Shugaba Tinubu Ya Rantsar Da Sabbin Kwamishinonin Hukumar INEC
Published: 12th, May 2025 GMT
Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da sabbin Kwamishinonin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) kafin fara taron Majalisar Zartaswa ta Tarayya a fadar gwamnati da ke Abuja.
Sabbin Kwamishinonin INEC din da aka rantsar su ne Mallam Tukur Yusuf, mai wakiltar yankin Arewa maso Yamma, da Farfesa Sunday Aja, mai wakiltar Jihar Ebonyi.
Haka kuma, an rantsar da mambobi biyu na Hukumar Da’a ta Kasa (CCB).
Mambobin su ne Ikpeme Ndem, daga Jihar Cross River, da Mai Shari’a Buba Nyaure mai ritaya, daga Jihar Taraba.
Daga Bello Wakili.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Kaddamar Da Tantance Malamai Da Ma’aikatan Lafiya
A kokarin ta na ci gaba da kula da harkokin ilimi a yankin, Karamar Hukumar Birnin Kudu dake Jihar Jigawa ta kaddamar da aikin tantance malaman makaranta na B teach da kuma ma’aikatan lafiya na wato B health.
A jawabin sa wajen fara tantance malaman da ma’aikatan lafiyar, Shugaban karamar hukumar, Dr Muhammad Uba Builder, yace aikin tantancewar ya zama wajibi domin tabbatar da ma’aikata na gaskiya da kuma gano na bogi.
Yana mai cewar akwai rahotannin daya nuna wasu suna aiki 2 wasu kuma suna amfani da takardun bogi.
A don haka, yace duk wanda aka samu da hakan zai rasa aikin sa gami da kama shi don fuskantar hukunci.
Builder Muhammad Uba, yace an ware ranar asabar domin tantance malaman da kuma ma’aikatan lafiya domin tabbatar na gaskiya da adalci.
Yayi nuni da cewar, duk malamin da aka samu da takardun bogi, shakka babu za’a maye gurbin sa da wani.
Kazakika, Builder yaja hakalin su da su kasance masu tsoran Allah wajen gudanar da aikin su tare da ganin suna zuwa wuraren ayyukansu akan lokaci.
A jawabin sa, kansila mai gafaka na sashen ayyuka na karamar hukumar, Malam Haladu Maigari ya zayyana ayyukan raya kasa da shugaban karamar hukumar ya aiwatar karkashin jagorancin Builder Muhammad Uba.
Ya kuma baiwa malaman da ma’aikatan lafiyan shawarar fadin gaskiya na al’amurran su.
A jawaban su, jami’in shirin B Teach, Malam Nazifi Bala da kuma jami’in shirin B Health Malam mujitafa Ibrahim sun yabawa shugaban karamar hukumar bisa kokarin sa na rage zaman kashe wando ga matasan yankin karamar hukumar ta Birnin kudu.
Usman Mohammed Zaria