HausaTv:
2025-05-08@11:17:18 GMT

Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-hassam Al-Mujtaba (a) 119

Published: 7th, May 2025 GMT

119-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin al-kur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtadha Muttari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na maulana Jalaluddin rumi, ko cikin cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da a cikin shirimmu na yau.

///…Madalla, Masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan al-Mujataba (a) da muke kawo maku, mun ji yadda aka yiwa Amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a) bai’a bayana kashe khalifa na uku Uthman bin Affan, munji yadda yaki mutane su yi masa bai’a har sai da shurtah, ko yansanda na lokacin suka yi barazanar zasu kashe dukkan mambobin shura na Khalifa Umar da suka rage idan basu fitar da shugaba a cikinsu ba. Asannan ne mutane suka matsa masa kan shi suke bukata ba waninsa ba. A takaice muna iya cewa sun tilasta masa karban Khalifanci, sabanin khalifofin da suka gabata.

Sannan a khudubarsa ta farko da ya yi a masallaci kafin ya fara karbar bai’a daga mutane, yana cewa:

(Ya ku mutane! Lalle wannan al-amarin naku ,(wato shugabanci) ba na kowa ba, sai wanda kuka shugabantar, a jiya munyi sabani da ku, na kasance bana bukatar shugabancinku, amma sai kuka ki kuka dage sai na shugabance ku, To ku saurara, (idan na karbi wannan shugabanci) ban da hakkin daukar Dirhami guda ba tare da na baku rabonku ba, idan kun amince, to idan baku abice ba in jada baya).

Sai mutane gaba daya a cikin masallacin suka ce, “muna kan abinda muka rabuta da kai a kansa jiya,

Sai yace: Ya Ugangji ka shaida mini a kansu !!, a sannan aka fara masa bai’a mun bayyana cewa Talha dan Ubaidullahi ne ya fara masa bai’a, sannan Zubair dan Awwam, sannan tawagar Misrawa, tawagar Irakawa, sannan sauran mutane. Ba wannan aka taba yiwa bai’a kamar haka ba, daga cikin khalifofin da suka gabace shi(a).

Dangane da wannan Amirul muminina (a), da kansa yana bada labarin yadda aka yi masa bai’a inda yake cewa: Farin cikin mutane da bai’aisu gareni, ya kai ga hatta yara kanana suna farin ciki, sannan tsoffi suna gaggawan yenta, hatta marasa lafiya suna ribibin yenta, yan mata suna sauran yenta har suka yada mayafansu.

Khuduba ta 229 Nahjul Balagha.

Hakika musulmi sun yiwa wasiyyin manzon All..(a) bai’a, kuma kofar ilminsa, farinciki ya game dukkan daular musulunci. Hukumar adalci ta bayyana a bayan kasa, bayan ta manzon All…(s). Hukumar shugaba wanda yake cewa: (Shin zan yarjewa kaina, ace mani: Wannan shi ne Amirul muminina, amma ba zai yi tarayya da su, a cikin wahalhalun zamani ba, ko in zama abin koikoyo a garesu, cikin jin dadin rayuwa?) .

Bayan bai’ar da aka yi masa, sahabban manzon All…(s) da dama, wadanda suke da Imani kan cewa shi ne magajin manzon All…(s) na gaskoya, sun fito sun bayyana farincikinsu da dawo masa da hakkinsa, sun kuma kodaitar da sauran musulmi su taimaka masa a cikin al-amuran jagorancin al-ummar musulmi.

Daga cikinsu akwai, Thabit dan Qais, wanda ya tsa gaban Imam Ali(a) bayan an masa bai’a yana cewa: Na rantse da All..ya Amiral Muminina! Idan sun gabace ka a khalifanci, ammam basu wuceka a addinin ba. Idan sun gabace a jiya ka riskesu a yau, kuma hakika a sanda suna nan kai ma kananan, amma basu iya boye matsayinka ba, bai yuwa a jahilci matsayinka, suna bukatarka a cikin abinda basu sani ba, amma baka bukatar wani tare da ilmin da kake da shi.

