HausaTv:
2025-05-10@14:41:26 GMT

Majalisar Da Take Kula Da Nukiliyar Pakistan Za Su Yi Taron Gaggawa

Published: 10th, May 2025 GMT

Fira ministan kasar Pakistan Shahbaz Sharif ya kira yi Majalisar kasa wacce take kula da makaman Nukiliyar kasar  da su yi taro.

Wannan matakin da ake yi wa Kallon mai hatsari yana faruwa ne a daidai lokacin da kasar ta Pakistan take yaki da Indiya.

Ita  dai Majalisar  kasar Pakistan dake kula da makaman Nukiliya da kuma manufofin kasa na koli, ta kunshi manyan kwamandojin soja, da fararen hula, aikinta kuma  shi ne kula da manyan batutuwa da su ka shafi kasa daga ciki har da siyasar makaman Nukiliya da kuma makamai masu linzami.

An kafa wannan majalisar ne dai a 2000.

Tashar talabijin din “Sama News” ta bayar da labarin dake cewa; Mahalarta taron za su yi bitar halin da ake ciki ne na yaki, da kuma tattaunawa matakan da za a dauka a fagen diplomasiyya da kuma hanyoyin tsaro da kare kai.

Ita dai kasar Indiya tana cewa ba za ta taba zama wacce za ta fara amfani da makamin Nukiliya ba, don haka ba za ta zama ta farko da za ta kai wa Pakistan hari ba. Ita kuwa Pakistan ta gina akidarta ta tsaro ne akan cewa za ta iya fara amfani da makamin Nukiliya da Zarar ta faminci cewa wanzuwar kasar tana fuskantar rushewa.

Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana aiki tukuru domin ganin ta shiga Tsakani da kawo karshen rikicin dake tsakanin kasashen biyu da suke makwabtanta.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Ficewar ’yan majalisa 3 a PDP: Raɗɗa ya halarci zauren majalisar Wakilai

Da safiyar Alhamis ɗin nan ne Gwamnan Jihar Katsina Dikko Umar Raɗɗa ya halarci zauren Majalissar Wakillai ta ƙasa domin sheda ficewar Ƴan Majalissa uku na Jihar Katsina daga Jam’iyyar PDP zuwa Jam’iyyar APC

Ƴan majalissar sun haɗa da Ɗan majalisa mai wakiltar (Mashi/Dutse) Hon. Salisu Yusuf Majigiri, da na (Bakori/Ɗanja) Hon. Abdullahi Balarabe Dabai, sai na (Batsari/Safana/Ɗanmusa) Hon. Iliyasu Abubakar.

An kama mutum 6 da ake zargi kan garkuwa da mutane A yi amfani da fasahar zamani don yaƙar ta’addanci — Ganduje

Gwamnan Raɗɗa ya taya ’yan majalissar murnar dawowa cikin Jama’iyyar APC, wanda dawowar su jam’iyyar ya nuna irin haɗin kai da jam’iyyar take da shi a Jihar Katsina.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yemen Tana Bukukuwan Samun Nasara Kan Amurka Kuma Zata Ta Ci Gaba Da Goyon Bayan Gaza
  • Ficewar ’yan majalisa 3 a PDP: Raɗɗa ya halarci zauren majalisar Wakilai
  • An Yi Taron Musayar Al’adu Da Cudanyar Jama’a Na Bikin Cika Shekaru 80 Da Nasarar Yakin Da Sinawa Suka Yi Kan Zaluncin Japan Da Yakin Ceton Kasa Na Tsohuwar Tarayyar Soviet
  • Xi Ya Aike Da Wasikar Taya Murna Ga Taron Musayar Al’adu Tsakanin Sin Da Rasha 
  • An Fara Gabatar Da Shirin “Kalaman Magabata Dake Jan Hankalin Xi Jinping” A Rasha
  • Gwamnatin Siriya Tana Neman Tattaunawa Da Gwamnatin Mamayar Haramtacciyar Kasar Isra’ila
  • Sabbin Fasahohin Noma Na Zamani Na Ci Gaba Da Bayyana A Kasar Sin
  • “Amnesty International”: Korar Falasdinawa Daga Gaza Laifin Yaki Ne
  • APC: Na Bar PDP Ne Domin Ci Gaba Da Amfana Da Ribar Ofishi Na – Kakakin Majalisar Edo