2025-08-13@06:01:07 GMT
إجمالي نتائج البحث: 312
«takarar gwamna»:
Sun fara soyayya ba da jimawa ba, inda suka fito fili suka bayyana alakar dake tsakaninsu a shekarar 2017, masoyan sun haifi yarsu ta farko, Alana, a watan Nuwamba na shekarar 2017, daga nan suka haifi tagwaye, Bella da Angel, a watan Afrilun 2022, amma jim kadan da haihuwarsu Angel ya rasu, Georgina ta kuma...

Sin Ta Gudanar Da Gwajin Farko Na Gagarumin Bikin Murnar Cika Shekaru 80 Da Cimma Nasarar Yakin Kin Jinin Harin Dakarun Japan
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta kama wanda ya kafa kuma yake kula da cocin ‘The Turn of Mercy’, Adefolusho Olasele, wanda aka fi sani da Abbas Ajakaiye, bisa zarginsa da hannu wajen safarar miyagun kwayoyi da dama daga Ghana zuwa Nijeriya. Fasto Olasele, wanda ya shafe watanni ba...
Ali Akbar Velayati mashawarcin jagoran juyin juya halin Musulunci da Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan harkokin kasa da kasa ya tabbatar da cewa “Jamhuriyar Musulunci tana adawa da shirin kwance damara na kungiyar Hizbullah” yana mai jaddada cewa Iran a ko da yaushe tana goyon bayan al’ummar kasar Labanon da kuma gwagwarmayarsu. Da yake magana...
Cibiyar binciken duniyar wata, karkashin hukumar kula da zirga-zirgar kumbuna a sararin samaniya ta kasar Sin, ta sanar da cewa, zuwa karo na 9, kasar Sin ta samar da kasar duniyar wata da jimilar nauyinta ya kai gram 125.42, ga kwararru masu nazarin kimiyya da fasaha na kasashe daban daban, ciki har da kason kasar...
A cewarsa, wannan gamayyar ta faro ne sama da wata 18 da suka wuce, wadda kuma an samar da ita ne saboda fargabar da ake da ita a ƙasar na kar a kasance ana da jam’iyya ɗaya tilo a Nijeriya. Lukman, wanda kuma shi ne tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC na Arewa maso Yamma kafin...
Wannan hukunci ya fito daga kwamitin ɗa’a da ladabtarwa na UEFA, kuma zai fara aiki nan take a wasan Barcelona na gaba a Turai. Barcelona za ta fara sabuwar kakar wasa ne da RCD Mallorca ranar Asabar, 15 ga watan Agusta. Za su ci gaba da fafutukar lashe kofuna a ƙarƙashin sabon kocinsu, Hansi Flick....
Ranar Cutar Daji Ta 2025: Akwai Matakan Kariya Daga Kamuwa Da Cutar Kansa -Masana Uwargidan Gwamnan Zamfara Ta Zama Sakatariyar Kungiyar Yaƙi Da Cutar Daji “Ta hanyar gudanar da ɗimbin ayyukan noma a Gandun Dazukan wannan ƙasa, zai yi matuƙar ƙara yawan ayyukan masana’antun ƙasar da ke sarrafa amfanin gona domin fitarwa zuwa kasuwannin duniya,...

Hizbullah Da Amal Na Kasar Lebanon sun Yi Tir Da gwamnatin Kasar Saboda Bukatar Kwance Damarar Hizbullah
Kungiyar Hizbullah da Amal na kasar Lebanon sun bayyan amincewar gwamnatin kasar Lebanon wajen kwance damarar kungiyar hizbullah wani abu ne wanda kasashen waje suka fada masu su yi haka, wanda ya yi watsi da diyaucin kasar Lebanon da kuma cikekken iko a kan kasar. Labarin ya kara da cewa shuwagabannin kasar ta Lebanon sun...

Cinikayyar Kayayyaki a Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.5 Cikin 100 Cikin Watanni 7 Na Farkon Shekarar Nan
Alkaluman kididdiga na hukumar kwastam ta kasar Sin sun nuna yadda cikin watanni 7 na farkon shekarar nan ta 2025, jimillar darajar cinikayyar kayayyaki ta kasar Sin ta kai kudin kasar yuan tiriliyan 25.7, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 3.5, wanda hakan ya nuna karuwar kashi 3.5 cikin 100 idan aka kwatanta da makamancin lokaci na...
