Masana Sun Bayyana Ingancin TELA Maize Ga Rayuwar Al’umma
Published: 9th, May 2025 GMT
Farfesa Bamaiyi ya bayyana ainihin aikin IAR a matsayin habaka nau’ikan dimbin amfanin gona da kuma jure fari wadanda suka dace da bukatun noma a Nijeriya.
Ya bayyana masarar TELA a matsayin wata sabon salo da kirkira ta zamani a kimiyyance domin magance matsalolin da ake ci gaba da addabar amfanin gona, kamar kwari da canjin yanayi.
Aikin “Masarar TELA bai takaita kan inganci da wadatar abinci ba, har ma tana ba da kariya ga rayuwar manoma, da inganta noman da kuma magance ainihin illar da tsutsotsi ke haifarwa, gami da juriya a yayin fari,” in ji shi.
Shi ma da yake jawabi a yayin ziyarar, Farfesa Muyideen Oyekunle, wani masani a fannin tsirrai kuma daya daga cikin jagorori masu bincike kan aikin masarar Tela, ya gano yadda akre bunkasa wannan noma tun a farkon shekarar 2019.
Ya jaddada cewa bayan shekaru masana kimiyya, tantance hadarin, da kuma bin ka’ida, sun tabbatar da cewa masara ba ta da wata illa ga dan’Adam da muhalli.
“Bincikenmu ya tabbatar da cikakkiyar hujja akan haka, kuma ya yi daidai da ka’idojin aminci na duniya. Abubuwan da ke tattare da GMOs ba a ma fara bayyana shi ba.
TELA maize ta samu duk wani bincike da ya dace a ce an yi domin kare lafiyar halittu, kuma muna da yakinin cewa ba ta da wata illa ga lafiyar dan’Adam,” in ji Farfesa Oyekunle.
Wata kwararriya daga Cibiyar, Farfesa Memuma Abdulmalik, wadda ta tabbatar da hakan, ta bayyana cewa an samar da TELA maide ne domin noman masara mai inganci tare da kawar da duk wani nau’i na kwari da kuma fari.
A cewarta, wadannan gyare-gyaren ba sa canza tsarin abinci mai gina jiki ko amincin amfanin gona.
“Manufar inganta kwayoyin halittar TELA maize ita ce kare amfanin gona daga kamuwa da tsutsotsi dake addabai tsirrai da kuma sanya jurewar fari. Bayan wannan babu abu abu mai cutarwa ga masarar ko kuma haifar da wani hadari ga muhalli,” in ji ta.
A nasa bangaren, Farfesa Shehu Ado ya bayyana cewa daga cikin amfanin masarar TELA maize, yana matukar rage bukatar magungunan kashe kwari, wadanda galibi ke haifar da illa ga lafiya da muhalli fiye da amfanin gona.
Ya kara da cewa, “Ta hanyar rage dogaro ga magungunan noma masu cutarwa, masara ta TELA maize na ba da gudummawa ga tsarin noma mai dorewa kuma wanda ya dace da muhalli,” in ji shi.
Masanan sun kuma yi nuni da cewa, bayanai marasa tushe da ake yadawa game da GMOs ya haifar da koma-baya ga sabbin ayyukan noma da za su ceto rayuka a Nijeriya. Sun bukaci kafafen yada labarai da su rika gaggauta yada sahihan bayanai masu alaka da kimiyya.
Masarar TELA maize, wadda aka samar a karkashin gidauniyar TELA ta fasahar noma ta Afrika wato (AATF) tare da hadin gwiwar IAR da sauran masu ruwa da tsaki, na ci gaba da gudanar da gwaje-gwajen gonaki da yawa, kuma a halin yanzu an amince da noman a yankuna da dama a Nijeriya.
Yayin da ake ci gaba da muhawarar jama’a game da kayan amfanin gonar, kungiyar IAR ta sake jaddada aniyarta ta tabbatar da gaskiya, aminci, da samar da mafita wadanda ke karfafa wa manoma domin tabbatar da an samar da isasshen abinci a kasa.
