Matsalar Tsaro: Zulum ya haramta sayar da man fetur a Bama
Published: 10th, May 2025 GMT
Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum ya haramta sayar da man fetur a Ƙaramar Hukumar Bama ta jihar, ciki har da garin Banki.
Gwamnan ya ce haramcin ya zo ne bayan tattaunawa da hukumomin tsaro a jihar, kuma an yi haka ne domin shawo kan matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta.
Gidauniya ta yi wa masu cutar gwaiwa dubu 12 tiyata kyauta a Katsina Za a faɗaɗa Gasar Kofin Duniya ta Mata zuwa ƙasashe 48 — FIFAWata sanarwa da mai taimaka wa gwamnan kan harkokin yaɗa labarai Dauda Iliya ya fitar, ya ce matakin wani ɓangare ne na tsare-tsaren da gwamnatin jihar ke yi na daƙile ayyukan ’yan ta-da ƙayar baya.
“Na bayar da umarnin haramta sayar da da man fetur a garuruwan Bama da Banki da kuma wasu sassa na karamar hukumar Bama nan take,” in ji gwamna Zulum.
Ya yi gargaɗin cewa duk wanda aka samu yana saɓa umarnin zai fuskanci hukunci mai tsanani.
“Babu wanda doka za ta ƙyale, sannan babu shafaffe da mai – za mu hukunta ko waye.
Gwamnan ya bai wa hukumomin tsaro damar kama duk wani gidan mai ko kuma mutum da ya take wannan umarnin.
Ya ƙara nanata zimmar da gwamnatinsa ke yi na dawo da zaman lafiya ma ɗorewa a jihar, inda ya yi kira ga al’ummar jihar da su ba da haɗin-kai a yaƙi da ƴan ta-da ƙayar baya da ake ci gaba da yi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Babagana Umara Zulum jihar Borno
এছাড়াও পড়ুন:
Dalilin Gwamnatin Kano Na Haramta Shirye-shiryen Siyasa Kai Tsaye
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp