2025-05-10@13:49:43 GMT
إجمالي نتائج البحث: 5

«yaɗa labarai da»:

    A cikin jawabin sa a taron, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana wasu manyan fa’idoji da kuma irin barazanar da ke tattare wajen amfani da AI a cikin ɗakunan buga labarai.   Ya ce duk da cewa AI na taimaka wa ‘yan jarida a Nijeriya wajen saurin bayar da rahoto, da nazarin bayanai da gudanar da bincike, yana da matuƙar muhimmanci a yi amfani da wannan sabuwar fasahar cikin hankali da bin ƙa’idoji.   Ya ce: “A yayin da muke rungumar aikin jarida da fasahar AI, dole ne mu tabbatar da cewa ba za a tauye ‘yancin jarida ba, illa ma a ƙara ƙarfafa shi.”   Ministan ya kuma ba da sanarwar cewa Nijeriya...
    Gwamnatin Tarayya ta nemi kafafen watsa labarai da su daina kawo rahoton ayyukan ‘yan ta’addan da ke tada hankali a jihohin Filato, Borno, Zamfara, Binuwai, da sauransu. Aminiya ta rawaito cewa jihohin na fama da tashe-tashen hankula musamman a baya-bayan nan in da aka yi asarar rayuka da dukiyoyin al’umma. Dangote ya karya farashin fetur karo na biyu a mako guda Hisbah ta kama matashi yana ‘baɗala’ da Akuya a Kano Wannan ya sanya wasu ‘yan Nijeriyar da suka haɗa da sarakuna, ‘yan siyasa, ƙungiyoyin cikin gida da na waje tuhumar gwamnati kan aikinta na kare ‘yan ƙasa. Sai dai gwamnatin ta bakin Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, Mohammed Idris, ta ce yaɗa labaran ayyukan ’yan ta’addan da ’yan jarida...
    Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja, a ranar Juma’a, ta haramta wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio tattaunawa da manema labarai yayin da ’yar majalisar ta shigar da ƙara a gaban kotu. Mai shari’a Binta Nyako ce ta yanke hukuncin a ranar Juma’a bayan ƙorafin da lauyan da ke kare Akpabio ya yi cewa Natasha na bin daga wannan gidan talabijin zuwa wancan, don tattaunawa da manema labarai kan shari’arsu, duk da cewa batun yana gaban kotu. ’Yan sanda ku yi amfani da iko cikin adalci — CP Wakili An ceto yara ’yan Taraba da aka yi safararsu zuwa Kudu Kotun ta ce daga yanzu babu wani ɓangaren da zai tattauna da manema labarai...
    Shugaba Donald Trump na Amurka ya ba da umarnin dakatar da ayyukan wasu hukumomin ƙasar guda shida da rushe wasu baki ɗaya, ciki har da kafar yaɗa labarai ta Voice of America wato VOA. Sauran hukumomin sun haɗa da gidajen adana kayan tarihi da ɗakunan karatu da ɓangaren kula da marasa galihu da ke kwana kan tituna. Mahaifiyar Sarkin Gwoza ta rasu Yadda za a girka ‘Kamoniya’ Daraktan Muryar Amurka, Mike Abramowitz, ya ce an aike kusan dukkanin ma’aikatan hutun dole na sai baba ta gani. Sannan kuɗaɗen da ake warewa wajen tafiyar da kafofin da ke ƙarƙashinta, irinsu Gidan Rediyon Turai da Asia da kuma Liberty an dakatar da su baki ɗaya. Babu dai wani takamaiman bayani daga gwamnatin...

۱