Ya kuma lura da cewa, tattaunawa da ‘yan bindiga a wasu jihohin suka yi ya kara ta’azzara satar shanu, inda ya ce, Sam hakan, ba za a amince da shi ba. Dangane da ta’azzarar rashin tsaro, Gwamna Bago ya ce, za a nemi taimako daga shugaba Bola Tinubu da mai bai wa shugaban kasa...
Shugaban ya kuma yabawa cibiyoyin koyon ilimi tare da bayyana cewa wadannan nasarorin da aka samu shaida ne na ingancin ilimin Nijeriya wanda ke kekkenshe yara masu basira a duniya. Tinubu ya yi imanin cewa, ilimi muhimmin abu ne ga ci gaban kasa; don haka, babbar hobbasar da gwamnatinsa ta yi a fannin, shi...
Gwamnan ya kuma jaddada kudirinsa na ci gaba da tabbatar da adalci, ladabtarwa, da yakar laifukan da suka shafi sha da fataucin miyagun kwayoyi da sauran munanan dabi’u da ke addabar matasa da al’umma jihar Kano. Gwamna ya kuma yi gargaɗi ga duk masu rike da mukaman siyasa da su rika yin taka-tsantsan kan al’amuran...
Kotun tsarin mulkin Kamaru ta haramta wa jagoran adawar ƙasar, Maurice Kamto tsayawa takarar shugaban ƙasa, a babban zaɓe mai zuwa na watan Oktoba, kan abin da ta bayyana rashin cika ka’idojin tsayawa takara. Lauyansa, Hippolyte Meli Tiakouang ne ya tabbatar wa manema labarai hukuncin kotun wanda ba za a iya ƙalubalanta ba, bayan kammala...
Sashen cinikayyar samar da hidimomi na Sin ya ci gaba da bunkasa yadda ya kamata cikin watanni shida na farkon shekarar nan ta 2025, inda ya karu da kaso takwas bisa dari kan mizanin shekara. A cewar ma’aikatar cinikayya ta Sin, darajar hidimomin shige da fice a wannan wa’adi ta kai kudin Sin tiriliyan 3.89,...
Gobara ta ƙone gidan Barden Bauchi Hakimin Ƙasar Lere, Alhaji Sulaiman Muhammad da ke unguwar Gwallaga a cikin garin Bauchi. Sa’in Tafawa Balewa Mallam Yunusa Ado ya tabbatar da faruwar lamarin, da cewa “Wannan gobara ta auku ne akamakon kawo wutan lantarki da hantsi ranar Litini 4/8/2025 lokacin Hakimin na Fadarshi dake garin Zwall.” Mallam...

Gwamnatin Kano Ta Karɓi Rahoton Binciken Kwamishinan Sufuri Kan Belin Wanda Ake Zargi Da Safarar Kwayoyi
Gwamnatin Jihar Kano ta karɓi rahoton kwamitin bincike da aka kafa domin bincikar zargin da ake yi wa Kwamishinan Sufuri, Ibrahim Namadi, kan hannu da yake da shi a ceto wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu. Shugaban kwamitin kuma mai bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Shari’a da Tsarin Mulki,...
Shima da yake gabatar da nasa jawabin, shugaban jam’iyyar APC magoya bayan Aminu Sani Jaji a Zamfara, Honorabul Lawalli Attahiru Dogon Kade, ya bayyana dan majalisar a matsayin Mutum jajirtacce mai hannun kyauta da taimakon jama’a, inda ya ce mutum irin Aminu Sani Jaji ake nema a matsayin Gwamnan Zamfara, domin shi kadai ne zai...
Mai Martaba Sarkin Dutse, Dr Hameem Nuhu Muhammadu Sunusi ya kaddamar da rabon zakkar kudi ta shekarar musulunci ta 1446 a gundumar Yayari dake Karamar Hukumar Buji. A jawabin sa, Mai Martaba Sarkin ya ja hankalin al’umma da su ci gaba da fitar da hakkin Allah domin samun makoma a nan duniya da kuma gobe...
