Aminiya:
2025-08-10@07:50:38 GMT

Inter Milan ta koro Barcelona daga Gasar Zakarun Turai

Published: 7th, May 2025 GMT

Inter Milan ta samu nasarar tankaɗo Barcelona daga Gasar Zakarun Turai, lamarin da ya ba ta damar kaiwa zagayen ƙarshe na gasar ta bana.

A daren wannan Talatar ce aka buga wasa falle na biyu a zagayen kusa da na ƙarshe a Gasar Zakarun Turai ta bana tsakanin ƙungiyoyin biyu.

‘Raini ne ya sa ake ƙalubalantar yunƙurin kafa ƙungiyar Hausawa zalla’ Majalisar Dattawa ta kafa kwamitin lura da gwamnan riƙo na Jihar Ribas

Inter Milan ce ta yi nasarar doke Barcelona da ci 4-3 a filin wasanta na San Siro da ke Italiya, bayan a makon jiya sun yi kunnen doki 3-3 a Nou Camp da ke ƙasar Sifaniya.

A wasan na yau da aka barje gumi har tsawon mintuna 120, Lautaro Martinez da Hakan Calhanoglu ne suka fara ci wa Inter ƙwallo a ragar Barcelona, daga baya Eric Garcia da Dani Olmo da Raphinha suka rama ƙwallayen har da ƙari.

Sai dai ana dab da tashi ne kuma Francesco Acerbi mai shekaru 37 ya rama wa Inter ƙwallo ta uku, abin da ya tilasta wasan zuwa ƙarin lokaci.

A minti na 99 ne Davide Frattesi ya ci wa Inter Milan ƙwallon da ya ba ta nasara.

Ƙungiyar wadda a yanzu Simone Inzaghi ke jagoranta, ta kai wasan ƙarshe na Gasar Zakarun Turai karo na biyu ke nan a cikin shekaru uku.

Yanzu Inter Milan za ta haɗu ne da PSG ko Arsenal waɗanda za su fafata nasu wasan a ranar Laraba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Barcelona Gasar Zakarun Turai a Gasar Zakarun Turai

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Tarayya da Ofishin Jakadancin Amurka Sun Haɗa Gwiwa Don Wayar Da Kan ‘Yan Nijeriya Kan Sababbin Ƙa’idojin Samun Biza

Idris ya ce a tsawon shekaru ‘yan Nijeriya suna tafiya Amurka saboda dalilai daban-daban, ciki har da yawon buɗe ido, kasuwanci, karatu, da kuma neman magani.

 

Ya ce: “An san Nijeriya a duniya a matsayin ƙasar da ‘yan ƙasar ta suke yawan yin tafiya zuwa ƙasashe daban-daban, suna hulɗa da ƙasashen duniya ta fuskar harkar kasuwanci, ilimi, yawon buɗe ido, da sauran muhimman fannoni. Amurka na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin wuraren da ‘yan Nijeriya suka fi ziyarta, abin da ke nuna zurfin dangantaka mai tsawo tsakanin ƙasashen biyu.

 

“Yawancin ‘yan Nijeriya suna zuwa Amurka ne domin karatu, aiki, neman magani, ziyartar ‘yan’uwa, yawon buɗe ido, da damar zuba jari.

 

“Wannan mu’amala mai ƙarfi tana ci gaba da bunƙasa al’ummomin biyu.

 

“Sababbin abubuwan da Ofishin Jakadancin Amurka ya bayyana game da sauye-sauye a ayyukan ofishin jakadancin da hanyoyin neman bizar sun jima suna cikin labarai kwanan nan.

 

“Waɗannan sauye-sauyen, kamar yadda Ofishin Jakadancin Amurka ya bayyana, wani ɓangare ne na ƙoƙarin inganta bayar da sabis, ƙara saurin aiki, da mayar da martani ga sauye-sauyen buƙatun ayyukan jakadanci.”

 

Ministan ya yaba wa gwamnatin Amurka bisa ƙoƙarin yin bayani kai-tsaye ga ‘yan Nijeriya a wannan taro tare da tabbatar da samun sahihan bayanai na zamani ga kowa.

 

Haka kuma ya jaddada girmamawa da haɗin gwiwa tsakanin Nijeriya da Amurka da kuma jajircewar Ofishin Jakadancin wajen sanar da matafiya ‘yan Nijeriya.

