mu muhimmancin yi wa yara kyakkyawar tarbiyya da yi musu addu’a tagari, wacce za ta bi su har girmansu. Idan iyaye suna yi wa yaransu addu’a mai kyau, ko da sun saba musu ko sun aikata ba daidai ba, ana sa ran za su tashi suna girmama iyayensu, suna masu tausaya musu, da kaucewa duk wani abin da zai bata musu rai. Yaran da muke gani suna shashanci da mummunar rayuwa, su ne ake ce wa masu bakin uwa, wato wadanda iyayensu ke aibata su tun suna kanana. Allah ya kiyaye mu daga yi wa yaranmu baki, ko tsine musu da fada musu munanan kalaman da za su lalata musu rayuwa, kuma su sanya su cikin fushin ubangiji. Amin
Sunana Badi’a Bashir Daga Sokoto:
Hakikanin gaskiya wanannan dabi’ar abu ne mara kyau. yadda iyaye za su sarrafa fushin shi ne su rinka tuna illolin hakan zai haifa yin hakan a lokacin da ‘ya’yensu suka kamar za su iya zama ‘yan daba, ‘yan fashi, masu sace-sace idan maza ne, idan mata ne kuma su zama masu bin maza da dai sauransu. Illolin yin hakan su ne wadansu yaran za su iya samun kalubale a rayuwarsu su zama su na gwagwarmaya a kan yadda za su kula da kansu da iyayen sun fadi magana maradadi a kan ‘ya’yayensu a lokacin da suke cikin fushi. Shawara wajen tarbiyyar yaran hana su fita ko’ina.
Sunana Muktari Sabo Jahun, A Jihar Jigawa:
Babu shakka iyayen yara sukan yi irin wannan dabi’a ta furta kalamai munana akan yaransu idan sun bata musu rai wanda hakan ba daidai bane. Lalla iyaye su guji yin hukunci cikin fushi domin yin hakan shi ke jawo furta mummunar kalma hakan kuma yana jawo yaro ya sami matsala a rayuwa. Yara su kan tashi da irin wannan dabi’a ta zage-zage da munanan kalamai domin sun ga na gaba suna yi sai su yi zaton daidai ne. Shawara ga iyaye su tarbiyanci ‘ya’yansu da tarbiyya me kyau bada zagi ba domin ba a tarbiyya da zagi ko munanan kalmomi.
Sunana Hafsat Sa’eed Jihar Neja:
Idan yaro ya bata maka rai ya kamata ka tausasa zuciyarka ka rika taya su da addu’a ka rika yi musu fatan shiriya, sabida muddin uwa ta ce za ta rika aibata su da bakinta za a ja wa yaro baki musamman a irin wannan halin da muke ciki.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary) Jihar Kano, Rano LGA:
Bai dace ba gaskiya domin yin hakan yana kara lalata tarbiyyar yara da kuma sakawa a ga yara suna munanan abubuwan da kamar ba ‘ya’yan sunna ba. Hakuri da kuma tuna fadin ma aiki (s.a.w) da yake cewa; “idan dayanku yana cikin fushi to yayi shuru, sannan ya zauna”. Kangarewa da rashin ji da janyo bacin tarbiyyar su kansu yaran. Shawarata a nan ita ce idan yaranmu sun bata mana rai to muna furta musu fatan shiriya sannan bayan mun huce daga haushin sai mu kira yaran mu zaunar da su cikin nasiha mu yi musu fada da nasihohi da misalai a kan irin abin da suke yi na ba daidai ba da kuma illar da abin yake haifarwa domin su gyara. Allah kasa mu dace ka shirya mana zuria.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Ya Ya Iyaye irin wannan
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Da Rasha Sun Fitar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Game Da Zurfafa Dangantakar Abokantaka Ta Hadin Gwiwa Bisa Manyan Tsare-tsare A Sabon Zamani
Bugu da kari, Sanarwar ta ce Sin da Rasha na goyon bayan kasancewar MDD jigo na shugabancin batutuwan da suka shafi kirkirarriyar basira ko AI, da jaddada muhimmancin martaba ikon mulkin kai na kasashe daban daban, da nacewa bin dokokin kasashe mabanbanta, da martaba ka’idojin MDD yayin gudanar da hakan. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp