BBC ta rawaito cewa, babban abin da ke damun kamfanin na Meta shi ne, yadda al’amarin ya shafi Hukumar Kare Bayanan Sirri ta Nijeriya (NDPC), wanda kamfanin ke zargin karya dokokin kare bayanan sirrin kasar.

Baya ga tarar Hukumar FCCPC, hukumar ta NDPC ta ci tarar kamfanin Meta dala miliyan 37.8, bisa zargin satar bayanan sirri, yayin da hukumar kula da tallace-tallace (ARCON) ta fitar da wani hukuncin daban na dala miliyan 37.

5, kan abin da ta kira da cewa, tallan da ba a ba da damar aiwatar da shi ba.   

Daga cikin ka’idojin da ake da su, akwai bukatar kamfanin na Meta ya samu izini kafin tura bayanan ‘yan Nijeriya zuwa kasashen waje, yanayin da kamfanin ke ganin “ba abu ne mai yiwuwa ba.”

Hukumar NDPC ta kuma bai wa kamfanin Metar umarnin kirkira da kuma nuna abubuwan ilimantarwa a kan hadarin bayanan sirri ta kebabbiyar hanya a kan shafukan nata. Dole ne a samar da wadannan bidiyoyi tare da cibiyoyin da aka amince da su da kuma masu zaman kansu, sannan kuma dole ne su magance ayyukan sarrafa bayanai da rashin adalci.

Amma kamfanin na Meta ya ja baya a kan wadannan umarni, yana mai bayyana su a matsayin “wadanda ba sa aiki” tare da tabbatar da cewa; hukumomin Nijeriya sun gaza aiwatar da fassarar dokokin bayanan nasu yadda ya kamata.

Hukumar ta FCCPC ta ci gaba da cewa, tarar ta biyo bayan cikakken binciken da aka gudanar tsakanin watan Mayun 2021 zuwa Disambar 2023, tare da hadin gwiwar hukumar ta NDPC.

Har ila yau, kamar yadda rahotannin ke nunawa, akwai yiwuwar a wayi gari a ga dib, wadannan shafuka na Facebook da na Instagram sun daina aiki a Nijeriya, sakamakon wannan dimbin tara da kamfanin Metan ya koka a kai.

Idan za a iya tunawa, a bara ne hukumomin sanya ido na Nijeriya suka lafta wa kamfanin tara ta fiye da dala miliyan 290, bisa zargin kamfanin da karya wasu dokoki.

Kazalika, sai ga shi kuma kamfanin na Meta bai samu nasara a karar da ya shigar a wata babbar kotu da ke Abuja ba, inda ya kalubalanci matakin.

Har wa yau, kamfanin Meta ya rubuta a takardun shigar da karar da ya yi cewa;  “Za a iya tursasa wa mai shigar da kara rufe ayyukan shafukansa na Facebook da Instagram a Nijeriya, domin rage hatsarin da zai iya fadawa a ciki, idan bai bi umarnin da ya kamata ya bi ba.”

Bugu da kari kuma, kamfanin Meta ne ke da manhajar WhatsApp, duk da cewa dai kamfanin bai ambaci shafin na WhatsApp din ba a jerin bayanan nasa.

Duk da cewa, babbar kotun ta bai wa kamfanin wa’din zuwa karshen watan Yuni, domin biyan wannan tara, amma da aka tuntubi kamfanin na Meta kan matakin da zai dauka, bai ce ko uffan ba.

Wadane Tasiri Manhajojin Facebook, Instagram Da WhatsApp Ke Da Su Kan ‘Yan Nijeriya

Ganin yadda ‘yan Nijeriya suka rumgumi wadannan shafuka ko manhajoji (Facebook, Instagram da WhatsApp), wasu suke ganin ba karamin nakasu za a samu ba, idan wannan kamfani na Meta ya janye daga Nijeriya.

Facebook ne shafin da al’umma suka fi amfani da shi a Nijeriya, domin kuwa miliyoyin al’ummar kasar ke amfani da shi a kowace rana. Wannan dalili, ya zama kusan na komai da ruwanka, kama daga abubuwan da suka shafi tallata hajoji, samun kowane labaru da dumi-duminsu da sauran makamantansu.

Har ila yau, shafin Facebook ya zama wata matattara ko dandali da ‘yan siyasa ke amfani da shi, musamman wajen yada farfagandar siyasa ko tallata manufofinsu ko kuma ayyuka da suka gudanar.

Kazalika, hatta kafofin yada labarai na amfani da wannan manhaja, wajen bayyana labaru da sauran shirye-shiryen da suke gudanarwa na yau da kullum.

A bangaren kasuwanci kuwa, wannan shafi ya shahara kwarai da gaske, domin kuwa kamfanoni da sauran ‘yan kasuwa; na amfani da shi, domin tallata hajojinsu iri daban-daban. Hatta masu shirya fina-finai, su ma ba a bar su a baya ba, domin kuwa sukan dan gutsuro wani abu daga ciki su nuna, don jan hankalin masu kallo.

Haka zalika, bangaren manhajar WhatsApp, ita ma na da nata matukar muhimmancin, musamman ta fuskar kasuwanci, sada zumunta, fadakarwa, ilimantarwa, tura wasu sakwanni masu muhimmanci da sauran makamantansu.

Wannan manhaja ta Whatsapp, kusan an fi amfani da ita wajen gudanar da kasuwanci, musamman ga daidaikun ‘yan kasuwa masu tasowa, har ma da wadanda wuyansu ya yi kauri.

Babban abin sha’awar shi ne, mata da dama daga gidajensu; na aiwatar da sana’o’i iri daban-daban, ta hanyar amfani da wannan manhaja, suna tallatawa ana kuma saya daga inda suke; ba tare da wata wahala ko kai-komo ba.

Haka nan, ga wadanda suke da ‘yan’uwa da sauran abokan arziki a kasashen ketare, wannan manhaja ta Whatsapp na matukar taimaka musu ta hanyar magana ko bidiyo kai tsaye a tsakaninsu, maimakon magudan kudaden da za su batar ta hanyar amfani da kiran waya.

Sannan uwa-uba, shafin Whatsapp; na da matukar muhimmanci wajen tura sakwannin karatuttuka, jaridu, labaru, hotuna, bidiyo da kuma sakon magana a kowane lokaci.

Haka zalika, ita ma manhajar Instagram na da nata muhimmancin, wajen tura sakwanni, sada zumunta, bidiyo, tallata hajoji da sauran abubuwa masu muhimmanci.

Koda-yake, akwai abubuwa da dama da ake ganin cewa; wadannan manhajoji sun taimaka wajen gurbacewarsu, wanda ko shakka babu, haka abin yake; musamman a bangaren gurbacewar tarbiyya da sauran abubuwan da suka shafi aikata ta’addanci da sauran makamantansu.

Duk da cewa, manhajojin sun taimaka wajen wayar da kan al’umma ta fuskoki daban-daban da suka hada addini, siyasa da sauran al’amuran rayuwa na yau da kullum, amma fa akwai abubuwa da yawa da suka yi tasiri a kan al’ummar wannan kasa ta hanyar amfani da manhajojin.

Kafin zuwan shafukan na Facebook, Instagram da Whatsapp, matasa da dama ba su da hanyoyin kale-kallen bidiyo da sauran hotunan batsa, barkatai. Amma bayan fitowarsu, yanzu za a iya cewa; lamarin ya riga ya zama jiki a tsakanin matasanmu.

Sannan, akwai sauran ayyukan rashin gaskiya da ta’addanci da matasa ke gani, maimakon su wa’antu; sai su buge da koya suna aikatawa. Akwai abubuwan da suka shafi damfara, aikewa da labarun karya da farfaganda, domin neman abun duniya ko wata daukaka a tsakanin al’umma.

