2025-04-30@19:54:56 GMT
إجمالي نتائج البحث: 629

«goyon bayan»:

    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce za a yi taro karo na hudu na shawarwari tsakanin Tehran da Washington kan shirin nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a birnin Rome na kasar Italiya a ranar Asabar mai zuwa. M. Araghchi ya fadawa manema labarai a gefen taron majalisar ministocin gwamnatin kasar na mako-mako yau Laraba cewa, inda ya ce taron na Rome zai kasance gabanin wani taro a ranar Juma’a na tsakanin Tehran da kasashen Turan nan uku da ake wa lakabi da E3 wato – Ingila, Faransa da kuma Jamus wadanda suka sanya hannu kan yarjejeniyar nukiliyar Iran ta 2015. Ya ce rawar da kasashen Turai uku ke takawa ta ragu sakamakon manufofinsu a tattaunawar da aka dade...
    Tsoffin ma’aikatan Hukumar Shirya Jarabawar (NECO), da suka yi ritaya na neman a biya su haƙƙoƙinsu da suke bin bashi. Shugaban ƙungiyar tsofffin ma’aikatan, Dokta Abdullahi Rotimi Williams ne ya bayyana hakan a bikin ƙaddamar da hedikwatar kungiyar a Minna, babban birnin Neja. Dokta Bashir ya zama shugaban Majalisar Shari’ar Musulunci ta Nijeriya Dokta Bashir ya zama shugaban Majalisar Shari’ar Musulunci ta Nijeriya Shugaban ya kuma koka kan yadda gwamnatin Nijeriya ta maida ritaya abin fargaba a wurin ma’aikata saboda tarin ƙalubalen da ke biyo bayan hakan, musamman maƙalewar haƙƙoƙinsu. “Da yawa tsoron ritaya ake yi yanzu. Don haka wannan ƙungiyar za ta taimaka wajen rage waɗannan matsalolin. “Babban ƙalubalen da muke fuskanta shi ne na lafiya. Don haka ina...
    Rayukan al’umma gami da dukiya musamman na ababen hawa na ci gaba da salwanta a Mahadar hanya ta yankin Tipper-garage da ke Dutse-Baupma, da ke kan titin da ya tashi daga garin Dutsen-Alhaji ya nufi garin Bwari, a yankin Birnin Tarayya Abuja. Titin da ke mastayin tagwaye ya haɗa yankin da garin Jere da ke Jihar Kaduna. Hanyar na ci gaba da ganin ƙaruwar kwararan motoci a sakamakon ingancinta da kuma karancin matsalar tsaro, idan a ka kamanta ta da babban titi Abuja zuwa Kaduna. Rawar da Arewa za ta taka a Zaɓen 2027 An ɗaure ’yar shekara 80 a kurkuku saboda dukan jikarta da silifas Adadin motoci da ke bin titin ya kara dagawa a bayabayan nan a dalilin...
    ’Yan siyasar yankin Arewa na ganin dole sai da goyon bayansu ɗan takara zai yi nasara a zaben Shugaban ƙasa. Hakan na zuwa ne bayan tsohon maitaimaka wa shugaban ƙasa a fannin siyasa, Alhaji Hakeem Baba-Ahmed ya yi wata hira, inda yake cewa, nan da wata shida yankin zai fitar da matsayarsa. An ɗaure ’yar shekara 80 a kurkuku saboda dukan jikarta da silifas Dalilin da manyan ’yan siyasa ke barin NNPP — APC Duk da cewa Hakeem ba shi ne mai magana da yawun al’ummar yankin ba, amma ana kallon sa a matsayin daya daga cikin manya a yankin, saboda tsohon matsayinsa na mai magana da yawun Kungiyar Dattawan Arewa (NEF). Tsarin siyasar kasar nan ya sa dole ne...
    A Kaduna, an kama wasu mutane uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, ciki har da wani da ya ce ya koma jihar ne domin kafa sabuwar ƙungiya bayan an kama abokan aikinsa a Kwara. Haka kuma, an kama wasu biyu da ke ɗauke da bindigogi. ‘Yansanda sun gano makamai da dama, ciki har da bindigogi ƙirar AK-47 da AK-49, da kuma wasu makamai da aka ƙera a gida. Wannan aiki na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na yaƙar garkuwa da mutane da safarar makamai a faɗin ƙasar. Kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya ce ana ci gaba da bincike, kuma za a gurfanar da waɗanda ake zargi a kotu da zarar an kammala binciken. Ya kuma yaba da goyon...
    A yammacin ranar Talata Arsenal ta karbi bakuncin PSG a matakin wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin zakarun Turai na bana. An dai barje gumi ne a filin wasa na Emirates, inda PSG ta yi wa Arsenal ci daya mai ban haushi har gida. DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya ISWAP ta ɗauki alhakin kashe mutum 26 a Borno PSG ta fara cin ƙwallo ta hannun Ousmane Dembele a minti na huɗu da take leda, haka suka je hutu har da zagaye na biyu, amma Gunners ba ta farke ba. Wannan shi ne karo na biyu da suka fuskanci juna a Champions League a kakar nan, inda Gunners ta yi nasarar cin 2-0...
    Ministan harkokin wajen kasar Brazil Mauro Vieira ne ya jagoranci wannan taro, inda bangarori daban daban suka tattaunawa kan yadda kasashen BRICS za su karfafa zaman lafiya da tsaron duniya. (Mai Fassara: Maryam Yang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Dabbobi sama da miliyan guda ne ake sa ran za a yi wa rigakafi a fadin karamar hukumar Babura da ke jihar Jigawa. Shugaban karamar hukumar Babura, Alhaji Hamisu Muhammad Garu, ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da aikin rigakafin dabbobi na bana. A cewarsa, fiye da tumaki da awaki miliyan daya da shanu dubu ashirin ake sa ran za a yi wa rigakafi a fadin karamar hukumar. Ya jaddada cewa karamar hukumar na da cikakken shiri da kudurin tallafawa sauyin noma na Gwamna Umar Namadi, domin inganta rayuwa da tattalin arzikin al’ummar jihar. Shugaban ya jaddada muhimmancin masu kiwon dabbobi su bada hadin kai yayin aikin rigakafin domin tabbatar da lafiyar dabbobinsu. Alhaji Hamisu Garu ya kuma nuna jin...
    Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Mista Mark Joseph Carney murna bisa zaɓensa a matsayin Firaiminista na 24 na ƙasar Kanada, bayan nasarar jam’iyyar Liberal a zaɓen majalisar dokokin da aka kammala kwanan nan.   A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya bayyana zaman Carney a wannan matsayi a matsayin wani muhimmin ci gaba, musamman a wannan lokaci da Kanada ke bukatar gogaggen shugaba domin fuskantar ƙalubale da dama.   Carney, wanda fitaccen masani ne a fannin tattalin arziki, ya taba rike mukamin Gwamnan Babban Bankin Kanada daga shekarar 2008 zuwa 2013, sannan ya ci gaba da zama Gwamnan Babban Bankin Ingila daga 2013...
    “Gwamnati ta amince da hada hannu da shugabannin al’umma na cikin gida domin tabbatar da tsaro.   “Muna gode muku kan abin da kuke yi. Amma muna bukatar Sarakuna su yi magana da mutanenmu kan kokarin da dukkanmu muke yi don kare al’ummominmu daga masu kutse.”   Gwamnan ya yi kira da a inganta hadin gwiwa a tsakanin al’umma da hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyi.   Mataimakin Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kwara, Alhaji Ibrahim Bologi II, wanda shi ne Etsu Patigi, ya yaba wa gwamnan bisa hada gwiwa da su domin tabbatar da tsaro a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
    Aƙalla wasu mutum 10 mafarauta sun rasa rayukansu yayin aikin ceto a ƙauyen Kopire da ke Ƙaramar Hukumar Hong ta Jihar Adamawa. Shugaban ƙungiyar mafarautan Nijeriya reshen Arewa maso Gabas, Shawulu Yohanna ne ya tabbatar wa Aminiya hakan a ranar Talata. Wani abin fashewa ya kashe mutum 26 a Borno An dawo da wutar lantarki a Sifaniya da Portugal A cewarsa, ajali ya katse hanzarin mafarautan ne yayin wani arbatu da mayaƙan Boko Haram da suka yi musu kwanton ɓauna a jeji. Ya bayyana cewa, mafarautan sun tunkari maharan ne bayan samun bayanan sirri da ke nuna cewa suna shirin kai hari. “Abin takaicin shi yadda ake yi wa Gwamnan Borno ƙafar ungulu a ƙoƙarin da yake yi na ganin...
    Gwamnan lardin Hormozgan (mai hedikwata a Bandar Abbas), Mohammad Ashouri, ya ce wani bangare na lamarin tashar jiragen ruwa na Shahid Raja’i ya faru ne sakamakon keta sanarwar adana kayayyaki ne, wani bangaren kuma na da alaka da sakaci da rashin kulawa (a wajen ajiya). AShouri, wanda ya bayyana ta hanyar faifan bidiyo a wata hira da aka watsa ta talabijin a yammacin jiya Litinin, ya bayyana sabbin alkaluman wadanda suka bata: Akwai mutanekusan 22 da suka bace, kamar yadda wasu gawarwakin mutane 22 ba a iya tantace su ba ko su waye ba. Ya ce: “Wasu daga cikin wadanda suka jikkata an hanzarta jigilar su ta jirgin saman soja zuwa asibitin birnin Shiraz.” Gwamnan lardin Hormozgan na Iran ya...