Nijeriya, wadda take ta daya a jerin ƙasashen da suka fi iya ƙwallon mata a Afirka, ta zura ƙwallon da ta ba ta nasara ne a gab da tashi wasa a karawarta da Afirka ta Kudu a wasan kusa da na ƙarshe. A yanzu za a iya cewa Nijeriya ta cimma burinta na ‘Mission ɗ’,...
A daren Juma’a ne dab da wayewar gari wata motar tirela ɗauke da awaki da kaji wadda ta taso daga Gwauron Dutse a Jihar Kano ta yi haɗari. Motar tirelar wadda take ɗauke da dakon awaki da kuma kwandunan kaji mai yawa a samanta baya ga mutane da ta ɗauko ta yi haɗarin a kusa...
“Kiyasin ƴan Nijeriya miliyan 20 ke rayuwa da cutar hanta, kuma mutum miliyan 18.2 sun kamu ne da cutar rukunin B, sannan wasu mutum miliyan 2.5 sun kamu da cutar rukunin C. Abin takaici, ƴan Nijeriya 4,252 ne ke mutuwa a duk shekara sakamakon ciwon hanta da aka kasa maganceta ke haifarwa,” ya shaida. A...
Kungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah ta Nijeriya reshen Jihar Benuwe, a ranar Alhamis, ta bayyana cewa aƙalla shanu 340 na mambobinta ne aka sace a cikin watan Yuli na 2025. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren ƙungiyar na jiha, Ibrahim Galma ya fitar kuma aka rabawa manema labarai a Makurdi. Tinubu...
Gwamnatin kasar Amurka ta umurci gwamnatin kasar Lebanon ta kwance damarar kungiyar Hizbullah a kudancin kasar ko kuma ba zata sake maganar tattaunawa da gwamnatin kasar kan samuwar sojojin HKI a wurare 5 a kudancin kasar ba, ko kuma maganar HKI ta dakatar da hare hare a kan kasar ba. Tashar talabijin ta Presstv a...

Rashin Nasarar DPP A Zagayen Farko Na Kuri’ar Kiranye Ya Nuna Rashin Amincewar Al’ummar Taiwan Da Salon Mulkin Jami’yyar
Kakakin ofishi mai lura da harkokin yankin Taiwan a majalisar gudanarwar kasar Sin Chen Binhua, ya ce kalaman da aka jiyo jagoran yankin Taiwan na kasar Sin Lai Ching-te na yi dangane da sakamakon zagayen farko na kuri’ar kiranye da al’ummar Taiwan suka kada, ya nuna rashin gamsuwarsu da salon mulkin jam’iyyar DPP mai mulkin...
Sai dai ya gode wa PDP bisa damar da ta ba shi ya tsaya takara a 2023, amma yanzu lokaci ya yi ne da zai yi gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don...
Shugaban kungiyar Hamass ya bayyana cewa HKI da gwamnatin kasar Amurka sun janye daga tattaunawa tsakaninsu da kungiyar ne don sake komawa yaki har zuwa lokacinda zasu shafe falasdinawa a gaza. Tashar talabijin nta Presstv a nan Tehran ya nakalto Kkalilul Hayya, yana fadar haka a wani jawabin da aka watsa a tashoshin talabijin nay...
A kokarinsa na gano hakikanin dalilan da suka sa aka bayar da beli ga wani sanannen mai safarar miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Dan Wawu, da aka ce an sako shi bisa umarnin Kwamishinan Sufuri na Kano, Ibrahim Ali Namadi, Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da wani kwamiti na mutum takwas domin...

Babban Jami’in Hamas A Gaza; Makiya ‘Yan Sahayoniyya Suna Rufe Gazawar Sojojinsu Da Kisan Kare Dangi
Babban jami’in kungiyar Hamas a Zirin Gaza ya bayyana cewa: Makiya yahudawan sahayoniya suna rufe gazawar sojojinsu da kisan kare dangi Khalil al-Hayya babban jami’in kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas a zirin Gaza ya jaddada cewa: Makiya yahudawan sahayoniyya suna rufe gazawar sojojinsu ta hanyar kisan kare dangi da suke aiwatarwa kan fararen hula. A...
