2025-05-07@22:17:22 GMT
إجمالي نتائج البحث: 62

«Hadaddiyar Daular Larabawa»:

    Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayana labarummu na yau zai yi magana dangane da ‘Mahangar Jumhuriyar Musulunci na Iran ta yadda za’a kai ga fahintar juna a tattaunawanta da kasar Amurka da suke yi wanda ni tahir amin zan karanta. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi a wata tattaunawa ta wayar tarho da tokwaransa na kungiyar tarayyar turai wato Kaja Kallas, ya bayyana mata yadda bangarorin Amurka da Iran za su kai ga cimma yarjeniya dangane da shirin makamashin nukliya na kasarsa. Ministan ya kara da cewa tun kimani shekaru 20 da suka gabata ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran bangaren tattaunawa dangane da shirin nukliyar kasar ta zaman lafiya. Kuma batun shirin nukliyar kasar Iran tana daga cikin ayyuka...
    Gwamnatin Sudan ta katse dangantakar diflomasiyya da (UAE), bisa zarginta da goyan bayan dakarun RSF. A cikin jawabin da aka watsa a talabijin, Ministan Tsaron Sudan, Yassin Ibrahim ya bayyana cewa Sudan ta “katse dangantakar diflomasiyya da UAE,” tare da janye jakadanta da rufe ofishin jakadanci da konsulat dinta a kasar . Da yake magana a gidan talabijin na gwamnatin kasa, ministan tsaron Sudan, Yassin Ibrahim Yassin, ya zargi Abu Dhabi da keta hurumin ‘yancin Sudan ta hanyar mara baya ta fuskar soji ga RSF, ciki har da samar da makamai, da jiragen yaki marasa matuka, da makamai masu linzami wadanda aka kai hari da su a baya-bayan nan a tashar jiragen ruwa, da filin jiragen sama, da kuma tashoshin...
    Gwamnatin Sudan da ke da goyon bayan sojoji ta katse dangantakar diflomasiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), tana bayyana ƙasar a matsayin mai katsalandan, a cewar Ministan Tsaron Sudan, Yassin Ibrahim. A cikin jawabin da aka watsa a talabijin ranar Talata, Ibrahim ya bayyana cewa Sudan ta “katse dangantakar diflomasiyya da UAE,” tare da janye jakadanta da rufe ofishin jakadanci da konsulat ɗinta a ƙasar Gulf ɗin. Dalilin faɗuwar ɗalibai a jarabawar JAMB bana — Ministan Ilimi Inter Milan ta kori Barcelona daga Gasar Zakarun Turai Ya zargi UAE da take hurumin Sudan ta hanyar “ƙawarta”, wato Rundunar RSF, wacce ke yaƙi da sojojin Sudan tun watan Afrilu 2023. “Dukkan duniya ta shaida, fiye da shekaru biyu, laifin kai hari...
    Kasar Sudan ta yanke huldar jakadancinta da kasar Hadaddiyar Daulart Larabawa tana mai ayyana UAE a matsayin ‘kasa mai cin zali’ Kamfanin dillancin labaran Sudan (SUNA) ya watsa rahoton cewa: Kwamitin tsaro da kula da matakan tsaron kasar Sudan ya sanar a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Talata cewa: Sudan ta yanke huldar diflomasiyya da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma kiran hanzarta dawowar ma’aikatan ofishin jakadancin Sudan gida daga Abu Dhabi. Kwamitin tsaro da kula da matakan tsaron Sudan ya bayyana cewa: Fiye da shekaru biyu, daukacin duniya take bibiyar laifuffukan wuce gona da iri kan kasar Sudan, da tabbatar da tsaron yankunanta, da tsaron ‘yan kasarta daga hadaddiyar daular Larabawa ta hanyar wakiliyarta na cikin...
    Kotun duniya ta yi watsi da karar da Sudan ta kai Hadaddiyar Daular Larabawa tana mai zarginta da hannu a kisan kiyashin da aka yi wa al’ummar wannan kasa. A yau Litinin ne kotun duniyar ta yi watsi da karar ta Sudan, tana mai wanke Hadaddiyar Daular Larabawa. Ita dai Sudan ta zargi Hadaddiyar Daular Larabawar da cewa ta hada baki da dakarun kai daukin gaggaawa wajen yi wa mutanen yankin Darfur kisan kiyashi. A nata gefen Hadaddiyar Daular Larabawan ta ki amincewa da tuhumar da Sudan ta yi mata  tana mai siffata ta da cewa; Farfaganda ce, kuma Sudan din ta yi hakan ne domin kawar da hankulan duniya daga kan laifukan da sojoji suke aikatawa.
    Yau Litinin ne kotun kasa da kasa ta ICJ za ta yanke hukunci kan karar da Sudan ta shigar kan Hadaddiyar Daular Larabawa. Khartoum ta kai karar UAE a gaban kotun kasa da kasa da ke birnin Hague, inda ta zarge ta da hannu wajen kisan kiyashin da ake yi wa al’ummar Masalit, sakamakon zarginta da goyon bayan dakarun (RSF) da suka shafe shekaru biyu suna yaki da sojojin Sudan. Khartoum na zarginsu da kasancewa masu goyan bayan kisan kare dangi” da ake ci gaba da yi wa al’ummar Massalit na Darfur, saboda zarginsu da goyon bayan dakarun gaggawa na Janar Hemedti (RSF). Khartoum na fatan alkalan kotun su umurci Hadaddiyar Daular Larabawa da ta daina goyon bayan kungiyar RSF,...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya soki mummunar rawar da Faransa ke takawa Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya soki kasar Faransa saboda abin da ya bayyana a matsayin gurgunta rawar da take takawa a kokarin diflomasiyya kan matsayin Shirin makamashin nukiliyar Iran na zaman lafiya. A wani rubutu da ya yi a dandalin X, kakakin ya yi tsokaci kan zargin na Faransa, yana mai cewa: Ikirarin da ministan harkokin wajen Faransa ya yi na cewa Iran na daf da kera makamin nukiliya, da’awa ce ta karya kuma marar tushe. Ya kara da cewa: Wadannan kalamai na karya, tare da barazanar sake kakabawa Iran takunkumi, suna kara karfafa ra’ayin cewa matsayar Faransa na rikidewa zuwa wani matsayi na...