    An fara kasuwar baje koli na kayakin kasuwancin da ake samarwa a cikin Iran ko IRAN EXPO 2025, karo na 3 a nan Tehran. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kasuwar baje koli na Iran EXPO 2025 zai jawa masu zuna jari daga kasashen Afirka. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya fadawa kamfanin dillancin labaran IP kan cewa Kasuwar ta bana dai, za ta tara kamfanonin  masu samar da kayaki daga yankuna daban daban na kasar Iran da dama, kuma akwai fatan cewa wannan kasuwar ta zama mabudi ga kyautatuwan tattalin arzikin kasar. EXPO dai ita ce kasuwar baje koli na kayakin kasar Iran mafi girma wanda ake gudanarwa a ko wace shekara, sannan...
    Ana ci ga ba da zaman dar-dar a kasar Burkina faso, bayan da shugaban kasa mai ci Ibrahim traure ya sake tsallaka rijiya da baya, a wani kokarin juyin mulki wanda bai sami nasara ba a makon da ya gabata. Shafin yanar gizo na labarai ‘Africa News’ya nakalto radiyo Faransa RFI yana fadar cewa an bankado juyin mulkin ne bayan da dukkan bakin da aka gayyata a ranar 22 ga watan Afrilu zuwa wani taro sun kasa halattan taron. Wanda ya nuna shakku kan abinda aka kulla a cikin taron. Labarin ya kara da cewa a cikin yan kwanaki masu zuwa mutanen kasar zasu fito zanga-zanga don nuna goyon bayansu ga shugaban Traore. Har’ila yau ana gudanar da bincike a...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana a yau Litinin cewa, babu wata tattaunawa da aka yi ta wayar tarho tsakanin shugabannin kasashen Sin da Amurka a baya-baya nan, haka kuma bangarorin biyu ba su cimma wata yarjejeniya ko su tuntubi juna game da batun haraji ba. (Fa’iza Mustapha)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban kasar Siriya ya ki amincewa da bukatar kurdawan kasar daga dakarun Democradiyyan  kurdawa wato (SDF), na samar da tsarin tarayya a kasar bayan kifar da gwanatin Basshar Al-Asab. Jaridar The Nation ta nakalto shuga Al-Ahmad Sharaa yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa tsarin tarayyar barazana ce ga hadin kan kasar ta Siriya sannan tsarin tarayya ya sabawa yarjeniyar da aka kulla da kurdawan a baya-bayan nan. A wani taron da suka gabatar a makon da ya gabata,  jam’iyyar kurdawan kasar ta Siriya (SDC) ta fadawa “ The National  ”  bayan taron kan cewa suna bukatar tsarin tarayyar a kasar Siriya don shi ne kadai zai tabbatar da hakkinsu a kasar. A cikin watan maris...
    Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa kuskure ne abin da jami’anta ke yi na cin zarafi da cin zalin fararen hula saboda sun sanya kayan sojoji. Shugaban Sashen Hulɗar Sojoji da Fararen Hula na rundunar, Manjo-Janar Gold Chibuisi, bayyana cewa rundunar tana hukunta duk jami’inta da aka kama da laifin cin zalin farar hula saboda sanya kayan sojoji. Ya ce duk da haka doka ta haramta wa fararen hula sanya kayan sojoji ba bisa ka’ida ba, kuma laifi ne da zai iya kai su gidan yarin. Manjo-Janar Gold Chibuisi, ya ci gaba da cewa doka ba ta ba ta ba sojoji ikon hukuntawa balantana cin zalin masu aikata hakan ba. Sai kuma ta ba su ikon kama masu sojan gona...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Fira ministan Indiya ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana kokari da zage dantse wajen taimakawa a fagen inganta zaman lafiyar yanki da na duniya baki daya Fira ministan Indiya Narendra Modi ya yaba da rawar da Iran ta taka wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya, yana mai cewa: Gwamnatin Indiya tana goyon bayan kokarin Iran na karfafa zaman lafiya a yankin da ma duniya baki daya, yana mai jaddada bukatar warware takaddama ta hanyar diflomasiyya, ciki har da na Iran da Amurka. Har ila yau fira ministan na Indiya ya bayyana matukar bakin cikinsa dangane da abin da ya faru a tashar jiragen ruwa na Shahid Raja’e da ke lardin Hormozgan a kudancin kasar Iran,...
    A shekarar bara, ’yan kasuwa, musamman masu hadahadar kayan abinci da na amfanin gona a Nijeriya, kakarsu ta yanke saka, saboda tashin gwauron zabon da kayan a kasar. Galibin wadannan amfanin gona na kasuwanci ana fitar da su zuwa kasashen a duniya. Hukumar Bunkasa Fitar da Kayayyaki ta Nijeriya (NEPC) ta sanar a watan Agusta na shekarar ta 2024, cewa Najeriya ta samu gagarumin ci-gaba a fannin fitar da kayayyaki da ba na man fetur ba a watanni shidan farkon shekarar, inda ta samu kudin shiga kimanin dala biliyan 2.7. Yawan bukatar kayan a kasuwannin duniya ya kawo hauhawar farashin kayan abinci na yau da kullum da amfanin gona na kasuwanci. An kuma yi hasashen cewa farashin zai ci gaba...
    Ana kara samun karin ta’aziyya da kuma tallafa daga kasashen waje bayan fashewar da ta auku a tasahr jiragen ruwa na Dr Rajai a Bandar Abbasa. Tashar talabijin ta Press Tv ta nakalto ministan harkokin cikin gida Eskandar mumunina yana fadar haka, yana kuma cewa ya zuwa yanzu, mutane 14 aka tabbatar da mutuwarsu a yaynda wasu a yayinda wasu tsakanin 700-750 suka ji rauni. Tankar dakon mai ce ta yi binda a cikin tashar jiragen ruwan, a jiya, ammam ba’a san musabbin fashewar ba hanyanzu. Wuta ta kona tankar ta kuma tsallaka zuwa wasu kayaki kusa da wurin. Sannan bindigan da tankar ta tayi ya watsa wutar zuwa wasu wurare daga nesa, ya fasa gilashan mutocin da suke gewaue,...
    Sama da kwanaki hamsin da suka shuɗe ne aka aiwatar da sasanci a tsakanin wasu ’yan bindigar daji da al’ummomin da suka addaba don ganin an samu zaman lafiya a tsakanin yankunan. Sasancin, rahotannin da muka samu sun ce, jami’an tsaron Gwamnatin Tarayya ne suka shirya tare da tsara yadda za a yi shi karkashin kulawar sojoji. Kazalika, mun samu rahoton cewa, su ’yan ta’addan ne suka nemi a yi sulhun, sabanin baya inda aka neme su da yin hakan har sau biyu a lokacin mulkin tsohon Gwamna Aminu Bello Masari, amma babu wanda yake daukar wani lokaci yake wargaje. Gwamna Radda ya tubure Duk da cewa, har zuwa rubuta wannan rahoto, Gwamna Dikko Radda yana nan kan bakansa na...
    Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da kashe-kashen kisan kiyashi, kuma ana ci gaba da fama da yunwa a Gaza a daidai lokacin da kasashen duniya suka yi shiru An shiga rana ta arba’in da fara sabon farmakin da haramtacciyar kasar Isra’ila ke kai wa Zirin Gaza, a daidai lokacin da ake ci gaba da samun ta’adi da kisan kare dangi da ba a taba ganin irinsa ba, a daidai lokacin da Amurka ke goyon bayan ta’asar da kuma shiru na kasa da kasa wanda masu lura da al’amura suka bayyana a matsayin babban abin kunya. A cewar ma’aikatar lafiya ta Gaza, adadin wadanda suka yi shahada  sakamakon hare-haren ta’addancin ‘yan sahayoniyya ya kai 51,355 da kuma jikkatan wasu 117,248...
    Kwamishina CP Ibrahim Maikaba ya yaba da ƙoƙarin jami’ansa, yana kuma ƙara jaddada niyyar rundunar na yin aiki tare da al’umma domin samar da tsaro. Ya buƙaci mutane su riƙa bai wa rundunar sahihan bayanai a kan lokaci domin taimaka wa yaƙi da laifuka. Rundunar ta kuma fitar da lambobin da za a iya kira idan aka ga wani abu da ba a gamsu da shi ba; 08034805544, 07032490813 da kuma 09053872244 Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Iyalan wata dattijuwa da suka nema suka rasa sun shiga fargaba bayan gano gawarta a cikin wani maciji. Lamarin na zuwa ne bayan kumburin ciki ya bayyana sosai a kasurgumin maciji — kafin dangin tsohuwar su gano cewa maciji ya haɗiye kakarsu a cikinsa. Sojoji sun kashe ’yan ta’dda 1,770 sun kama 3,070 a Arewa —Janar Musa Magidanci ya kashe kansa saboda mutuwar matarsa a Neja  Iyalan matar da ta ɓace sun bi sawun macijin zuwa wani mai yawan ciyayi a kudancin Sulawesi na kasar Indonesia. ’Yan yankin sun tsorata matuka lokacin da suka ga maciji mai tsawon kafa 26 ya yi nauyi da wani babban kumburi a cikinsa. A lokacin da suka farka cikin macijin, sun gano gawar matar...
    Manyan kungiyoyin kwallon kafa Barcelona da Real Madrid zasu sake haduwa a wasan da ake yima kallon wasa mafi kayatarwa da akeyi a tsakanin kungiyoyin kwallon kafa a halin yanzu. Manyan kungiyoyin biyu duka na da dadadden tarihin iya taka leda da nuna kwarewa a harkar kwallon kafa, nasarorin da suka samu a kwallo ya sa ana yimasu kallon gagarabadau kokuma ace daukakakkun kungiyoyin kwallon kafa a Duniya. UEFA: Mbappe Zai Jagoranci Real Madrid Yayin Da Ta Ke Fatan Kafa Sabon Tarihi A Santiago Copa Del Rey: Real Madrid Ta Buƙaci A Sauya Alƙalin Wasa A Karawarta Da Barcelona Yau Asabar Barcelona da Real Madrid zasu buga wasan karshe na kofin Copa Del Rey a filin wasa na De La...
    ’Yan kasuwar kayan abinci sun bayyana yadda suke tafka asara  bayan sun saye wasu kaya sun ajiye suna jiran samun tuna mai tsoka idan kayan sun yi tashin gwauron zabo. A shekarar bara, ’yan kasuwa, musamman masu hadahadar kayan abinci da na amfanin gona a Nijeriya, kakarsu ta yanke saƙa, saboda tashin gwauron zabon da kayan a ƙasar. Galibin waɗannan amfanin gona na kasuwanci ana fitar da su zuwa ƙasashen a duniya. Hukumar Bunƙasa Fitar da Kayayyaki ta Nijeriya (NEPC) ta sanar a watan Agusta na shekarar ta 2024, cewa Najeriya ta samu gagarumin ci-gaba a fannin fitar da kayayyaki da ba na man fetur ba a watanni shidan farkon shekarar, inda ta samu kuɗin shiga kimanin dala biliyan 2.7....
    Karo na hudu kenan da Arsenal ta kara da Real a kofin Zakarun Turai, inda ta ci uku aka yi canjaras daya. A ranar 29 ga watan Afrilu Arsenal za ta karbi bakuncin PSG a wasan farko, kafin a buga na biyu mako daya bayan haka. Kungiyar dai ita ce a mataki na biyu a kan teburin gasar Firimiya ta kasar Ingila inda a wannan satin ake saran Liberpool za ta zama zakara a bana. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Rashin samar da daidaito a hada-ahadar kasuwanci, ya kasance abinda ya sanya Hukumar ta NPA ke cazar kudaden gudanar da aiki da yawa,” Inji Dantsoho.   Dantsoho wanda Janar Manaja na sashen hudda da jama’a da gudanar da tsare-tsare na Hukumar NPA Miista Seyi Iyawe Akinyemi ya wakilce shi a wajen taron, ya ce, NPA ta bai wa kamfanini biyar Lasisi a jihar Legas, bisa kokarin da take yi, na bunkasa fitar da kaya zuwa waje ta hanyar amfani da Tashoshin ta.   Sai dai, ya sanar da cewa, Hukumar na duba yuwuwar samar da rangwamen cazar kudaden, musamman domin ta kara inganta ayyukanta.   Ya yi nuni da cewa, Tashoshin Jiragen Ruwa waje ne da ke taimaka wa wajen...
    A watan Janairu, kwamitin ya raba naira tiriliyan 1.703 tare ga gwamnatoin tarayya da jihohi da kananan hukumomi. A wannan kudade, gwamnatin tarayya ta karbi naira biliyan 552.59, jihohi sun karbi naira biliyan 590.61, yayin da kuma kananan hukumomi sun karbi naira biliyan 434.57.   Rabon kudaden ya dogara ne kan kudaden shiga na naira biliyan 749.73, harajin BAT naira biliyan 718.78, harajin canja wurin kudi ta hanyar lantarki na naira biliyan 20.55, da kuma karin naira biliyan 214.   Rabon watan Fabrairu ya kai naira biliyan 1.678, inda gwamnatin tarayya ta karbi naira biliyan 569.66, jihohi sun karbi naira biliyan 562.20, sannan kuma kananan hukumomi sun sami naira biliyan 410.56.   Kudaden shiga sun hada da naira biliyan 827.63...
    Mai Magana da yawun dakarun ‘Kassam” Abu Ubaidah ya sanar da cewa; sun harbo sojojin mamaya 4 ta hanyar wani kwanton bauna da su ka yi musu a Beit-Hanun. Kakakin dakarun na ” Kassam” ya  kuma ce; Har yanzu suna ci gaba da kwamawa da ‘yan mamaya da kuma yi musu kwanton bauna a wurare mabanbanta.” Abu Ubadah ya kuma jaddada cewa; ‘yan gwgawarmaya su ne ke zabin lokacin da wurin da za su kai wa abokan gaba hari, kuma jaruntarsu tana bayyana daga garin Beit Hanun zuwa Rafah, da hakan yake a a matsayin abin alfahari ta fuskar soja. A ranar Alhamis din da ta gabata, ‘yan gwgawarmayar sun harbo sojojin HKI 4 daga cikinsu har da masu manyan...
    Ya koka kan halin da kasar ke ciki, kuma ya bukaci ‘yan arewa da su yi taka-tsantsan da ‘yan siyasa masu rarraba kawunan mutane da yaudara, gabanin babban zabe mai zuwa.   “Muna son gwamnati da za ta fahimci matsalolinmu kuma ta magance su. Bayan shekaru takwas na mulkin Muhammadu Buhari, mun dauki darasi.   ”Yanzu haka muna cikin wata gwamnati, kuma har yanzu muna kuka. Kuka kadai ne muka san yadda za mu yi?” Baba-Ahmed ya tambaya.   Baba-Ahmed ya ce arewa ta sha wahala sosai a lokacin Boko Haram, wanda ya shafi dukkan kungiyoyi, ciki har da Musulmi da Kiristoci da Fulani da Baju, da sauransu, yana mai jaddada bukatar hadin kai.   “Kafin Buhari ya zama shugaban...
    Li ya kara da cewa, Sin da Rasha sun bayyana goyon baya ga Iran wajen karfafa tattaunawa da hadin gwiwa da hukumar IAEA. (Mohammed Yahaya)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Manchester United ta kai zagayen kusa da karshe ne bayan doke Olympic Lyon ta Faransa da 5-4, bayan an yi canjaras da 2-2 a wasan farko da aka buga a Faransa. Kenan United ta yi nasara da 7-6 jimilla. Yanzu United za ta fafata wasan gab da na karshe ne da kungiyar Athletic Bilbao a ranar 21 ga watan Mayu.   Kungiyar ta Bilbao ta kai wasan karshe a gasar Europa sau biyu, na karshen a shekarar 2012, lokacin da Atletico Madrid ta doke ta da ci uku da nema a Bucharest.   Shekara 13 ke nan rabon United ta hadu da Athletic Bilbao, inda kungiyar ta Sifanya ta doke United da 2-1 a gasar ta Europa a shekarar 2012....
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran yayi kashedin kan illar ci gaba da killace Gaza da kuma hare-haren ta’addancin ‘yan mamaya Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Ci gaba da rashin hukunta ‘yan sahayoniyya kan kisan gillar da suke yi a zirin Gaza da Gabar yammacin kogin Jordan, da kuma mamayar wasu yankunan kasar Labanon da Siriya yana da matukar barazana ga zaman lafiya da tsaro a yankin. A cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Juma’a, Isma’il Baqa’i ya yi kakkausar suka kan ci gaba da ayyukan wuce gona da iri da na ta’addancin yahudawan sahayoniyya a Gaza da Lebanon.
    Sayyid Fadlallah ya bayyana cewa: Ana samar da makamai ne domin kare kasa da kuma matsa wa abokan gaba A cikin hudubar sallar Juma’arsa daga mumbarin masallacin Imamain al-Hassanain (amincin Allah ya tabbata a gare su) da ke Haret Hareik a kudancin birnin Beirut, Sayyid Ali Fadlallah ya yi kira da a dauki dukkan matakai na tursasawa makiya yahudawan sahayoniyya janyewa daga yankin kasar Lebanon da ta mamaye, da daina kai hare-haren wuce gona da iri kullum rana kan yankunan Lebanon, da kuma sakin mutanen da suka kama a matsayin fursunonin yaki. Malamin ya bukaci dukkanin ‘yan kasar Lebanon, ba tare da la’akari da mazhabobin su ba, ko kungiyoyinsu, ko kuma matsayinsu na siyasa, da su tashi tsaye wajen gudanar...
    Wasu mutane 13 sun faɗa a komar ’yan sanda ka zargi da zubar da ciki da kuma mutuwar wata budurwa ’yar shekara 18 a Jihar Bauchi. Kakakin ’yan sandan jihar, CSP Mohammed Ahmed Wakil, ya ce ana tuhumar huɗu daga cikin mutanen da aikata laifin fyade, zubar da ciki da kuma mutuwar budurwa a garin Misau da ke Ƙaramar Hukumar Misau. Wakil ya ce, a ranar 4 ga Afrilu, 2025 sun samu bayanai ewa, kimanin watanni hudu da suka gabata, wasu matasa biyu a yankin Lariski da ke Misau, sun kama wata yarinya mai shekaru 18 da suka yi ta yi lalata da ita sau da yawa. Ya ce a lokacin da suka lura tana ɗauke da juna biyu, sai...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayan labarammu zai yi magana a kan ‘wani makircin da kasar faransa ta kullawa falasdinawa a gaza’ don su amfana da kwararrunsu’ wanda ni tahir amin zan karanta. ///… Shugaba kungiyar kare hakkin bil’adama masi suna [the Euro-Mediterranean Human Rights Monitor] ta fallasa wani shiri tsakanin gwamnatin kasar faransa da HKI na fitar da kwararru da kuma masana falasdinawa da suka rage a Gaza, zuwa wajen yankin, kafin HKI ta fa wani gagarumin kissan kiyashi a yankin kashe falasdinawa da suka rage a yankin. Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya nakalto Ramy Abdu shugaban kungiyar na fadar haka, ta kuma kara da cewa, offishin jakadancin kasar Faransa da ke birnin Qudus da aka...
    Bankin Duniya ya yi hasashen cewa talauci a Najeriya zai ƙaru da kashi 3.6 cikin ɗari a cikin shekaru biyar masu zuwa, ciki har da shekarar zaɓe ta 2027. Wannan hasashe yana ƙunshe ne a cikin rahoton Bankin wanda aka fitar a lokacin taron bazara na Bankin Duniya da Asusun Lamuni na Duniya (IMF) da ake yi a birnin Washington, D.C., a ƙasar Amurka. Rahoton ya jaddada cewa duk da wasu nasarorin da aka samu a harkokin tattalin arziki a kwanakin baya, musamman a ɓangaren da ba na man fetur ba a cikin rubu’i na ƙarshe na shekarar 2024, matsalolin da suka shafi dogaro da albarkatun ƙasa da kuma raunin ƙasa na iya kawo cikas ga ci gaba. A cewar...
    Kasar faransa ta jaddada anniyar na ci gaba da tattaunawa kan shirin nukiliyar iran. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Faransa ya bayyana a ranar Alhamis cewa, Faransa na ci gaba da jajircewa wajen ganin an warware matsalar nukiliyar Iran ta hanyar diflomasiyya, kuma a shirye take ta ci gaba da tattaunawa da Tehran. A yayin taron manema labarai na mako-mako a birnin Paris, Christophe Lemoine ya jaddada cewa: “Muna ci gaba da jajircewa wajen warware matsalar nukiliyar Iran ta hanyar diflomasiyya, kuma a shirye muke mu ci gaba da tattaunawa da Tehran.” Wannan bayanin na zuwa ne bayan da ministan harkokin wajen Iran Seyyed Abbas Araghchi ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na X cewa, Tehran a shirye ta ke...
    Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah sayyid Ali Khamnei wanda ya gabatar da jawabi dangane da zagayowar ranar shahadar Imam Ja’afar Assadiq ( a.s) ya bayyana cewa: Tafarkin Imaman Ahlul-Bayti (a.s) ya kasance na gwgawarmaya da jajurcewa, kuma koyarwarsu ta ginu ne akan mandiki da kafa dalili. Jagoran juyin musuluncin na Iran ya ce; rayuwar Imam Ja’afar Assadiq           (  A. S ) ta ginu ne akan tafarkin koyar da ilimin addinin Allah, wacce ta kasace mai cike  da abin mamaki. Jagoran juyin musuluncin na Iran ya siffata mutanen Gaza da Lebanon da cewa suna tafiya ne akan wannan tafarki na Imaman shiriya.
    Ya ce, “Muddin muna da kwarin gwiwa, da karfin goyon bayan juna da hadin kai, za mu kai ga kawar da manufofi masu illa, da wanzar da daidaito da ci gaba a manufofin jagoranci a fannin kare yanayi da samar da ci gaba. ” (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) Bauchi ta sallami ɗaya daga cikin malamanta, Dokta Usman Mohammed Aliyu daga jami’ar bisa zargin neman yin lalata da wata ɗaliba matar aure da ke karatun digiri na biyu. Idan dai ba a manta ba, Kamila Rufa’i Aliyu, ɗalibar Sashen koyon aikin injiniya ce, a shekarar bara ta roƙi mahukuntan Jami’ar ta hannun tsangayarsu da su binciki lamarin. Yobe na ɗaya daga cikin jihohin Najeriya mafi zaman lafiya – Buni An kama mata 2 na ƙoƙarin sayar da ƙananan yara da aka sace Ɗalibar ta kuma zargi Dakta Aliyu da yi mata barazanar rashin samun nasarar karatunta idan har ta ƙi amincewa da biyan buƙatarsa. Malamin da ya samu labarin ƙarar da aka shigar da...
    Hukumar lura da gidajen bashin ma’aikatan gwamnatin tarayya (FGSHLB) ta sanar da cewa ta fara tattara jerin sunayen ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya amma ba su biya bashin gidajen da suka karɓa ba. Shugabar sashin sadarwa da hulɗa da jama’a na FGSHLB, Ngozi Obiechina, ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis a Abuja, inda ta ruwaito cewa shugabar hukumar, Salamatu Ahmed, tana cewa wannan matakin yana nufin dawo da dukiyoyin da aka yi rance daga ma’aikatan da suka yi ritaya amma ba su kammala biyan bashin ba. Rashin Tsaro: Gwamnatin Neja Ta Saka Dokar Zama A Gida A Minna Gina Al’umma Mai Kyakkyawar Makomar Bai Daya: Jigon Ziyarar Xi A Kudu Maso Gabashin Asiya Salamatu...
    Sabuwar gwamnatin Siriya tana kara matsa lamba kan bangarorin ‘yan gwagwarmaya domin Isra’ila ta janye daga wasu yankunan kasarta Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da tura kayayyakin soji zuwa tsaunukan Dutsen Harmon, yayin da suke hanzarta gina abin da suka kira “Katangar tsaro.” Har ila yau, sun karfafa wuraren tsaro da suka kafa a cikin yankunan Siriya, a cikin abin da gwamnatin Isra’ila ta kira “yankin da ke da kariya,” wanda ya hada da mamaye wasu sassan garuruwan Quneitra da Dara’a. Majiyoyin cikin gida a garin Nawa da ke cikin karkarar Dara’a na cewa, mahukuntan kasar Siriya na ci gaba da daukan matakan matsin lamba, ta hanyar shugabannin kabilu da kwamandojin ma’aikatar tsaro a Dara’a, na tilastawa bangarorin da...
    Gwamnatin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da ƴan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda sun amince su dakatar da faɗa a gabashin ƙasar har sai an kammala tattaunawar sulhu da ke gudana a halin yanzu wanda Qatar ke shiga tsakani. Wannan dai ita ce yarjejeniyar sulhu ta baya-bayan nan tun bayan da ƴan tawayen suka ƙara kai farmaki a gabashin ƙasar inda hukumomi suka ce an kashe mutane 7,000 tun daga watan Janairu. A ranar Larabar da ta gabata ce, ɓangarorin biyu suka ba da sanarwar yin aiki tare don samar da zaman lafiya, bayan shafe sama da mako guda suna tattaunawa, wanda suka ce an gudanar cikin aminci tare da mutunta juna. A watan da ya gabata, shugaban ƙasar...
    Babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya ba da umarnin ga rundunar sojin Najeriya da ta fatattaki ‘yan bindigar da ke addabar al’ummar kananan hukumomin Baruten da Kaiama na jihar kwara da Borgu da ke dajin Kainji a jihar Neja cikin wata guda.   A jawabin da ya yi wa dakarun rundunar soji bataliya ta 22  a Sobi Ilorin, Oluyede ya ce sojojin Najeriya ba za su bari tashin hankalin yankin arewa maso gabas ya rikide zuwa arewa ta tsakiya ba.   A cewarsa nauyi ne da ya rataya a wuyan sojojin Najeriya su kare martabar yankunan kasar.   Shugaban hafsan sojin ya ce dole ne a fatattaki ‘yan bindigar daga yankin Najeriya nan da wata guda.  ...
    Sanarwar ta kara da cewa, Shugaban tawagar ‘yan fashin, Baba-Beru ya samu munanan raunuka, wanda daga baya ya rasu a Asibiti.   “An garzaya da dukkan wadanda suka samu raunuka zuwa Asibitin kwararru na Murtala Mohammed da ke Kano, inda Baba-beru ya rasu a lokacin da ake jinyarsa, amma jami’an ‘yansanda an sallame su bayan sun gama jinya,” in ji sanarwar.   Rundunar ‘yansandan ta ce Baba-Beru, mazaunin Kofar Mazugal a karamar hukumar Dala, na cikin jerin sunayen wadanda ake nema ruwa a jallo kafin faruwar lamarin.   Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Ibrahim Bakori, ya yabawa bajintar jami’an da suka dakile yunkurin ‘yan fashin tare da jaddada aniyar rundunar na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a jihar.  ...
    Gwamnatin Shugaban kasa John Mahama ta tsige Gertrude Torkornoo daga mukaminta na babbar mai shari’ar kasar, bisa wasu zarge-zarge da ake yi mata, domin bayar da damar gudanar da bincike. Matakin da gwamnatin ta dauka na tsige babbar mai shari’ar ya jawo cece-kuce a tsakanin mutanen kasar. Tsohon mai shigar da kara na kasar Godfrred Yeboah Dame ya yi tir da matakin na gwamnati da ya siffata da farmaki mafi girma akan ma’aikatar shari’a a tarihin kasar.”  Ita kuwa jam’iyyar hamayya ta zargi shugaban kasa da tsoma baki a harkokin shari’ar kasar, domin nada alkalan da za su  zama masu biyayya ga jam’iyyar da take Mulki ta ( NDC). Torkornoo da ta hau mukamin nata a 2023, kuma  ta kasance...
    Hukumar lafiya ta duniya  (W.H.O ) ta sanar da cewa rashin magani da na’urorin wanke koda a Gaza, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 400 masu fama da wannan cutar. Hukumar lafiyar ta duniya ( w.h.o) ta kuma yi ishara da yadda ‘yan mamaya su ka lalata bangarorin da suke kula da cutuka na musamman a cikin asibitoci. Ita ma hukumar lafiya ta Gaza ta bayyana cewa; masu fama da cutar koda a yankin suna fama da matsaloli na rashin Magani, kuma daruruwa daga cikinsu sun mutu saboda hakan. Haka nan kuma ta  yi ishara da yadda mutane 400 daga cikinsu su ka rasu, da hakan yake nufin kaso 40% na adadin masu wannan cutar. A gefe daya, ma’aikatar kiwon lafiyar...
    Al’ummar Gaza sun bukaci kasashen duniya da su tilasta daukan matakin shigar da kayan agaji cikinsu Al’ummar Falasdinawa a Zirin Gaza sun yi kira ga hukumomin kasa da kasa da na Larabawa da su tilasta shigar da kayan agaji cikin yankin, duba da munanan bala’in jin kai da al’ummar yankin ke fuskanta. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Akif al-Masri, kwamishinan hukumar koli ta al’amuran da suka shafi Falasdiwa a Gaza, ya ce: “Matsalar yunwa tana barazana ga rayuwar dubban daruruwan mutanen Gaza,  yana mai cewa: Mafi yawan gidaje kusan babu kayan abinci, kuma iyalai ba za su iya samun abincinsu na yau da kullum ba.” Al-Masry ya tabbatar da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun ketare dukkan iyakokin kasa...
    Kungiyar raya tattalin arziki ta kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta fara taro a kasar Ghana don tattauna al-amura da suka shafi kasashen Niger Burkina Faso da kuma Mali. Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa agendar taron nasu na kwanaki biyu, sun hada da huldar kungiyar da kasashen uku, musamman cibiyoyin ECOWAS da suke cikin kasashen, sannan da batun kudaden fito na kashi 0.5% wanda kungiyarsu ta (AES) ta dorawa kayakin da suke shigowa  kasashensu da sunan gudanar da kungiyarsu. Labarin yace kungiyar ECOWAS bata karban kudaden fito da Visa  daga kasashen kungiyar gaba daya tun kafin kasashen uku su fita amma a halin yanzu su suna karba. Kasashen uku sun bayyana ficewarsu daga ECOWAS ne daga farkon wannan...
    Kungiyar Hamas ta yi kira ga jami’o’in Yammacin Kogin Jordan da su shirya zanga-zangar nuna goyon baya ga Gaza da kuma kin amincewa da kisan kare dangi Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, ta yi kira ga jami’o’in Yammacin Kogin Jordan da su tashi tsaye wajen gudanar da gangami da zanga-zanga a ranar Talata, domin nuna goyon baya ga Gaza, da tsayin dakanta, da kuma kawo karshen kisan kiyashi. A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, shugaban kungiyar Hamas Abdel Rahman Shadid ya bukaci ‘yan Falasdinu gami da daliban jami’o’in Falasdinu masu ‘yanci a Yammacin Gabar Kogin Jordan da suke mamaye da su da su tashi tsaye tare da gudanar da zanga-zangar bacin rai da aka shirya za a fara a yau...
    Munanan abubuwan da suka faru na zubar da jini bayan wasa tsakanin Al-Ahly Tripoli da Al-Suwaihli a Libya A kusa da filin wasa na birnin Tripoli an ga abubuwan na zubar da jini bayan wasan da aka yi tsakanin Al-Ahly Tripoli da Al-Suwaihli, lokacin da wasu motocin ma’aikatar harkokin cikin gida ta gwamnatin hadin kan kasa suka bindige magoya bayanta da gangan. Shaidun gani da ido sun bayyana cewa bayan an kammala wasan ne wata mota dauke da makamai ta kutsa cikin wurin da jama’a ke cunkoso, inda suka bi ta kan wasu matasa, lamarin da ya haifar da firgici da hargitsi. An kuma ji karar harbe-harbe a wurin, lamarin da ya ta’azzara lamarin tare da jikkata wasu da ke...
    Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya dakatar da basaraken yankin Masarautar Uwano Kingdom, Dakta George Oshiapi Egabor, nan take saboda matsalar yi garkuwa da mutane a yankin. Dakta George Oshiapi Egabor shi ne Okumagbe na Masarautar Uwano da ke Agenebode a Karamar Hukumar Etsako ta jihar. Kakakin gwamnan, Fred Itua, a cikin wata sanarwa, ya bayyana cewa an dakatar da basaraken ne har sai abin da hali ya yi, saboda yawan samun kashe-kashe da kuma garkuwa da mutane a masarautarsa a baya-bayan nan. Ya ce tuni jami’an tsaro suka tsare sakataren basaraken, Cif Peter Omiogbemhi, sakamakon wani sabon hari a da ya yi ajalin wani bafade, Cif John Ikhamate. Mutanen da aka kashe a Binuwai sun ƙaru zuwa 72 An...
    Wang Yi ya ce, yana son yin aiki tare da Monday Semaya, domin aiwatar da matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da karfafa cudanya da hadin gwiwa a tsakanin sassan biyu, da daukaka zumuncin kawancen Sin da Sudan ta Kudu a bisa manyan tsare-tsare. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A daren yau ne shugaba Bola Tinubu ya dawo Abuja bayan kammala ziyarar aiki ta makonni uku a Turai, inda ya gudanar da muhawara da manyan jami’an ƙasa da ƙasa don inganta dangantakar Najeriya a fannin tsaro da ci gaban tattalin arziki. Jirgin shugaban ya sauka ne a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe a Abuja da misalin ƙarfe 9:50 na daren ranar, inda ya samu tarɓa daga manyan jami’an gwamnati, ciki har da Sakataren Gwamnatin tarayya, Sanata George Akume; Shugaban Ma’aikatan Shugaban ƙasa, Hon. Femi Gbajabiamila; Mai Ba da Shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu; Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare-Tsare, Sanata Atiku Bagudu, da Ministan Birnin Tarayya, Barrister Nyesom Wike. Zuba Jari Daga Kasashen Waje A Noman...
    Kasar Cambodiya ce zangon ziyararsa ta karshe. Inda kasashen biyu suka amince da gina al’umma kyakkyawar makomar bai daya a sabon zamani, wanda kamar yadda bangarorin biyu suka jaddada, ya dace da muhimman muradun jama’ar kasashen biyu. La’akari da kalubalan da ake fuskanta a tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban daban, kasar Sin ta taka rawa wajen samar da zaman lafiya a duniya. Kuma ziyarar shugaba Xi a kudu maso gabashin Asiya a daidai lokacin da duniya ke fuskantar barazanar bangaranci da daukar matakai bisa radin kai da Amurka ta rike a matsayin makamin mu’amalantar sauran kasashen duniya, ta sa kaimi ga samar da zaman lafiya da wadata a yankin da ma duniya baki daya. (Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana...
    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Burnley United tare da takwararta ta Leeds United sun samu nasarar dawowa gasar Firimiya bayan samun nasara a mabanbantan wasannin da suka buga. Burnley ta doke Sheffield United da ci 2-1 da yammacin yau domin samun wannan nasarar, hakazalika Leeds United ta samu nasara akan Stoke City da ci 6-0 a daya wasan na yau, dukkan kungiyoyin biyu zasu buga gasar Firimiya Lig ta badi. Alex Iwobi Ya Kafa Tarihi A Gasar Firimiya Salah Ya Kafa Tarihi Yayin Da Liverpool Ke Dab Da Lashe Gasar Firimiya Yayinda kungiyoyin Firimiya Southampton da Leicester City suka koma gasar Championship su kuma Burnley da Leeds United sun samu nasarar tsallakawa zuwa gasar Firimiya a kakar wasa ta badi....
    Ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta tabbatar da tsare-tsaren da kwamitin tsakiyar jam’iyyar kwaminis ta Sin da majalisar gudanarwar kasar suka tsayar don gaggauta kyautata tsarin tafiyar da ciniki daidai da zamani, da ingiza ingantaciyar bunkasuwar cinikin sarin kaya da sayen kayan masarufi bisa matakai daban-daban. Bisa alkaluman da hukumar kididdigar Sin ta fitar a rubu’in farko wato daga watan Janairu zuwa Maris na bana, darajar wadannan bangarori ta karu da dalar biliyan 452.5 a wadannan watanni uku, wanda ya karu da kashi 5.8% bisa na makamancin lokacin bara, kana adadin ya kai kashi 10.4% bisa na dukkan GDPn kasar.   Nagartacciyar bunkasar wadannan sana’o’i na nuna goyon baya na tsarin habaka bukatu cikin gidan kasar da tafiyar da tattalin...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, sharhin bayan labarammu na yau za yi magana dangane da “Rage kisasfin kudan ma’aikatar harkokin wajen Amurla da kimani kasha 50% da kuma tasirinsa ga matsayin Amurka a duniya da kuma cikin gida. Wanda ni tahir amin zan karanta. A makon da ya gabata ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bada sanarwan, rahe kasafin kudi na ma’aikatar harkokin wajen kasar da kasha 50%, saboda haka kuma ya rufe wasu daga cikin ofisoshin jakadancin kasar da kananan ofisoshin jakadancin kasar fiye da 30 a yankuna daban daban a duniya amma mafi yawansu a nahiyar Afirka. Dangane da wannan matakin da gwamnatin kasar Amurka masana daga ciki ga wajen kasar ta Amurka masu yawa...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaba Tinubu ya bar Nijeriya ne a ranar 2 ga watan Afrilu zuwa birnin Paris na kasar Faransa, domin wata ‘yar gajeriyar ziyarar aiki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wasu Falasdinawa sun yi shahada a cikan kwana na 35 a sabon yakin da yahudawan sahayoniyya suka sake daurawa kan Zirin Gaza Sojojin gwamatin mamayar Isra’ila suna ci gaba da yakin kisan kiyashi a Zirin Gaza tun bayan sake ci gaba da yau tsawon kwanaki 35 da suka gabata, bayan da Fira minista Benjamin Netanyahu ya yi watsi da yarjejeniyar tsagaita bude wuta, kuma yana gudanar da wannan ta’asa ne tare da goyon bayan siyasa da na sojan Amurka, sannan kungiyoyin kasa da kasa gami da gwamnatocin kasashe sun daukin matakin yin shiru da rashin gwada wani yunkurin kalubalantar wannan danyen aiki. Cibiyar yada labaran Falasdinu ta watsa rahoton cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun kaddamar da hare-hare da dama tare...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A daidai lokacin da ake tunanin samun sauƙi daga tarin matsalolin tsaro da na tada ƙayar baya a Najeriya, sai ga wasu sabbin matsalolin na ƙara kunno kai. Yayin da a wannan lokaci ake fuskantar hare-haren da ake zargin na ƙungiyar Boko Haram ne a Arewa maso Gabas, da kuma sabbin kashe-kashe a sassan jihohin Filato da Binuwai, sai kuma ga wata sabuwar ƙungiya da ake zargin ta ’yan ta’adda ce mai suna Mahmuda ta ɓulla a Jihar Kwara. To ko mene ne ya haddasa wannan koma-baya ta fuskar tsaro? Shin a ganinku, me ya sa matsalar tsaro “ta gagari gwamnatin” Najeriya? NAJERIYA A YAU: Sabbin dabarun hana matasa aikata laifi DAGA LARABA:...
    Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa tace uranium din ta tamakar jan layi ne a tattaunawar dake wakana tsakaninta da Amurka. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar ne Kazem Gharibabadi ya bayyana hakan, inda ya ce hakkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ne inganta sinadarin Uranium, yana mai jaddada cewa, wannan batu a matsayin jan layi a tattaunawar da Amurka. Mista Gharibabadi ya bayyana haka ne a yayin taron kwamitin majalisar dokoki kan tsaron kasar da manufofin ketare, inda ya yi wa ‘yan majalisar bayani kan shawarwari zagaye na biyu tsakanin Tehran da Washington, wanda ya gudana a Rome, babban birnin kasar Italiya. Jami’in na iran ya kara da cewa tawagar kasar ta jaddada matsayinta na cewa Iran ba ta neman...
    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Leicester City dake buga babbar gasar Firimiya ta kasar Ingila ta koma gasar yan dagaji ta Championship bayan da tayi rashin nasara a guda a wasanta da Liverpool. Leicester wadda ta lashe gasar Firimiya a shekarar 2016 ta samu maki 18 kacal a wasanni 33 da ta buga, ta zura kwallaye 27 yayinda aka zura mata kwallaye 73 a ragarta, Leicester ta koma gasar Championship duk da cewar akwai sauran wasanni 5 da su ka rage ba a buga ba a gasar Firimiya ta bana. Yaushe Liverpool Za Ta Lashe Gasar Firimiyar Ingila? Salah Ya Kafa Tarihi Yayin Da Liverpool Ke Dab Da Lashe Gasar Firimiya Kocin Leicester Ruud Van Nistelrooy ya karbi ragamar horarwar...
    Tsohon mashawarcin Shugaba Bola Tinubu kan harkokin siyasa, Dokta Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana cewa babu wani ɗan siyasa da zai iya lashe kujerar shugabancin Nijeriya a Zaɓen 2027 ba tare da goyon bayan yankin Arewacin ƙasar ba. Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana hakan a wata hira ta bidiyo tare da tsohon Babban Sakataren Hukumar Kula da Inshorar Lafiya (NHIS), Farfesa Usman Yusuf. NDLEA ta kama hodar iblis da aka ɓoye cikin littafai ana shirin kaiwa Saudiyya Zaɓen 2027: Me ya sa jam’iyyu ke neman tabarrakin Buhari? Ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba yankin Arewacin Nijeriya zai fuskanci alƙiblarsa ta siyasa. “Nan da watanni shida mutanen Arewacin Nijeriya za su fayyace inda suka dosa, saboda haka zaɓi ya rage wa...
    An samu rahoton cewa, Fursunoni tara a gidan yari na Oko Erin a jihar Kwara a ranar 19 ga watan Afrilu, sun tsere. Majiyoyin leken asiri sun shaida wa Zagazola Makama cewa, da misalin karfe 10:00 na dare, wani ma’aikaci a gidan, mai suna Joseph Issa, ya sanar da faruwar lamarin. Rugujewar Gini A Legas: Adadin wadanda Suka Mutu Ya Kai Biyar, An Ceto 20 Wang Yi Ya Yi Bayani Kan Ziyarar Shugaba Xi Jinping A Vietnam Da Malaysia Da Cambodia Ba tare da bata lokaci ba, ‘yansanda suka yi gaggawar isa wurin, inda suka sake kama daya daga cikin wadanda suka tsere, mai suna Abdul Raman Misa mai shekaru 15. An mayar da Misa gidan yarin, yayin da ake...
    A faransa ana ci gaba da tsare wata ‘yar Iran mai goyan bayan Falasdinu, bis azarginta da iza ta’addanci. Mahdieh Esfandiari (mai shekaru 35) ana tsare da ita tun ranar 28 ga watan Fabrairu, bayan kama ta a binrin Lyon, inda ta ke da zama. Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, Esmail Baghai, ya yi Allah wadai da kama Mahdieh Esfandiari, yana mai yin Allah wadai da “manufofin kasashen Turai” wanda “ya kunshi murde adawa da “kisan kare dangi” da Isra’ila ta yi a Gaza. Ya kara da cewa ba a sanar da ofishin jakadancin Iran da ke birnin Paris da kuma iyalan yarinyar ba. A nasa bangaren, lauyan Mahdieh Esfandiari, Nabil Boudi, ya nuna rashin jin dadinsa...
    ’Yan ta’addar ISWAP sun tarwatsa wata gada da ta haɗa garin Ngirbuwa da garin Goneri a Ƙaramar Hukumar Gujiba da ke Jihar Yobe. Wannan na zuwa ne ƙasa da mako guda da ‘yan ta’addan suka lalata gadar nan ta Mandafuna da ta haɗa garin Biu da Damboa a Jihar Borno. JAMB ta sauya ranar soma jarrabawar bana Manyan jami’an gwamnati sun halarci auren ’yar tsohon Gwamnan Bauchi Majiyar leƙen asiri ta shaida wa Zagazola Makama cewa harin ya afku ne da misalin ƙarfe 10:30 na daren ranar ranar Alhamis ɗin da ta gabata, ta hanyar amfani da wani bam wajen lalata sauran sassan gadar. Wannan aikin ta’addanci ya kawo cikas ga zirga-zirga tsakanin al’ummomin biyu da ma sauran al’ummomin yankin,...
    A yayin wannan ziyara har ila yau, shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, yakin cinikayya zai gurgunta tsarin cinikayyar kasa da kasa, da haifar da mummunan tasiri a kan tattalin arzikin duniya, da tarnake halaltacciyar moriyar kasashen duniya, musamman ma ta kasashe masu tasowa.   Sai dai kuma, yayin da ake fuskantar karuwar masu nuna ra’ayin kariyar ciniki a duniya, kasar Sin za ta tsaya kan kokarin tabbatar da ci gaban tattalin arziki, kuma za ta ci gaba da samar da dimbin gudummawa ga yunkurin raya tattalin arzikin duniya, in ji shugaban kasar Sin. (Bello Wang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga...
