2025-09-24@15:51:36 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3859
«Katsina Ba Ƙorafi»:
Darajar Naira ta ɗan ƙaru a kasuwanni, bayan Babban Bankin Najeriya (CBN), ya sanar da rage kuɗin ruwa daga kashi 27.5 zuwa kashi 27. Wannan mataki, a cewar masana tattalin arziƙi, na nufin gwamnati na ƙoƙarin rage matsin tattalin arziƙi da farashin kayayyaki ga ’yan ƙasa. ’Yan bindiga sun kashe mai juna biyu, sun sace mutum 8 a Kwara Mawaki Davido ya ba matarsa kyautar motar miliyan 240 A ranar Talata, an sayar da dala ɗaya kan Naira 1,487.36 a hukumance, inda hakan ya nuna samun sauyi idan aka kwatanta da Naira 1,488.60 da aka sayar da ita a baya. Hakazalika, farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya ya tashi zuwa dala 67.82 a kan kowace ganga ɗaya, abin da ya...
Fitaccen mawakin nan na kudancin Najeriya David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya ba matarsa Chioma kyautar sabuwar motar alfarma kirar Mercedes-Benz G-Wagon ta shekarar 2025. Wannan motar mai tsada, wadda aka kaddamar da ita kwanan nan a kasuwar duniya, tana da farashin sama da $150,000 (kimanin Naira miliyan 240). Yada labaran karya a intanet babban laifi ne a Musulunci – Sheikh Ibrahim Khalil UNGA: Yau Shettima zai gabatar da jawabin Najeriya a MDD Sabuwar motar ta 2025 na dauke da sabon fasali mai ban sha’awa da kuma Zubin da ya sa ta fi tsofaffin nau’ikan da suka gabace ta inganci. A wani bidiyo da Davido ya wallafa a shafinsa na Instagram a ranar Laraba, an ga lokacin...
Shugaban Majalisar Malamai ta Jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya gargadi masu yada labaran karya musamman a kafafen sada zumunta da su daina, domin Musulunci ya haramta hakan. Ya bayyana cewa a Musulunci, yada labaran karya daidai yake da yin karya, kuma addinin Musulunci yana tsananin kin masu karya. UNGA: Yau Shettima zai gabatar da jawabin Najeriya a MDD Kotun Indiya ta daure dan Najeriya shekara 10 kan safarar miyagun kwayoyi Sheikh Khalil ya fadi hakan ne a Kano a ranar Talata yayin wani taron horaswa na kwanaki biyu da aka shirya wa malamai da limamai kan yadda za a yaki labaran karya da kuma inganta fahimtar kafofin yada labarai, wanda kungiyar Alkalanci ta shirya, wata kungiya da ke tantance...
Kafar watsa laabrun Politico ta fitar da wani rahoto a jiya Talata wanda yake cewa, hukumar bincike ta ‘yan sandan Amurka ta sami bayanan sirri da su ka shafi muhimman matakan siyasa na gwamnatin Amurka da kuma masu alaka da makaman kare dangi. Majiyar ta ambaci cewa binciken da aka yi a ranar 22 ga watan Ogusta da ya shude ya sami bayanan da aka bayyana a matsayin “Na sirri’ matuka”. Kafar watsa labarun ta ” Politico” ta kuma ce bayan binciken ofishin bolton da a ka yi, da aka sami na’urar kwamfuta mai cike da bayanan sirri, an kuma kai wani samamen a gidansa dake Jahar Maryland, said ai kuma babu wani bayanai akan nau’oin abubuwan da aka samu...
Babban magatakardar malajisar koli ta tsaron kasar Iran Dr. Ali Larijani ya bayyana cewa; Batun sake kakabawa Iran takunkumi yana nuni da gajiyawar kasashen turai. Dr. Ali Larijani wanda tashar talabijin din al’mayadin’ta yi hira da shi, ya kara da cewa, matakin da kasashe uku na Faransa, Birtaniya da Jamus, su ka dauka akan batun sake kakabawa Iran takunkumi, yana sake yin nuni ne da tsohuwar gabar da kasashen turai da Amurka suke da ita akan al’ummar Iran. Haka nan kuma ya ce wannan tsohuwar gaba ta yi tasiri mai girma a cikin siyasar mulkin mallaka ta kasashen turai da yadda suke son Dannen sauran kasashe. Dr. Ali Larijani ya kuma ce, wanann irin kiyayya da siyasa tana cin karo...
HKI tana ci gaba da kai wa muhimman cibiyoyi da gidajen Falasdinawa a fadin Gaza. Majiyar Falasdinawa ta ce daga safiyar yau Laraba adadin wadanda su ka yi shahadar sun kai 45 sanadiyyar hare-haren da jiragen yakin ‘yan sahayoniyar su ka kai. Har ila yau an sami wasu Karin shahidan biyar a wuraren karbar agaji dake arewacin Rafaha. A wani labarin mai alaka da hakan shugaban hukumar lafiya ta duniya ( w.h.o) Tedross Adhanom ya ce; Kai hare-haren da ake yi a kusa da asibitin Rantisy, dake Gaza, ya yi sanadiyyar tsayuwar aikin Asibiti, domin rashin tsaro. Har ila yau ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta kara da cewa; Jinkirin shigar da makamashi zuwa yankin yana barazanar tsayar da aikin...
Kamfanin GTCO, mamallakin bankin GT, ya bayyana samun ribar Naira biliyan 601 a watanni shida na farkon shekarar 2025. Sai dai bankin ya ce duk da haka ribar tasa raguwa ta yi a kan ta Naira tiriliyan daya da ya ci a farkon shekarar da ta gabata. Kotun Indiya ta daure dan Najeriya shekara 10 kan safarar miyagun kwayoyi DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamata Wannan na kunshe ne a cikin sakamakon binciken kudi kamfanin ya fitar, wanda ya ƙare ranar 30 ga Yuni, 2025. Bankin ya kuma ce amma ribar kafin a cire haraji ce, idan aka cire kuma za ta koma biliyan 449.01, idan aka kwatanta da biliyan 905.57...
Jagoran juyin juya halin Musulunci a cikin jawabinsa ya bayyana cewa: Dangane da hadin kan al’ummar Iran, batu na farko shi ne cewa a lokacin yakin kwanaki goma sha biyu, hadin kai da hadin kan al’ummar Iran ya sanya makiya kunya. Jagoran ya jaddada cewa tun tsakiyar tsakiyar yakin makiya sun gane cewa ba za su cimma manufa da manufofin da suka cimma ba. A yammacin ranar Talatar da ta gabata a wani jawabi da ya gabatar ga al’ummar Iran, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa;“Na ga ya wajaba a wadannan kwanaki, a ranar shahadar shahidan Sayyid Hassan Nasrallah, a tuna da shi. Sayyed Hassan Nasrallah ya kasance wata babbar kadara ga duniyar Musulunci...
Ali Larijani, sakataren majalisar koli ta tsaron kasa, ya rubuta a daren Talata a wani sako da ya wallafa a dandalin sada zumunta na X:“Da farko dai Amurka ta fice daga JCPOA, sannan Turai ta kasa cika alkawuran da ta dauka, a karshe ma sun kai harin bama-bamai, yanzu haka jam’iyyu suna yin kamar su ne ake bi bashi.” A cewar Pars Today, Larijani ya kara da cewa Iran tana da tsayin daka wajen kare tsaron kasarta, kuma ba za ta bari a sanya wasu sharudda na wulakanci ba, kamar takunkuman da aka dora wa makamai masu linzami. Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran ya jaddada cewa kafa sharadin takaita iyaka da makamai masu linzami zuwa kasa da kilomita...
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya jaddada cewa: Iran ba za ta taba yin watsi da inganta uranium ba, kuma tattaunawa da Amurka za ta haifar da illa A jawabin da ya yi wa al’ummar Iran ta gidan talabijin a yammacin jiya Talata, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce: Ba za su mika wuya ga matsin lamba kan wani lamari na su ba. A cikin jawabinsa ta gidan talabijin ga al’ummar Iran a daren jiya, Jagoran ya taya al’ummar Iran murnar shigowar watan Mehr (23 ga watan Satumba, bisa kalandar Iran), da watan komawa makarantu da jami’o’i da ilmantarwa, da kuma shirin kaddamar da miliyoyin matasa a fadin kasar wajen samun ilimi da mulki. Wannan...
Shawarwari biyu na Turai da na Rasha suna gaban Iran, kuma za ta amince da duk wata mafita ta gaskiya da ke kiyaye muradunta Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Larijani, ya bayyana ikirarin cewa; Iran ba ta amincewa da tattaunawa, a matsayin “karya” ne, yana mai tunatar da cewa, Iran na cikin wani yanayi na tattaunawa ta fuskanci farmakin soji na wuce gona da iri. Larijani ya ce: Iran za ta amince da duk wata shawara mai ma’ana da adalci da za ta kiyaye muradunta, yana mai bayyana cewa, “Iran tana nazarin shawarwarin Turai da na Rasha da suka gabatar mata.” Larijani ya tabbatar da cewa: Iran ta amince da duk shawarwarin biyu a kan wasu sharudda,...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya tattauna da fira ministan Norway game da alakar kasashen biyu da ci gaban kasa da kasa Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi wanda ke ziyara a birnin New York domin halartar taron shekara shekara na Majalisar Dinkin Duniya ya gana da fira ministan kasar Norway Jonas Gahr Støre. A yayin ganawar da aka yi a ranar Talata, bangarorin biyu sun tattauna kan dangantakar da ke tsakanin kasashen Iran da Norway, tare da yin musayar ra’ayi kan ci gaban yankin da kasa da kasa. Taron dai ya yi tsokaci kan matsalar jin kai da Falasdinawa ke fuskanta daga sojojin mamayar Isra’ila sakamakon kisan kiyashin da ake ci gaba da yi a zirin Gaza da kuma...
Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ya sanar da cewa: Masu binciken hukumarsa suna kan hanyarsu ta zuwa Iran Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi ya bayyana cewa: Masu sa ido na hukumar IAEA na kan hanyarsu ta zuwa Iran. Rafael Grossi ya bayyana cewa: Masu sa ido na hukumar kula da makamashin nukiliya ta IAEA na kan hanyarsu ta zuwa Iran, amma shigarsu ta dogara ne da manufofin siyasar Iran. Ya ce: “Damar da suke da shi tana da kunci sosai, don haka tawagar hukumar IAEA tana da ‘yan sa’o’i kadan ko ‘yan kwanaki don sanin ko yarjejeniya da bangarorin biyu suka rattaba hannu a kai za...
A ɓangaren hukuncin Omitoye Rufus, an yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekaru 15. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rundunar ’yan sanda a Jihar Kano ta sanar da cafke wani mutum da ke yi mata sojan-gona yana yaudarar jama’a domin karɓar musu kuɗi. An cafke wanda ake zargin ne a ranar Lahadi, 21 ga Satumbar 2025 a yankin Kofar Dawanau, sanye da kayan ’yan sanda, wanda bayanai suka ce ya daɗe yana aika-aikar. An yi wa sojoji ɗaurin rai da rai kan sayar wa ’yan ta’adda makamai a Borno Sanata Natasha ta koma Majalisar Dattawa Sanawar da rundunar ta fitar ta bayyana cewe an kama shi ne bayan da jama’a suka shigar da ƙorafe-ƙorafe da dama game da ayyukan wasu da ke yin kutse da shigar ’yan sanda domin damfarar jama’a. Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa,...
Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya isa birnin New York na Amurka da yammacin jiya Litinin, don halartar babban taron mahawara na MDD karo na 80. Yayin da yake birnin na New York, Li zai halarci wasu jerin ayyuka da Sin ta tsara, ciki har da taron manyan jami’ai game da shawarar tsarin shugabancin duniya, kana zai gana da babban magatakardar MDD Antonio Guterres da shugabannin kasashe masu ruwa da tsaki. Yayin tarukan cudanyar mabanbantan sassa, da na bangaren Sin da daidaikun kasashen, Li zai yi karin haske dangane da mahangar kasar Sin game da yanayin da ake ciki a harkokin kasa da kasa a halin yanzu, da manyan batutuwa da ayyukan MDD. Zai kuma fayyace manufofin kasar Sin na...

Kuri’ar Jin Ra’ayoyi Ta CGTN: Guguwar Amincewa Da Kasar Falasdinu Ta Nuna Yadda Amurka Da Isra’ila Suka Zama Saniyar Waren Da Ba A Taba Gani Ba
Ya zuwa ranar 23 ga watan Satumba agogon Beijing, kasashe 152 cikin 193 na Majalisar Dinkin Duniya sun amince da Falasdinu a matsayin kasa. A cikin kasashe biyar masu kujerun dindindin a kwamitin sulhun MDD, Amurka ce kadai ba ta amince da kafuwar kasar Falasdinu ba. Wannan guguwar ta amincewa da kafuwar kasar Falasdinu ta sanya Amurka da Isra’ila sun zama saniyar ware a fannin diflomasiyya game da batun rikicin Falasdinu da Isra’ila. Wata kuri’ar jin ra’ayoyin jama’a da CGTN ta gudanar a duniya ta nuna cewa kashi 78.2 cikin 100 na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu sun yi imanin cewa, babbar hanyar warware matsalar Falasdinu ita ce aiwatar da shawarar “kafa kasashe biyu”, wadda kuma ita ce ginshikin samar da...
Wata Kotun Soji ta yanke wa wasu sojoji uku hukuncin ɗaurin rai da rai kan sayar da makamai da harsasai ba bisa ka’ida ba a Maiduguri, Jihar Borno. Kotun sojin ƙarƙashin jagorancin Birgediya-Janar Mohammed Abdullahi, ta bayyana cewa an yanke wa mutum uku daga cikin sojojin huɗu hukuncin ɗaurin rai da rai yayin da aka ɗaure mutum ɗaya shekaru 15 a gidan yari. Sanata Natasha ta koma Majalisar Dattawa Yarima Salman ya jagoranci jana’izar babban mai ba da fatawa na Saudiyya Sojojin da abin ya shafa sun haɗa da Raphael Ameh da Ejiga Musa masu muƙamin sajan, da kuma Patrick Ocheje mai muƙamin kofura. Binciken kotun ya nuna cewa Ameh ya karɓi sama da ₦500,000 daga harƙallar sayar da harsasai...
Wannan ne dai karo na farko da adadin gejin kuɗin ruwa ya yi ƙasa, wato mafi ƙaranci a cikin shekaru biyar. Gwamnan na CBN ya ce an yanke shawarar rage kuɗin ruwan ne domin ci gaba da bunkasuwar tattalin arzikin cikin gida (GDP), da karyewar hauhawar farashi, wanda tsawon watanni biyar kenan ana samu a jere. Tuni, dama masana suka yi hasashen cewa malejin tsadar rayuwa zai ƙara yin ƙasa sosai a sauran watannin ƙarshen 2025. Haka kuma wani dalilin rage kuɗin ruwan shi ne domin a ci gaba da ƙarfafa tattalin arziki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
Yarima mai jiran gado na Masarautar Saudiyya, Sheikh Muhammad bin Salman, ya jagoranci sallar jana’izar fitaccen malamin addini, Sheikh Abdulaziz bin Abdullah bin Muhammad Al-Sheikh. Shafin Inside Haramain ya ruwaito cewa an gudanar da jana’izar ce a Masallacin Imam Turki bin Abdullah da ke birnin Riyadh. CBN ya rage kuɗin ruwa zuwa kashi 27 cikin 100 Kotu ta hana NUPENG rufe Matatar Ɗangote Aminiya ta ruwaito cewa za a yi masa Salatul Ga’ib a Masallacin Harami na Makkah da kuma Masallacin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama da ke Madina. A wannan Talatar Allah Ya yi wa Babban Mai Ba da Fatawar na Saudiyya rasuwa yana da shekara 82. Fadar Masarautar ƙasar da kuma Shugaban Majalisar Malaman Masallata Haraman Makkah da...
Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae, zai gabatar da jawabi ga mutanen kasar Iran nan gaba kadan, saboda shigowar makin tsaro mai tsarki, inda ake saran zai tabo al-amura da suka shafi tsaron kasar da kuma siyasar kasa da kasa. Makon tsaro dai shi ne makon da aka fara yakin tsaron kasar mai tsari wanda ya zama masomin yakin tsaron na shekaru 8 tare da gwamnatin Ba’ath ta kasar Iran karkashin shugabancin Saddam Hussain a lokacin An fara yakin ne a ranar daya ga watan Mehr shekara 1359 wato a shekara 1980 har zuwa shekara 1988. Har’ila yau ana saran zai yi Magana kan sabbin al-amura da suke tasowa a cikin gida. Share...
Kwamitin da ke kula da tsare-tsare da manufofin kuɗi na Babban Bankin Najeriya (CBN) ya zaftare maki 60 daga nauyin kuɗin ruwa da ke kan masu karɓar basussuka. Wannan dai shi ne karo na farko cikin shekaru biyar da aka samu babban bankin ya yi rangwamin kuɗin ruwa a ƙasar. CBN ɗin ya ce kwamitin a wannan Talatar ya rage yawan kuɗin ruwan daga kashi 27.5 da yake karɓa a baya zuwa kashi 27 a yanzu. Mahara sun kashe ɗan sanda sun ɗauke bindigarsa a Taraba An yi garkuwa da ɗan Majalisar Dokokin Jihar Filato Gwamnan Babban Bankin, Olayemi Cardoso, ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai bayan kammala taron kwamitin karo na 302 da ya gudana a Abuja....
Allah Ya yi wa Babban Mai Ba da Fatawa na kasar Saudiyya, Sheikh Abdulaziz bin Abdullah bin Mohammed Al Al-Sheikh, rasuwa. Hukumomin ƙasar Saudiyya sun sanar da cewa Sheikh Abdulaziz bin Abdullah bin Mohammed Al Al-Sheikh ya rasu yana da shekara 82 a duniya. Fadar Masarautar ƙasar da kuma Shugaban Majalisar Malaman Masallata Haraman Makkah da Madina, Sheikh Abdul Rahman Sudais, sun gabatar da ta’aziyyar iyalai da ɗaliban mashahurin malamin. Za a gudanar da Sallar Jana’izarsa a Masallacin Imam Turki bin Abdullah da ke birnin Riyadh bayan Sallar La’asar. Kazalika za a yi masa Salatul Ga’iba a Masallacin Harami na Makkah da kuma Masallacin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama da ke Madina.
Shugaban kasar Afirka Ta kudu Cyril Ramaphosa da ya gabatar da jawabi a taron babban zauren MDD ya jaddada matsayar kasarsa na son ganin an bai wa al’ummar Falasdinu kasarsu akan iyakar 1967. Da yake Magana akan abinda yake faruwa yanzu a Gaza, shugaban kasar ta Afirka Ta Kudu ta caccaki HKI akan yadda take azabatar da al’ummar Falasdinu a dunkule. Haka nan kuma ya yi kira da a kawar da dukkanin abubuwan da suke kawo cikas wajen kafawa Falasdinawan kasar tasu. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks...
Majalisar Dokoki ta Kasa ta ɗage ranar dawowarta daga hutu zuwa 7 ga watan Oktoba, 2025. Karin bayani na tafe..
Rundunar ’Yan sandan Jihar Kebbi ta cafke wasu mutum huɗu a yankin Kamba da ke jihar, bisa zargin su da shigar da babura uku da suka saya daga Jamhuriyar Benin domin kai wa kungiyar ta’addanci ta Lakurawa. Haka kuma an kama wani Mubarak Ladan bayan ya yi tayin cin hancin naira dubu dari shida (₦600,000) ga DPO na Kamba, SP Bello Mohammad Lawal, domin a saki waɗanda aka kama. Kakakin rundunar ’yan sanda ta jihar, CSP Nafiu Abubakar, ya ce baburan da ake kira “Boko Haram” guda uku an saye su ne kan kudi naira miliyan 5 da dubu 400, kuma an tanadar da su ne domin kai wa kungiyar Lakurawa ta hannun wani Alhaji da ke a Kangiwa. Sanarwar...
