Aminiya:
2025-09-24@11:15:59 GMT

Gwamna Buni ya tallafawa iyalan sojojin da suka mutu 

Published: 9th, May 2025 GMT

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni a ranar Alhamis ya ziyarci sojojin Hedikwatar Task Force Brigade ta 27 Buni Gari, domin jajantawa waɗanda aka kashe kan harin da ’yan tada ƙayar baya suka kai. 

A cikin jawabinsa Gwamna Buni ya bayyana cewa, abin takaici ne ga sake ɓarkewar tashe-tashen hankula da kuma hare-haren da ake kaiwa jami’an tsaro.

’Yan sanda sun ƙaddamar da ƙwararrun Jami’an tsaro saboda makarantu a Bauchi An gurfanar da mutum 10 kan yi wa nakasasshiya fyaɗe a Kaduna

Gwamnan ya jajanta wa sojoji da iyalan ma’aikatan da suka mutu, yana mai cewa, “Jami’an ba su mutu a banza ba, sun mutu suna ƙoƙarin kare ƙasarsu sosai”.

Ya bayar da tallafin Naira miliyan 2m ga kowane iyalan jaruman da suka mutu, sannan kuma Naira miliyan 1m ga jami’an da suka samu raunuka.

Buni ya ce, gwamnati za ta kuma bayar da tallafin ilimi kyauta ga yaran sojojin da suka mutu.

Hakazalika, Gwamnan ya sanar da bayar da gudunmuwar Naira miliyan 50 da za a raba wa dakarun rundunar ta 27 Brigade Buni Gari, baya ga kayan abinci, katifa, barguna da sauran kayayyaki da gwamnatin jihar ta bayar.

Ya kuma ba da tabbacin goyon bayan gwamnati da al’ummar jihar ga sojoji da sauran jami’an tsaro domin yaƙar waɗannan ’yan ta’addan yadda ya kamata tare da fatattakarsu.

Gwamna Buni ya ba da umarnin ƙarfafa tsaro a kewayen rundunar, inda ya ba da tabbacin goyon bayan gwamnati ga jami’an tsaro, “Za mu ci gaba da ƙara ƙaimi wajen inganta tsaro a kewayen.

Kwamandan rundunar Birgediya Janar Usman Ahmed, wanda ya jagoranci Gwamnan wajen duba wannan runduna, ya yabawa Gwamna Buni kan yadda ya ke nuna damuwa da kulawa ga sojojin a kowane lokaci.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Buni Gari Gwamnan Jihar Yobe jami an tsaro Gwamna Buni

এছাড়াও পড়ুন:

An Yanke Wa Sojojin Da Suka Sayar Wa ‘Yan Ta’adda Makamai Hukuncin Ɗaurin Rai-da-rai A Borno

 

A ɓangaren hukuncin Omitoye Rufus, an yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekaru 15.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Yanke Wa Sojojin Da Suka Sayar Wa ‘Yan Ta’adda Makamai Hukuncin Ɗaurin Rai-da-rai A Borno
  • Sojoji Sun Daƙile Hare-haren ISWAP, Sun Bai Wa Magidanta 10,000 Kariya A Borno
  • NAJERIYA A YAU: Abin Da Doka Ya Ce Kan Kisan Jami’an ‘Yan Sanda
  • Da Ɗumi-ɗumi: Gwamnan Ribas, Fubara Ya Ziyarci Tinubu A Fadar Gwamnati A Abuja
  • Jariri ya mutu a bayan uwarsa yayin tsere wa ’yan bindiga a Neja
  • Cikin Mako 2, An Kashe Jami’an Tsaro 53 A Faɗin Nijeriya
  • An kashe jami’an tsaro 53 a cikin mako biyu —Bincike
  • Lokaci Yayi Da Shugabannin Arewa Za Su Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Yankin –  ACI
  • Gwamnan Gombe ya bai wa maharba kyautar motoci da babura don bunƙasa tsaro
  • Ranar Zaman Lafiya ta Duniya: Kungiyar Arewa Ta Nemi Ƙarfafa Sirrin Tsaro Don Kare ‘Yan Najeriya