    Ana sa alamar tambayar cewa: Shin gobarar da ta tashi a birnin Kudus… shin sako ne na ranar tunawa da kafuwar gwamnatin ‘yan sahayoniyya? Gobarar da ta tashi a tsaunin Kudus da aka mamaye ta bazu zuwa manyan yankuna a cikin haramtacciyar kasar Isra’ila, inda ta kewaye wani sansanin soji tare da cinye filayen masu girma da tsayi. Hakan ya sa hukumomin gwamnatin mamayar Isra’ila suka kafa dokar ta baci tare da neman taimakon kasashen duniya. Yayin da Ministan tsaron cikin gidan Isra’ila Itamar Ben-Gvir yake neman dora wa Falasdinawa, alhakin tashin gobarar. Gobarar ta kunno kai ne a daidai lokacin da yahudawan sahayoniyya suka fara gudanar da bukukuwan cika shekaru 77 da kafuwar gwamnatinsu ta mamaya a kasar Falasdinawa,...
    Haka kuma Wang ya halarci taron ministocin waje na kasashe mambobin kungiyar BRICS da na kasashe kawayensu a wannan rana, inda aka tattauna game da yadda za a karfafa ra’ayin cudanyar bangarori daban daban.   Wang ya bayyana cewa, mafitar matsalolin da ake fuskanta a duniya ita ce kiyayewa da aiwatar da ra’ayin cudanyar bangarori daban daban. Ya ce bayan da ta habaka mambobinta, ya kamata kungiyar BRICS ta ci gaba yayata manufar yin shawarwari da juna da tabbatar da ci gaban juna da cin moriya tare, da kiyaye muhimman ka’idojin huldar kasa da kasa, da kuma kare tsarin ciniki tsakanin bangarori daban daban.   Wang ya jadadda cewa, amsar da Sin ta bayar game da yakin cinikayya a bayyane...
    Shugaban kasar Siriya ya ki amincewa da bukatar kurdawan kasar daga dakarun Democradiyyan  kurdawa wato (SDF), na samar da tsarin tarayya a kasar bayan kifar da gwanatin Basshar Al-Asab. Jaridar The Nation ta nakalto shuga Al-Ahmad Sharaa yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa tsarin tarayyar barazana ce ga hadin kan kasar ta Siriya sannan tsarin tarayya ya sabawa yarjeniyar da aka kulla da kurdawan a baya-bayan nan. A wani taron da suka gabatar a makon da ya gabata,  jam’iyyar kurdawan kasar ta Siriya (SDC) ta fadawa “ The National  ”  bayan taron kan cewa suna bukatar tsarin tarayyar a kasar Siriya don shi ne kadai zai tabbatar da hakkinsu a kasar. A cikin watan maris...
    A nasa jawabin, Gwamna Dauda Lawal ya yaba da ziyarar da cibiyar ta kai Zamfara domin duba ƙoƙarin gwamnati na magance matsalar rashin tsaro a jihar.   “Ina yawan cewa, idan ku ka yi ƙoƙarin shawo kan Zamfara yadda ya kamata ta fuskar rashin tsaro, za ku magance kashi 80 na matsalolin tsaro a Arewa.   “Daga dukkan tsare-tsaren da na gani ya zuwa yanzu, mun mallaki abin da ake buƙata domin tunkarar waɗannan ƙalubale bisa tuntubar juna da haxin gwiwa tsakanin jihar Zamfara da ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, wannan abin a yaba ne.   “Na yi farin ciki da jin cewa Tarayyar Turai ta ware wasu kuɗaɗe, duk da cewa za mu samar da...
    Mazauna Ƙauyen Batakashi da ke ƙaramar hukumar Garki a Jihar Jigawa sun yaba wa Gidauniyar Aliko Dangote bisa tallafin abinci da ta kai musu. Wasu daga cikin mazaunan da suka tattauna da wakilinmu sun bayyana farin cikinsu kan wannan karamci, tare da fatan alheri ga gidauniyar. Daya daga cikin waɗanda suka amfana da tallafin, Malam Umar Abdullahi, ya ce gidauniyar ta kawo sassauci ga al’umma bayan iftila’in gobara da ya cinye gidaje kusan 45 a kwanan nan. Haka shi ma Malam Usman Auwal,  ya nuna farin cikinsa, inda ya yaba da gwamnatin jihar Jigawa da kuma Gidauniyar Dangote, bisa tallafinsu ga al’umma. A jawabinsa yayin kaddamar da rabon tallafin na buhunan shinkafa guda 500 masu nauyin kilogiram10, Shugaban ƙaramar...
    Munanan azabtarwa kan fursunonin Falasdinawa a gidajen kurkukun haramtacciyar kasar Isra’ila da suka hada da fyade da dangogin azaba Rahoton da Hukumar Kula da Fursunoni Falasdinawa dakungiyar Fursunonin Falasdinawa da aka saka daga gidan kurkukun haramtacciyar kasar Isra’ila sun fiyar da rahoton hadin gwiwa a yau Alhamis, 24 ga watan Afrilun shekara ta 2025, da ya kunshi munanan shaida daga fursunonin Zirin Gaza da ke tsare a gidan yarin Negev da sansanin Ofer na gwamnatin haramtaciyar kasar Isra’ila. Rahoton ya bayyana yadda ake ci gaba da yin fyade da cin zarafi ga wadanda ake tsare da su a Gaza. Wanda ake tsare da shi a sansanin Ofer ya bayyana cewa da gangan masu gadin sansanin suke kara radadin yadda wanda...
        Kungiyar Sarakunan Afirka ta jaddada muhimmancin gudunmuwar da Sarakuna ke badawa wajen tabbatar da hadin kai da zaman lafiya a Najeriya. Da yake jawabi a wajen bikin nadin Alhaji Aliyu Dauda a matsayin Sardaunan Najeriya na farko, wanda aka gudanar a Yankari, Jihar Bauchi, Shugaban Kungiyar, Alhaji Ibrahim Haruna, ya bayyana gudunmuwar da Sarakuna ke badawa wajen ci gaban kasa. Alhaji Ibrahim Haruna ya ce, masarautun ba wai kawai suna zama uba ga al’umma ba ne, kawai har ila yau suna bada gagarumar gudunmawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasa. Ya bayyana cewa goyon baya da gudunmawar da Alhaji Aliyu Dauda ke bayarwa ga masarautun gargajiya, musamman a Arewacin Najeriya, ne ya sa aka zabesa domin karbar wannan gagarumar...
    Babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa na yankin tekun Farisa (PGCC) ya yi fatan alkhairi ga kasashen Iran da Amurka a tattaunawa ba kai tsaye ba a tsakaninsu dangane da shirin Nukliya ta kasar Iran na zaman lafiya wanda suka fara, a birnin Mascat na kasar Omman a ranar Asabar da ta gabata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Jasem Mohamed AlBudaiw yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa, kungiyar tana bukatar gidan an warware matsaloli tsakanin kasashen duniya ta hanyar tattanawa.  Haka ma tsakanin kasashen yankin. AlBudaiw ya yabawa kasar Omman da shirya wannan tattaunawar, sannan ya yi fatan tattaunawan da aka fara zai kai ga rage tada jijiyoyin wuya a yankin da...
    Sanarwar ta ƙara da cewa, ƙungiyar ta karrama gwamna Lawal tare da gwamnonin Akwa Ibom, Kaduna, da kuma jihar Legas.   “A jiya a Legas, ƙungiyar ‘yan kasuwa ta Nijeriya da Amurka (NACC) ta gudanar da bikin cika shekaru 65 da ƙaddamar da Alhaji Sheriff Balogun a matsayin shugaban ƙungiyar na 20.   “Taron mai taken ‘Ƙarfin Haɗin Kai: Shekaru 65 na inganta dangantakar tattalin arzikin Nijeriya da Amurka’ ya samu halartar manyan jami’an Amurka da Nijeriya da kuma ‘yan kasuwa.   “Ƙungiyar ta amince da goyon bayan da Gwamna Lawal yake baiwa harkokin kasuwanci a jihar Zamfara, musamman a fannin noma.   “Karramawar da aka baiwa gwamnan na nuni ne da irin kwazonsa na jagoranci, da kwazonsa na inganta...
    Jakadan Sudan a Tehran, Abdul Aziz Hassan Saleh, ya tabbatar da cewa, za a gudanar da zaman farko na kotun kasa da kasa da ke birnin Hague a yau Alhamis, domin duba korafin da Sudan ta shigar kan kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, kan rawar da take takawa a yakin da ake ci gaba da yi a kasar, da kuma goyon bayan da take baiwa mayakan sa kai na Rapid Support Forces, tana mai kallonta a matsayin wani bangare na haddasa rikicin da ke faruwa a Sudan. A wani taron manema labarai da ya gudanar a wannan Laraba 9 ga watan Afrilu a ofishin jakadancin Sudan da ke Tehran, jakadan Sudan ya yi tsokaci kan laifukan da dakarun RSF suka aikata...
    Al’ummar Karamar Hukumar Maigatari sun yi kira ga gwamnatin jihar Jigawa da ta taimaka wajen gina hanyoyin da za su hada garuruwansu. Wani mazaunin yankin, Malam Ali A. Bulama Turbus, wanda ya wakilci al’ummomin yayin da yake magana da Rediyon Najeriya a Maigatari, ya jaddada muhimmancin aikin gina hanyar. Ya bayyana cewa samar da hanya a yankin zai rage matsalolin sufuri da mazauna yankin ke fuskanta, musamman wajen samun damar zuwa asibiti da sauran wuraren kula da lafiya. Ya ce, samar da hanyar kuma zai kara bunkasa harkokin kasuwanci, da karfafa dangantaka tsakanin al’umma da kuma saukaka wasu bukatu na yau da kullum da ke da matukar muhimmanci ga cigaban yankin. Malam Ali Turbus ya kuma roki shugabannin karamar hukumar...
    Kungiyar tarayyar Turai ta yi maraba da tattaunawa tsakanin Amurka da JMI dangane da shirinta na makamashin Nukliya, tare da kara jaddada cewa hanyar diblomasiyya kadai ta rage don warware wannan matsalar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a halin yanzu dai kungiyar tarayyar ta Turai ta na ci gaba da takurawa JMI da takunkuman tattalin arziki, masu  tsanani, a lokaci guda tana fadar cewa hanyar Diblomasiyya ce kadai ta rage wajen warware matsalar shirin makamashin nukliya na kasar Iran, wanda ya tabbatar da fuska biyu na kasashen na Turai. Labarin ya kara da cewa, wani mai magana da yawun kungiyar ta EU wanda kuma baya son a bayyana sunansa, ya fadawa kamfanin dillancin labaran IRNA...
    Masu ababen hawa da dama sun maƙale a gadar Namne da ta rufta daura da hanyar Jalingo zuwa Wukari a Ƙaramar hukumar Gassol ta Jihar Taraba sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a da aka yi ranar Laraba. Ruwan sama ya kawar da gadar da aka gina ta wucin gadi a hanyar da aka yi ta taimakon kai don taimakawa matafiya a kan hanya. Jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji ya kama da wuta a Legas Ruwan sama ya lalata aƙalla gidaje 70 a Filato Gadar taimakon kai da aka gina a madadin babbar gadar da ta rufta watanni bakwai da suka gabata, ta kasance hanyar shiga ga masu ababen hawa da ke bin hanyar. Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas...
    Jami’ar Bayero Kano (BUK) ta kaddamar da wani tsari na yanar gizo wanda zai baiwa dalibai damar shiga da duba sakamakon kammala karatunsu ta hanyar lambobi.   Wannan sabon yunkuri shine karo na farko da cibiyar ta samar da sakamako ta hanyar irin wannan dandali.   An sanar da shirin ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun mataimakin magatakarda kuma shugaban hukumar kula da harkokin jama’a Lamara Garba Azare.   A cewar sanarwar jami’ar, tsarin da myBUK Team ya kirkira kuma yana bawa ɗalibai damar dawo da sakamako kai tsaye ta hanyar amfani da sashen rajistar dalibai.   Takardun sakamakon za su nuna a sarari na kowane kwasa amma dole ne ɗaliban da suka kammala shekarar ƙarshe...
    Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin, 31 ga watan Maris, da Talata, 1 ga watan Afrilu, a matsayin ranakun hutun ƙaramar salla. Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da sakataren ma’aikatar, Magdalene Ajani, ya fitar a ranar Laraba. Ahmad Lawan ya raba tallafin N27m da buhun shinkafa 300 a Yobe Tsohon hadimin gwamnan Kano, Abdullahi Tanka Galadanci, ya rasu Ya taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan cikin nasara, tare da yin kira a gare su da su ci gaba da halaye nagari da suka koya a watan. Haka kuma ya jaddada muhimmancin soyayya, yafiya, da haɗin kai wajen gina al’umma. Tunji-Ojo, ya buƙaci ’yan Najeriya da su yi amfani da wannan...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Duniyarmu a yau shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhummanci a makon da ya gabata, dangane da siyasa tattalin arziki zamantake tsaro da sauran, sannan mu yi masu karin bayani daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane da su. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ////.. Madallah, masu sauraro shirinmu na yau zai yi dubi dangane da “ranar Qudus ta Duniya’ wacce aka rayata a jiya Jumma’a ce 27 ga watan Ramdan shekara ta 1446 wanda yayi dai-dai da 28 ga watan Maris shekara ta 2025 miladiyya ne aka gudanra da ranar Qudus ta duniya, a nan kasar Iran da kuma...
    Ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF), ta buƙaci Shugaba Bola Tinubu da gaggauta janye dakatarwar da ya yi wa Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, Mataimakiyarsa, da ’Yan Majalisar Dokokin jihar. Da yake magana a madadin ƙungiyar, Farfesa Abubakar Jika Jiddere, ya ce babu wani dalili da ya dace da zai sa shugaban ƙasa ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar. Mace ta farko ta zama shugabar ƙasar Namibia ’Yan bindiga sun yi garkuwa da jami’in FRSC a Benuwe Ya bayyana cewa, kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi ayyana dokar ta-ɓaci ne kawai a lokuta na matsanancin rikici kamar yaƙin basasa, ko rushewar doka da oda, wanda a cewarsa babu ɗaya daga cikinsu da ya faru a Jihar Ribas. NEF, ta zargi Gwamnatin Tarayya...
    Cibiyar ta “ Global 196” ta bakin babban shugabanta ta sanar da cewa a cikin watanni 18 da su ka gabata, ta tattara bayanai akan laifukan yakin da Isra’ila ta tafka a Gaza.” Haka nan kuma  cibiyar mai matsuguni a Birtaniya ta ce, ya zuwa yanzu ta tattara da dalilai da su ka dace da ka’idojin shari’a a  kotunan manyan laifuka na kasar. Har ila yau cibiyar ta ce, bayan kammala tattara bayanai a zango na farko, za kuma ta bude shafi na gaba domin kara samun wasu bayanan da za su tabbatar da cewa an yi wa Isra’ilawan hukunci a cikin kasashen duniya, musamman masu dauke da zama ‘yan kasashe biyu. Wani shiri da wannan cibiyar take da shi,shi...
    Yan tawayen M-23 na kasar Kongo wadanda suke samun goyon bayan gwamnatin kasar Ruwanda sun kara nosawa zuwa gaba a mamayar da sukewa gabancin kasar ta Kongo. Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa yan tawayen sun kama garin Walikale a jiya Laraba kuma a halin yanzun sun kokarin zuwa sauran garuruwa a yankin. Labarin ya kara da cewa wannan labarin na zuwa ne a dai dai lokacinda shuwagabanninkasashen Kongo da Rwanda suke kira ga bangarorin biyu su tsagaita budewa juna wuta su kuma dawo kan teburin tattaunawa. Wani mazaunin garin walikale ya fadawa reuters yana jin karar bindigogi a garin Nyabangi wanda yake kusa da inda yake. Janvier Kabutwa yace, yan tawayen sun afafatawa da sojojin Gwamnati da kuma...
    HKI ta keta yarjeniyar tsagaita wuta a Gaza, a jiya inda ta kai hare-hare masu yawa, wadanda suka yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 300 ya zuwa safiyar yau. Tashar talanijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, jiragen yakin HKI sun kai hare-haren a kan yankunan zirin Gaza da dama, kuma yawan mutanen da suka yi shahada ya zuwa yanzu ya kai 342 kumamafi yawansu mata da yara ne. Labarin ya kara da cewa a garin Khan Yunus na kudancin Gaza jiragen yakin HKI sun kashe falasdinawa 77 sannan falasdinawa akalla 20 suka kashe a birnin Gaza. SAMA kamfanin dillancin labaran Falasdinawa ya bayyana cewa daruruwan Falasdinawa sun rasa rayukansu, kuma har yanzun ana neman wasu a wuraren...
    Mai bai wa shugaban Daular Hadaddiyar Daular Larabawa da ya kawo ziyara Iran ya bayyana cewam ganawarsa da ministan harkokin wajen Iran ya yi kyau. Mai bai wa shugaban daular ta Hadaddiyar Daular Larabawa shawara, Muhammad Anwar Karkush ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa:  Muna kimanta ttataunawa mai amfani da kuma  aiki tare.” Baya ga batutuwan da su ka shafi alaka a tsakanin kasashen biyu,  da kuma abubuwan da suke faruwa a cikin wannan yankin, Anwar Karkash ya zo da wasiki daga shugaban kasar Amurka Donald Trump.