Sai Khizaima dan Thabit, wanda aka fi saninsa da Zushahadataini, ya tashi a gabansa (a) yana cewa: Ya Amiral muminin! Ai bamu taba samun shugaban irinka ba, babu wanda shuganci ya cancanta a gareshi sai kai, kuma idan da zamu fadawa kammu gaskiya dangane da kai, da zamu san cewa kai ne na farkon Imani, mafi sanin All.. daga cikin mutane, kuma kai kafi cancanta da matsayin manzon All..(s), kana da abinda suke da shi amma basa da abinda kake da shi.

Sai ya rare kasida inda a cikinta yana cewa:

Idan mun yi bai’a ga Aliyu, to Baban Hassan ya wadatar da mu daga abinda muke tsoronsa na daga fitinu… har zuwa karshen baitocin.

Sai kuma Sasa’atu dan Sauhan , wanda ya tashi ya yi magana yana cewa: Ya amiral Muminina !! Hakika kai ka kawata khalifanci, bata kawataka ba, ka daukakata, bata daukaka ba. Kuma wallahi ta fi bukatarka a kan bukatarka gareta.

Sai Malikul Ashtar, wanda ya tashi a gabansa yana cewa: Ya ku mutane! Wannan wannan shi ne wasiyin wasiyyai, kuma magajin ilmin annabawa, mai jarrabawa babba, … har zuwa inda yake cewa …wanda littafin All..ya shaida masa da Imani, sannan manzonsa kuma da Aljanna, wanda dukka daukaka sun cika a gareshi, ba wanda yake shakkan gabatarsa, da ilminsa da falalarsa, daga na farko zuwa na karshe. .

Sai kuma Ukbatu dan Aamir,  yana cewa : Wa yake da rana kamar ranar Akabah, da bai’a kamar Bai’ar Ridwana? Da kuma limamin shiriya wanda ba’a jin tsoron zai yi zalynci, da kuma masanin da ba’a jin tsoron jahilci daga gareshi.? Da wasu da dama amma zamu taikaita da wadannan.       

Amma manya-manyan kuraishawa da suke karkata, sun sabawa Amirul muminina (a), sun kuma ki shi ne, ba don kome ba sai don abinda yayi na kissan iyayensu da danginsu Mushrikai a kan tafarkin All..a farkon daular musulunci, a yake yakin Badar da Uhudu da Ahzab da sauransu. Don haka sun shiga cikin dimwa da firgishi ganin wanda ya halaka iyayensu da danginsu wadanda suka tsaya a gaban gaskiya ya sami iko a kansu. Har yanzun sun jin haushinsa da kashe wadannan danginsu mushrikai.

Daga cikin manya-manyan  Quraishawa wadanda suka tsaya a gaban gaskiya daga cikin dangin Banu’ Umayya, Imam Ali(a) ya kashe Utbatuh dan Rabi’a, a yakin Badar, tare da umurnin manzon All..(s).

Shi Utbatu dan Rabi’ii, kakan Mu’awiya dan Abusufayan ne, ta mahaifiyarsa Hindu, sannan Walid dan Utbah kawon Mu’awiya ne, dan uwan Hindu.

Kafin haka, dai wata rana a Makka, Utbatu dan Rabii, da kuma Abu Jahal. Sun cutar da manzon All..(s) a Makka, cutar da ya kai ga Utbatun ya tofa yawansa a kan faskar manzon All..(s). Sai manzon All..(s) yace masa: Idan na sameka a wajen Makka sai na kasheka, ‘sabran’, wato baka da makami. Sai a lokacinda kuraishawa zasu fita zuwa yakin Badar, suka fadawa Utbatu dan Rabii ya fita tare da su, sai yace yana jin tsaron Muhammad zai kashe shi, don ya fada masa cewa, idan ya sameshi a wajen Makka zai kashe shi. Sai suka cewa masa, ai sai mu baka rakumi mai sauri sai ka tsare daga gareshi. Sai ya yarda ya fito zuwa yakin Badar, manzon All..(s) da musulmi sun sami nasara a kansu, aka kashe kurashawa 70 sannan aka kama wasu 70, kimani rabin wadanda aka kashe a yakin Badar Aliyu dan Abitalib (a) ya kashesu.