Amma duk da wadannan abubuwa da ke faruwa a tsakanin manhajojin, muna iya cewa; amfaninsu ya fi rashin amfaninsu yawa a tsakanin al’ummar wannan kasa.

Shi yasa muke ganin janyewar kamfanin Meta daga Nijeriya, ba karamin koma-baya zai kawo mana ba. Amma wannan ya rage ga mahukunta, wajen dubawa tare da aiwatar da abin da ya dace, tun kafin alakar ta yi tsami.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: wannan manhaja

এছাড়াও পড়ুন:

Sharhin bayan Labarai: Mahangar Iran Dangane Da Tattaunawa Kan Shirinta na Makamashin Nukliya Na Zaman lafiya

Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayana labarummu na yau zai yi magana dangane da ‘Mahangar Jumhuriyar Musulunci na Iran ta yadda za’a kai ga fahintar juna a tattaunawanta da kasar Amurka da suke yi wanda ni tahir amin zan karanta.

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi a wata tattaunawa ta wayar tarho da tokwaransa na kungiyar tarayyar turai wato Kaja Kallas, ya bayyana mata yadda bangarorin Amurka da Iran za su kai ga cimma yarjeniya dangane da shirin makamashin nukliya na kasarsa.

Ministan ya kara da cewa tun kimani shekaru 20 da suka gabata ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran bangaren tattaunawa dangane da shirin nukliyar kasar ta zaman lafiya. Kuma batun shirin nukliyar kasar Iran tana daga cikin ayyuka masu muhimmanci wadanda ma’aikatar harkokin wajen ta aiwatar a cikin wannan lokacin.

Kasashen ya mamma karkashin jagorancin Amurka suka dorawa kasar Iran takumkuman tattalin arziki masu yawa, saboda hana JMI amfani da hakkinta na amfani da fasahar makamashin nukliya, da sunan wai iran tana shirin gina makaman Nukliya.

Don biyan wannan bukatarsu wadannan azzaluman kasashe suka sanya mafi yawan mutanen kasar Iran cikin matsaloli na rayuwa daban-daban. Amma jami’an gwamnatin JMI  don tabbatarwa duniya da kuma wadannan kasashe kan cewa ba ta da wani shiri na mallakar makaman nukliya, ta bude tattaunawa da wadannan kasashe na tsawon shekaru biyu, har sai da bangarorin biyu daga ciki har da Amutka, suka cimma yarjeniya ta ganin JMI ta amfana da fasaha da kuma makamashin nukliya wanda yarjenyar NPT ta amincewa ko wace kasa a duniya ta yi amfani da shi. Wannan ya kaiga samar da yarjeniyar JCPOA a shekara 2015.  

Inda JMI ta aiwatar da dukkan alkawulan da ta dauka a cikin yarjeniyar. Banda haka hukumar makamashin nukliya ta duniya IAEA ta bada rahoto har 16 kan cewa shirin makamashin nukliya na kasar Iran bai karkata daga yarjeniyar JCPOA ba,

Ana cikin wannan halin ne sai shugaban kasar Amurka mai ci ya hau kan kujerar shugabancin kasar Amurka, ya kuma fidda Amurka daga cikin yarjeniyar a shekara ta 2018, tare da dalilin cewa yarjeniyar bata yi masa ba.

Sai dai a dole JMI ta sake dawowa kan teburin tattaunawa dangane da shirin ta na makamashin nukliya. Sannan ta kara yawan takunkuman tattalin arzikin da ta dorawa JMI, don tursasa mata ta yi abinda take bukata. Banda haka ta sha alwashin sai ta maida cikinin danyen man fetur na JMI a kasuwar duniya ya zama sifir.

Amma bukatar kasar Amurka a lokacin bata ga rana ba har wata gwamnati ta maye gurbinta, sannan a dayan bangaren kasashen turai wadanda tare da su aka kulla yarjeniyar JCPOA a shekara ta 2015 suma sun saba alkawalunsu a wannan yarjeniyar suka ci gaba da dorawa JMI takunkuman tattalin arziki ba iyaka. Wadanda duk wanda ya nazarcesu zai fahinci cewa suna son faduwar gwamnatin JMI ne. Amma har yanzun basu ga hakan ya auku ba. Kuma da yardar All…ba zasu taba gani ba.