 

A nasa jawabin, Jakaden Amurka, Ambasada Mills, ya ce bin ƙa’idojin neman biza da dokokin Amurka na ‘yan Nijeriya abu ne mai muhimmanci wajen ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.

 

“Bin dokokin neman biza na Amurka ba kawai wani nauyi ba ne, amma ginshiƙi ne na amincewa da girmama juna tsakanin ƙasashen biyu,” inji Ambasada Millis.

 

Ya ƙara da cewa: “Kamar yadda Minista ya bayyana, ni da shi mun yi tattaunawa mai amfani game da dokokin biza na Amurka da kuma yadda za mu isar wa ‘yan Nijeriya muhimmancin bin waɗannan dokokin.

 

“Bari in fayyace cewa Amurka tana daraja ƙarfaffar dangantakar ta da Nijeriya da kuma nau’o’in hulɗa da yawa da ke tsakanin ƙasashen biyu.

 

“Bizar Amurka na taka muhimmiyar rawa wajen ci gaba da riƙe waɗannan lamurran dangantaka da ƙarfafa su, ko ta hanyar bai wa mutane damar tafiya domin ilimi, kasuwanci, yawon buɗe ido, ko musayar al’adu.”

 

Jakaden ya jaddada cewa ya zama dole a yi amfani da biza bisa ga dokoki da ƙa’idojin Amurka.

 

Ya ce: “Tabbas, muna maraba da baƙi ‘yan Nijeriya a Amurka kamar yadda Nijeriya take maraba da ‘yan Amurka masu zuwa wannan ƙasa. Dukkan gwamnatoci suna son baƙi su girmama dokokin ƙasashen mu da ƙa’idojin mu.”

 

Ya gargaɗi masu neman biza cewa yin amfani da ita ba bisa ƙa’ida ba ko bayar da bayanan ƙarya yayin neman ta yana iya rage amincewar juna a tsakanin ƙasashen biyu.

 

Ya ce: “Muna kira ga dukkan masu neman biza da su bayar da sahihan bayanai kuma su bi sharuɗɗan biza ɗin su, domin na sani, mafi yawan ‘yan Nijeriya suna yin hakan. Ta yin haka, za mu ƙarfafa ɗorewar zumunci tsakanin ƙasashen mu.”

 

Ambasada Mills ya kuma yaba wa Idris bisa jajircewar sa wajen kare ‘yancin faɗar albarkacin baki a Nijeriya, yana mai jaddada cewa wannan ɗabi’a ce da ta yi daidai da manufofin Amurka.

 

Ya kuma yaba wa haɗin kai da ake samu daga hukumomin Nijeriya, ciki har da Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa, Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya, Hukumar Kwastan ta Nijeriya, da Fadar Shugaban Ƙasa, wajen wayar da kan jama’a kan ƙa’idojin biza.

 

Haka kuma ya shawarci ‘yan Nijeriya da su nemi sahihan bayanai daga shafin soshiyal midiya na Ofishin Jakadancin Amurka kuma su tabbatar da cewa duk wata tambaya da suke da ita za su samu amsa cikin lokaci.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Al-Hilal ta ɗauki Nunez daga Liverpool
  • Gwamnan Kano Ya Sallami Mataimaka Biyu Kan Zargin Karkatar Da Kayan Tallafi
  • Gwamnatin Tarayya da Ofishin Jakadancin Amurka Sun Haɗa Gwiwa Don Wayar Da Kan ‘Yan Nijeriya Kan Sababbin Ƙa’idojin Samun Biza
  • Nijeriya Ta Horar Da Likitoci 360 Don Magance Mutuwar Mata Masu Juna Biyu
  • UEFA Ta Ci Tarar Lamine Yamal Da Lewandowski Kan Karya Dokar Shan Ƙwayar Ƙara Kuzari
  • NAJERIYA A YAU: Shekara nawa shugabanni ke bukata don cika alkawuran zabe?
  • Majalisar Jigawa Ta Yi Karatu Na Biyu Kan Dokar Fansho Ga Tsofaffin Shugabanni
  • Barcelona Ta Tube Ter Stergen Daga Mukaminsa Na Kaftin Din Kungiyar 
  • An Bude Gasar Wasannin Ta Duniya Ta 2025 A Chengdu
  • An kashe matafiya biyu da yin garkuwa da uku a Kwara