Sannan daga cikin wadanda aka kama har da shi Utbatu Rabii, da aka kawosu, manzon All..(s) ya ganshi a cikin wadanda aka kama, sai yace a fito da shi, sai ya ce wa manzon All..(s) ni kadai zaka kashe a cikin wadan nan? Sai yace : Yace ee, don tufin da kayi a fuskata a Makka, sai ya umurci Aliyu kan buge wuyansa . Aliyu (a) ya sare wuyarsa ya kashe shi.

Don haka danginsa Banu umayya da wasu kuraishawan suna jin haushin Aliyu (a) saboka kashe, iyayensu da kakaninsu da danginsu da yayi a yake-yaken da manzon All..(s) ya yi da Mushrikan Kuraishawa da suke makka, a lokacinda manzon All..(s) ya kwace birnin Makka a shekara ta 8 bayan hijira, ya yafe masu kan cutar da suka yi masa.

Da dama daga cikinsu, sun shiga musulunci ne ba tare da imini ya shiga zukatansu ba. Sai dai don manzon All..(s) ya fi karfinsu. Don haka ne manzon All..(s), ya sanya wasu daga cikinsu cikin mu’allafatu kulubuhum, wadanda ake son karkatar da zukatansu zuwa musulunci, saboda sun musulunta ne a baki.

Daga cikinsu akwai Abu sufayan baban Mu’awiya, manzon All…(s) ya bashi rakumi 100 bayan yakin Hunain don karkatar da zuciyarsa zuwa musuluni da kuma kiyaye sharrinsa idan bai harhata ba.

An ruwaito cewa, wata rana Khalifa Uthman, ya fadawa Aliyu (a) yana cewa: Me zan yi da kai ne?, sai zaka yi dani kuwa, idan ban kashe mushrikai wadanda suka tsaya gaban addinin musulunci ba, kai ka is aka zama Khalifan musulmi? Sai Uthman yi shiru. Wannan saboda manya-manyan kuraishawa dangin Uthman wadanda Aliyu(a) ya kashe a Badar da Ukhud.

Banda haka sun yi mulki an gani, mutane sun kisu, don irin siyasarsu ko shugabancinsu na, na satar dukiyar Al-umma, da fafita kansu kan sauran mutane da sauransu. Wanda duk Aliyu dan Abitalib (a) bai yi ba, kuma bai yarda a yi karshen khalifancinsa ba.

To amma yaya zasu yi, dole su zo su yiwa sabon Khalifa bai’a, don haka Wilid Dan Utbah wanda manzon All..ya sa aka kashe babansa bayan yakin Badar, shi ne ya jagoranci umaiyawa zuwa wajin Amirulmuminina Aliyu dan Abitalinb don su yi masa bai’a.. Zamu ji yadda suka yi bai’ar a shirimmu na gaba. Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu na yau sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: a yakin Badar wadanda suka a yana cewa

এছাড়াও পড়ুন:

‘Raini ne ya sa ake ƙalubalantar yunƙurin kafa ƙungiyar Hausawa zalla’

Wata ƙungiya mai rajin kare muradun al’ummar Hausawa a Nijeriya mai suna Kungiyar Hausawan Nijeriya ta tsaya kai da fata cewa dole a ƙyale Hausawa su kafa ƙungiyarsu kamar kowacce ƙabila tun da dai doka ba ta hana su ba.

Martanin nasu na zuwa ne a daidai lokacin da masu kiran ke shan sukar cewa suna ƙoƙarin rura wutar ƙabilanci ne a Arewacin Nijeriya Najeriya, musamman a daidai lokacin da yankin ke buƙatar haɗin kai domin magance matsalolinsa.

Alƙaluman sakamakon jarabawar bana — JAMB Friedrich Merz ya zama sabon shugaban gwamnatin Jamus

To sai dai ƙungiyar ta ce ba ta ga dalilin da zai sa a ƙalubalanci yunƙurin nasu ba, tun da dai ’yan ƙabilar Yarabawa suna da ƙungiyar Afenifere, ’yan kabilar Ibo suna da Ohaneze, Fulani kuma suna da Miyetti-Allah.

Sun ce hakan na nufin Hausawa ne kawai a cikin manyan ƙabilun ƙasar ba su da ƙungiyarsu ta ƙashin kansu.

A yayin wata zantawarsu da manema labarai a Kano, shugaban kungiyar, Abdullahi Abdullahi, ya ce yunƙurin ya zama wajibi domin kare muradun Hausawa a ƙasar ta kowacce fuska, musamman ta ɓangaren tsaro da ya ce ’yan bindiga na neman hana Hausawa rayuwa a yankunansu.

A cewarsa, “Akwai yunkurin da ake yin a kore samuwar asalin Hausawa ta hanyar cewa a yanzu babu cikakkun Hausawa na asali, a daidai lokacin da ake kiran wasu da cikakkun ’yan kabilar Ibo, Yarabawa da Fulani.

“Ayyukan ta’addancin da ake yi wa Hausawa a kasarsu abin takaici ne.

“Ina wadanda suka kashe Sarkin Gobir? Ina mutanen da Bello Turji ya ƙone ƙurmus a motar bas a Sakkwato ranar da Buhari ya tafi Legas ƙaddamar da littafi?

“Ina matan da ’yan ta’adda suka yi wa fyade a masallaci? Ina labarin jariran da ’yan ta’adda suka ba wa karnuka suka cinye da ransu? Ina labarin mafarautan da aka kashe a jihar Edo a kwanan nan? Waye zai nema musu hakki kuma waye zai bi musu kadi?

“Dole wadannan abubuwan suka sa dole mu Hausawa mu tashi tsaye mu tunkare su tare da masu goya musu baya daga cikin malaman addini, ’yan siyasa, masu rike da sarautun gargajiya da dukkan kungiyoyinsu,” in ji shugaban kungiyar.

Kungiyar ta kuma ce sam ba ta goyon bayan kiran da wasu ke yi na a yi wa rikakken dan ta’addan nan, Bello Turji afuwa, inda suka ce hakan babban kuskure ne da za a yi da-na-sani a kai.

Daga nan sai ƙungiyar ta yi Allah-wadai da abin da ta kira rashin sanin ciwon kai, kan yadda ta ce an kafa wani babban allon talla mai dauke da rubutun “Katsina babu korafi” ɗauke da hoton Shugaban Kasa Bola Tinubu yayin ziyarar da ya kai Jihar Katsina a ’yan kwanakin nan, a maimakon a fada masa matsalar da ake ciki ta rashin tsaro.

Sai dai kuma ƙungiyar ta ce idan zaɓe na gaba ya zo, babu wanda Hausawa za su sake zaɓa sai ɗan uwansu Bahaushe.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kwanaki 40: Iyalan Maharban Da Aka Kashe A Edo Na Neman A Biya Su Diyya
  • Ministan Ilimi Ya Ce Hana Satar Amsa Ne Ya Sa Ɗalibai Suka Faɗi JAMB A Bana
  • Dalilin faɗuwar ɗalibai a jarabawar JAMB bana — Ministan Ilimi
  • ‘Raini ne ya sa ake ƙalubalantar yunƙurin kafa ƙungiyar Hausawa zalla’
  • Bukhaiti: HKI Ta Ketari Jan Layimmu, Ta Jira Maida Martanimmu
  • Alƙaluman sakamakon jarabawar bana — JAMB
  • Majalisar Kano Ta Amince Da Dokar Wutar Lantarki Da Za Ta Raba Wa Jihohi 3 Wuta
  • Manzon Shugaban Kasar Sin Ya Halarci Bikin Rantsar Da Shugaba Nguema Na Gabon
  •  Sojojin  HKI Sun Rushe Gidajen Falasdinawa Fiye Da 100 A Yammacin Kogin Jordan