Hukumar Alhazan Jigawa Ta Shirya Taro da Shugabannin Alhazai na Kananan Hukumomi
Published: 8th, May 2025 GMT
Hukumar jindadin Alhazai ta jihar jigawa ta gudanar da taro da shugabanin shiyya shiyya da kuma jami’an alhazai na kananan Hukumomi Jihar 27 a shelkwatar hukumar dake Dutse gabannin fara jigailar maniyatan aikin hajjin bana.
A lokacin da yake jawabi, Darakta Janar na Hukumar Alhaji Ahmed Umar labbo ya ce taron yana da muhimmanci kasancewar aiki yayi nisa na fara jigilar maniyata zuwa kasa mai tsarki.
Yana mai cewar, hukumar ta kammala duk wani shiri ga maniyyata domin fara jigilar su zuwa kasa mai tsarki.
Alhaji Ahmed Umar Labbo ya kara da cewar, a lokacin taron da suka gudanar da jami’an sun rabawa shugabanin shiyya-shiyya da jami’an su dukkanin kayayyakin maniyyata da dukkan sauran muhimman abubuwa daya dace.
Game da batun biza kuwa, Labbo yace an kammala yiwa maniyatan biza wadda daga yanzu zuwa kowane lokaci za’a sanar da maniyyatan zuwa sansanin alhazai domin jigilar su zuwa kasa mai tsarki.
A sabili da haka nema, Ahmed Labbo ya bukaci shugabanin shiyya-shiyya da suyi takatsantsan da kayayyakin maniyyata saboda mahimmacin sa.
Darekta Janar na hukumar, ya kuma godewa gwamnatin Jihar bisa tanadin dukkanin Muhimman abubuwa da suka kamata a filin jirgin saman kasa da kasa na Muhammadu Sunusi dake birnin Dutse domin fara jigailar maniyyatan a dan kankanin lokaci.
Kazalika, yace Gwamna Umar Namadi yasha alwashin ci gaba da kyautata jin dadin maniyyatan bana tun daga nan gida Najejriya har zuwa kasa Mai tsarki.
Usman Mohammed Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Taro zuwa kasa mai tsarki
এছাড়াও পড়ুন:
Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Gamsu da Gudanar da Aikin Tantance ‘Yan Fansho
Karamar Hukumar Birnin Kudu ta nuna gamsuwa da yadda aikin tantance yan fansho ya gudana a yankin.
Shugaban Karamar Hukumar, Dr Builder Muhammed Uba ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin jami’an gudanar da aikin tantance yan fanshon jim kadan da kammala aikin a sakatariyar Karamar hukumar.
Yace karamar hukumar ta gamsu matuka bisa yadda aikin ya gudana cikin kyakkyawan tsari mafi dacewa.
Alhaji Builder Muhammad Uba ya kuma yabawa hukumar asusun adashen gata na fansho kan yadda take biyan hakkokin ma’aikatan da suka yi ritaya akan lokaci ta hanyar basu hakkokin su.
Shima a nasa jawabin, Daraktan kudi da mulki na karamar hukumar, Malam Haruna Ibrahim Kwaimawa ya godewa Karamar Hukumar bisa karamci data nuna a lokacin aikin tantancewar tare da godewa yan fanshon yankin bisa hadin kai da suka bayar a lokacin aikin.
Usman Mohammed Zaria