2025-04-30@19:22:17 GMT
إجمالي نتائج البحث: 6
«masu kwacen waya»:
Matsalar faɗace-faɗacen daba da kuma ƙwacen waya na ci gaba da ci wa al’umma Jihar Kano tuwo a ƙwarya, domin kuwa babu ranar da za ta zo ta wuce ba tare da an samu rahoton faɗan daba ba ko na ƙwacen waya a sassan jihar ba, abin da ke sanya fargaba a zukatan al’umma. Munin lamarin ya kai matakin da akwai wuraren da mutane ba sa iya zuwa da daddare saboda tsoron mummunan abin da ke iya samun su. An kashe sojoji 12 a barikin Nijar An kama mutum 9 kan zargin satar mutane a Taraba Wasu na ganin yadda ake gudanar da siyasar jihar da kuma yadda rashin aikin yi su ne ummulahaba’isin wannan matsalar musammam a tsakanin matasa....
Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya nuna damuwarsa kan yadda sarautar gargajiya ke rasa martabarta a ƙasar nan. A cikin sabon littafinsa mai suna ‘Nigeria: Past and Future’, ya bayyana cewa yanzu akwai masu laifi, ’yan daba, da masu safarar miyagun ƙwayoyi da suka zama sarakuna a wasu yankuna na Najeriya. Afirka ta Kudu ta yi martani kan korar jakadanta daga Amurka Trump ya dakatar da kafar watsa labarai ta VOA “A yau, akwai ’yan daba, masu safarar miyagun ƙwayoyi, ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane da ake kira sarakuna,” in ji Obasanjo. “Wannan abu ne mai matuƙar ban takaici, kuma yana daga cikin matsalolin da ke addabar Najeriya.” Ya ce dole ne a dawo da mutunci da ƙimar sarautar...
Rundunar ’yan sandan Kano ta cafke wasu matasa biyu kan zargin satar wayoyin hannu a kasuwar waya ta Beirut da ke birnin na Dabo. Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ta ce an cafke ɗaya daga cikin ababen zargin ne yana yunƙurin satar waya a wani shago. Sarkin Sasa ya rasu bayan shafe shekaru 125 a doron ƙasa HOTUNA: Gobara ta laƙume shaguna 100 a Kasuwar Sakkwato Sai dai kakakin ’yan sandan ya ce wani abokin ɓarawon da suka yi yunƙurin aika-aikar tare ya tsere da wayar da suka sata. SP Kiyawa ya ce bayan binciken da aka gudanar ne ’yan sanda suka cafke wani mai suna Abduljabbar Musa Sheka kan zargin...
An cafke wani saurayi mai kimanin shekaru 13 bayan ya je rajistar layin wayar salula a yankin ’Yan Katako da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa. Rundunar ’yan sandan Filato ce ta yi wa manema labarai holen saurayin mai suna Umar Hashim tare da wasu mutum shida da ake zargi da garkuwa da kuma kisan wani mai suna Tasiu Abdullahi a ranar 20 ga watan Disamba. DAGA LARABA: Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar Hausa An harbe ’yan sanda biyu a Yobe Sai dai da yake yi wa manema labarai jawabi, Hashim ya bayyana cewa jami’an tsaron har gida suka je suka kama shi da cewa an yi amfani da lambar wayarsa wajen karɓar kuɗin fansar...
Kungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) ta kira zanga-zangar adawa da ƙarin data da kiran waya a Najeriya. NLC ta umarci rassanta na jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya da su shirya domin fara zanga-zangar daga ranar Takara 4 ga watan Fabrairu mai kamawa. Ta bayyana cewa manufar zanga-zangar ita ce ganin an janye karin kashi 50% da aka yi wa kuɗin kiran waya da na data, da kuma adawa da tsadar rayuwa wadda ta jefa ’yan Najeriya cikin tasku. Shugaban ƙungiyar, Joe Ajaero, ya bayyana cewa zanga-zangar zai zama gargaɗi ga shugabanni kan dore wa al’umma abin da bai dace ba sa rashin adalci. “Wannan gangami zai yaƙi ƙare-ƙaren ganin dama rashin adalci da aka yi na man fetur da...
Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam da Gaskiya a Harkokin Jama’a (SERAP), ta maka Shugaba Bola Tinubu da Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC), a kotu kan karan kudin kiran waya da data zuwa kashi 50. NCC ta amince da karin, wanda ya sa kudin kiran waya ya tashi daga Naira takwas zuwa 16.5 a minti daya, yayin da kudin sayen data 1G ya tashi daga Naira 287.8 zuwa Naira 431.25. Shin wannan ce kaka mafi muni ga Man-United a Gasar Firimiya? Ƙungiyoyin da za su fafata da juna a Copa del Rey Shi kuwa kudin aika sakon kar ta kwana ya tashi zuwa Naira shida daga na hudu da ake biya a baya. SERAP, ta ce wannan karin an yi sa...