Kungiyar Malaman Jami’o’i Ta Ba Dalibai 164 Tallafin Karatu
Published: 10th, May 2025 GMT
Farfesa Lawan Abubakar tsohon jagora na ASUU shiyyar Bauchi shi, ya wakilci wanda ya kira taron, ya ce yadda aka yi zaben wadanda suka cancanci samun tallafin kuma an yi amfani da adalci tsakanin jinsin mace da namiji, suma wadanda suke da bukata ta musamman, saboda a taimaka masu wajen bunkasa iiminsu.
Ya ce a shekaru biyu da suka gabata kungiyar ASUU ta kashe fiye da Naira milyan 164.kudaden bada tallafin karatu ga wadanda ba su da halin biyan kudin a Jami’oin da ake da su a fadin tarayyar Nijeriya.
Ya ce“Kungiyarmu ta ci gaba da amfani da kuma kula da lamarin bayar da tallafin karatu na Gani Fawehinmi,tsawon shekrun da suka gabata.Ba kawai mun tsaya bane sai kawai ta shi Chief Fawehinmi, amma muma mu kafa tamu.Wannan damar ta samu ne saboda muka lura da yadda gwamnati take tsauwalawa dalibai kudin makaranta masu wuyar iya biya.’
“Lokacin da muka ce lamarin tallafin karatu na Hukumar NELFUND, muna da wata manufa ce sabod ai bamu ce wani Uba ko wanda ya amfana da tallafin ya biya mu a wani lokaci ba kamar yadda Farfesa Piwuna ya kara jaddadawa,”.
Wasu daga cikin wadanda suka amfana da tallafin na yin karatu da aka yi hira da su,sun nuna jin dadinsu,ga kungiyar ta ASUU saboda tallawa iliminsu da tayi, suka kuma yi alkawarin za su yi amfani kudaden daidai wurin da ya dace.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: tallafin karatu
এছাড়াও পড়ুন:
Kakakin Gwamnatin Iran Ta Yi Suka Kan Masu Son Canja Sunan Tekun Fasha Saboda Jahilcin Tarihin Iran
Kakakin gwamnatin kasar Iran ta bayyana cewa: Duk wanda ya canza sunan Tekun Fasha, tabbas ya jahilci tarihin dubban shekaru na Iran
Mai magana da yawun gwamnatin Iran Fatimah Mohajerani ta yi tsokaci kan rahotannin da suke cewa: Shugaban Amurka Donald Trump na yunkurin sauya sunan yankin tekun Fasha. Ta jaddada cewa “wadanda ke neman canza sunan Tekun Fasha ba su fahimci tarihin dubban shekaru na Iran ba.”
Malama Mohajerani ta rubuta a dandalin na X cewa: Tekun Fasha bai takaita da kasancewa sunan yanki kadai ba, a’a ya zama wani muhimmin bangare na tarihin al’ummar Iran.
Ta kara da cewa: “Wadanda ke neman canza sunan ‘Tekun Fasha’ ba su fahimci tarihin Iran na dubban shekaru ba. Wannan yunkuri na nuna rashin sanin gaskiya da tarihi kafin ya zama batun neman tunzura Iran.”