Indonesia: Tawagar Iran Tana Halartar Taron Majalisun Kungiyar Kasashen Musulmi
Published: 12th, May 2025 GMT
‘Hudu daga cikin ‘yan majalisar shawarar musulunci ta Iran sun isa birnin Jakarta na kasar Indonesia domin halartar taron majalisun kungiyar kasashen musulmi.
A yau Litinin ne dai aka bude taron majalisun kasashen kungiyar kasashen musulmi a birnin Jakarta na kasar Indonesia wanda shi ne karo na 19.
Taken da aka bai wa taron karo na 19 shi ne: “Kafa Gwamnatoci masu hikima a kuma cibiyoyi masu karfi a matsayin ginshikin jajurcewa.
Tawagar ta Iran dai wacce Ruhullah Mutafakkir Azad yake jagoranta, ta kuma kunshi Sara Fallahi, Sayyid Yahya Sulaimani, da Muhammad Mahdi Shahriyari.
Taron zai ci gaba har zuwa ranar 15 ga watan nan na Mayu da ake ciki, kuma tawagar ta Iran za ta gabatar da jawabi a wurin taron, akan batutuwan da su ka shafi siyasa, al’adu, mata da iyali.
A yayin wannan taron za a tabo batun da ya shafi al’ummar Falasdinu da halin da suke ciki,musamman a yankin Gaza.
A gobe Talata kuwa shugaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran, Muhammad Kalibaf zai isar birnin na Jakarda domin halartar taron.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Dan wasan Barcelona Inigo Martinez ya koma Al-Nassr
A ranar Asabar kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta sanar da cewa dan wasan bayanta, Inigo Martinez zai bar kungiyar, kuma jaridun Sifaniya sun ruwaito cewa zai koma kungiyar Al-Nassr da ke gasar Saudi Pro League.
Tafiyar Martinez za ta taimaka wajen rage nauyin biyan albashin ’yan wasa a Barcelona, kungiyar da a bayan nan ke fama matsalar rashin kudi.
MDD za ta yi zaman gaggawa kan yunƙurin ƙwace Gaza Dubban mutane sun yi zanga-zangar goyon bayan Falasɗinu a Isra’ila da PakistanMartinez mai shekara 34 ya buga wasa a wasanni 71 a dukkan gasanni tun bayan komawarsa kungiyar daga Athletic Bilbao a shekarar 2023, inda ya taimaka wa Barcelona ta lashe kofin La Liga a kakar bara.
Kafin haka, ya shafe shekaru bakwai yana murza leda a Real Sociedad bayan fitowa daga makarantar horas da kwallon kafarta, sannan ya shafe shekaru shida a Bilbao.
Martinez, wanda ya buga wa kasar Spain wasanni 21 tsakanin 2013 zuwa 2023, ya koma Al-Nassr wadda ta kare a mataki na uku a gasar Saudi Pro League a kakar da ta gabata, wadda Cristiano Ronaldo ya zama dan wasa mafi zura kwallaye da kwallaye 25.
AFP