2025-05-09@20:03:37 GMT
إجمالي نتائج البحث: 245
«masarar TELA»:
Farfesa Bamaiyi ya bayyana ainihin aikin IAR a matsayin habaka nau’ikan dimbin amfanin gona da kuma jure fari wadanda suka dace da bukatun noma a Nijeriya. Ya bayyana masarar TELA a matsayin wata sabon salo da kirkira ta zamani a kimiyyance domin magance matsalolin da ake ci gaba da addabar amfanin gona, kamar kwari da canjin yanayi. Aikin “Masarar TELA bai takaita kan inganci da wadatar abinci ba, har ma tana ba da kariya ga rayuwar manoma, da inganta noman da kuma magance ainihin illar da tsutsotsi ke haifarwa, gami da juriya a yayin fari,” in ji shi. Shi ma da yake jawabi a yayin ziyarar, Farfesa Muyideen Oyekunle, wani masani a fannin tsirrai kuma daya daga cikin jagorori masu...
Ƙungiyar Allied Group of Nasarawa Professionals (AGNP), wadda ta ƙunshi ’yan kasuwa da masu sana’o’in hannu, ta goyi bayan tsohon Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Mohammed Adamu, wanda ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Gwamnan Jihar Nasarawa a 2027. A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a ofishinta da ke Keffi, AGNP ta ce matakin da Adamu ya ɗauka na tsayawa takara ya sanya al’ummar jihar cikin farin ciki. ’Yan sanda sun kama harsasai 500 a Filato Jami’an tsaro na ba da gudunmawar aikata miyagun laifuka a Nijeriya — Zulum “Wannan lokaci ne na kyawawan fata ga jiharmu,” in ji ƙungiyar. Ƙungiyar ta yi alƙawarin tattara ƙuri’u aƙalla miliyan daya domin mara wa Adamu baya a zaɓen. AGNP ta yaba...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar kare hakokin masu sayayya ta ta kasa tare da haka da Hukumar Kare Data ta kasa NDPC ne, suka gudanar da binciken na watanni 38. A cikin binciken na su, sun bayyana yadda ake take saba ka’ida tare da take dokar kasa da kuma take hakkin ‘yan Adama na kasa da kasa. Wannan Jaridar na da ra’ayin cewa, ‘yayan Kotun uku da Mai Shari’a Alkalan Kotun Thomas Okosun da ya yanke wannan hukunci, sun canci yabo kan tsaywar da suka yi kai da Fata na yanke wannan hukuncin, duk da matsin lambar da suka fuskanta, inda suka tabbatar da ikon da Hukumomin FCCPC da NDPC suke da shi. Kazalika, abinda ya kara nuna mahimmancin hukuncin Kotun,...

An Yi Taron Musayar Al’adu Da Cudanyar Jama’a Na Bikin Cika Shekaru 80 Da Nasarar Yakin Da Sinawa Suka Yi Kan Zaluncin Japan Da Yakin Ceton Kasa Na Tsohuwar Tarayyar Soviet
An gudanar da taron musayar al’adu da cudanyar al’umma na murnar cika shekaru 80 da samun nasarar yakin turjiya na jama’ar kasar Sin a kan zaluncin kasar Japan da kuma kazamin yakin ceton kasa na tsohuwar tarayyar Soviet, wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) da kamfanin gidajen talabijin da rediyo na kasar Rasha suka shirya a birnin Moscow. An karanta wasikun taya murna daga shugaban kasar Sin Xi Jinping da na Rasha Vladimir Putin a wajen taron. A jawabinsa, babban darektan CMG, Shen Haixiong, ya bayyana cewa, yayin da bikin shekarar al’adun Sin da Rasha ya kankama, bari mu dauki ruhin sakon wasiku na taya murna a matsayin jagora, karkashin jagorancin shugabannin kasashen biyu....
Burin Arsenal na lashe gasar UEFA a karon farko a tarihinta ba zai cika a wannan shekarar ba, sakamakon rashin nasarar da ta yi a hannun PSG a wasan zagayen na kusa da na karshe, Arsenal ta buga wasan karshe a UEFA sau daya a shekarar 2006 tsakaninta da Barcelona. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wani rahoto na musamman da HKI ta gudanar akan asarar da ta fuskanta sanadiyyar yaki da Hizbullah, ya bayyana cewa, a fagen aikin gona kawai sun yi asarar dalar Amurka miliyan 108 wacce ta fara daga 8 ga watan Oktoba 2023. Kungiyar ReGrow Israel” ta ce, yakin da aka yi da Hizbullah ya yi barna gagaruma a fagen aikin gona da asarar da ta kai ta dala miliyan 108 a kan iyaka da Lebanon. Nazarin wannan kungiyar ya kuma kara da cewa; Tun daga ranar 8 ga watan Oktoba 2023 har zuwa lokacin tsagaita wutar yaki a karshen 2024, hare-haren Hizbullah sun lalata muhimmacin cibiyoyi a “Isra’ila” da kuma haddasa gobara mai girma, da hakan ya tilastawa mazaunan yankin, musamman...
Kasashen duniya na ci gaba da nuna matukar damuwa game da rikicin da ya barke tsakanin Pakistan da Indiya. Iran na daga cikn jerin kasashen da a baya bayan nan suka nuna damuwa. Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Iran ta fitar ta ce “Jamhuriyar Musulunci ta bayyana matukar damuwarta kan yadda takun saka tsakanin Indiya da Pakistan ke ci gaba da ruruwa. Iran ta ce a matsayinta na kasa mai iyaka da Pakistan wacce kuma ke da kyakkyawar alaka da Indiya, ta yi tayin shiga tsakani a rikicin tun cikin watan Maris. Kasar Turkiyya ma ta yi gargadin game da rikicin. Inda a wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar ta yi Allah wadai da hare-haren da ake...
Mamba a majalisar gudanarwa ta kungiyar Ansarulla ta kasar yemen Muhammad Bukhaiti ya bayyana cewa hare-haren da HKI da Amurka suka kai fararen hula a kasar yemen wuce jan layi, ko ketare haddi ne na kungiyar don haka su jira maida martani mai tsanani. Kamfanin dillancin labaran Iran ya nakalti yana fadawa tsahar talabijin ta Al-mayadeen ta kasar Lenamon a yau Talata. Ya kuma kara da cewa hare-haren da Amurka suke kaiwa ma’aikatu da wuraren fararen hula a kasar Yemen na baya-bayan nan duk sun nuna cewa an sami nasara a kansu. Albukhaiti ya kara da cewa sadaukarwa da mutanen kasar Yemen suke yi saboda Gaza, ba zai tsaya ba, sannan muna son fadawa kasashen Amurka da ingila da kuma...
Shugaban Ghana a wannan Litinin ɗin ya bayyana ɗaukar mataki kan ministoci da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa fiye da 40 da suka gaza bayyana kadarorin da suka mallaka. Wannan na zuwa ne a yayin da Shugaba John Mahama ke ci gaba da zage dantse wajen yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙasar da ke yammacin Afirka. ’Yan bindiga sun kashe matar aure bayan karɓar N10m kuɗin fansa ’Yan fashi sun kashe matashi a Kano A yayin karɓar rantsuwar kama aiki a watan Janairun bana ne Shugaban Ghana ya sha alwashin yaƙi da rashawa domin fitar da ƙasar daga ƙangin matsalar tattalin arziki A watan Afrilun da ya gabata ne mahukunta suka gurfanar da wani babban jami’in tsaro...
A jajibirin bikin cika shekaru 80 da samun nasarar babban yakin ceton kasa a kasar Rasha, rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, tare da hukumar kula da harkokin fina-finai ta kasar Sin, za su gudanar da bikin tallata fim din “Red Silk” wanda Sinawa da ‘yan Rasha suka shirya a birnin Moscow. A wannan lokacin, mashirya fim din Sinawa da ‘yan Rasha, za su yi musayar ra’ayoyinsu kan yadda suka shirya fim din, tare da sanar da cewa, za a fitar da fim din a kasar Sin a watan Satumba na wannan shekara a lokacin da kasar Sin ke bikin cika shekaru 80 da samun nasarar yakin juriya na jama’ar kasar Sin kan zaluncin Jafanawa da...
Kotun duniya ta yi watsi da karar da Sudan ta kai Hadaddiyar Daular Larabawa tana mai zarginta da hannu a kisan kiyashin da aka yi wa al’ummar wannan kasa. A yau Litinin ne kotun duniyar ta yi watsi da karar ta Sudan, tana mai wanke Hadaddiyar Daular Larabawa. Ita dai Sudan ta zargi Hadaddiyar Daular Larabawar da cewa ta hada baki da dakarun kai daukin gaggaawa wajen yi wa mutanen yankin Darfur kisan kiyashi. A nata gefen Hadaddiyar Daular Larabawan ta ki amincewa da tuhumar da Sudan ta yi mata tana mai siffata ta da cewa; Farfaganda ce, kuma Sudan din ta yi hakan ne domin kawar da hankulan duniya daga kan laifukan da sojoji suke aikatawa.
Jami’in ya kara da cewa, dakarun tsaron yankunan teku na Sin sun aiwatar da dukkanin matakan da suka wajaba, na gargadi da korar jirgin saman na Japan, wanda hakan mataki ne halastacce da kuma ya dace da doka. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rundunar sojojin Najeriya ta 1 karkashin jagorancin Birgediya Janar Timothy Opurum ta samu gagarumar nasara a yakin da take yi da ta’addanci da ‘yan bindiga a jihar Zamfara, musamman a kananan hukumomin Talata Mafara da Kaura Namoda. A wata sanarwa da mukaddashin mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar soji, Kyaftin Sulaiman Omale ya fitar tace a farkon farkon watan Mayun 2025, dakarun su da ke sintiri na yaki sun ci karo da dimbin ‘yan ta’adda da suka kutsa kai kauyen Mai Kwanugga a karamar hukumar Talata Mafara. Ya yi bayanin cewa, ‘yan ta’addan sun rika kai hari kan mutanen yankin tare da kona gidaje kafin isowar sojojin, inda ya ce, bayan tuntubar rundunar, sojojin sun yi nasarar...
A cewar hukumar, kamfanonin mai da iskar gas da ke aiki a kasar sun samar da iskar gas na naira biliyan 22.3 daga ayyukansu na teku. Hukumar ta lissafa asarar ta amfani da Babban Bankin Nijeriya (CBN) na musayar canji na naira 1,520 zuwa dala daya. Hukumar kula da muhalli ta lura cewa yawan iskar gas da ya tashi daga bangaren teku na masana’antar a watan Janairu da Fabrairu, ya ba da gudummawar tan miliyan 1.2 na iskar ‘carbon diodide’ zuwa sararin samaniya, tare da samar da wutar lantarki na Gigawatts 2,200, yayin da kamfanonin da suka kunna iskar gas ke da alhakin takunkumin dala miliyan 44.7 (Naira biliyan 67.944). A daidai wannan lokacin a cikin 2024,...
Ana gwabza kazamin fada a Sudan, inda dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces suka kashe fararen hula kusan 300 A tsakiyar bala’in Sudan, ana ci gaba da gwabza kazamin fada tsakanin sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa, a daidai lokacin da ake fama da munanan ayyukan jin kai da ke ba da mummunan hoto kan makomar kasar. A yammacin jihar Kordofan, sojojin kasar Sudan sun sanar da janyewa daga birnin Nahud, bayan kazamin fada da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces, wadanda suka sanar da kwace iko da birnin da kuma hedikwatar Brigade ta sha takwas, baya ga birnin Al-Khawi. Yayin da ake ci gaba da gwabza fada, gwamnatin Sudan ta zargi dakarun kai daukin...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bukaci matasan kasarsa da su zage damtse, wajen bayar da gudummawar cimma nasarar zamanantar da kasa, ta hanyar yin dukkanin sadaukarwa da kasar ke bukata daga gare su. Shugaba Xi, ya yi wannan tsokaci ne cikin martanin wasikar da ya aike ga rukunin malamai masu aikin sa kai, a wata makaranta dake yankin kan iyakan kasar mai nisa, karkashin jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kai dake arewa maso yammacin kasar Sin. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe ...