    Hukumar Shirya Jarrabawa Shiga Manyan Makarantu ta Najeriya, JAMB, ta sanya Alhamis, 24 ga watan Afrilu, a matsayin ranar soma jarrabawar wannan shekarar maimakon ranar 25 ga wata da ta fara sakawa. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Dokta Fabian Benjamin ya fitar ranar Asabar. Manyan jami’an gwamnati sun halarci auren ’yar tsohon Gwamnan Bauchi NAJERIYA A YAU: Sabbin dabarun hana matasa aikata laifi A cewarsa, an samu sauyin ranar ne domin tabbatar da muhimman matakan da ta ɗauka sun yi daidai da tnade-tanaden sauran hukumomin da za su taimaka mata wajen gudanar da aikin. Dokta Benjamin ya ce a yanzu haka waɗanda za su rubuta jarrabawar za su iya fitar da katin shiga jarrabawar –...
    Yadda za ku hada: Idan kuka samu filawa kamar kofi daya, sai suga kamar babban cokali biyu, sai gishiri kadan haka, sai baikin fauda rabin babban cokali , baikin soda rabin babban cokali, kwai daya, sai mai babban cokali biyu, madara rabin kofi. Sai ki tankade filawar sannan ki zuba suga ki zuba gishiri baikin fauda ki zuba duk kayan da na ambata sai ki cakuda su gaba daya, ki dame su sosai, sannan ki dora firayin fan dinki idan ya danyi zafi sai ki fara zubawa daidai fadin da kike so, sannan za ki iya yi mishi dan kunne haka a sama zai dauki hankalin yara, amma za ki rage wuta ne sosai saboda shi baya son wuta, idan...
    Mayakan kungiyar ta’addanci ta ISIS sun sake kunno kai a garuruwan Deir ez-Zor da Hasaka na kasar Siriya Yankunan Deir ez-Zor da Hasakah dake arewa maso gabashin kasar Siriya suna ci gaba da samun karuwar bullar ayyukan ta’addancin kungiyar ISIS tun daga farkon wannan wata. Hare-hare 13 sun kai sune kan Dakarun Syrian Democratic Foeces ta (SDF) ta Kurdawa masu samun goyon bayan Amurka da kuma fararen hulan yankunan, lamarin da ya janyo hasarar rayuka. A cewar kungiyar kare hakkin bil- adama ta Syria, hare-haren sun bambanta wajen aiwatar da su, daga harin kwanton bauna zuwa na kai hari kai tsaye, wanda ke nuni da yadda kungiyar ta canza yanayin kai hare-hare a yankunan saboda matakan tsaron a garuruwan. Wadannan...
     Sojojin Sudan sun sanar da kashe mayakan dakarun kai daukin gaggawa 70, ciki har da kwamandojin mayakan a birnin a El Fasher fadar mulkin jihar Darfur ta Arewa A ranar Alhamis ne rundunar sojin Sudan ta sanar da kashe mayakan da jami’an dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces fiye da 70 da suka hada da kwamandojin ‘yan tawaye a shiyar kudu maso gabas da arewa maso gabashin El Fasher. Kamfanin dillancin labaran Sudan (SUNA) ya watsa rahoton cewa: A ranar Alhamis ne sojojin kasar Sudan tare da hadin da tallafin dakarun hadin gwiwa na kungiyoyin fafutuka, da hukumar leken asiri ta kasar da ‘yan sanda, suka dakile wani mummunan hari da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support...
    Shugaban ya kuma bai wa masu ruwa da tsaki a fannin cewa, ako da yaushe, kofar Hukumar ta NPA, bode take domin hadaka wacce ta zarce ta gudanar da baje koli. Dakta Dantsoho ya kara da cewa, an samar da tsarin na EPT domin a tabbatar da cewa, ana fitar da kaya zuwa waje, ta hanyar yin amfani da na’urar zamani. “Wannan na zai taimaka matuka wajen kaucewa samun jinkiri da kuma mai-maita aiki da Hukumar ta saba fuskanta a baya,” A cewar Dantsoho. Kazalika, Dantsoho ya bayyana cewa, domin a samu sauki wajen kai kaya a tsakanin masu kananan da matsakaitan sana’oi, musamman duba da cewa, tsarin na EPT, zai taimaka matuka ga guraren da ake adana kaya a...
    Ilimi na da muhimmanci wajen gina al’umma, amma ga daliban Makarantar Firamare ta Bare a karamar Hukumar billiri, Jihar Gombe, wannan lamari ya zama kamar mafarki mai wahalar tabbatuwa. Duk da ikirarin da Gwamnatin Jihar Gombe ke yi na cewa, tana fifita ilimi ta hanyar manyan ayyuka kamar gine-ginen makarantu masu hawa biyu a kowace mazabar Sanata, a halin da ake ciki a Makarantar Firamare ta Bare ba ta san da hakan ba. Wannan makaranta tana nuna sakaci da gazawar masu mulki. An kafa makarantar ce a shekarar 2005 karkashin shirin Hukumar Kula da Ilimin Firamare ta Jihar Gombe (SUBEB). Tun daga lokacin har zuwa yanzu, ba a taba samun gyara ko ci-gaba ba. Maimakon zama alamar ci-gaba, makarantar ta...
    Kasashen Nijar da Najeriya sun sha alwashin inganta dangantaka a tsakaninsu domin cin moriyar juna a matsayinsu na makobta. Wannan bayyanin ya fito bayan tattaunawa data wakana tsakanin ministocin harkokin wajen kasashen biyu a birnin Yamai bayan kwashe watanni ana takaddama. Yayin ziyarar da ministan harkokin wajen Najeriya ya kai Nijar an gudanar da wani babban taro tsakanin shugabannin diflomasiyyar kasashen biyu don sake farfado da hanyoyin hadin gwiwa a bangarori da dama da suka hada da tattalin arziki da tsaro. Ministan harkokin waje da hadin gwiwa na  Nijar Bakary Yaou Sangaré da takwaransa na Najeriya Yusuf Maitama Tuggar sun gana a ranar 16 ga ga watan nan, lamarin dake nuni da wani gagarumin sauyi na dangantakar da ke tsakanin...
    Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo ya bayyana cewa masu garkuwa da mutane da aka samu da laifi a jihar za su fuskanci hukuncin kisa ta hanyar rataya. Okpebholo ya bada tabbacin a shirye yake ya sanya hannu akan sammacin kisa na waɗanda aka yankewa hukunci a jihar idan kotu ta same su da laifi. An tsinci gawar mabaraci mai shekara 75 a Neja PDP ba ta shirya yin zaɓen 2027 ba – Wike Gwamna Okpebholo ya bayyana hakan ne a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a garin Uromi, inda ya tattauna da shugabanni da ’yan uwa na yankin unguwar ’yan Arewa mazauna Esan. “Ku tuna cewa Majalisar Dokokin Jihar Edo (EDHA) ta zartar da wani ƙudiri...
    Waɗanda suka take wa Ministan sawu a tafiyar su ne jagororin hukumomin yaɗa labarai da wayar da kai da ke ƙarƙashin ma’aikatar sa. Ya yi zama daban-daban tare da ƙwararru inda suka tattauna kan yadda za a inganta ƙwarewa da kuma kayan aiki na zamani na kafafen yaɗa labarai na gwamnatin Nijeriya.   Ya ce: “Ina sanar da ku waɗannan abubuwan ne domin jaddada ƙudirin gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na ganin an samu cigaba mai ɗorewa a fannin watsa labarai a ƙasar nan.   “Wannan ne ma ya sanya muke gudanar da irin wannan taron bita na ministoci, da kuma shirin ƙaddamar da Taron Tattaunawa da Jama’a a sassan ƙasar nan nan gaba kaɗan.” Idris ya kuma...
    Wani mutum mai suna Muhammad Ma’aba daga ƙauyen Fujeregi da ke Ƙaramar hukumar Gbako a Jihar Neja, ya mutu a hannun tsohon mijin matar da yake shirin aura. Rahotanni sun bayyana cewa, wata Ƙungiya ƙarƙashin jagorancin tsohon mijin matar mai suna Alhaji Yikangi, daga ƙauyen Yikangi Chikan ne suka kai wa Ma’aba hari a tsakanin garin Saganuwa da Fujeregi. PDP ba ta shirya yin zaɓen 2027 ba – Wike Benuwe: Har yanzu ba a gano wasu mutanen ƙauyuka ba – Gwamna Alia Mazauna garin sun shaida wa Daily Trust cewa, tsohon mijin ya saki matar mai suna Fatima Suleiman sau uku, amma ya dage cewa ba za ta ƙara aure ba — ko da ta samu sabon mai neman aurenta....
