‘Yan sanda sun bankaɗo masana’antar man gyaɗa na bogi a Kaduna
Published: 8th, May 2025 GMT
Rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna ta bankaɗo wata haramtacciyar masana’antar man gyaɗan bogi, tare da cafke mutane uku da ake zargin suna da hannu a harkar.
Wannan samame da jami’an sashen leƙen asiri na rundunar suka gudanar ƙarƙashin jagorancin SP Sani Bello, ya gudana ne da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar ranar 5 ga Mayu bayan samun bayanan sirri.
An gano haramtacciyar masana’antar ce a wani fili da aka kewaye da katanga a titin Mamadi, a yankin Maraban Jos da ke Kaduna.
Mai magana da yawun ‘yan sanda na jihar, DSP Mansir Hassan, shi ne ya fitar da sanarwar a madadin Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Rabiu Muhammad, a ranar Laraba.
Ya bayyana cewa waɗanda aka kama a masana’antar sun haɗa da Zailani Shuaibu, mai shekaru 33, wanda ake zargin shine mamallakinta, da Nasiru Usman mai shekaru 24, da kuma Salisu Usman mai shekaru 49 – dukkansu mazauna Maraban Jos ne.
A cewarsa, ‘yan sanda sun samu ganguna biyu maƙare da kayan aikin sarrafa man, da jarkoki goma sha biyar masu nauyin lita 25 na man da ba a kammala tacewa ba, sai jarkoki biyu da ke ɗauke da man gyaɗa na bogi da aka gama tacewa, da kuma ganga guda mai kyau.
DSP Hassan ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar ya jaddada ƙudirin rundunar na kare lafiyar jama’a da kuma kawar da ayyukan laifi a cikin al’umma.
Haka kuma, ya buƙaci mazauna da su ci gaba da lura da abin da ke faruwa a yankunansu domin kai rahoton motsin da ba su gamsu da shi ba zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa da su.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan sanda a Kaduna masana antar
এছাড়াও পড়ুন:
Jigawa Ta Kaddamar Da Kwamitin Likitocin Da Su Duba Lafiyar Mahajjatan Bana A Saudiyya
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta kaddamar da manyan jami’an likitocin kasa a shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin shekarar 2025.
Babban Daraktan Hukumar Alhaji Umar Ahmed Labbo ne ya bayyana haka a yayin bikin kaddamar da aikin da aka gudanar a Dutse babban birnin jihar.
Ya bayyana cewa, hukumar ta kaddamar da tawagar likitocin guda 10, inda ya bukaci kungiyar da ta yi aiki da gaskiya, hakuri, da jajircewa wajen yi wa alhazan jihar hidima a kasar Saudiyya.
Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ce aikin amana ce da bai kamata kungiyar ta dauka da wasa ba.
Ya yabawa Gwamna Umar Namadi bisa amincewa da wannan tawagar, inda ya nuna cewa, wannan shi ne karon farko da jihar ke tura ma’aikatan lafiya irin wannan aikin zuwa kasashen waje.
Ya jaddada godiya na zabarsu da kuma bukatar kare jin dadin alhazan Jigawa a duk tsawon wannan lokaci na aikin Hajji.
A nasa jawabin shugaban kwamitin yada labarai Abdulrashid Yusuf ya yi kira ga ‘yan wakilan da su ci gaba da gudanar da ayyukansu cikin himma tare da sanin ya kamata da kuma tsoron Allah.
Yusuf, ya yabawa gwamnatin jihar bisa kara adadin ma’aikatan lafiya zuwa 10.
USMAN MZ