Amurka ta matsa wa ƙasashe da ke fuskantar haraji su amince da Starlink
Published: 8th, May 2025 GMT
Amurka ta matsa wa gwamnatocin wasu ƙasashe da Shugaba Donald Trump ya ƙaƙaba musu haraji su amince da kamfanin intanet na Starlink mallakin Elon Musk a ƙasashensu.
Elon Musk shi ne mai kuɗin duniya kuma babban makusanci ne ga Shugaba Donald Trump.
Jaridar Washington Post ce ta ruwaito hakan a ranar Laraba, tana mai ambaton sakonnin waya na Ma’aikatar Harkokin Waje.
Sakonnin sun nuna yadda ofishin Jakadancin Amurka da ma’aikatar suka matsa wa ƙasashe don su kawar da duk wata cikas ga kamfanonin tauraron dan Adam, yana mai ambaton kamfanin Starlink da sunanta, kamar yadda jaridar Post ta ruwaito.
Takardun ba su nuna cewa gwamnatin Trump ta buƙaci a ba da fifiko ga Starlink a musayar rage haraji ba, kamar yadda jaridar ta ruwaito.
’Yan sanda sun kama harsasai 500 a Filato An kwantar da kishiyoyi a asibiti bayan sun sha ‘Kayan Mata’Amma sun nuna cewa Sakataren Harkokin Waje, Marco Rubio, ya umurci jami’ai da su matsa ƙaimi don samun amincewar ka’idoji ga kamfanin tauraron dan Adam na Starlink, mallakar Elon Musk.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Starlink
এছাড়াও পড়ুন:
Yadda kwacen babur da waya ya maye gurbin garkuwa da mutane a Birnin Gwari
Bayan kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin tubabbun ’yan bindiga da jama’ar gari a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna, mazauna yankin sun ce yanzu matsalar tsaron ta dauki sabon salo.
A watan Oktoban 2024 ne dai aka kulla yarjejeniyar sulhun tsakanin bangarorin biyu.
Yarjejeniyar na zuwa ne bayan shafe sama da shekara 10 ana fama da rikicin da ya mayar da babbar hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari daya daga cikin mafiya hatsari a Najeriya.
Bai kamata ake bai wa ɓarayi muƙamin ministoci ba — Sarki Sanusi II Ma’aikatan gwamnati na amfani da kudaden sata wajen gina rukunin gidaje – EFCCDaga shekara ta 2015, mazauna yankin sun sha fama da hare-hare da garkuwa da su, yayin da matafiya kuma ala tilas suka koma neman rakiyar sojoji kafin su iya wuce hanyar.
Yanzu dai yankin ya fara samun saukin matsalar, yayin da mazauna yankunan suka fara komawa gidajensu manoma kuma suka ci gaba da noma gonakinsu.
To sai dai da alama yanzu a maimakon garkuwa da mutanen, rahotanni na cewa a yanzu ’yan bindigar sun fara yawo a gonaki suna kwace babura, wayoyi, kudade da ma kayan aikin gona daga hannun manoman yankin.
Mazauna kauyen Kuyello da ma wasu kauyukan sun ce yanzu suna zaman dardar.
Wasu daga cikinsu sun kyale gonakin gaba daya, wasu kuma sun ce yanzu sukan bar wayoyinsu a gida saboda tsoron za a iya yi musu fashi.
“Yanzu ’yan bindiga sun daina garkuwa da mutane, amma sun koma yi mana kwace. Yanzu suna yawo a gari hankalinsu kwance ba sa tsoron kowa,“ in ji wani mazaunin garin na Kuyello.
Hakan dai ya sake jefa tsoro a kan ingancin zaman sulhun da aka ce an yi.
Mazauna yankin dai sun yi korafin cewa babu wani yunkuri da ake yi na dakile tubabbun ’yan bindigar daga kwacen da suke yi, lamarin da ya sa suka ce suna tsoron sake komawa gidan jiya.
Bayanai dai na cewa yanzu matafiya na bin hanyar ta Kaduna zuwa Birnin Gwari, wacce babbar mahada ce tsakanin kudanci da arewacin Najeriya, ba tare da wata barazana ba.