Mohammad Eslami mataimakin shugaban kasar Iran kuma shugaban hukumar makamashin nukiliya na kasar Iran ya bayyana cewa Tehran da mosko za su rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniya akwanaki masu zuwa ta gina tashar nukiliya domin kara fadada alakarsu a wannan bangaren na makamashi. Wannan sanarwar tana zuwa ne adaidai lokacin da iran ke fuskantar matsin lamba kan shirinta na nukiliya na zaman lafiya ,bayan da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA ta kasa tabuka komai akan batun. Karkashin yarjejeniyar da aka cimma tsakani, kasar rasha za ta samar da riaktors guda 8 a cikin iran, hudu daga cikinsu za’a yi amfani da su a tashar ta ta bushahar ne. Yace an kammala komai game da Tattaunawa da...
Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya ayyana gobe Talata, a matsayin ranar ɗaya ga watan Rabi’ul Thani, 1447 bayan hijira, wanda ya kawo ƙarshen watan Rabi’ul Awwal, 1447, daidai da ranar 23 ga Satumba, 2025. Sanarwar ta fito ne a wata takarda da Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaid, wanda shi ne shugaban kwamitin da ke bai wa Majalisar Sarkin Musulmi shawara kan al’amuran addini, ya sanya wa hannu ya kuma raba wa manema labarai. A sanarwar, Sarkin Musulmi bai fayyace wuraren da aka ga sabon watan ba, sai dai ya bayyana cewa ya gamsu da sahihan rahotannin da aka gabatar, lamarin da ya sa ya ayyana ganin watan a hukumance. Ya yi addu’ar Allah Ya kawo zaman lafiya da...

Nau’o’in Jirage Uku Sun Kammala Sauka Da Tashin Farko Bisa Taimakon Majaujawar Maganadisu A Jirgin Dako Na Fujian Na Kasar Sin
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tawagar jami’an diflomasiyyan Falasɗinu ta gudanar da bikin ɗaga tutar ƙasar a Litinin ɗin nan a birnin Landan kamar yadda kafar labarai ta DW ta ruwaito. Bikin ɗaga tutar na zuwa ne kwana guda bayan da Birtaniya ta amince da Falasɗinu a matsayin kasa mai cin gashin kanta. CAC ta soma yi wa kamfanoni rijista da fasahar AI Dalilin da muke goyon bayan Tinubu kan karɓo bashi — Majalisar Wakilai Shugaban tawagar jami’an diflomasiyyan Falasdinawa a Burtaniya Husam Zomlot, ya daga wani allo mai ɗauke da rubutun ‘Ofishin jakadancin Falasɗinu’ sannan kuma ya ce nan ba da jimawa ba za a buɗe ofishin a hukumance bayan kammala wasu sharudda dangane da dokoki da kuma tsarin gudanarwa. Mista Zomlot ya yi...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi maraba da amincewar da kasashen Birtaniya, Australia, da Canada suka yi wa kasar Falasdinu, tana mai bayyana hakan a matsayin wani muhimmin mataki na tabbatar da hakkin al’ummar Palasdinu na kasarsu. A cikin wata sanarwa da ta fitar jiya Lahadi, kungiyar ta yi kira ga kasashen duniya da MDD da su mayar da Isra’ila saniyar ware tare da dakatar da duk wani nau’i na hadin gwiwa da ita. Hamas ta yaba da wannan amincewa da ita a matsayin wani muhimmin mataki na tabbatar da ikirarin da al’ummar Falastinu ke yi na neman kare filayensu da wuraren ibadarsu masu tsarki, tare da fatan samun kasa mai cin gashin kanta wacce take da Quds a...
Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, ta bayyana cewa “Kisan kare dangi da ake ci gaba da yi a zirin Gaza ya zama babban gwaji ga Majalisar Dinkin Duniya. Idan muna son kungiya mai inganci kuma mai amfani, dole ne mambobinta su dauki matakin gaggawa tare da tsayin daka wajen dakatar da wannan zalunci da hukunta masu laifi.” Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmail Baghai ya ce zasu hadu a birnin New York domin halartar taron shekara-shekara na Majalisar Dinkin Duniya. Wannan zaman dai na gudana ne a daidai lokacin da MDD ke bikin cika shekaru 80 da kafuwa, a daidai lokacin da muhimman ka’idojinta da manufofinta ke fuskantar barazanar da ba a taba ganin irinta ba da...
Iran ta yi Allah wadai da harin da aka kai kan wani masallaci a Sudan tare da yin kira da a kawo karshen hare-haren da ake kai wa fararen hula cikin gaggawa. Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi Allah-wadai da harin na baya-bayan nan da aka kai da jirage marasa matuka a wani masallaci a birnin Al-Fashir na kasar Sudan, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da jikkata wasu da dama da ba su ji ba ba su gani ba. A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, ma’aikatar harkokin wajen Iran ta kira harin a matsayin ” keta dokokin jin kai na kasa da kasa.” Ta kuma jaddada bukatar gaggauta dakatar da kai hare-hare kan...
Majalisar Wakilai ta bayyana cewa ta amince da duk wasu tsare-tsare da dabarun karɓo rancen kuɗaɗe na Shugaba Bola Tinubu, bisa la’akari da ƙoƙarin da yake yi na farfaɗo da tattalin arziki da kuma rage talauci a ƙasar nan. Shugaban Majalisar, Abbas Tajudeen ne ya bayyana hakan a yayin da yake jawabi ranar Litinin, a taron shekara-shekara karo na takwas kan bitar kasafin kuɗaɗe na majalisun dokokin nahiyyar Afirka (African Network of Parliamentary Budget Offices) da ke gudana a Abuja. Sarkin Ruman Katsina ya rasu Jariri ya mutu a bayan uwarsa yayin tsere wa ’yan bindiga a Neja Abbas ya ƙaryata raɗe-raɗin cewa majalisar ta ƙi amincewa da tsare-tsaren karɓo rance na shugaban ƙasar, inda ya ce zantuka ne marasa...
Majalisar Wakilai ta bayyana cewa ta amince da duk wasu tsare-tsare da dabarun karɓo rancen kuɗaɗe na Shugaba Bola Tinubu, bisa la’akari da ƙoƙarin da yake na farfaɗo da tattalin arziki da kuma rage talauci a ƙasar nan. Shugaban Majalisar, Abbas Tajudeen ne ya bayyana hakan a yayin da yake jawabi ranar Litinin, a taron shekara-shekara karo na takwas kan bitar kasafin kuɗaɗe na majalisun dokokin nahiyyar Afirka (African Network of Parliamentary Budget Offices) da ke gudana a Abuja. Sarkin Ruman Katsina ya rasu Jariri ya mutu a bayan uwarsa yayin tsere wa ’yan bindiga a Neja Abbas ya ƙaryata raɗe-raɗin cewa majalisar ta ƙi amincewa da tsare-tsaren karɓo rance na shugaban ƙasar, inda ya ce zantuka ne marasa tushe...
A yau Litinin Allah Ya yi wa Sarkin Ruman Katsina kuma Hakimin Batsari, Alhaji Tukur Ma’azu, rasuwa. Marigayin, wanda ya shafe shekaru 74 a duniya, ya daɗe yana fama da jinya gabanin rasuwarsa. Hisbah ta kama masu safarar mata zuwa Saudiyya a Kano Jariri ya mutu a bayan uwarsa yayin tsere wa ’yan bindiga a Neja Alhaji Tukur wanda ya shafe shekaru 43 yana riƙe da sarautar Hakimin Batsari, ya rasu ya bar mata biyu, ’ya’ya da kuma jikoki. Za a gudanar da jana’izarsa da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin yau a gidansa da ke cikin garin Batsari, kamar yadda sanarwa daga iyalansa ta tabbatar.
Kwamandan sojan Iran Amir Hatami wanda ya gana da kwamandan dakarun kare juyin musulunci Janar Muhammad Pakpour saboda tunawa da makon hadin kai, ya kara da cewa; Bayan cin nasarar juyin musulunci a Iran, Iran da al’ummarta sun fara aiki tukuru domin kare cikakken ‘yancin Iran.” Har ila yau, Amir Hatami ya yi ishara da hadin gwiwa a tsakanin sojojin da dakarun kare juyin juya halin yana a matsayin ginshikin tsaron kasar Iran, kuma wata kofa ta kai wa mataki na koli na tsaro. A gefe daya dakarun kare juyin musulunci ( irgc) sun jaddada matsayarsu ta ci gaba da zama cikin Shirin fuskantar abokan gaba. A cikin wata sanarwa da suka fitar a farkon makon tsaro mai alfarma, na...
Shugaban kasar Korea Ta Arewa Kim jung Un ne ya sanar da cewa kasarsa ta kera wani sabon makami na sirri, kuma ta samu ci gaba sosai a fagen nazari da binciken kayan tsaro. Shugaban kasar ta Korea Ta Arewa Kim Jun Ung wanda ya yi Magana da kamfanin dillancin labarun kasar ya kara da cewa; Sabbin makaman da su ka kera za su taimaka matuka wajen karfafa sojojin kasar.” Haka nan kuma ya ce, kasar Korea ta Arewa ta kuma karfafa sojojinta na ruwa ta hanyar kara samar da jiragen ruwa na yaki masu ninkaya a karkashin ruwa.” Kamfanin dillancin labarun Korea Ta Arewa ya sanar da cewa, a ranar Juma’ar da ta gabata ne shugaban kasar Kim Jun...
