Inter Milan ta kori Barcelona daga Gasar Zakarun Turai
Published: 7th, May 2025 GMT
Inter Milan ta samu nasarar tankaɗo Barcelona daga Gasar Zakarun Turai, lamarin da ya ba ta damar kaiwa zagayen ƙarshe na gasar ta bana.
A daren wannan Talatar ce aka buga wasa falle na biyu a zagayen kusa da na ƙarshe a Gasar Zakarun Turai ta bana tsakanin ƙungiyoyin biyu.
‘Raini ne ya sa ake ƙalubalantar yunƙurin kafa ƙungiyar Hausawa zalla’ Majalisar Dattawa ta kafa kwamitin lura da gwamnan riƙo na Jihar RibasInter Milan ce ta yi nasarar doke Barcelona da ci 4-3 a filin wasanta na San Siro da ke Italiya, bayan a makon jiya sun yi kunnen doki 3-3 a Nou Camp da ke ƙasar Sifaniya.
A wasan na yau da aka barje gumi har tsawon mintuna 120, Lautaro Martinez da Hakan Calhanoglu ne suka fara ci wa Inter ƙwallo a ragar Barcelona, daga baya Eric Garcia da Dani Olmo da Raphinha suka rama ƙwallayen har da ƙari.
Sai dai ana dab da tashi ne kuma Francesco Acerbi mai shekaru 37 ya rama wa Inter ƙwallo ta uku, abin da ya tilasta wasan zuwa ƙarin lokaci.
A minti na 99 ne Davide Frattesi ya ci wa Inter Milan ƙwallon da ya ba ta nasara.
Ƙungiyar wadda a yanzu Simone Inzaghi ke jagoranta, ta kai wasan ƙarshe na Gasar Zakarun Turai karo na biyu ke nan a cikin shekaru uku.
Yanzu Inter Milan za ta haɗu ne da PSG ko Arsenal waɗanda za su fafata nasu wasan a ranar Laraba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Barcelona Gasar Zakarun Turai a Gasar Zakarun Turai
এছাড়াও পড়ুন:
Tarayyar Turai: Muna Goyon Bayan Warware Batun Nukiliyar Iran Ta Hanyar Diplomasiyya
Jami’ar siyasar waje ta tarayyar turai Kaja Kallas ta bayyana cikakken goyon baya ga warware batun makamashin Nukiliyar Iran ta hanyar diplomasiyya.
Jami’ar ta wallafa a shafinta na X cewa: Na tattauna da ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci domin tabbatar da goyon bayan kungiyar tarayyar turai akan aiki da hanyar diplomasiyya domin warware batun Nukiliyar Iran da kuma rage rikice-rikice a cikin wannan yankin.”
Haka nan kuma Kallas ta jaddada abinda a baya tarayyar turai din ta rika riyawa da ba shi da tushe na cewa, Iran tana bai wa Rasha taimakon soja tana mai cewa: ” Na kuma yi kira ga Iran da ta dakatar da bai wa Rasha taimakon soja.”
Iran dai ta sha yin watsi da wannan irin zargin na cewa tana bai wa kasr Rasha makamai.
Matsayar tarayyar turai din dai ta zo ne bayan yin zango na uku na tattaunawa a tsakanin Iran da Amurka ta hanyar shiga tsakanin kasar Oman wacce aka fara tun a karshen watan Afrilu.