Sojojin kasar Pakistan sun sanar da yin nasarar gwajin makamai mai linzami da ake harbawa daga kasa, wanda yake cin Zangon kilo mita 450. Sanarwar sojojin kasar ta Pakistan ya kunshi cewa; Sun yi gwajin ne dai domin tabbatar da zama cikin shiri na sojoji, da kuma tabbatar da ingancin aikin makamin. Gwajin makamin na sojojin Pakistan ya zo ne a daidai lokacin da ake zaman dar-dar a tsakaninta da kasar Indiya, bayan wani harin ta’addanci da aka kai a yankin Kashmir. A ranar 22 ga watan Afrilu ne dai aka kai wani hari akan masu yawon bude ido a yankin na Kashmir wanda ya yi sanadiyyar kashe mutane 26. Da akwai fargabar cewar kasashen biyu za su tsunduma cikin...
Ya ci gaba da cewa, tuni aka fara gudanar da wasu manyan ayyukan a Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar, musamman a ta Lekki da ta Tin Can Island. Shugaban ya bayyana cewa, an kuma samar da kafar sadarwa ta zamani ga masu ruwa da tsaki a daukacin Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar, domin a rinka yin musayar Data, har da lokacin da ya dace, a fara gudanar da aiki. Ya sanar da cewa, idan an kammala wannan aikin, za su kara taimaka wa wajen kara inganta ayyukan Hukumar, na tsawon sa’oi 24. Dantosho wanda Manajan Sashen Tashar da ke a jihar Legas Lawal Ibrahim ya wakilce shi a wajen taron ya bayyana cewa, Hukumar ta kuma yi hadaka da Rundunar Sojin Ruwa,...
Masana harkokin tsaro sun ja hankalin hukumomi su ɗauki matakan da suka dace bayan gobarar ma’ajiyar makamai a babban Barikin Sojoji na Giwa da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno. Sun bayyana damuwa game da mummunan abin da ke iya biyo baya ta fuskoki daban-daban, tare da bayar da shawarar matakan da ya kamata a ɗauka domin daƙile ayyukan miyagu da ke iya ƙoƙarin cin gajiyar yanayin a matsayin wata dama ta aikata mugun laifi ko ta’addanci. Damuwar ƙwararru kan ƙarsashi da karfin sojoji Wani ƙwararre kan harkokin tsaro, Kabiru Adamu, ya ce illar wannan lamari ta wuce ɓarnar zahiri da kuma yiwuwar asarar rayuka. Ya ce, “Lalacewar makamai, harsasai, da sauran muhimman kayan aikin soja a barikin babban asarar...
Masana harkokin tsaro sun ja hankalin hukumomi su ɗauki matakan da suka dace, lura da abin da ke iya biyo bayan gobarar ma’ajiyar makamai a babban Barikin Sojoji na Giwa da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno. Sun bayyana damuwa game da mummunan abin da ke iya biyo baya ta fuskoki daban-daban, tare da bayar da shawarar matakan da ya kamata a ɗauka domin daƙile ayyukan miyagu da ke iya ƙoƙarin cin gajiyar yanayin a matsayin wata dama ta aikata mugun laifi ko ta’addanci. Damuwar ƙwararru kan ƙarsashi da karfin sojoji Wani ƙwararre kan harkokin tsaro, Kabiru Adamu, ya ce illar wannan lamari ta wuce ɓarnar zahiri da kuma yiwuwar asarar rayuka. Ya ce, “Lalacewar makamai, harsasai, da sauran muhimman...

Sabon Tsarin Ci Gaba Na Sin Ya Kawo Sauyi Daga Samar Da Takalma Miliyan 100 Zuwa Kera Mattarar Bayanai Ta Microchip
Kamar yadda firaministan kasar Malaysia Anwar bin Ibrahim ya fada a kwanan baya cewa, yayin da kasa da kasa ke fuskantar mawuyacin hali, suna bukatar samun tabbaci da wani nagartaccen shiri na samun ci gaba. Don haka, ana ganin yadda kasar Sin ta samu nasarori, an nuna yabo ga kasar ta Sin, kasar Sin ta kawo tabbaci da kuma kyakkyawar makoma ga duniya. (Zainab Zhang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Kimanin Naira biliyan ɗaya ce aka ƙiyasta ta salwanta sakamakon gobarar da ta ƙone wani sashe na babbar kasuwar da ke tsakiyar garin Jos, babbar birnin Jihar Filato. An rawaito cewar gobarar ta laƙume shaguna fiye da ɗari biyar, galibinsu na masu sayar da kayan gwanjo. Mutane da dama dai sun rasa hanyar cin abincinsu, kasancewar galibinsu sun dogara ne da samun da suke yi a kullum a wannan kasuwa don ciyar da iyalansu. Ko a wane hali waɗanda suka tafka wannan asara suke ciki bayan wannan ibtila’i? NAJERIYA A YAU: Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta DAGA LARABA: Asarar Da Hausawa Ke Tafkawa Sakamakon Bacewar Tatsuniya Wannan na...

