Amurka da Iran zasuyi tattaunawa ta hudu a ranar Lahadi
Published: 9th, May 2025 GMT
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce za a gudanar da zagaye na hudu na tattaunawa tsakanin Iran da Amurka ranar Lahadi.
Araghchi ya bayyana a yau Juma’a cewa Oman ce, zata kasance mai shiga tsakani, kuma ita ce ke tantance lokaci da wurin da za a yi tattaunawar.
Ya kara da cewa bisa ga dukkan alamu kasar Oman ta tattauna da bangaren waccen bangaren.
Babban mai shiga tsakani na Iran ya jaddada cewa tattaunawar Tehran da Washington tana ci gaba.
Iran da AMurka dai sun yi jerin tattaunawa har guda uku a Oman, sannan a Italiya sai kuma a Oman.
Dukkan bangarorin dai sun bayyana tattaunar da mai kyakyawan fata.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Yi Tsokaci Kan Jita-Jitar Da Ake Yadawa Cewa: Shugaban Kasar Iran Zai Gana Da Shugaban Amurka
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi tsokaci kan jita-jitar cewa: Shugaban kasar Iran zai gana da shugaban kasar Amurka
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya yi watsi da jita-jitar da ake yadawa game da batun cewa shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian zai yi wata ganawa da shugaban Amurka Donald Trump a mako mai zuwa, da rashin gamsuwar bangaren Amurka da Iran da shiga tsakanin masarautar Oman, da kuma cewa Iran ta gabatar da shawarar gudanar da shawarwari kai tsaye da Amurka, da sauran da’awar karya a matsayin batutuwa na jita-jita maras asali da tushe.
Dangane da wata tambaya game da jerin jita-jita da ake yadawa a kafafen yada labarai game da matsayin tattaunawar da ake yi tsakanin Iran da Amurka, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa duk wadanda batutuwa da suke fitowa daga majiyoyi marassa tushe da asali kuma mafi yawansu labarai ne na karya na bogi da ba su da wata madogara mai tushe. Baqa’i ya jaddada cewa: Ma’aikatar harkokin wajen kasar ita ce ke da alhakin ba da bayanai dangane da ayyukan jami’an diflomasiyya, ciki har da batun tattaunawar da ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, cikin gaskiya, kwarewa, da kuma lokacin da ya dace.