Matsalar tsaro san rufe kasuwannin shanu a yankin Kwara ta Kudu da kuma ɗauke sansanin masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) da ke Yikpata, Ƙaramar Hukumar Edu an mayar da ita zuwa Ilorin, hedikwatar jihar. Ƙananan hukumomin biyu na Kwara ta Kudu da arewacin jihar na daga cikin wuraren da matsalolin tsaro suka fi taɓarɓarewa duk da ƙoƙarin gwamnati da hukumomin tsaro. Rufe kasuwannin dabbobi Sanarwar farko ta fito daga Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomi bakwai na Kwara ta Kudu, inda suka bayar da umarnin rufe duk kasuwannin Kara a yankin. Shugabannin —Abdulrasheed Yusuf (Ifelodun), Benjamin Jolayemi (Isin), Azeez Yakub (Irepodun), Awelewa Gabriel (Ekiti), James Fadipe (Oke-Ero), Sulyman Olatunji (Offa), da Akanbi Olarewaju (Oyun)— sun ce matakin ya zama dole don...

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Jinjinawa Tawagar Kokawar Greco-Roma Ta Iran Murnar Lashe Gasar Cin Kofin Duniya
Jagoran juyin juya halin Musulunci yana taya tawagar kokawa ta Greco-Roma ta Iran murnar lashe gasar cin kofin duniya Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya taya tawagar kokawa ta Greco-Roman ta kasar Iran murnar nasarar da ta samu a gasar cin kofin duniya, yana mai godiya ga ‘yan wasa da masu horar da ‘yan wasa da masu gudanarwa da suka sanya farin ciki a zukatan al’ummar Iran da kuma abin alfahari ga kasar Iran. A cikin sakon nasa, Jagoran ya ce: Ina taya matasan kokawa murna. Ƙudurin ku da himma a cikin kokawa na Greco-Roman sun kawo farin ciki ga zukatan mutane da kuma alfahari ga ƙasar. Ina rokon Allah Ya ba ku daukaka da nasara,...

Pezeshkian: Kasashen Da Ba Su Cika Alkawura Da Suka Dauka Ba Suke Zargin Iran Kan Rashin Mutanta Yarjejeniyar Nukiliya
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Kasashen da ba su cika alkawuran da suka dauka ba suke zargin Iran da rashin mutunta yarjejeniyar makamashin nukiliya Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Kasashen da ba su cika alkawuran da suka dauka ba, a yanzu suke zargin Iran da kin mutunta yarjejeniyar makamashin nukiliyar. A cikin wata hira da gidan talabijin na CCTV na kasar China, Pezeshkian ya ce, “Suna sa ran za a aiwatar da yarjejeniyar manyan tsare-tsare na shekaru 25 da aka tsara a baya tsakanin Iran da China.” Pezeshkian ya yi ishara da gazawar Amurka da kasashen Turai wajen cika alkawuran da suka dauka karkashin yarjejeniyar makamashin nukiliya, yana mai cewa, a yau kasashen da ba su...
Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci na Iran sun bayyana cewa: Duk wani sabon kuskuren lissafin makiya zai fuskanci mayar da martani mai muni A cikin wata sanarwa da suka fitar a farkon makon tsaro mai alfarma, na ranar tunawa da arangama da gwamnatin Saddam ta yi da Jamhuriyar Musulunci ta Iran a tsakanin shekarun 1980-1988, dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) sun jaddada cewa: Duk wani sabon kuskuren lissafi da makiya za su yi, za su fuskanci mummunan martani da zai zame babban darasi a gare su. A cikin bayanin da suka yi na farkon makon tsaro na dakarun IRGC sun bayyana cewa: A hakikanin gaskiya makon tsaro, biki ne na nasarar gwagwarmayar jama’a, kuma abin...

Kungiyar Ansarullahi Ta Yemen: ‘Yan Koren Amurka Da Isra’ila Suke Neman Wargaza Hadin Kan Larabawa Da Na Musulmi
Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya jaddada cewa: ‘Yan koren Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila na da nufin wargaza hadin kan Larabawa da na Musulmi Jagoran kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen Sayyed Abdulmalik al-Houthi ya jaddada cewa: ‘Yan koren Amurka da na haramtacciyar kasar Isra’ila suna neman tada fitina da sanya kiyayya a tsakanin al’ummomin Larabawa da na Musulmi. Ya yi nuni da cewa wadannan ‘yan kore ba su da wani aiki na gaske da zai yi hidima ga kasashensu na asali, sai dai mayar da hankali kan kokarinsu wajen wargaza zamantakewar al’umma, karkashin kulawar Amurka da tallafin Larabawa da kuma jagorancin yahudawan sahayoniyya. A cikin jawabin da ya gabatar a jiya Lahadi, a daidai lokacin da ake gudanar...
Sojojin mamayar Isra’ila sun kai hari kan fararen hula, inda suka kashe mutane 5 da suka hada da yara 3 a kudancin kasar Lebanon Ma’aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta sanar da mutuwar wasu ‘yan kasar 5 da suka hada da yara uku sakamakon wani hari da jiragen saman yakin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai a kudancin birnin Bint Jabeil. Kamfanin dillancin labaran kasar Lebanon ya watsa rahoton cewa: Wani jirgin sama mara matuki na makiya yahudawan sahayoniyya ya kai hari kan wani babur da wata mota dauke da makamai masu linzami a garin Bint Jabeil, lamarin da ya yi sanadin mutuwa da jikkata. Wannan harin wuce gona da iri ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin mamayar Isra’ila...
Ministan harkokin wajen Falasdinawa Varsen Aghabekian Shahin, ta godewa kasashen duniya da suka amince da samuwar kasar Falasdinu ya zuwa yanzu kuma kuma wadanda suke shirin yinhaka, sannan tana kodaitar da sauran kasashen duniya da su yi hakan. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shahin tana fadar haka a taron yan jarida da ta kira a yau Lahadi a birnin Ramallah, sannan ta kara da cewa ya zuwa yanzu kasashe da dama sun bayyana amincewarsu da kasar Falasdinu, Kuma sakone mai kyau ga Falasdinwa, kuma banda haka wannan sakonnin fata ne na samuwar kasar Falasdinu mai zaman kanta. Ta kara da cewa, amincewa da kasar Falasdinu mai zaman kanta yana nufin HKI bata da iko a kanta....
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bar Abuja zuwa birnin New York na Ƙasar Amurka, domin halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80. Taron zai gudana daga ranar Litinin, 22 ga watan Satumba, zuwa ranar Lahadi, 28 ga watan Satumba, 2025. Birtaniya za ta amince da ƙasar Falasɗinu Jami’ar European-American ta musanta bai wa Rarara digirin girmamawa Shettima zai wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a wannan babban taro. Zai gabatar da jawabi, tare da shiga muhawarar shugabannin ƙasashe a zauren taron. A yayin taron, Mataimakin Shugaban zai kuma bayyana sabbin muradun Najeriya a ƙarƙashin yarjejeniyar kare muhalli. Wannan zai gudana ne a wani taro na musamman kan sauyin yanayi da Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya zai shirya a...
Ƙaramar Hukumar Gombe, ta raba wa mata masu juna guda 400 kayan haihuwa kyauta, domin kare lafiyarsu da rage mace-mace a yankin. An gudanar da rabon ne a Cibiyar Haihuwa ta Gombe a ranar Alhamis, inda shugaban Ƙaramar Hukumar, Barista Sani Ahmad Haruna, ya jagoranci rabon. Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 4, 16 sun jikkata a Yobe Gwamnan Gombe ya bai wa maharba kyautar motoci da babura don bunƙasa tsaro Shugaban ya ce shirin ya yi daidai da umarnin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, na bunƙasa kiwon lafiya a matakin farko, musamman ga mata masu juna biyu daga lokacin ɗaukar ciki har zuwa haihuwa. Ya kuma bayyana cewa an fara gwajin jini kyauta ga mata masu juna biyu a dukkanin...
Aƙalla mutum ne sun rasu, yayin da wasu 16 suka jikkata a wani hatsarin mota da ya auku a Ƙaramar Hukumar Karasuwa, a Jihar Yobe. Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Yobe, SP Dungus Abdulkareem ne, ya tabbatar da faruwar hatsarin ya faru a ranar Asabar da misalin ƙarfe 2:50 na rana a ƙauyen Zangon Kanwa. Gwamnan Gombe ya bai wa maharba kyautar motoci da babura don bunƙasa tsaro An sanya tukwicin N10m domin kama makasan limamin coci a Enugu Hatsarin ya rutsa da mota ƙirar Toyota Hiace wadda ke ɗauke da fasinjoji daga Jakusko zuwa kasuwar Jajimaji da kuma mota ƙirar Volvo daga garin Azare. Rahoto ya nuna cewa mota ƙirar bas ce ta ƙwace ta buga wani Keke Napep...
Kasashen Pakistan da Iran suna shirin fadada dangantakar tattalin arzikin da ke tsakanin daga dalar Amurka biliyon $3 a ko wace shekara zuwa dalar Amurka billion $10. plan to expand bilateral trade from its current level of just over $3 billion to an ambitious $10 billion. Tashar talabijan ta Presstv a nan ta nakalto bangarorin biyu na fadar haka ne a yau Lahadi, a taron kwamitin tattalin arziki na hadin giwa tsakanin kasashen biyu karo na 22nd da aka gudanar a nan Tehran. Labarin ya kara da cewa, kasashen biyu sun amince da cewa, halin da harkokin tattalin arziki tsakanin sub a na gaskiya bane, tunda a kwai bangarori da dama dabasu taba ba, ko kuma yi magana a kansu...
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bukaci kasar Agfanistan ta mayarwa kasar Amurka san sanin sojojin sama na kasar wanda ke Bagram ko kuma zata ga ba dadi. Kafanin dillancin labaran tasnim na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka da farko a shafinsa na zumunta na ‘ Truth Social’. Shugaban ya gargadi Taliban kan vewa idan sun ki mayarwa Amurka sansanin sojojin Bagram to wani abu ba dadi zai faru da sun. Trump ya dade yana zargin gwamnatin shugaba Biden da ya gada da yin ba dai-dai ba, daga ciki har da ficewa daga kasar Afganistan bayan mamaya na tsawon shekaru 20 ba tare da shiri ba. Amurka ta mamaye kasar Afganistan tun shekara 2001 har zuwa 2022...