Don haka bayan ficewar Trump daga yarjeniytar JCPOA da kuma sabawa sauran kasashen Turai alkawulan da suka dauka a yarjeniyar,  yarjeniyar ta zama babu wani amfani da JMI.

Amma bayan da Donal Trump ya sake komawa Fadar white House a farkon wanan shekara ta 2025 ya sake da ta wannan maganar sannan ya farfado da dukkan takunkuman tattalin arzikin da ya dorawa JMI a shugabancinsa na farko sannan yana kara wasu, daga lokaci zuwa lokaci. A wannan karon har da baraza na farwa kasar da yaki idan ta ki amincewa da sake tattauna shirin nukliyar kasar.

Ganin cewa JMI ta san cewa Amurka musamman Donal Trump ba mai cika alkawali ne ba, sai ta zabi tattaunawa ba kai tsaye ba da ita, saboda yaki zabi ne na karshe.

Don haka aka gudanar da zagaye na farko na tattaunawar a ranar 5 ga watan Afrilun da ya gabata a birnin Mascat na kasar Omman, sannan zagaye na biyu da na uku a ranar 12 da kuma 19 na watan Afrilu a biranen Roma da maskat, amma sai aka dage zaman a 4, wanda yaka mata a gudanar da ita a ranar 26 ga watan a birnin Roma.

Amma dan dan tsakanin nan sai muka fara jin maganganu daga jami’an gwamnatin kasar Amurka na cewa manufarsu ita ce hana JMI sarrafa makamashin nukliya kwatw-kwata, al-hali a zaman tattaunawa guda uku da aka gudanar Amuka bata kawo wannan batun ba. Amma an ji Trump da sakataren harkokin wajensa Rubio suna maganar hana JMI mu’amala da makamashin nukaliya kwata-kwata ne.

Sai dai wannan ketare jan layi ne, ga JMI, don ba zata taba amincewa da hakan ba, ko da za ta ga shiga yaki ne da wadannan kasashe.

Sayyid Abbas Aragchi ya fadawa Kajal Kallas jami’a mai kula da al-amuran harkokin waje na tarayyar Turai kan cewa bangarorin biyu zasu kai ga fahintar juna ne kawai idan dayan baranagren bai gabatar da wani abu wanda ya tabbatar da dayan bangaren ba zai taba amincewa ba. Ko kuma wani abu wanda ba zai taba yiyuwa ba.

Ya kammala da cewa Iran tana da tarjuba na saba alkalin Amurka, don haka idan ta kuskra da shigar da wani abu wanda ta san cewa JMI ba zata amince ba, ba inda tattaunawar zai je.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ECOWAS Ta Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Bunkasar Tattalin Arzikin Afrika Ta Yamma – Kwamred Bishir Dauda
  • Nijeriya ta soke ba da tallafin karatu a ƙetare
  • AIRLIN Ta Buƙaci Ƴan Arewa Su Ƙara Ƙaimi Wajen Rijistar Katin Zaɓe Da Na Shaidar Ɗan Ƙasa 
  • Hukuncin Tarar Dala Miliyan 220 Da Kotu Ta Ci Kamfanin Meta Ya Yi Daidai
  • Amurka ta matsa wa ƙasashe da ke fuskantar haraji su amince da Starlink
  • Ma’aikatar Yaɗa Labarai Ta Fara Bitar Ayyuka Na Tsakiyar Wa’adi
  •  Hare-haren Hizbullah Sun Jazawa HKI A Fagen Gona Asarar Dala Miliyan 108
  • Sharhin bayan Labarai: Mahangar Iran Dangane Da Tattaunawa Kan Shirinta na Makamashin Nukliya Na Zaman lafiya
  • Jami’an tsaro na ba da gudunmawar aikata miyagun laifuka a Nijeriya — Zulum