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jami’an tsaro da ke rakiyar tawagar Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, sun daƙile wani harin Boko Haram a kusa da garin Gujba a Jihar Yobe. Gwamnan da tawagarsa na kan hanyarsu ta komawa Maiduguri daga Biu lokacin da suka haɗu da ’yan ta’addan, wanda hakan ya tilasta musu tserewa bayan musayar wuta. Majalisar wakilai ta dakatar da CBN daga ƙara kuɗin cajin ATM Ba abin da zai faru idan aka tsige Fubara – Wike Bayanai sun ce dakarun tawagar sun ƙwato bindigogi, harsasai, babur, tare da ceto wasu fasinjoji da aka sace. Wani direba da aka ceto, Malum Ari, ya bayyana yadda maharan suka tare hanyar: “Sun karɓe motata suka tilasta mana kwanciya a ƙasa. “Amma da suka hango...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi maraba da matakin da kasar Yemen ta dauka na haramtawa jiragen ruwan Isra’ila shiga tekun Bahar Maliya Bayan sanarwar da kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen ta fitar na cewa za ta dawo da haramcin da ta yi wa jiragen ruwan Isra’ila na tsallakawa tekun Bahar Rum, Hamas ta fitar da sanarwa inda ta yi maraba da matakin. ta bayyana wannan mataki a matsayin wanda ke nuna hakikanin matsayin al’ummar Yemen da gwamnatin kasar na goyon bayan gwagwarmayar al’ummar Falastinu. Har ila yau kungiyar ta yi kira ga dukkanin kasashen Larabawa da na Musulunci da kuma ‘yantatun kasashe a duniya da su kara zage damtse wajen matsin lamba ga ‘yan mamaya da magoya bayansu...
    Shugaban kwamatin duba rabon abincin azumi na majalisar dokokin jihar Jigawa a shiyyar Dutse kuma mataimakin Shugaban Majalisar, Alhaji Sani Isiyaku Abubakar ya bukaci masu aikin dafa abincin a karamar hukumar Gwaram da su dauki wannan aiki a matsayin turbar samun lada daga Allah Madaukakin Sarki ba wai hanyar neman riba kadai ba. Alhaji Sani Isayku Abubakar ya yi wannan kiran ne lokacin da ya jagoranci Yan kwamatin domin duba aikin dafawa da kuma rabon abincin azumi a unguwar Sabon Layi da ke karamar hukumar Gwaram. Ya ce rangadin duba rabon abincin azumi na daga aikin majalisa na duba ayyuka da shirye-shiryen gwamnati domin tabbatar da inganci da kuma shugabanci nagari. Alhaji Sani Isayku Abubakar tare da Yan kwamatin sun...
    A dai dai lokacinda ake bukukuwan ranar mata ta duniya kungiyar Hamas wacce take iko da Gaza, ta yi allawadi da HKI saboda kissan mata kimani 12.000 a gaza a cikin yakin tufanul Aksa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar Hamas na fadar haka a yau Asabar, ta kuma kara da cewa kasashen yamma musamman Amurla da kasashen Turai, idan magana ta zo kan matan Falasdinawa wadanda HKI ta kashe, suna nuna faska biyu. Kashe mata Falasdinawa ba take hakkin mata ne ba, tunda HKI ce ta kashe su. Kungiyar ta kara da cewa HKI ta kashe mata 12,000 sannan ta raunata wasu dubbai, haka ma ta kori wa su da dama daga godajensu.
    Bangaren soja na kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ya ce a shirye yake kan komi ma, kuma zai ci gaba da kasancewa cikin “kyakyawan shiri”, yana mai jaddada cewa barazanar da Isra’ila ke yi na sake yaki a zirin Gaza da aka yi wa kawanya ba zai sa a sako Isra’ilawan da aka yi garkuwa da su ba. Abu Ubaida, kakakin kungiyar al-Qassam Brigades, ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya yi a faifan bidiyo a ranar Alhamis, yana mai jaddada cewa, abin da ‘yan mamaya suka kasa cimma ta hanyar “makamai da yaki” ba za a taba samun shi ba ta hanyar “barazana da yaudara ba.” Kalaman nasa sun zo ne kwana guda bayan da shugaban Amurka...
    “Ina son in nuna jin daɗina ga Babban Hafsan Sojin Sama, wanda kafin ziyarar tasa a yau, ya aiko da wata tawaga mai ƙarfi ƙarƙashin jagorancin ɗaya daga cikin manyan hafsoshi daga hedikwatar domin jajanta mana da al’ummar Zamfara. Ya aika da tawaga zuwa Zamfara a lokuta biyu daban-daban. “Ina son nanata cewa a lokacin da lamarin ya faru, mun yi magana da manema labarai, inda muka fayyace cewa ba da gangan ba ne, illa hatsari ne. Kasancewar Hafsan Sojin Sama a Zamfara na nuna ƙwarewa da kulawa ta musamman. Gwamnan ya bayyana cewa rundunar sojin saman Nijeriya na da matuƙar muhimmanci wajen yaƙar ‘yan bindiga a Zamfara, Arewa maso Yamma, da ma kasa baki ɗaya. “Ina godiya da...
    Shugaban Amurka Donald Trump ya shaidawa kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas cewa zai ba da izinin sake kai sabbin hare-hare a zirin Gaza muddin kungiyar bat a saki sauran Isra’ilawan da ta yi garkuwa da sub a. Barazanar ta Trump ta zo ne a wata tattaunawa kai tsaye a Doha tsakanin wakilinsa kan al’amuran da suka shafi fursunonin, Adam Boehler, da shugabannin Hamas, a yunkurin cimma sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma musayar fursunoni a Gaza. Trump ya ambaci haka ne bayan ganawa da fursunoni shida da aka sako a wani bangare na matakin farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta. Wani babban kusa na kungiyar Hamas ya shaidawa Al Mayadeen cewa, taron na baya-bayan nan ya bar wa bangaren Amurka...
    Sakataren watsa labarai na Fadar white House ta tabbatar da cewa gwamnatin Amurka ta shiga tattaunawa da kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza kai tsaye. Tashar talabijin ta Presstv a nann Tehran ta nakalto Karoline Leavitt tana fadar haka a jiya Laraba, ta kuma kara da cewa, shugaban kasar Amurka Donal Trump ya aiki Adam Boehler mutumin da yake wakiltansa a al-amuran fursinonin Amurka a waje, zuwa kasashen yankin kudancin Asiya don tattauna batun Amurkawa da suke hannun kungiyar Hamas a Zirin Gaza. Leavitt ta kara da cewa Amurkawa sun cancanci a shiga tattaunawa ko kuma a bi duk hanyoyin da suka dace don ganin, an kubutar da Amurka wadanda suka shiga hanun makiyansu a ko ina suke...
    Kungiyar ECOWAS, ta sanar da cewa tawagarta da ta je Guinea Bissau, ta bar kasar bayan barazanar data fuskanta daga shugaban kasar. A wata sanarwa da ta fitar, tawagar ta ce ta bar kasar “da sanyin safiyar Asabar sakamakon barazanar korar da shugaba Umaro Sissoco Embalo ya yi.” Tawagar kungiyar ECOWAS ta ziyarci kasar Guinea-Bissau tsakanin ranakun 21 zuwa 28 ga watan Fabrairu domin taimakawa wajen warware rikicin siyasar kasar dangane da sanya ranar gudanar da zaben shugaban kasa. ECOWAS ta ce ta bar kasar ne don gujewa wannan wulakanci. Kafin hakan dai shugaban kasar ya gana da tawagar ta masu shiga tsakani na kungiyar ta ECOWAS a ranar Litinin da ta gabata.  Amma daga bisanio ya zarge su da...
    Kasashen Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa sun gudanar da taron kwamitin Siyasa da al-adun na kasashen biyu a karon farko a birnin Abu Dhabi wanda ya kara tabbatar da irin ci gaban da suke samu a dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa kyautata dangantaka tsakanin kasashe makobta na daga cikin manufofin JMI ta harkokin wakashen waje. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Majid Takht-e Ravanchi ya bayyana cewa karfafa dangantaka da Hadaddiyar Daular Larabawa yana daga cikin manufofin JMI don biyan bukatun ko wace kasa daga cikin kasashen biyu. Ya kuma kara da cewa akwai bukatar kasashen musulmi su kara hadin kai a tsakaninsu don magance  matsalar da Falasdinawa suke...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
      Kungiyar Tarayyar Makiyaya ta CORET ta ce zata tallafawa yara makiyaya 1,600 a makarantun makiyaya guda shida a Jihohin Kaduna da Jigawa a wani yunƙuri na rage ƙarancin abinci da rashin ingantaccen abinci.   Sakataren Janar na CORET, Mohammed Bello Tukur ne ya bayyana hakan a lokacin ƙaddamar da shirin ciyar da ɗalibai na haɗin gwiwa a Laddauga, wurin kiwon dabbobi na Kachia a Jihar Kaduna.   Ya bayyana cewa, manufar wannan shiri ita ce tallafa wa shirin ciyar da ɗalibai na makarantun makiyaya.   Sakatare Janar ya ƙara da cewa kashi 60 na waɗanda za su amfana ‘yan mata ne, kuma shirin zai ƙarfafa ilimin kyawawan ɗabi’u a fannin abinci mai gina jiki, tsafta, tsabtace muhalli, da kuma...
    Tawagar Iran a Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa: Ba a hana sayar da jirgin mara matuki ciki na ‘Shahed’ ba Tawagar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya ta mayar da martani kan baje kolin jirgin saman Iran a babban taron jam’iyyar Republican inda ta ce: Babu wata doka da ta haramta sayar da jirgin sama maras matuki ciki na Shahed. Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya kara da cewa: Jirgin sama mara matuki ciki na Shahed yana daya daga cikin mafi kyawun nau’ikan jiragen sama marasa matuka ciki a duniya, kasancewar yana da kwarewa sosai wajen ganowa, sa ido da kuma aiwatar da aiki inda ya dace, sannan kuma yana da araha da...
    Manufar ita ce a kawo karshen wannan tashin hankalin ta hanyar adalci, mai dorewa, wace dukkanin bangarorin da abin ya shafa za su aminta da ita” in ji Rubio ga menema labarai, duk da cewa babu jami’an Yukiren ko na Turai a wurin tattaunawar. A wani labarin kuma, shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa ya shaida wa Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio cewa kasarsa ba za ta amince da korar Falasdinawa daga Gaza ba. Mohammed bin Zayed Al Nahyan na mayar da martani ne ga shirin Shugaba Trump na Amurka na karbe ikon Zirin bayan sauya wa al’ummar Gaza matsuguni. Shugaban na Hadaddiyar Daular Larabawa ya ce sake ginin Gaza abu ne da ya kamata a hada shi da shirin da...
    Ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi furuci da cewa: Nan da wasu ‘yan makonni za a fara tilastawa Falasdinawa mazauna Gaza fara yin gudun hijira Ministan kudin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Bezalel Smotrich ya bayyana cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana tuntubar Amurka domin tattaunawa kan aiwatar da shirin shugaban Amurka Donald Trump na tsugunar da mazauna Zirin Gaza a wasu kasashe. A wata hira da ya yi da tashar talabijin ta 12 ta haramtacciyar kasar Isra’ila Smotrich ya furta cewa: Za a fara aikin kwashe mutanen daga Gaza nan da makonni masu zuwa. Smotrich ya ci gaba da cewa: Mazauna Gaza ba za su samu abin da suke nema ba a Gaza nan da shekaru goma zuwa goma...
    Sojojin HKI sun kaseh Falasdinawa 4 a yankin yamma da kogin Jordan a lokacinda suke fadada hare-haren da suke kaiwa kan falasdinawa wanda kuma yake daukar rayukar Falasdinawa a yankin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jaridar WAFA ta falasdinwa wacce ta nakalti majiyar ma’aikatar kiwon lafiya a yankin tana cewa sojojin yahudawan sun kashe Adel Abdel Bashkar a sansanin yan gudun hijira na Askar a kusa da garin Nablus bayan albarusai sun sameshi a kirjinsa. Labarin ya kara da cewa bayan an kai shi asbine sai yace ga garinku, ko kuma yayi shahada. Har’ila yau majiyar ta kara da cewa Falasdinawa matasa uku ne suka yi shahada a lokacinda sojojin yahudawan suka kai hari a sansanin...
    Majiyoyin watsa labarai sun bayyana cewa: Shugaban kasar Masar ya dage ziyararsa zuwa Amurka har sai bayan taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen Larabawa Majiyoyin watsa labaran Masar sun watsa labaran cewa: Gwamnatin kasar ta sanar da dage ziyarar da shugaban Masar Abdul Fattah al-Sisi zai kai birnin Washington na Amurka har sai bayan taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen Larabawa da aka shirya gudanarwa a birnin Alkahira a ranar 27 ga wannan wata na Fabrairu. Majiyoyin sun yi nuni da cewa: Dage ziyarar ya zo ne domin shugaban kasar Masar ya shirya irin martani da zai mayar wa takwaransa na Amurka Donald Trump, bisa hangen nesa da ke samun cikakken goyon bayan Larabawa kan shirin shugaban Amurka...
    Kungiyar masu samar da motoci ta kasar Sin CPCA, ta ce bangaren fitar da motoci daga kasar Sin zuwa kasashen ketare, ya ci gaba da samun tagomashi a shekarar 2024. A cewar CPCA, kasar Sin ta fitar da jimilar motoci miliyan 6.41 zuwa kasashen waje a bara, adadin da ya karu da kaso 23 bisa dari a kan na shekarar 2023. Kasashen da ke kan gaba, wadanda aka kai wa motocin na kasar Sin sun hada da Rasha da Mexico da Hadaddiyar Daular Larabawa, yayin da kasashen da suka ingiza ci gaban da Sin ta samu wajen fitar da motocin suka hada da Rasha da Hadaddiyar Daular Larabawa da Brazil da Belgium da Saudiyya. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Masar ta sanar da kiran taron kasahen larabawa a karshen wannan watan na Febrairu da ake ciki domin tattauna batun tilasta wa Falasdinawa yin hijira daga Gaza a karkashin shirin Amurka da Isra’ila. Da safiyar yau Lahadi ne dai ma’aikatar harkokin wajen ta Masar ta bayyana cewa za ta karbi bakuncin taron kungiyar kasashen Larabawa a ranar 27 ga watan nan na Febrairu,domin tattauna sabbin batutuwan da su ka taso dangane da Falasdinu. Har ila yau sanarwar ta ce, Masar din ta yi wannan gayyatar ne bayan tattaunawa da kasar Bahrain wacce a halin yanzu take rike da shugabancin kungiyar kasashen Larabawan, haka nan kuma tuntubar babbar shalkwatar kungiyar. Bugu da kari Masar din ta sanar...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta bayyana cewa yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakaninta da Isra’ila “tana cikin hadari” kuma “zata iya rugujewa,” Bassem Naïm, ne wani mamba a ofishin siyasa na kungiyar, ya bayyana hakan ga kamfanin AFP, yayin da tattaunawar da ake yi kan mataki na biyu na tsagaita bude wuta, da ya kamata a fara ranar Litinin, ke ja da baya ba kamar yadda aka fara ba inji shi. Da yake zargin Isra’ila da “jinkiri” wajen aiwatar da kashi na farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta na makonni shida, wanda ya fara aiki a ranar 19 ga watan Janairu, Bassem Naim ya yi gargadin cewa wannan lamarin ya jefa yarjejeniyar cikin hadari kuma zata iya haifar da rugujewarta....
    “Ina so na fara da godiya ga Bankin Duniya kan tallafin da yake ci gaba da bai wa jiharmu. Mun daidaita manufofin ci gabanmu da manufar Bankin Duniya na kawar da talauci da inganta ci gaba mai dorewa.” “Mun kuma lura da kalubalen tsaro da a baya suka yi tasiri wajen aiwatar da ayyuka a jihar Zamfara, musamman wadanda suka kawo cikas ga cimma burin da aka sanya a gaba. Duk da haka, muna samun ci gaba yayin da ake fuskantar ƙalubalen, kuma abubuwa suna komawa daidai.” “Mun inganta matakan tsaro ta hanyar kwararan matakai da jihar ta dauka na inganta tsaro da kara daukar matakan dakile barazanar tsaro.” “Gwamnatinmu ta dukufa wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi ta...
    Bama-bamai da mayakan Boko Haram suka binne sun kashe mutane biyu a hanyarsu ta zuwa kasuwa a Jihar Adamawa. Kakakin ’yan sanda a jihar Borno, ASP Kenneth Daso, ya ce mutane shida ne a cikin motar a lokacin motar da ta taka bam din a ranar Talatar bayan ta taso daga Karamar Hukumar Hawul ta Borno zuwa Kasuwar Garkida ta jihar Adamawa. “Ana zargin cewa ’yan Boko Haram ne suka dasa bama-baman, kuma motar da ke jigilar mutanen kauyen zuwa kasuwa a Garkida ta taka ta kuma ta fashe. “Wani dan shekara 25 ya mutu nan take, amma sauran fasinjojin an garzaya da su asibiti domin yi musu magani,” inji shi. Shugaban karamar hukuma ya biya wa al’ummarsa kudin wutar...
    Kasashen Italiya da Spain sun ki amincewa da tilastawa Falasdinawa yin gudun hijira daga Zirin Gaza Ministan harkokin wajen kasar Italiya Antonio Tajani, a yayin wani taron manema labarai da takwaransa na haramtacciyar kasar Isra’ila Gideon Sa’ar a tashar jiragen ruwa ta Ashdod, ya jaddada kin amincewa da kakkausar murya da kasarsa ta yi na korar Falasdinawa daga zirin Gaza karkashin dabarar gudun hijira. Tajani ya bayyana cewa: Ba za a tilastawa Falasdinawan shiga kowane irin zabi ba, yayin da yake magana kan shirin da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar na neman kwace yankin Zaga. A cikin wani yanayi mai alaka da wannan batu, ministan harkokin wajen kasar Spain José Manuel Albares ya bayyana rashin amincewarsa da shawarar da...
    Kungiyar Hamas wacce take iko da yanin zirin gaza ta bada sanarwan cewa a shirye take, masu shiga tsakanin, wato kasar Masar ta fara tattaunawa marhala ta biyu na tattaunawar tsagaita wuta a Gaza. Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto kamfanin dillancin laran AFP na kasar Faransa yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa, wani jami’in kungiyar wanda baya son a bayyana sunansa ya ce kungiyar a shirye take a fara tattaunawar.. A wannan tattaunawa dai ana saran za’a fayyace filla-filla kan yadda al-amura zasu kasance a nan gaba a zirin gaza. Labarin ya kara da cewa jami’an Hamas sun bayyana haka ne a ranar da aka yi musayar fursinoni da HKI a garin Khan Yunus....
