Kakakin Gwamnatin Iran Ta Yi Suka Kan Masu Son Canja Sunan Tekun Fasha Saboda Jahilcin Tarihin Iran
Published: 8th, May 2025 GMT
Kakakin gwamnatin kasar Iran ta bayyana cewa: Duk wanda ya canza sunan Tekun Fasha, tabbas ya jahilci tarihin dubban shekaru na Iran
Mai magana da yawun gwamnatin Iran Fatimah Mohajerani ta yi tsokaci kan rahotannin da suke cewa: Shugaban Amurka Donald Trump na yunkurin sauya sunan yankin tekun Fasha.
Malama Mohajerani ta rubuta a dandalin na X cewa: Tekun Fasha bai takaita da kasancewa sunan yanki kadai ba, a’a ya zama wani muhimmin bangare na tarihin al’ummar Iran.
Ta kara da cewa: “Wadanda ke neman canza sunan ‘Tekun Fasha’ ba su fahimci tarihin Iran na dubban shekaru ba. Wannan yunkuri na nuna rashin sanin gaskiya da tarihi kafin ya zama batun neman tunzura Iran.”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Nijar Ta Soke Yarjejeniyar Tattara Bayanai Da Rasha Da Turkiyya, Ta Fara Neman Sabbin Abokan Hulɗa
Sai dai, rikice-rikicen cikin gida da matsalolin tsaro da tattalin arziƙi sun sa gwamnatin ke ci gaba da yin gyare-gyare don samar da hanyoyin da za su ba ta kariya da cikakken iko kan harkokin leƙen asiri da tsaro.
Wannan mataki yana iya nuni da cewa Nijar na ƙoƙarin zama mai dogaro da kai a fannin tsaro, ko kuma tana neman ƙawancen da zai fi dacewa da manufofinta na cikin gida da waje.
Duk da haka, ƙwararru na ganin cewa hakan na iya janyo sabon matsin lamba daga ƙasashen duniya da ƙungiyoyin yanki kamar ECOWAS.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp