2025-11-21@12:35:28 GMT
إجمالي نتائج البحث: 8015

«Libya»:

    Jami’an rundunar ’yan sanda ta Jihar Delta sun kama wani fasto na cocin Omega da ke Sapele bisa zargin lalata, fyade da kuma cin zarafin mata uku. Ana zargin Faston, wanda aka bayyana sunansa da Daniel Ololo mazaunin garin Sapele da yin lalata da ’yan mata uku ’ya’yan uwa ɗaya waɗanda mambobin cocinsa ne. Gwamnatin...
    Shugaban kasar rasha vladmir putin ya bayyana cewa ba zamu ja baya daga ayyukan soji da muke yi a kasar Ukrain ba, bayan rahoton da fadar kremlin ta fitar dake nuna cewa dakarunta sun kutsa cikin kasar ukrain suna kusa da birnin Kupiansk mafi mahumimmanci a kasar A loakcin ziyara da babban kwamanda kasar rasha...
    Rahotanni sun bayyana cewa a zaman da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya yayi a baya bayan nan yayi kira a dauki matakin gaggawa don kawo kareshen yaduwa ayyukan ta’addanci a kasashen yammacin Afrika da kuma yankin sahel, yana gargadin cewa yankin na so ya zama cibiyar tsattsauran raayi da rikice- rikice Anasa bangaren babban...
    Kafofin yada labarai na duniya sun mayar da hankali kan taron majalisar shugabannin kasashe mambobin kungiyar Shanghai SCO na 24 da aka gudanar kwanan nan a birnin Moscow na kasar Rasha.  Fira ministan kasar Sin Li Qiang ya yi kira ga kungiyar SCO da ta aiwatar da shawarar inganta tsarin shugabanci na duniya da  kasar...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Esmail Baghaei yayi tir da shigar isara’ila kasar Siriya ba bisa kaida ba, yayi gargadin cewa ci gaba da kai hare-hare da fadada siyasarta ta mamaya babbar barazana ce ga zaman lafiya da tsaron yanki. Haka zalika tahren ta yi gargadin cewa matakin baya bayan nan da isra’ila ta...
    ’Yan bindigar da suka yi garkuwa da masu ibada a cocin Christ Apostolic Church da ke Eruku, a jihar Kwara, sun nemi Naira miliyan 100 a matsayin kudin fansar kowanne mutum da suka kama. A cewar Faston cocin, Lawrence Bamidele, tsakanin mutane 30 zuwa 35 aka yi garkuwa da su a daren Talata lokacin da...
    Kungiyar Gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi kira da a saka gwamnatin mamayar Isra’ila cikin jerin ‘masu aikata abin kunya’ saboda take hakkin yara Majalisar Dinkin Duniya ta yi bikin Ranar Yara ta Duniya a ranar 20 ga Nuwamba, yayin da yaran Falasdinawa ke fuskantar mummunan yanayi sakamakon laifukan Yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya, wanda ya...
    Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya umarci Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, da ya koma jihar Kebbi da aiki sakamakon sace ɗalibai ’yan mata 25 da wasu ’yan bindiga suka yi a jihar. Tinubu ya umurci Matawalle, wanda tsohon Gwamnan Jihar Zamfara ne, da ya zauna a Kebbi domin sa ido kan dukkan matakan tsaro da...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Hukuncin da kotun tarayya ta Abuja ta yanke wa shugaban haramtacciyar ƙungiyar IPOB, Mazi Nnamdi Kanu, ya sake tayar da kura a tsakanin magoya bayansa, ‘yan yankin Kudu maso Gabas, da al’ummar Najeriya gaba ɗaya.   Yayin da gwamnati ke cewa hukuncin ya biyo bayan dogon shari’a da...
    Shugaban Cocin Katolika na Duniya, Fafaroma Leo XIV, ya musanta zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya. Babban limamin, ya bayyana cewa duk da cewa akwai damuwa dangane da matsalar tsaron Nijeriya, amma babu wani mabiyi na kowanne addini da matsalar ta ƙyale. Sai da Kwankwaso APC za ta iya samun nasara...
    Shugaban jam’iyyar NNPP na Jihar Kano, Hashimu Sulaiman Dungurawa, ya ce jam’iyyar APC ba ta da ƙarfin da zai kai ta ga samun nasara a 2027, sai dai idan ta jingina da tasirin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a sakatariyar NNPP ta jihar, Dungurawa ya ce APC a...
    Ƙungiyar ɗalibai ’yan Jihar Kano ta roƙi Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, gwamnoni da ’yan Majalisar Tarayya da su kawo ƙarshen taƙaddamar Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU. Ƙungiyar ɗaliban ta ƙasa reshen Jihar Kano (NAKS) ta roƙi shugabannin da su gaggauta aiwatar da duk mai yiwuwa domin warware taƙaddamar da ke tsakanin gwamnati da ASUU....
    Kwamitin hukumar hana yaɗuwar makamin nukiliya IAEA a Majalisar Dinkin Duniya, ya buƙaci ƙasar Iran da ta bayyana yawan makamashin nukiliyar da ta mallaka. Wannan dai na zuwa ne bayan kwamitin ya amince da wani ƙuduri da zai tilasta wa Iran bayyana musu yawan makamashin nukiliyarta. An yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin ɗaurin rai da...
    Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, babban birnin Nijeriya, ta yanke wa fitaccen jagoran masu fafutukar kafa ƙasar Biafra Nnamdi Kanu, hukuncin ɗaurin rai-da-rai, bayan samunsa da aikata laifukan ta’addanci. Masu gabatar da ƙara sun buƙaci a yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin kisa, to amma Mai Shari’a James Omotosho, ya bayyana cewa a yanzu ba...
    Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sami jagoran haramtacciyar ƙungiyar neman kafa kasar Biyafara ta IPOB, Nnamdi Kanu, da laifukan ta’addanci da aka zarge shi da aikatawa. Da yake yanke hukunci a ranar Alhamis, Mai Shari’a James Omotosho, ya amince da batutuwa uku da aka gabatar a shari’ar, inda ya yanke hukunci a kan...
    Mutum uku da wani yaron babbar motar kaya sun rasa ransu bayan wayar wutar lantarki kashe su a lokacin wani bikin nadin sarauta a unguwar Idimu da ke Ƙaramar Hukumar Alimosho ta jihar Legas, bayanai sun nuna cewa lamarin ya faru ne ranar Talata, 11 ga watan Nuwamba, kuma an gano cewa yaron motar, wanda...
    Mai bai wa shugaban kasa shawara kan sha’anin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya jagoranci manyan jami’an Gwamnatin Nijeriya zuwa Amurka don tattaunawa game da zargin kisan ƙare dangi da ake yi wa Kiristoci. Lamarin ya samo asali ne bayan Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya goyi bayan kafa ƙasashe biyu na Isra’ila da Gaza....
    Gwamnatin Tarayya ta ɗora alhakin dawowar hare-haren ta’addanci, ciki har da sace dalibai mata a jihar Kebbi da kai hari a coci a jihar Kwara, kan kalaman da Amurka ta yi kwanan nan a kan Najeriya. Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya ce sakonnin da Shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa, inda ya zargi Najeriya...
    Bayan kwashe watanni da dama ana ta cece-kuce tsakanin hukumar kula da sufurin jiragen sama ta najeriya da kuma kamfanin jiragen sama na kasar Qatar, daga karshe dai hukumar kula da zirga zirgar jiragen sama ta najeriya ta ci tarar kamfanin naira miliyan 5 saboda kate dokokin da suka shafin fasinjojinta. An fitar da wannan...
    Rahotanni sun bayyana cewa kasashen Iran da malesiya sun cimma yaejejeniyar kara fadada dangantar yin aiki tare a bangaren Addinin da Ala’adu musamman a bangaren kimiyar alkur’ani bayan tarurruka da manyan jami’an gwamnati suka yi a birnin kuala Lumpur babban birnin kasar, Wannan yarjejeniyar za ta kara karfafa hadin guiwa tsakanin manyan kasashen musulmi  adaidai...
    Gwamnan Jihar Binuwai, Hyacinth Alia, ya ce babu wani addini ko mabiyansa da ake yi wa kisan ƙare dangi a jiharsa ko a Najeriya baki ɗaya. Ya yi wannan jawabi ne a ranar Laraba a wani taron da Hukumar Kare Haƙƙin Dan Adam ta Ƙasa (NHRC) ta shirya a Abuja kan kare haƙƙoƙin mutanen da...
    Wani magidanci tare da ɗaukacin iyalinsa huɗu sun rasu sakamakon wata gobara da ta tashi a sanadin kunna maganin sauro a layin Baba Impossible da ke Unguwar Kundila, da ke Ƙaramar Hukumar Tarauni a Jihar Kano. Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ta tabbatar da tashin wutar da misalin ƙarfe 4:13 na Asubar ranar Laraba....
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Mata da dama da aka yi garkuwa da su na shiga wani irin mawuyacin hali yayin da suke hannun wadanda suka sace su, suna fuskantar rayuwar kaskanci, da cin zarafi, da muzgunawa da wasu irin yanayi wanda sai ka tausaya musu. Irin wadannan mata a wasu lokutan basa...
    Wata Kotun Tarayya da ke Abuja, ta sanya ranar 15 ga watan Janairun 2026, don fara shari’ar shugabannin ƙungiyar ’yan ta’adda ta Ansaru; Mahmud Usman da Abubakar Abba. Ana zargin su da jagorantar ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru, kuma Hukumar DSS ce ta kama su tare da gurfanar da su a kotu. Ribadu ya jagoranci tawaga...
    Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa daftarin kudirin da kasar Canada ta gabatar yana cike da siyasa ne kawai hasali ma nuna kin jinin Iran ne.    Mataimakin Wakilin Iran a Majalisar Dinkin Duniya, game da daftarin kudurin da Canada ta gabatar, ya ce: “Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta nuna adawarta ta musamman ga...
    Kamfanonin labarai na Reuters da AFP sun rawaito cewa Amurka ta shawarci Ukraine ta amince da Crimea da sauran yankunan da Rasha ta mamaye mata da kuma rage girman sojojinta zuwa rabi kamar yadda yake kunshe a sabuwar shawarar da Amurka ta gabatar na samar da zaman lafiya tsakanin kasashen biyu. Ukraine ta sami sabuwar,...
    Sudan ta yaba da kokarin zaman lafiya da Amurka da Saudiyya suka yi na dakatar da zubar da jini a kasar. A cikin wata sanarwa da ta fitar a shafin X, Majalisar Mulkin Sojan Sudan ta yi maraba da “kokarin Saudiyya da Amurka na kawo zaman lafiya mai ga Sudan.” Ta gode wa Washington da...
    Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu, ya jagoranci wata tawagar gwamnati zuwa Amurka domin mayar da martani kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi a Najeriya. Wannan zargi ya samo asali ne bayan mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, ya nuna goyon bayansa wajen kafa ƙasashe biyu tsakanin Isra’ila da...
    Ana sa ran za a karrama shahararren ɗan damben boksin na Birtaniya, Fabio Wardley, da kambun zakarun ajin masu nauyi na WBO, bayan Oleksandr Usyk ya janye daga kare kambunsa a fafatawar da zai yi da Wardley. Janyewar ta faru ne bayan Usyk, ɗan kasar Ukraine, ya shaida wa Hukumar Damben Boksin ta Duniya (WBO)...
    Tauraron ƙwallon ƙafar ƙungiyar PSG da ƙasar Morocco, Achraf Hakimi, ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana.  
    Fitaccen ɗan wasan gaba na Najeriya da ke taka leda a ƙungiyar Galatasaray ta Turkiyya, Victor Osimhen, ba zai halarci bikin karrama gwarazan ‘yan wasan Afirka na 2025 ba. Osimhen, wanda ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Afirka a 2023, ya bayyana cewa ya koma Turkiyya ne domin duba lafiyarsa, bayan raunin da ya samu...
    An shiga jimami a garin Zugai da ke Ƙaramar Hukumar Roni ta Jihar Jigawa, bayan da wani tankin ruwa ya faɗo tare yin sanadin rasuwar mutum da jikkata wasu. Daga cikin waɗanda suka rasu har da wata mace mai juna biyu. An yanke wa shugaban ISWAP hukuncin ɗaurin shekara 20 a gidan yari Gwamna Abba...
    Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta yanke wa wani shugaban ISWAP Hussaini Ismaila, hukuncin ɗaurin shekaru 20 a gidan yari bayan samun sa da aikata laifukan ta’addanci. Alƙalin kotun, Mai Shari’a Emeka Nwite, ya yanke hukuncin ne bayan Ismaila, wanda ake kira Mai Tangaran, ya amsa tuhume-tuhume guda huɗu da Hukumar DSS ta...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da kasafin 2026 na kuɗi Naira tiriliyan 1.36 a Majalisar Dokokin jihar. Kasafin wanda aka yi laƙabi da “Kasafin Gine-gine, Ci Gaban Kowa da Ɗorewar Ci Gaba.” Dukiyar sama da miliyan 500 ta kone a gobarar kasuwar katako ta Gombe Tinubu ya fasa zuwa taron G20 saboda...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da kasafin 2026 na kuɗi Naira tiriliyan 1.36 tiriliyan a Majalisar Dokokin jihar. Kasafin wanda aka yi laƙabi da “Kasafin Gine-gine, Ci Gaban Kowa da Ɗorewar Ci Gaba.” Dukiyar sama da miliyan 500 ta kone a gobarar kasuwar katako ta Gombe Tinubu ya fasa zuwa taron G20...
    Cibiyar Blue Sapphire ta kaddamar da wani shiri na musamman da aka kirkiro domin ƙarfafa gwiwar mata ’yan kasuwa a fannin dinkin kayan sawa da kuma harkokin kirkira a arewa maso yammacin Najeriya. Cibiyar na aiwatar da wannan shiri ne tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar ’Yan Kasuwa Mata ta Arewa (ANWE) da Jami’ar Northwest Kano,...
    Shugaban ƙungiyar masu sayar da tsofaffin ƙarafa a jihar Gombe, A.A. Laja, ya ce gobarar da ta tashi a kasuwar tsofaffin ƙarafa da ke kasuwar katakon jihar ta jawo masa asara da ta kai sama da Naira miliyan 500. Lamarin ya faru ne a daren Laraba, inda wutar ta ƙone shaguna fiye da 30 da...
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya dakatar da tafiyarsa zuwa Birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu, da Luanda na Angola, sakamakon sace ɗalibai a Jihar Kebbi da kuma harin da aka kai wa masu ibada a wata coci da ke yankin Eruku a Jihar Kwara. Tinubu, shirya barin Abuja a ranar Laraba domin halartar taron...
    Majalisar Dattawa ta shiga cikin jimami a ranar Laraba bayan mutuwar Sanata Okey Ezea, mai wakiltar mazabar Enugu ta Arewa. Bayanai sun nuna marigayin ya rasu ne a kasar Burtaniya inda yake jinya. ‘Yadda aka harbe mijina a gabana lokacin sace daliban Kebbi’ Mai taɓin hankali ya kashe soja a Legas Ezea, wanda aka zaɓe...
    Shugabar kasar maziko Claudia shinbaum ta fadi a cewa kasarta ta yi watsi da duk wani kokarin tsoma bakin kasashen wajen da kuma kalaman da shugaban Amurka Donald Trump yayi na kai harin soji kan iyakar kasar. A farkon makon nan ne trump yace yana so ya umarci sojoji su kaddamar da wani samame a...
    Amina Hassan, matar Yakubu Makuku, mai gadin makarantar ’yan mata ta GCGSS Maga da ke Ƙaramar Hukumar Danko Wasagu a Jihar Kebbi, wadda aka kai wa hari da safiyar Litinin, ta bayyana yadda aka kashe mijinta. Da take magana da ’yan jarida a wurin da lamarin ya faru, ta ce bayan da maharan suka kutsa...
    Majalisar Wakilai ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya sake kawo sabuwar dabarar da za ta kawo karshen kashe-kashe, da sace-sace da sauran ayyukan ‘yan bindiga a Jihar Zamfara da ma kasa baki daya.  Wannan ya biyo bayan amincewa da kudirin gaggawa na kula da muradun jama’a da dan majalisa mai wakiltar mazabar...
    Wani mutum da ake zargin yana fama da matsalar tabin hankali ya kai hari tare da kashe wani soja a yankin Imota da ke Ikorodu a jihar Legas. Lamarin, wanda ya faru a fili da rana tsaka a ranar Lahadi, ya sa makwabtan wurin da dama guduwa don neman tsira. Gobara ta laƙume kasuwar Katako...
    Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa dole ne kudirin Amurka da MDD ta amince da shi ya tabbatar da kare hakki da yancin Falasdinawa a sahun gaba samar da kasar Falasdinu. Jakadan Iran kuma wakilin dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Saeed Iraqini, ne ya bayyana haka, a matsayin martanin ga amincewar da kwamitin...
    Kasar Saudiyya ta sanar cewa za ta kara hannun jarinta a Amurka zuwa dala tiriliyan daya, daga dala biliyan 600 da kasar ta zuba a baya. Yariman Saudiyyar ne Mohammed Ben Salman ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai tare da Shugaban Amurka Donald Trump a ziyarar da ya kai fadar...
    Wani harin Isra’ila ya kashe akalla mutane 15 a sansanin ‘yan gudun hijira na Falasdinawa mafi girma a Lebanon. An kuma kwantar da adadi mai yawa na mutane a asibitoci a birnin Sidon bayan harin na Ain al-Hilweh da ke can ranar Talata, in ji kamfanin dillancin labarai na kasar Lebanon (NNA).   Sojojin Isra’ila...
    A ranar Alhamis, 20 ga watan Nuwamban 2025, ake sa ran Majalisar Wakilan Amurka za ta gudanar da zama na musamman domin bincikar zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Nijeriya. Kwamitin Majalisar Wakilan kan Afirka ya sanya ranar domin bitar fasalin da Shugaba Donald Trump ya yi kwanan nan na sanya Nijeriya a matsayin...
    Gwamnan Taraba, Agbu Kefas ya sanar da dakatar da sauya sheƙa daga jam’iyyarsa ta PDP zuwa APC a dalilin sace ɗalibai mata ’yan sakandire da aka yi a Jihar Kebbi. Gwamnan ya ce zai ci gaba da tattaunawa da kuma nazari kan lokacin da ya fi dacewa ya sauya sheƙar tare da magoya bayansa. Mutane...
    Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila suna ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta a Lebanon, da a yau Talata su ka kai wani hari a garin Bint-Jubail da ya yi sanadiyyar shahadar mutum daya da kuma jikkatar wani. Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya ambato ma’aikatar kiwon lafiya ta Lebanon tana cewa; Birnin na Bint...
    A wani labari da kungiyar “ISWAP” mai alaka da “Isis” ta watsa, ta sanar da kashe wani babban jami’in sojan Najeriya a wani kwanton bauna da ta yi wa sojoji a kusa da kauyen Wajiroko dake Jahar Borno a ranar Juma’ar da ta gabata. Sanarwar kungiyar ta “Isis” ya kuma kunshi cewa, baya ga Birgediya...