Nijeriya na iya tanadin Naira Biliyan 900 duk shekara ta hanyar TELA Maize – IAR
Cibiyar Binciken Aikin Noma ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta bayyana cewa Nijeriya za ta iya yin tanadin sama da Naira biliyan 900 a duk shekara ta hanyar amfani da irin masarar TELA da aka samar ta hanyar kwayoyin halitta.
A cewar cibiyar, daga cikin irin gudunmawar da masarar TELA za ta bayar, akwai rage dogaro da magungunan kashe kwari da ake shigowa da su daga waje da ake amfani da su don yakar kwari masu lalata amfani kamar farin Dan go.
Babban daraktan hukumar ta IAR, Farfesa Ado Adamu Yusuf, ya bayyana irin gagarumar fa’idar da masara ta TELA ke samarwa a fannin tattalin arziki da noma, sannan ya jaddada bukatar a gaggauta gyara kura-kuran da jama’a ke yi game da amfanin gonakin fasahar kere-kere.
A cewarsa, Nijeriya na kashe sama da Naira biliyan 900 (kimanin Dalar Amurka miliyan 600) a duk shekara wajen shigo da magungunan kashe kwari don magance kwarin masara kamar farin Dan go, ban da kudin aikace-aikace.
Ya lura cewa bullo da masarar TELA mai jure kwari da jure fari (SAMMAZ 72T zuwa 75T) zai rage kashe kudaden da ake yi sosai, tare da habaka amfanin gona, da kuma adana ajiyar waje.
Muhimman fa’idodin masarar TELA da aka bayyana a yayin ziyarar sun haɗa da: jurewar kwari, jure fari, ƙara yawan amfanin gona da kuma samar da abinci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Masara masarar TELA tabbatar da
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan sanda sun bankaɗo masana’antar man gyaɗa na bogi a Kaduna
Rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna ta bankaɗo wata haramtacciyar masana’antar man gyaɗan bogi, tare da cafke mutane uku da ake zargin suna da hannu a harkar.
Wannan samame da jami’an sashen leƙen asiri na rundunar suka gudanar ƙarƙashin jagorancin SP Sani Bello, ya gudana ne da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar ranar 5 ga Mayu bayan samun bayanan sirri.
An gabatar da sabbin shaidu kan Nnamdi Kanu Mazauna gari sun kori Boko Haram bayan kashe kyaftin ɗin sojaAn gano haramtacciyar masana’antar ce a wani fili da aka kewaye da katanga a titin Mamadi, a yankin Maraban Jos da ke Kaduna.
Mai magana da yawun ‘yan sanda na jihar, DSP Mansir Hassan, shi ne ya fitar da sanarwar a madadin Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Rabiu Muhammad, a ranar Laraba.
Ya bayyana cewa waɗanda aka kama a masana’antar sun haɗa da Zailani Shuaibu, mai shekaru 33, wanda ake zargin shine mamallakinta, da Nasiru Usman mai shekaru 24, da kuma Salisu Usman mai shekaru 49 – dukkansu mazauna Maraban Jos ne.
A cewarsa, ‘yan sanda sun samu ganguna biyu maƙare da kayan aikin sarrafa man, da jarkoki goma sha biyar masu nauyin lita 25 na man da ba a kammala tacewa ba, sai jarkoki biyu da ke ɗauke da man gyaɗa na bogi da aka gama tacewa, da kuma ganga guda mai kyau.
DSP Hassan ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar ya jaddada ƙudirin rundunar na kare lafiyar jama’a da kuma kawar da ayyukan laifi a cikin al’umma.
Haka kuma, ya buƙaci mazauna da su ci gaba da lura da abin da ke faruwa a yankunansu domin kai rahoton motsin da ba su gamsu da shi ba zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa da su.