Firay ministan kasar Burtaniya da tokwarorinsa na kasashen Canada da Australia duk sun bayyana amincewar gwamnatocinsu da samuwar kasar Falasdinu mai zaman kanta. Wanda ya nuna sauyi babba a al-amuran diblomasiyya wadanda suka sha fi HKI da kuma Falasdinawa. Kafin haka dai, idan an masu maganar samar da kasar Falasdinu sai suce sun barwa HKI ta tattunawa da Falasdinawa don warware matsalar tsakaninsu. Sauya matsayinda wadan nan manya-manyan kasashen duniya suka yi ya sake bude batun samar da kasashe biyu, wanda kuma zai kara tura HKI zuwa bongo don amincewa da samar kasar Falasdinu da kuma bukatar ta dai kissan kiyashin da takewa al-ummar Falasdinu a Gaz da kuma yankin yamma da kogin Jordan. Kafin haka Falasdinawa sun bukaci kasashen...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa tattalin arzikin kasar Iran nan gaba zai ginu ne bisa shirin bayan karewar man fetur ne, inda fasahohi da ilmi da kirkire-kirkire da kuma darussan da za’a dauko daga kasashe kawayen kasar a kungiyoyin BRICS da kuma SCO ne zasu zama abin dogaru. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya nakalto shugaban yana fadar haka ne a daren jiya Asabar a wani taro wanda yake magana a kan hanyoyin da Iran zata bi don bunkasa fasaha da ilmin kere-keren kasar da samar da ci gaba masu dorewa a kasar. Pezeshkiya yace sauye-suyen da sauri da ake samu a duniya musamman a yankin tekun fariya sun sanya dabarbarun ci gaba na sauyawa...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya bai wa ƙungiyar maharba ta ƙasa (PROHAN) reshen Gombe, kyautar motoci Hilux guda biyu da kuma babura guda biyar domin taimaka musu wajen yaƙi da ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane. An miƙa wa shugaban ƙungiyar, Rabiu Baushe (Baushen Gombe) kyautar, wanda yana cikin shirin gwamnatin na ƙara bunƙasa tsaro da bayar da kyautar kayan aiki don kare rayuka da dukiyoyin jama’a. ’Yan sanda sun kama mutane 5 kan zargin satar abincin yara a Borno Birtaniya za ta amince da ƙasar Falasɗinu Gwamna Inuwa ya ce: “Tsaro shi ne ginshiƙin ci gaban al’umma. Ba za mu samu ci gaba, ba tare da zaman lafiya ba. “Gwamnatina za ta ci gaba da tallafa...
Sabo da irin mawuyacin halin da ake ciki ta fannin tsarin jagorancin duniya musamman a daidai wannan lokaci, ya sa shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar inganta tsarin jagorancin duniya a kwanakin baya, shawarar da ta yi nuni da cewa, ya kamata a tsaya tsayin daka a kan kin yarda da daukar matakai na kashin kai, tare da kiyaye matsayin MDD, don ta taka rawar da ba wanda zai iya maye gurbinta a cikin tsarin jagorancin duniya. Lallai kasar Sin ta gabatar da shawarar, musamman don neman dakile ayyukan nuna fin karfi da ake fama da su a duniya, tare da samar da mafita ga kasa da kasa da suka shiga duhu. A sati mai zuwa, za...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta kama mutum biyar da ake zargi da satar fakiti 7,871 na abincin yara, wanda aka fi sani da Tamuwa, wanda aka tanada don yara masu fama da cutar yunwa. Kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar 19 ga Satumba, 2025 . Ya bayyana cewa an gano kayan ne a samame guda biyu da aka kai a Maiduguri. Shettima ya bar Abuja don halartar taron majalisar ɗinkin duniya a New York An sanya tukwicin N10m domin kama makasan limamin coci a Enugu Samamen farko ya auku ne a ranar 12 ga Afrilu, lokacin da aka tsayar da wata mota a Njimtilo, kusa da Maiduguri, inda...
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bar Abuja zuwa birnin New York na Ƙasar Amurka, domin halartar taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80. Taron zai gudana daga ranar Litinin, 22 ga watan Satumba, zuwa ranar Lahadi, 28 ga watan Satumba, 2025. Birtaniya za ta amince da ƙasar Falasɗinu Jami’ar European-American ta musanta bai wa Rarara digirin girmamawa Shettima zai wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a wannan babban taro. Zai gabatar da jawabi, tare da shiga muhawarar shugabannin ƙasashe a zauren taron. A yayin taron, Mataimakin Shugaban zai kuma bayyana sabbin muradun Najeriya a ƙarƙashin yarjejeniyar kare muhalli. Wannan zai gudana ne a wani taro na musamman kan sauyin yanayi da Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya zai shirya a...
A cewar Atiku, wannan kalmomi (ƙabilanci da yanki) an tanade su ne don raba kan jama’a da nufin cimma burinsu na siyasa ta hanyar roƙon ’yan ƙabilarsu da kada su zaɓi wani ɗan takara wanda ya fito daga wata ƙabila’ maimakon tantance shi da kyawawan halayensa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ƙasar Birtaniya a wannan Lahadin za ta amince a hukumance da kafa ƙasar Falasɗinu a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta. Birtaniya wadda ta daɗe tana goyon bayan Isra’ila za ta juya mata baya, sakamakon hare-haren da Isra’ilar take kai wa Zirin Gaza, wanda ya samo asali bayan da ƙungiyar Hamas ta kai wani mummunan hari a ranar 7 ga watan Oktoban 2023. Jami’ar European-American ta musanta bai wa Rarara digirin girmamawa An sanya tukwicin N10m domin kama makasan limamin coci a Enugu Tun a watan Yulin wannan shekarar Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya ce zai goyi kafa ƙasar Falasɗinu yana mai gindaya wa Isra’ilar sharaɗin yanke wannan shawarar. Starmer ya ce zai amince da ƙasar Falasɗinu muddin Isra’ilar ba...
Ministan harkokin wajen Iran ya kore abinda wasu kafafen watsa labaru su ka watsa na zantawa a tsakaninsa da manzon Amurka a gabas ta tsakiya Steven Witkoff. Ministan harkokin wajen na Iran, Abbas Arakci ya fada wa kamfanin dillancin labarun “Tasnim” na Iran cewa; Babu gaskiya a cikin labarun da wasu kafafen watsa labaru su ka watsa.” Ministan harkokin wajen na Iran ya kuma ce; Da akwai tuntubar juna a tsakanin Tehran da Washington kodai ta kai tsaye ta hanyar wasiku, ko kuma ta hanyar masu shiga Tsakani idan bukatar hakan ta taso.” Wasu kafafen watsa labarun kasashen turai ne dai su ka watsa labarin dake cewa; Ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya gana da manzon musamman na Amurka...
Kungiyar Hizbullah ta fitar da wata sanarwa ta gayyata domin halartar taron tunawa da zagayowar ranar shahadar Sayyid Hassan Nasrallah wanda za yi a ranar 27 ga watan nan na Satumba. Tunawa da Shahid Sayyid Hassan Nasrallah da sauran wadanda su ka yi shahada a lokacin, kamar su Shahid Sayyid Hashim Safiyuddin, zai kasance a wani gagarumin taro a birnin Beirut da kuma sauran garuruwan Lebanon a ranar 27 ga watan Satumba da misalin karfe: 4;30. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hamas...
Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas ta bayyana cewa, laifukan da HKI take tafkawa akan jami’an kiwon lafiya suna da bukatar duniya ta yunkura cikin gaggawa. A wata sanarwa da kungiyar ta Hamas ta fitar a jiya Asabar wacce ta kunshi wannan bayanin ta kuma ce; Sojojin mamaya suna ci gaba da rusa sauran cibiyoyin kiwon lafiya da su ka saura a yankin Gaza,haka nan kuma kai wa likitoci da ma’aikatan kiwon lafiya hari. Kungiyar ta Hamas ta bayyana abinda HKI take yi a karkashin ci gaba da rusa duk wani abu mai amfani a yankin Gaza. Wani sashe na sanarwar kungiyar ta Hamas ya kuma ambaci cewa; Ya zuwa yanzu adadin likitoci da ma’aiaktan kiwon lafiya da HKI ta kashe...
A wata sanarwa da dakarun kare juyin juya halin musulunci ta Iran ta fitar a jiya Asabar ya ce; Abinda ya faru a lokacin yakin tsaron kasa mai tsarki na farko da na biyu, mayar da martanin Iran ya haifar da sakamako mai karfi wanda aiki ne na tsawon lokaci. Haka nan kuma sanarwar ta ce, duk wani sabon kuskure da abokan gaba za su yi na kawo wa Iran hari, to jamhuriyar musulunci ta Iran za ta sami fifiko akansu a fagen daga, domin martaninta zai zama mai tsanani. Dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran sun kuma bayyana makon tsaron kasa mai tsarki na tunawa da yake-yaken da aka kallafawa Iran, a matsayin daya daga cikin lokuta...
A ɓangare ɗaya kuma Turkiyya na ƙara nuna damuwa bayan harin da Isra’ila ta kai a birnin Doha. Mai magana da yawun ma’aikatar tsaro ta Turkiyya, Rear Admiral Zeki Akturk ya yi gargaɗin cewa “Isra’ila za ta iya faɗaɗa hare-harenta baya ga Ƙatar. Za ta iya ingiza yankin baki ɗaya cikin bala’i.” Mece ce shawarar da Masar ta bayar? Shawarar da Masar ta bayar ya ƙunshi samar da tsarin haɗe ayyukan sojin ƙasa da na sama da cibiyoyin tsaro, tare da haɗe cibiyoyin horaswa da ayyukan soji. Haka nan kuma ƙasashen ne za su yanke hukunci kafin amfani da dakarun bayan tattaunawa a tsakaninsu. Kafar yaɗa labarai ta Al Akhbar da ke Lebanon ta ce a ƙarƙashin tsarin, Masar ta...
Gwamnatin yahudwan sahuniya ta kaddamar da hari da makami mai linzami kan wata motar hawa a layin Nabatiya- marjiyun dake khardali a kudancin labanon a ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da buda wuta da aka cimma tun 27 ga watan nuwamba na shekara ta 2024. Wannan hari wani bangare ne na kata yarjejeniyar da bangarorin biyu suka cimma, da hakan ya jawo mutuwar daruruwan mutane kuma ke kara jawo zaman dar-dar yankunan dake iyakar kasar da kuma HKI. Rahotanni da kafafen yada labarai na kasar labanon suka fitar ya nuna cewa wadannan hare haren wani nau’I ne na keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma , da kuma ci gaba da wuce gona da iri a yankin...
Shugaban kasar Iran Masud pezishkiyan ya bayyana cewa Iran ba za ta mika wuya ga bukatun da suka wuce kima ba, kuma za ta iya shawo kan duk wani takunkumi da aka kakaba mata, Shugaban ya fadi haka ne a wajen bukin karrama yan kasar da suka samu lambobin yabo a gasar Olympic ta kimiyya ta duniya , bayan da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya kada kuriar amincewa da kudurin dawo da takunkumi dake da alaka da shirinta na nukiliya. Haka zalika shugaban kasar yace makiya suna iya kai hari kan sakamakon binciken fasaha da aka yi, amma kwararru da masana ilimin kimiya wadanda suka samar da wadannan naurorin su ne hakikanin gaskiyar dukiya ga kasarmu, don haka...
Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin, ta ce matsayin Sin dangane da batun kamfanin TikTok a bayyane yake, kuma tana jaddada aniyar gwamnatin kasar na martaba hakkokin kamfanoni yadda ya makata. Ma’aikatar ta ce Sin na maraba da matakin gudanar da shawarwari da kamfanoni bisa doron dokokin kasuwa, ta yadda za a iya kaiwa ga shawo kan matsaloli daidai da dokokin kasar Sin, da ka’idoji, da daidaita moriyar dukkanin sassa masu takaddama. Ma’aikatar ta ce Sin na fatan Amurka za ta dauki makamancin wannan tafarki, ta cika alkawuran da ta dauka, da samar da wata kafa ta adalci, marar nuna wariya, kuma ta bunkasa muhallin kasuwanci ga kamfanonin kasar Sin, ciki har da kamfanin TikTok, ta yadda zai ci gaba da...
Kamfanin dillancin labaran Nijeriya ya bayar da rahoton cewa, lamarin wanda ya faru ne a lokacin da ake gudanar da aikin a ƙarshen mako a masana’antar, ya yi sanadin mutuwar ma’aikata biyu ciki har da wani jami’in soji da ke aiki tare da jikkata wasu huɗu. “Na ji wani babban ƙara har sai da ya girgiza gine-ginen da ke kewayen DICON. Mutane na ta gudu daga wurin, amma muna tunanin fashewar bam ne, amma daga baya mun gano cewa daga masana’anta ne,” inji wani mazaunin da ya nemi a sakaya sunansa. Shaidun gani da ido sun ce fashewar na da nasaba da samar da hoda mai matukar muhimmanci wajen ƙera hodar harsashi ga sojojin Nijeriya. Daga...
A kwanan nan ne aka rufe taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ko SCO a takaice, a birnin Tianjin dake arewacin kasar Sin, inda shugaban kasar, Xi Jinping ya gabatar da shawarar tsarin inganta jagorancin duniya. Wakiliyar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, ta zanta da shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, wanda ya halarci taron, inda ya ce, ana amfani da ma’aunai biyu a halin yanzu a duk duniya. A cikin shawarar tsarin inganta jagorancin duniya da shugaba Xi Jinping ya gabatar, akwai wani muhimmin bangare na gudanar da harkokin duniya bisa dokokin kasa da kasa, wato ya kamata a mutunta ka’idoji. Masoud Pezeshkian, ya ce bai kamata a aiwatar da ma’aunai biyu a...
Iran ta yi gargadin cewa za ta kawo karshen duk wata yarjejeniyarta da hukuar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, muddin ake sake dawo mata takunkuman MDD. Kwamitin koli na tsaron kasar Iran ya ce Tehran za ta dakatar da hadin gwiwar da take yi da Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) bayan da Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri’ar dage takunkumin da aka kakabawa Tehran na dindindin. A cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Asabar, babban jami’in tsaron kasar Iran ya yi Allah wadai da matakin “marasa hankali” da Birtaniya, Faransa, da Jamus –wanda aka fi sani da E3– game da shirin nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran cikin lumana Mataimakin ministan shari’a da...

Spain za ta hada kai da kotun ICC domin gudanar da bincike kan laifukan da Isra’ila ta aikata a Gaza
Tsarin shari’a na kasar Spain zai hada kai da kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa da kotun duniya domin binciken laifukan yaki da Isra’ila ta aikata a zirin Gaza.” Wannan yunkurin “ya mayar da martani ga shawarar rahoton kwamitin bincike na Majalisar Ɗinkin Duniya mai zaman kansa (IOC) kan yankin Falasɗinawa da aka mamaye, wanda ya bukaci bangarorin Amurka su ba da hadin kai ga binciken da ofishin mai shigar da kara na kotunan manyan laifuka ta kasa da kasa.” Za a sanar da sakamakon binciken ga kotun kasa da kasa da kuma ofishin mai gabatar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya. ministan harkokin cikin gida na Spain, Fernando Grande-Marlaska, ya goyi bayan matakin shari’ar...
Bayanai daga Falasdinu na nuni da cewa akalla Falasdinawa 47 ne sukayi shahada a ranar Asabar din nan a hare-haren da Isra’ila ta kai ta sama da jiragen yaki a Gaza yayin da sojojin suka sabunta bukata ga mazauna birnin da su fice daga birnin su koma kudu. A wani labarin kuma harin da Isra’ila ta kai ta sama ya kashe Falasdinawa takwas a Gaza, ciki har da yara biyu ,a cewar hukumomin lafiya. Wata majiyar lafiya ta shaida wa kamfanin dilancin labaren Anadolu cewa, yara biyu ne suka mutu a lokacin da jiragen yakin Isra’ila suka yi ruwan bama-bamai a makarantar Al-Mu’tasim a kusa da filin wasa na Yarmouk da ke birnin Gaza. Haka zalika wani bafalasdine ya mutu...
Sama da mako uku da suka gabata, wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da wani magidanci da matarsa mai juna biyu da kuma ’yarsu a unguwar Kanada da ke Ƙofar Ƙaura a garin Katsina. Masu garkuwar sun fara neman a biya su naira miliyan 100 kafin su sako su, amma daga baya aka daidaita da su a kan naira miliyan 50. Mahaifin Halimatu, Alhaji Ali Turare, ya tabbatar da biyan kuɗin kafin a sako ’yarsa da mijinta da jikarsa. “Bayan kwana uku da biyan kuɗin ne suka kira mu ta waya, suka ce an sako su, a je a karɓe su a Gurbin Ɓaure. Yanzu haka duk suna asibiti ana duba lafiyarsu,” in ji shi. Sai dai har zuwa lokacin...
Sama da mako uku da suka gabata, wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da wani magidanci da matarsa mai juna biyu da kuma ’yarsu a unguwar Kanada da ke Ƙofar Ƙaura a garin Katsina. Masu garkuwar sun fara neman a biya su naira miliyan 100 kafin su sako su, amma daga baya aka daidaita da su a kan naira miliyan 50. Mahaifin Halimatu, Alhaji Ali Turare, ya tabbatar da biyan kuɗin kafin a sako ’yarsa da mijinta da jikarsa. “Bayan kwana uku da biyan kuɗin ne suka kira mu ta waya, suka ce an sako su, a je a karɓe su a Gurbin Ɓaure. Yanzu haka duk suna asibiti ana duba lafiyarsu,” in ji shi. Sai dai har zuwa lokacin...
Mutum tara sun rasu a wani hatsarin jirgin ruwa da ya auku a ƙauyen Zalla Bango, da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Birni, a Jihar Sakkwato. Wani mazaunin yankin ya ce hatsarin ya faru ne bayan sallar Magariba a ranar Alhamis, lokacin da jirgin da ya ɗauki mata, maza da yara, domin tsallaka ruwa saboda hanyar mota ta yanke sakamakon ambaliya. Wata mata ta haifi ’ya’ya huɗu a Bauchi Kwalara ta kashe mutane 58, wasu sun kamu a Bauchi Yayin da yake tafiya, jirgin ya bugi wata ƙaramar gada ta nutse a ruwa, lamarin da ya jawo mutuwar mutum tara, yayin da wasu suka samu rauni. Rahotanni sun ce ba a san adadin mutanen da ke cikin jirgin ba saboda ya...
Wata mata ta haifi jarirai huɗu — maza biyu da mata biyu — a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Tarayya ta Kimiyyar Kiwon Lafiya (FUHSTHA) da ke Azare, a ranar Alhamis, 18 ga Satumba, 2025. Sakataren yaɗa labarai na asibitin, Abdu Mohammed, ya shaida wa Aminiya cewa Malama Hauwa ta haifi yaran ne ta hanyar tiyata, kuma tana ci gaba da jinya tare da ’yan huɗun. A washegarin haihuwar, Hajiya Halima Garba, matar shugaban asibitin (CMD), ta ziyarci mai jegon tare da mijinta da manyan ma’aikatan asibitin. Ta taya iyalan murna tare da addu’ar samun lafiya cikin gaggawa. ’Yan bindiga sun kashe basarake, sun tarwatsa mutane a Sakkwato Kwalara ta kashe mutane 58, wasu sun kamu a Bauchi Kamar yadda ta...