    Tashar Talabijin din “ Almanar” ta sanar da cewa, da marecen yau Lahadi ne babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kassim sai yi jawabi akan muhimman abubuwan da suke faruwa a Lebanon da kuma wannan yankin. Har ila yau, Almanar ta ce babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah Sheikh Na’im Kassim zai yi bayani akan lokacin da za a yi jana’izar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah. Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah ya yi shahada ne a sanadiyyar hare-haren masu muni da jiragen yakin HKI su ka kai wa unguwar Dhahiya dake birnin Beiruta. Majiyar ‘yan sahayoniya ta ce sun jefa bama-bamai da su ka nai nauyin tan 85 akan ginin da Shahid Sayyid Hassan Nasrallah yake ciki.
    Ministocin harkokin waje da wasu jami’an gwamnatocin kasashen sun ki amincewa da korar Falasdinawa daga kasarsu kamar yadda shugaban AMurka Donal Trump ya bada shawara. Tashar talabijib ta Presstv a nan Tehran ya nakalto ministoci da jami’an gwamnatin kasashen kungiyar kasashen larabawa suna fadar haka, a wani taron hadin giuwa a cibiyar kungiyar dake birnin Alkahira na kasar Masar. Labarin ya kara da cewa taron ya sami halattar ministocin harkokin waje na kasashe Masar, Jordan, Saudia, Qatar, da gwamnatin Palestinian Authority, sannan da wakilia daga sauran kasashen kungiyar ta ‘Arab League’ . Kungiyar ta bayyana cewa kasashen kungiyar basy amince da duk wani kokari na canza yadda kasashen larabawa suke ciki don tabbatar da samuwar HKI a yankin ba, kamar...
    Shekara 18 da fara aikin gina babban asibitin kwararru mai gado 300 a unguwar Sabuwar Kaduna (Millennium City) amma har yanzu aikin bai kammalu ba. Aikin wannan katafaren asibiti, wanda ake hasashen babu irinsa a fadin yankin Yammacin Afirka, ya yi zamani da gwamnoni biyar, kowannensu na sa lokacin kammala shi, amma har yanzu abin ya gagara. Sau hudu gwamnonin jihar daban-daban suna sa wa’adin kammalawa da kaddamar da wannan katafaren asibiti, ba tare da haka ba ta cimma uwa ba. A shekarar 2007 tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Muhammad Namadi Sambo tare da hadin gwiwar Bankin Raya Musulunci na Duniya suka assasa aikin ginin asibitin da wa’adin kammala shi a cikin shekara biyar, wato 2012. An yi fatan zai kasance...
    Jaridar “Le Monde” ta kasar Faransa ta dauki labarin da yake cewa iyalai masu yawa sun fice daga HKI baki daya zuwa  kasashen Portugal,Cyprus, da kuma Girka. Rahoton ya ci gaba da cewa; Dalilan yin hijirar daga HKI zuwa kasashen waje sun kunshi yaki, rashin tsaro da kuma siyasar gwamnatin Benjemine Netanyahu. Har ila yau, jaridar ta kasar Faransa ta ce, dubban ‘yan share wuri zauna ne suke ficewa daga  Falasdinu dake karkashin mamaya a wasu lokutan iyalai ne kaco kau suke ficewa.  Kwanaki kadan da su ka gabata wasu iyalai da suke kunshe da mutane 20  da su ka hada iyaye, kakanni da jikoki sun yi hijira zuwa Cyprus domin su rayu a can. A cikin kafafen sadarwa na...
    Bikin bazara shi ne biki mafi dadewa da muhimmanci a bukukuwan gargajiya na Sin. Kuma bikin na ci gaba da kara bazuwa da samun karbuwa a fadin duniya. A kwanakin baya-bayan nan, kasashe da hukumomin kasa da kasa da dama sun gudanar da shirye-shirye da nune-nunen dake da alaka da bikin bazara, kuma jama’a a fadin duniya sun hadu domin a dama da su cikin bikin murnar sabuwar shekarar ta Sin. A wannan lokaci, 1 bisa 5 na al’ummar duniya ne ke murnar bikin ta mabanbantan hanyoyi, lamarin da ya mayar da bikin bazara zuwa wata al’adar gargajiya ta duniya tare da inganta fahimta da abota tsakanin jama’ar dukkan kasashe. Alkaluman Watsa Shirye-Shiryen Shagalin Bikin Bazara Na CMG Na 2025...
    Harkar Murnar Sabuwar Shekara Bisa Kalandar Gargajiyar Sinawa Da Tawagar Sin A MDD Ta Shirya Ta Nuna Al’adun Gargajiya
    Wakilin babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin (CMG) kwanan nan ya tattauna tare da shugaban kasar Sri Lanka Anura Kumara Dissanayake, wanda ya kawo ziyara kasar Sin a karon farko tun bayan hawansa mulki. Da yake magana game da nasarar da kasar Sin ta samu na zamanantar da kanta, Dissanayake ya bayyana cewa, yawan al’ummar kasar Sin ya kai kusan kashi daya bisa biyar na al’ummar duniya, amma kasar Sin ba ta da kashi daya bisa biyar na albarkatun duniya. Ya ce Kasar Sin ta dage kan bin hanyar ci gaba da ta dace da ita, kuma kasar ta samu ci gaba, jama’arta kuma suna rayuwa da aiki cikin kwanciyar hankali. Ya ce, ina ganin yin nazari...
    Daga cikin yara ‘yan makaranta miliyan 242 da matsanancin yanayi ya raba da muhallansu a kasashe 85 a shekarar 2024, dalibai  miliyan 2 da dubu 200 ne a Najeriya suka rabu da muhallansu, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin ilimi a shekarar. Rahoton wanda Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar a daidai lokacin da duniya ke bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025, ya nuna cewa a Najeriya baki daya dalibai miliyan 2,200,200 ne suka daina makaranta sakamakon ambaliyar ruwa. Da take gabatar da jawabi kan tasirin da sauyin yanayi ke da shi ga ilimin yara, shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah ya bayyana cewa, ambaliyar ruwa da ta...
۱