Daga ranar 24 ga wata, zuwa jiya Asabar 26 ga wata, an gudanar da babban taron kasa da kasa, dangane da fasahar rage asarar hatsi a birnin Jinan na kasar Sin, inda a wajen taron aka sanar da sakamakon da kasar Sin ta samu a fannin takaita asarar hatsi. An bayyana cewa, a bangaren asarar...
Tawagar ƙwallon ƙafa ta mata a Nijeriya (Super Falcons) ta samu nasarar lashe kofin ƙasashen nahiyar Afirika na mata bayan doke masu masaukin baƙi Maroko a wasan ƙarshe da ci 3 da 2. An buga wasan ne a daren ranar Asabar, wanda ya ƙayatar da masu kallo. Musuluntar Wata Ce Ya Ja Hankalina Shiga Fim...
Tawagar ƙwallon ƙafa ta mata a Nijeriya (Super Falcons) ta samu nasarar lashe kofin ƙasashen nahiyar Afirika na mata bayan doke masu masaukin baƙi Maroko a wasan ƙarshe da ci 3 da 2. An buga wasan ne a daren ranar Asabar, wanda ya ƙayatar da masu kallo. Musuluntar Wata Ce Ya Ja Hankalina Shiga Fim...
Yayin da gasar wasannin kasa da kasa ta shekarar 2025 ke karatowa, an gudanar da bikin karba, da kaddamar da fitilar gasar a Asabar din nan, a shahararren gidan adana kayan tarihi na Sanxingdui, dake birnin Chengdu na kasar Sin. Kaddamar da fitilar gasar a yau, ya alamta fara kidayar kwanaki 12, gabanin bude gasar...
Kwanan nan jam’iyyar PDP ta gudanar da taron kwamitin zartarwa karo na 100 da aka gudanar ranar 30 ga Yuni, PDP ta warware rikicin da ya dade yana ci mata tuwo a kwarya na batun mukamin sakataren jam’iyyar na kasa wanda ta tabbatar da Sanata Samuel Anyanwu a matsayin sakataren jam’iyyar. Duk da wannan warware...
JMI ta cilla taurarun dan’adam masu suna Nahid-2 kirar cikin gida zuwa sararin samaniya tare da nasara. Kuma ta yi amfani da kombo na kasar Rasha mai suna Vostochiny Cosmodrome don isar da tauraron zawa inda take so a sararin samaniya, a yau Jumma’a 25 ga watan Yulin shekara ta 2025. Tashar talabijin ta Presstv...

Maraba Da Shekarar Hijirah Ta 1447: Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar (4)
Hikimar Rashin Hade Farkon Shekarar Musulunci Da Tarihin Manzancin Annabi (SAW) Masu karatu har yanzu dai muna kan bayani game da abubuwan da suka sa Sahabbai ba su kafa tarihin kirgen shekarar musulunci ba da wasu manyan alherai na Musulunci, sai suka zabi Muharram ta zama farkon shekarar tare da lakaba mata shekarar Hijirah....
“Mun kasance muna jiran a ba mu garin alkama, saboda muna jin yunwa sosai, muna neman abin sha da abinci, kwatsam tankokin sojan Isra’ila suka zo suka kewaye mu, suka fara harba bindiga a kanmu, ba mu iya motsawa ba. Ba mu samu gari ba, an kuma kewaye mu na tsawon sa’a daya da rabi...
Masu ƙarar sun bayyana cewa an ce an bai wa kamfanin kuɗin ne domin samo kuɗin hannu don biyan ma’aikatan wucin gadi da aka ɗauka a zaɓukan ƙananan hukumomi na 2024. Daga bisani kuma, an ce an dawo da kuɗin a matsayin tsaba zuwa hukumar. Lauyan ICPC, Barr. Enosa Omoghibo, ya shaida wa kotu cewa...
Jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara ta zabi Hon. Kamilu Sa’idu (Wamban Kasuwar Daji) a matsayin dan takararta na Majalisar Dokokin Jihar Kaura Namoda ta Kudu da za a yi ranar 16 ga Agusta, 2025. A wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC na Jihar, Yusuf Idris Gusau ya fitar, ya ce Kamilu...
3. Girman Lambar Yabo da Za a Baiwa Zakaran Gasar Kungiyar da ta lashe kofin za ta samu fam miliyan 97 daga hukumar FIFA. Hakanan, za ta sanya tambarin kofin na tsawon shekaru 4, sabanin shekara 1 da ake yi a baya. 4. Muhimmancin Wasan ga Duka Kungiyoyin Ga PSG, wannan kofi na iya zama...
An haifi Peter Rufa’i a ranar 24 ga watan Agusta, 1963, a Oshodi, Legas, a wani gidan sarautar gargajiya, Mahaifinsa shi ne sarkin kabilar Idimu a Jihar Legas, duk da hasashen da ake yi na cewa zai yi gadon sarautar gidansu, Rufa’i ya yi watsi da sarautar don ci gaba da fuskantar abin da yake...
An dai yi ta tsokaci kan cewa ko Obi zai amince da mukamin mataimakin shugaban kasa tare da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, kamar yadda ya yi a 2019. Obi ya ce, “Takarar shugaban kasan Nijeriya zan yi a 2027, kuma na tabbatar da cancanta.” A kan ko zai hakura ya zama mataimakin takarar...
Ba laifi idan an yi murna ta shigar sabuwar shekarar Musulunci. Ba za a bi na wadanda za su bidi’antar da abin ba, domin hatta murnar haihuwar Manzon Allah (SAW) sun ce bidi’a ne. Har kai kanka ma za su iya ce maka bidi’a, saboda ba ka zo a zamaninsa ba. Masu wannan fahimtar Malamai...
Hukumar hana fasa ƙwauri ta Najeriya (Kwastam), ta ce ta kama wata mota da ke ɗauke da wata kontena maƙare da mazaƙutar jakai a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja. Hukumar ta Kwastam ta sanar da kama motar ne a ranar Alhamis. Sojoji sun tarwatsa matsugunin ’yan ta’adda da kashe wasu a Borno An gurfanar da...

Tsohon Ɗan Takarar Gwamna A CPC, Haruna Sa’eed Kajuru, Ya Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Binciki Kisan ‘Yan Zariya A Filato
Tsohon ɗan takarar gwamna ƙarƙashin jam’iyyar CPC ta shuɗe a Jihar Kaduna, Alhaji Haruna Sa’eid Kajuru, ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta gudanar da cikakken bincike kan kisan da aka yi wa wasu mazauna Zariya da suka je dauren aure a Jihar Filato kwanan nan. Alhaji Kajuru ya yi wannan kira ne a lokacin...
Kamfanin CRCC na Sin ya cimma nasarar kammala shimfida layin dogo mai tsawon kilomita 135 a jiya Litinin. Aikin ya kasance mataki na farko na shirin shimfida layin dogo na farko a hamadar Afrika, na jiragen kasa masu dakon kayayyaki mafiya nauyi, wanda zai hada jihar Bechar da yanki mai samar da karfe na Gala...
Shugaban Kungiyar Harka Islamia a tarayyar Najeriya Sheikh Irahim Zakzaky ya taya mutanen kasar murna saboda nasarar da suka samu kan HKI da kuma Amurka a yakin kwanaki 12 a cikin watan da ya gabata. Ya ce wannan nasarar bata takaita da mutanen kasar Iran kadai ba , hada har da al-ummar Musulmi da kuma...
Ibrahim ya bayyana cewa, sun rarraba mukamai na rikon jam’iyyar a tsakaninsu, kafin babban taro na kasa a nan gaba. Gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai ya tabbatar cewa; hadakar ta ADC, ta zabi Aregbesola a matsayin sakatarenta na kasa na riko, har ma ya wallafa a jawabin karbar mukamin da ya yi a shafukan sada...
Salim Sani Shehu Jam’iyyar NNPP ta bayyana a hukumance cewa tsohon ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ba zai sake yin takarar shugaban ƙasa karkashin jam’iyyar a zaɓen 2027 ba. Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Agbo Major, ne ya bayyana hakan a ranar Asabar yayin da yake mayar da martani...
Datti Baba-Ahmed, wanda ya tsaya takarar mataimakin shugaban ƙasa a jam’iyyar LP a zaɓen 2023, ya bayyana cewa ADC za ta fuskanci babban ƙalubale wajen fitar da wanda zai yi mata takarar shugaban ƙasa a 2027. Sabuwar haɗakar ta haɗa da fitattun ’yan siyasa irin su tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar; ɗan takarar shugaban...