    Jawabin shugaban majalisar, ya biyo bayan dambarwar hankalin al’ummar kasar ne, bayan shelar ranar 18 ga watan Maris da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi na ayyana dokar ta-baci na tsawon wata shida a Jihar Ribas. Matakin ya zo ne daidai lokacin da rikicin siyasa ke kara kamari, inda aka dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara tare da rusa majalisar dokokin jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rundunar sojin sama na Operation Hadin Kai ta yi nasarar aiwatar da wasu hare-hare ta sama guda biyu, inda ta auka wa maboyar ‘yan ta’adda a yankin Sambisa na jihar Borno da kuma Kudancin Tumbun.   A wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame ya fitar, ya ce harin farko ya afku ne da misalin karfe 5:30 na safe a Kollaram- sanannar tungar ‘yan tada kayar baya, a ranar 15 ga watan Afrilu, inda aka kawar da mayaka da dama tare da lalata muhimman ababen more rayuwarsu.   Farmaki na biyu kuwa ya biyo bayan da misalin karfe 3:55 na rana a garin Arra na Sambisa, bayan binciken sirri da bincike...
    Uwargidan Gwamnan Sakkwato Hajiya Fatima Ahmad Aliyu ta ɗauki nauyin ragon suna da abinci da kayan barka ga duk wata mata da tahaifi ’yan uku a jihar. Hahiya Fatima ta sanar da haka ne a ranar Laraba nan a lokacin da ta yi takakkiya takanas zuwa garin Ƙaurar Yabo da ke Ƙaramar Hukumar Yabo domin kai ragunan suna da kayan barka da na suna ga wata mai jego mai suna Malama Bela’u, wadda ta haifi ’yan uku a garin. Daga cikin kayan da ta kai wa mai jego kyauta, har da buhun abinci goma da akwatunan tufafi da tsabar kudi Naira dubu dari biyar. A bayanin da mataimaka wa gwamna kan harkokin kafofin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A ranar 17 ga watan Afrilun nan, yayin ziyarar aiki ta shugaba Xi jinping a kasar Cambodia, an yi bikin kaddamar da shirin bidiyon “Bayanan magabata dake jan hankalin Xi Jinping” na harshen Cambodia, wanda CMG ya shirya a birnin Phnom Penh.   Shugaban CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo. Inda ya ce a shirye CMG yake ya yi aiki tare da abokai daga sassan daban daban na kasar Cambodia domin ci gaba da zurfafa hadin gwiwarsu a fannoni daban daban, da samar da karin haske a fannin musayar al’adu, da sanya sabon kuzari a aikin gina al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya tsakanin Sin da Cambodia. (Mai fassara: Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana...
    An tabbatar da cewa, tashin hankalin ya barke ne jim kadan bayan da alkalin wasa ya busa tashi daga wasan, kawo yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance da rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta fitar har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto a safiyar ranar Alhamis, kuma kawo yanzu babu tabbacin ko an samu raunika a yayin rikicin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Pakisatan ta kara jaddada matsayinta na rashin amince da HKI a matsayin kasa tana kuma goyon bayan Falasdinawa a gwagwarmayan da suke yi na kwatar yencinsu da kuma kasarsu daga hannun HKI da kuma kasashen yamma musamman Amurka masu goya mata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran wannan sanarwan tazo ne bayan da hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD ta samar da wani kuduri dangane da rikicin da ke faruwa a gabas ta tsakiya.   A dai-dai lokacinda aka kara yawan tashe-tashen hankula a kasar Falasdinu da aka mamaye tsakanin HKI da kuma Falasdinawa masu gwagwarmaya. Kungiyar kasashe masu musulmi mafi rinjaye wato OIC ta yanke  shawara kan cewa bai kamata kasashen su samar da huldar...
    Shanu 36 sun mutu baya ga wasu 42 da ake zargin an ba su guba guba a kusa da yankin mahaɗar Tafi Gana a Ƙaramar Hukumar Bassa ta Jihar Filato. Shugaban Ƙungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) a Karamar Hukumar Bassa, Ya’u Idris, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 4:30 na yamma lokacin da shanun ke kiwo a yankin. Ya’u ya ƙara da cewa an sanya guba ne a cikin gauta, waɗanda aka warwatsa a kewayen wurin kiwon kuma shanun suka ci. Ya ci gaba da cewa sun kai rahoton lamarin ga dukkan hukumomin tsaro ciki har da Hukumar DSS, da ’yan sanda, ya kuma  Babban Kwamandan Rundunar ta kuma din ya ziyarci wurin da abin ya...
    Mako guda bayan rage farashin fetur da Naira 45, matatar mai ta Dangote ta sake karya farashin man ga ‘yan sari da ragin Naira 30 duk lita. Aminiya ta rawaito cewa matatar na sayar da man ne a ranar Laraba akan ₦835, saɓanin makon da ya gabata da ta sayar da shi akan ₦865 bayan rage farashin daga ₦880 da ta sayar a makon da ya gabata. Majalisa ta gayyaci Kantoman Ribas, Ibok-Ete Ibas An naɗa mace ta farko mai magana da yawun rundunar sojin Nijeriya Hakan dai na nufin a cikin makonni shida, Dangoten ya rage farashin fetur ɗin sau uku.
    Kwamitin wucin-gadi na Majalisar Wakilan Nijeriya wanda aka ɗora wa alhakin kula da harkokin gudanar da mulki a Jihar Ribas, ya gayyaci gwamnan riƙon jihar, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas. Wannan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Majalisar Wakilan, Akin Rotimi ya fitar a ranar Laraba. An naɗa mace ta farko mai magana da yawun rundunar sojin Nijeriya An taƙaita zirga-zirgar babura da haramta kiwon dare a Filato Rotimi ya ce gayyatar na zuwa ne bayan ƙaddamar da kwamitin da Shugaban Majalisar Abbas Tajudeen ya yi a ranar Talata. Ya ce gayyatar za ta bai wa kwamitin damar yin bita kan yadda al’amura ke gudana tun bayan kama ragamar aiki da Ibas ya yi a...
      Ya kara da cewa, CMG ta dade tana kasancewa ingantacciyar gada dake inganta fahimtar juna tsakanin kasashen biyu, kuma ya yi imanin cewa, hadin gwiwarsu a wannan karo zai kara karfafa daddaden dankon zumunci a tsakanin kasashen biyu. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, ya sanar da haramta kiwo da daddare tare da taƙaita amfani da babura a faɗin jihar sakamakon yawaitar hare-haren da ake kai wa a wasu sassan jihar. A cikin wani jawabi da ya yi a jihar a ranar Laraba, Mutfwang ya bayyana hare-haren a matsayin “ayyukan ta’addanci” da ke da nufin tarwatsa mazauna yankin da kuma tauye hakkinsu na kasancewa cikin lumana a yankunansu. Gwamnan ya kuma haramta safarar shanu cikin ababen hawa bayan karfe 7 na dare. Ya kuma hana amfani da babura daga karfe 7 na yamma zuwa karfe 6 na safe a faɗin jihar har na wani tsawon lokaci inda ya ce umarnin zai fara aiki ne nan take. Ya ce ” Ina...
    Paris St Germain ta kai zagayen daf da na ƙarshe a Gasar Zakarun Turai duk da rashin nasara da ta yi a hannun Aston Villa ranar Talata a Villa Park. Aston Villa ta yi nasarar cin PSG 3-2, inda Tielemans da McGinn da kuma Konsa suka ci mata ƙwallayen a wasa falle na biyu a zagayen kwata fainal. DAGA LARABA: Dalilan Ɓaraka A Tsakanin Iyayen Riƙo Da Ƴaƴan Riƙo Ana barazanar korar sojojin Isra’ila da ke neman a kawo ƙarshen yaƙin Gaza Ita kuwa ƙungiyar ta Faransa ta ci nata ƙwallayen ta hannun Hakimi da kuma Nuno Mendes. PSG ta kai zagayen gaba da cin 5-4 gida da waje jimilla, bayan da ta yi nasarar cin 3-1 a makon jiya...
    A yayin ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai kasar Malaysia, daga yanzu manyan kafofin sadarwa kamar kafar yada labarai ta kasar Malaysia za su fara nuna shirin bidiyon “Bayanan magabata dake jan hankalin Xi Jinping” na harshen Malay wanda CMG ya shirya.   Shirin ya mai da hankali ne kan muhimman batutuwa kamar gina al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya ga bil Adama, da gadan al’adun gargajiya da kirkire-kirkire, da kare nau’ikan halittu, da mu’amala da koyo a tsakanin al’ummomi, ya kuma gabatar da fitacciyar hikimar shugaba Xi Jinping wajen gudanar da mulkin kasar. (Mai fassara: Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
    Lauyoyin Landan suna tattara bayanai kan ‘yan Birtaniya da suka yi aiki a cikin rundunar sojojin mamayar Isra’ila Kwararru kan harkokin shari’a na kasar Biritaniya sun ce gurfanar da wasu ‘yan kasar masu takardar ‘yan kasa biyu da ke aiki a cikin sojojin mamayar Isra’ila a gaban kuliya bisa zargin hannu a tafka laifukan yaki a Gaza, zai yi tasiri ga wadanda ke tunanin shiga cikin sahunsu. Hakan ya biyo bayan gabatar da rahoto ga rundunar ‘yan sandan birnin Landan ne mai kunshe da shaidun da suka shafi ‘yan Birtaniya guda 10 da suka yi aikin soja karkashin rundunar mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila da ake zargi da aikata laifukan yaki a Gaza. A cewar wani rahoto da kamfanin dillancin labarai...