Kididdigar da aka fitar akan adadin Falasdinawan da su ka yi shahada da kuma jikkata sun haura 230,000,wanda ya faro tun daga watan oktoba 2023. Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ce ta fitar da wannan kididdigar a jiya Juma’a, sannan kuma ta bayyana cewa an kara samin wani adadi mai yawa na shahidai a cikin sa’oi 24, yayin da wasu 146 su ka jikkata. Ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza din ta kuma bayyana cewa; Da akwai ma’aikatan agaji da suke aiki tukuru domin fito da shahidan da suke kwance a karkashin baraguzai. A fagen yunwa da take ci gaba da daukar rayukan mutanen Gaza kuwa, ma’aikatar kiwon lafiyar ta Gaza, ta ce, an sami Karin wasu shahidai 4 da yunwa...
Sheikh Na’im Kassima wanda ya gabatar da jawabi a jiya juma’a ya kuma kara da cewa; A halin yanzu kungiyar gwagwarmaya tana fuskantar matsanancin yanayi mai hatsari,tare da jaddada cewa; Wanzuwar HKI, manufarsa ita ce a samar da wani yanki na turai da Amurka a cikin wannan yankin domin hana al’ummar yankin ci gaba da bunkasa ta fuskokin ttatalin arzki, siyasa da al’adu da ci gaba. Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya kira yi kasar Saudiyya da ta bude sabon shafin alakarta da kungiyoyin gwagwarmaya. Har ila yau Sheikh Na’im Kassim ya ce, HKI wani makami ne na kasashen turai da aikinsa shi ne yin kisan kare dangi akan duk wanda ya ki yin biyayya a gare su....
Ukraine ta ce Rasha ta kai sabbin hare-haren makamai masu linzami da na jirage marasa matuka wasu yankuna da dama na kasar cikin dare. A gabashin birnin Dnipro, an kai hari kan wani gini kuma an ji ƙarar fashewar wasu abubuwa a Zaporizhzhia kusa da tungar da ke zaman iyakar dakarun Rasha da na Ukraine din. A kudancin ƙasar ma, hukumomi a Mykolaiv sun bayar da rahoton tashin gobara bayan harin da aka kai kan wasu masana’antu. Yankunan yammacin Lviv da Ivano-Frankivsk ma sun fuskanci gobara sakamakon hare-haren da aka kai masu. Suna kusa da iyakar Poland, inda sojoji suka ce sun tura jiragen sama domin tabbatar da tsaron sararin samaniyar yankin.
An shawarci Musulmi da su yi koyi da kyawawan halaye na tawali’u kamar yadda Annabi Muhammadu ya yi misali da su don yin rayuwa mai inganci. Babban Limamin Masallacin Darul Khair Imam Abdulmumini Abdulrafiu-Onilaru ya bada nasihar ne a cikin hudubar Juma’a da ya gabatar a garin Ilorin na jihar Kwara. Ya ce yin rayuwar da za ta yi tasiri kai tsaye ga wasu za ta jawo lada mai kyau daga Allah. A cewarsa ana sa ran musulmi za su gudanar da rayuwarsu daidai da koyarwar Alkur’ani da Hadisin Annabi Muhammad. Imam Abdulrafiu-Onilaru ya bukaci al’ummar musulmi da su kasance masu kula da ‘yan uwansu da kuma taimaka wa mabukata. Ya kuma yi kira gare...
Kwamitin bincike na Majalisar Dinkin Duniya (MƊD) ya ƙasar samu Isra’ila da laifin aikata kisan ƙare dangi kan Falasɗinawa a zirin Gaza. Wani sabon rahoton kwamitin binciken ya ce akwai ƙwararan hujjoji da za a iya cewa Isra’ila ta aikata huɗu daga cikin nau’ika biyar na kisan ƙare dangi a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa, tun farkon yaƙinta da wungiyar Hamas a shekarar 2023. Sun haɗa da: Kashe ’yan ƙungiyar, wanda ya janyo musu lahani a jiki da ƙwaƙwalwa; da kuma ƙirƙirar wani yanayi da gangan don lalata ƙungiyar, da hana haihuwa. Rahoton ya ba da misali da kalaman shugabannin Isra’ila, da kuma abubuwan da sojojinta suka yi a Gaza, a matsayin shaida na aikata kisan ƙare dangi. Ma’aikatar...
Da yake magana game da taron, Maiha ya ce sadarwa ita ce jigon ciyar da harkar kiwon dabbobi gaba, “Bayan wannan taron, muna sa ran za ku yi amfani da dabarun ku don ƙara faɗaɗa labarin fannin kiwo. “Muna yaba wa ƴ an jarida bisa aikinku na ƙwarewa da muke sa ran za ku ci gaba da amfani da dabarun da suka dace wajen kyautata sashin kiwo. “Rahotonin da kuke bayar sun taka rawar gani wajen tsara fahimtar jama’a game da manufofinmu da kuma yin tasiri kan manoma, makiyaya, masu zuba jari, da sauran masu ruwa da tsaki,” in ji shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Iran ba ta yarda da duk wani aiki na siyasa ko matsin lamba na rashin adalci ba Rafael Grossi, babban darektan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, ya gana da ministan harkokin wajen Iran Seyyed Abbas Araqchi ta wayar tarho. Kamfanin dillancin labaran Tasnim ya bayar da rahoton cewa, a yayin wannan kiran, bangarorin biyu sun tattauna batutuwan baya-bayan nan a yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Iran da hukumar ta IAEA, da batun maido da takunkuman da aka kakabawa Iran, da kuma matakin ci gaba da dage takunkumin da aka kakabawa Iran a kwamitin sulhu na MDD. Araqchi da Grossi sun cimma yarjejeniya a birnin Alkahira kan sabbin hanyoyin hadin gwiwa...

Jakadan Iran A Majalisar Dinkin Duniya Ya Ce: Kwamitin Sulhu Ya Rasa Damar Tattaunawa Da Fahimtar Juna
Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Kwamitin sulhun Majalisar ya rasa damar tattaunawa da fahimtar juna a yau Jakadan kasar Iran kuma wakilin din-din-din a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani, ya yi tsokaci kan rashin amincewa da daftarin kudiri na ci gaba da dage takunkumin da aka kakabawa Iran a taron kolin na yau, sakamakon matsin lamba daga kasashen Amurka da Turai. Irawani ya bayyana a yayin taron kwamitin sulhun a jiya Juma’a cewa: Kwamitin sulhun ya yi watsi da damar tattaunawa da fahimtar juna, yayin da Rasha da China bisa gaskiya suka gabatar da wani madaidaicin kudiri na tsawaita kudurin Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 2231 da kiyaye tsarin diflomasiyya. Ya ce: “Maimakon amincewa da...
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta jaddada cewa: Iran tana da ‘yancin mayar da martani ga duk wani mataki da ya sabawa doka Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fitar da wata sanarwa a jiya Juma’a dangane da haramtaccen matakin da kungiyar Tarayyar Turai Troika ta dauka na mayar da takunkumin Majalisar Dinkin Duniya kan Iran a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ta hanyar yin amfani da tsarin warware takaddama kan shirin hadin gwiwa na hadin gwiwa (JCPOA) (yarjejeniyar nukiliya ta 2015) da kuma kuduri mai lamba 2231. Bayanin ya ci gaba da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah-wadai da matakin da kasashen Turai uku wato Faransa da Jamus da kuma Birtaniya suka dauka na yin amfani da...
Mataimakin ministan harkokin wajen Iran mai kula da harkokin shari’a da na kasa da kasa ya mayar da martani kan zargin shugaban Faransa Emmanuel Macron Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’a da na kasa da kasa, Kazem Gharibabadi, ya musanta zargin da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya yi a baya-bayan nan, yana mai jaddada cewa, a yayin da ministan harkokin wajen Iran ke magana, ko tattaunawa, ko ya aika da sako, ko gabatar da wata shawara, wannan mataki ya nuna ra’ayin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, kuma yana samun matsaya na cikin gida, kamar yadda aka gani a tattaunawar fahimtar juna tare da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya a birnin Alkahira. A cikin...
Daga baya an ƙara nata wani nauyin kula da Tashoshin Warri, Koko, Burutu da kuma ta Sapele, waɗanda kamfanonin ƴ an kasuwa masu zaman kansu ne, ke tafiyar da su, amma har zuwa yau, mahukunta a NPA ne, ke tafiyar da duk wata ragamar hukumar baki ɗaya. A shekaru da dama da suka gabata, matsaloli da dama, sun dabaibaye NPA da suka haɗa da, cin hanci da rashawa da rashin ingantattun kayan aiki, musamman na zamani da sauransu, inda waɗannan matsalolin suka haifar wa da NPA koma baya matuƙa, musamman na wajen zama a kan gaba wajen gudanar da harkar hada-hadar kasuwanci a nahiyar Afirka. Amma, za mu iya cewa, Allah san barka da naɗa Dakota Abubakar Ɗantsoho, a matsayin...
1- Musayar yawu ta hanyar sumbatar juna- Ma’ana, ta hanyar sumbatar juna a tsakanin ma’aurata, idan guda daga cikinsu na ɗauke da cutar, nan da nan ɗayan shi ma zai kamu da cutar. 2- Gaurayewar jini ko haɗuwar jini- Haɗuwar jini, misali; idan wani ya yi amfani da reza ya yanke, ɗayan ya yi amfani da ita, zai iya kamuwa da cutar, ko kuma wani abu maikama da haka. 3- Ɓangaren saduwa a tsakanin ma’aurata- A wajen saduwa tsakanin mata da miji, ta hanyar haɗuwa maniyyi ko maziyyi da sauran makamantansu, wannan cuta za ta samu hanyar shigewa nan take da ɗaya daga cikinsu na ɗauke da ita. Don haka, waɗannan hanyoyi da aka ambata dukkanninsu na iya faruwa a...
Firaministan kasar Sin Li Qiang, zai halarci babban taron mahawara na MDD karo na 80 a birnin New York na kasar Amurka, tsakanin ranakun 22 zuwa 26 ga watan Satumban nan. A cewar kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, firaminista Li, zai kuma halarci wasu ayyuka da Sin za ta shirya, ciki har da taron manyan jami’ai dangane da shawarar bunkasa ci gaban duniya da Sin ta gabatar, kana zai gana da babban magatakardar MDD, da jagororin kasashe masu ruwa da tsaki kan batun. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake...
Rundunar ’yan sandan Jihar Yobe, ta ƙaryata rahotannin da ke nuna cewar an kai hari sakatariyar ƙungiyar ’yan jarida ta Najeriya (NUJ) da ke Damaturu. Wannan na cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Juma’a. An cafke mutum 6 kan tono gawa a kabari don yin asiri a Gombe Wata mata ta ƙona al’aurar ’yarta da wuta kan zargin maita a Bauchi Kakakin rundunar, SP Dungus Abdulkarim, ya ce abin da ya faru shi ne wani jami’in tsaro da ke gadin wajen ne ya samu rauni a ƙafarsa ta hagu. A cewarsa, raunin ba shi da alaƙa da harbin bindiga, kamar yadda wasu shafukan Internet suka wallafa. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:45 na daren ranar...
A yau a Nijeriya, kalmar “Japa” ta zama gamagari wajen bayyana yadda matasa da dama ke barin ƙasar domin neman ingantacciyar rayuwa a wasu ƙasashe. Abin da ya bambanta shi yanzu shi ne inda suke nufa: ba kawai Turai da Amurka ba kawai, har ma da ƙasashen Afirka maƙwabta. Yawaitar tsadar rayuwa da ƙarancin ayyukan yi da rashin tsaro, da kuma faɗuwar darajar Naira sun sanya matasa su fara duba wasu ƙasashen Afirka a matsayin mafaka. Mutum 1,666 ne suka kashe kansu a Legas cikin shekaru biyar – ’Yan sanda Akasarin masu kai mana hare-hare daga jihohin da suka kewaye mu suke – Gwamnatin Filato Maimakon tsallaka tekun Bahar Rum da haɗarin mutuwa, da dama daga cikinsu sun fara kallon...
Bayan tattaunawa ta wayar tarho da ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi yayi da babbar jami’ar diplomasiyar kungiyar tarayyar turai kaja kallas ta maimaita bukatar kungiyar na sa ido kan tashohin nukiliyar iran, kana tayi gargadin cewa kofar diplomasiya tana gab da rufewa, matsayin da iran taki amincewa da shi kuma ta bayyana shi a matsayin mara inganci, Iran a matsayinta na member a NPT ta yi aiki da nauyin da ya rataya akanta, karkashin yarjejeniyar JCPOA yayin da Iran ke jiran kungiyar tarayyar turai ta yi aiki da abin da ya hau kanta kuma ta cire takunkumi, amma hakan bai samu ba, kasashen turai da hadin bakin Amurka suna barazanar sake dawo da takunkumai don matsin lamba ga...
Rahotanni sun bayyana cewa tankunan yakin HKI na ci gaba da kutsa kai a tsakiyar gaza a yau juma’a, lamarin da ya jawo tsananta kai hare-hare ta kasa da tilastawa dubban mutane barin muhallinsu sakamakon yankewar hanyoyin sadarwa, A gefe daya kuma Amurka a karo na 6 ta hau kujerar naki kan kudurin kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya na bukatar dakatar da bude wuta da kuma sakin fursunoni da aka kama. Yankin gaza yana dauke da mutane miliyan daya kafin yaki, sai dai rahutanni sun bayyana cewa ya zuwa yanzu sama da 350,000 ne suka bace. Hare hare Isra’ila tun daga 7 ga watan oktoban shekara ta 2023 ta kashe falasdinawa 65141 kuma ta jikkkata 165925 kamar yadda majiyar...
Mutane da dama na nuna damuwa game da mmakomar ayyukansu tun bayan fitowar fasahar AI. Sai dai yayin da wasu manazarta suke ganin fasahar za ta raba mutane da ayyukansu, wasu kuwa gani suke yi wannan ba abu ne mai yiwuwa ba. NAJERIYA A YAU: Wadanne Kalubale Gwamna Fubara Zai Fuskanta Bayan Dawowa Mulkin Ribas? DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya Shirin Najeriya A Yau na wanna lokaci zai yi nazari ne kan sayyukan da fasahar AI za ta iya raba mutane da su. Domin sauke shirin, latsa nan
Matsayar kasar Faransa na amincewa da Falasdinu a matsayin kasa a hukumance a babban taron zauren majalisar dinkin duniya dake zuwa, ya kawo tarnaki sosai a alakar diplomasiya tsakanin ta isara’ila. Shugaban kasar faransa Emmanuel Macron ya sanar tun a watan yuli cewa faransa za ta amince da falasdinu a matsayin kasa, za ta shiga cikin jerin kasashe da ke goyon bayan kafa kasashe biyu masu yancin kai. Ana sa bangaren ministan harkokin wajen Isra’ila Gidion Saar ya gargadi Macron da cewa ba’a maraba da shi a Isra’ila har sai faransa ta canza shirinta na amincewa da falasdinu ,yace wannan shirin zai cutar da tsaron Isra’ila kai tsaye. Shi ma wani babban jami’in tarayyar turai yayi gargadin cewa alaka tsakanin...
Wani rahoto da kwamitin bincike da Gwamna Caleb Mutfwang ya kafa kan kashe-kashen da ke ci gaba da faruwa a Jihar Filato ya ce akasarin masu kai hare-hare suna fitowa ne daga jihohin da ke makwabtaka da Filato. Shugaban kwamitin, Manjo Janar Rogers Ibe Nicholas, ya bayyana cewa sun gana da kabilu daban-daban da kungiyoyin masu ruwa da tsaki, tare da ziyartar dukkan al’ummomin da rikici ya shafa domin samun sahihan bayanai kan tashin hankalin da kuma hanyoyin samar da zaman lafiya mai ɗorewa. Amurka ta hau kujerar-na-ƙi kan buƙatar MDD ta tsagaita wuta a Gaza Kasar Albania ta nada mutum-mutumi a matsayin minista Ya ce daga binciken da suka gudanar, an gano cewa masu kai hare-hare kan al’ummomin Filato...
Sojojin HKI 12 ne suka halaka ko suka ji rauni wani harin da dakarun hamas suka kai masu a zirin gaza. A dai-dai lokacinda suke kai mummunan hare- hare kan Falasdinawa don nufin mamayar birnin Gaza. Tashar talabijin ta Al-mayadeen ta kasar Lebanon tanakalto majiyar labarain na yahudawan na fadar haka takumakara da cewa sojojinsu 4 ne suka halaka a yayinda wasu 8 suka ji rauni a wani harin da kungiyoyin Falasdinawa suka kaiwa sojojinsu a birnin Gaza. Rahoton ya kara da cewa hare-haren da Falasdinawan suka kai yakamata a ce wuri ne maiaminciga sojojin yahudawan a Gaza. Wannan yana faruwa ne a dai dai lokacinda dakarun falasdinawa sun shaalwashin kare mutanensu a gaza. Wadanda suke fuskantar kissan kare dangi...
Kwamitin tsaro na MDD a jiya Alhamis 18 ga watan Satumba, ta kasa samun wani kuduri wanda kenufin tabbatar da zaman lafiyaa gaza da kuma tsagaita wuta a dai-dai lokacinda gwamnatin kasar Amurka wacce take da hakkin hawan kujeran na ki wato Veto ta haka kudurin wucewa. Tashar talabijan ta Al-Mayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto dan rahotonta a NewYork yana cewa dalilan da gwamnatin Amurka ta bayar na hana wannan kudurin wucewa sun hada da abinda ta kira rashin yin allawadai da kungiyar Hamas da kuma da kuma ambatun hakkin HKI na kare kanta a gaban hamas. Kafin haka dai ta sami amincewar dukkan sauran mambobin kwamiton tsaron 14. Jami’an diblomasiyya sun bayyana cewa, ba wannan ne karon farko...
HKI ta kai hare-hare kan wurare 5 a kudancin kasar Lebanon a jiya Alhamis. Tashar talabijin Al-mayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa kafin hare-haren yahudawan sun bada sanarwan cewa zasu kai hare-hare kan warare uku a gudancin kasar ta Lebanon a jiya Alhamis kuma sune Meis al-Jabal, Debbine, da kuma Kafar Tebnit. Mai aikawa tashar talabijin ta kasar Lebanon rahoto daga kudancin kasar ta bayyana, amma a lokacinda ta fara kai hare-hare jiragen yakin da ake sarrafawa daga nesa, suka fara shawagi a kan wadan nan wurare, suna ayyukan leken asiri. Sannan bayana wani lokacin makaman Drones suka ketasararin samaniya kasar Lebanon suka kai hare-hare har guda biyu a kan garin Meisal-Jabal, inda ya jiyamutum guda rauni. Yar rahoton...
Wasu kafafen diblomasiyya nakasashen yamma sun tabbatarwa wakilin tashar talabijin ta Al-mayadeen na kasar Lebanon kan cewa gwamnatin Amurka ce zata jagoranci kasashen yamma wajen tattaunawa da karar Iran. Majiyar ta kara da cewa turawan sun mika wuya ga takurawar washintong don jagorantar tattaunawa da JMI kan shirinta namakamashin nukliya da kuma batun yin watsi da sabon yarjeniyar da Iran ta kulla da hukumar IAEA a al-kahira a baya bayan nan. Banda haka suna son suyi amfani da tsarin Snapbackdon kara takurawa JMI. Sannan kasashen turaiba zasu sararawa JMI ko kadan ba a takurawar da suke mata a tattaunawar. Duk da cewa yarjeniyar Al-kahiri wani bangaremai muhimmanci ne ga bukatun kasashen Turai daga Tehran, amma har yanzun akwai sabbin sharuddan...