Masifar Gobara Tana Kara Bunkasa A Haramtacciyar Kasar Isra’ila Tare Da Fara Raba Yahudawa Da Muhallinsu
Ana sa alamar tambayar cewa: Shin gobarar da ta tashi a birnin Kudus… shin sako ne na ranar tunawa da kafuwar gwamnatin ‘yan sahayoniyya? Gobarar da ta tashi a tsaunin Kudus da aka mamaye ta bazu zuwa manyan yankuna a cikin haramtacciyar kasar Isra’ila, inda ta kewaye wani sansanin soji tare da cinye filayen masu girma da tsayi. Hakan ya sa hukumomin gwamnatin mamayar Isra’ila suka kafa dokar ta baci tare da neman taimakon kasashen duniya. Yayin da Ministan tsaron cikin gidan Isra’ila Itamar Ben-Gvir yake neman dora wa Falasdinawa, alhakin tashin gobarar. Gobarar ta kunno kai ne a daidai lokacin da yahudawan sahayoniyya suka fara gudanar da bukukuwan cika shekaru 77 da kafuwar gwamnatinsu ta mamaya a kasar Falasdinawa,...
A ranar Laraba ne jami’an sojojin ruwa na Najeriya da ke Fatakwal suka ceto fasinjoji 99 daga wani hatsarin kwale-kwale da ya rutsa da su a kogin Bukuma da ke ƙaramar hukumar Degema a Jihar Ribas. Jirgin ruwan, wanda yake na jigilar fasinja yana kan hanyarsa ta daga Fatakwal zuwa Ƙaramar hukumar Akuku-Toru, inda ya yi karo da wani jirgin ruwa a tsakiyar kogin. Gobara ta lalata shagunan kasuwar waya a Kwara Dalilin da ya sa aka samu fashewar abubuwa a barikin Maiduguri – Sojoji Jami’ar yaɗa labarai na sansanin, Laftanar Kwamanda Bridget Bebia, a wata sanarwa da ta fitar a Fatakwal, ta ruwaito Kwamandan sojojin masu aikin bincike, Commodore Cajethan Aniaku, ya tabbatar da faruwar lamarin. A cewar Aniaku,...
Wata gobara da ta tashi a yammacin ranar Laraba a wata shahararriyar kasuwar wayoyin salula da ke ‘Challenge Market’, a Ilorin babban birnin Jihar Kwara, ta yi mummunar ɓarna. Gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 9:06 na dare kuma ana kyautata zaton wutar lantarki ce ta haddasa ta. Dalilin da ya sa aka samu fashewar abubuwa a barikin Maiduguri – Sojoji ’Yan fashin teku sun sace mata 4 a hanyar ruwa ta Bayelsa Kasuwar tana da shaguna sama da 120, rumfunan 80, da wasu wuraren kasuwancin wayar da yawa. Rahotanni sun ce gobarar ta shafi rumfuna 10. A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta Jihar Kwara, Hassan Adekunle ya fitar a ranar Alhamis, ya...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tatsuniya wata hanya ce ta ilmantarwa da bayar da tarbiyya da kuma koyar da al’adu da halaye na gari a tsakanin Hausawa. Tatsuniyoyi na ɗauke da darussa na rayuwa, suna kuma koya wa yara da manya jarumta da tausayi da sauran dabi’u kyawawa. Sai dai a yayin da duniya take sauyawa, ba kasafai matasa suke sha’awar sauraron tatsuniya ba. NAJERIYA A YAU: Dalilin karyewar farashin shinkafa a kasuwannin Najeriya DAGA LARABA: Dalilan Rashin Wutar Lantarki A Wasu Jihohin Arewa Wannan ne batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
Haka kuma ya nemi kotu da ta bayar da umarnin ci gaba da amfani da tsoffin takardun kuɗi na Naira 200, 500 da kuma 1000. Baya ga haka, ya buƙaci a umarci su da su nemi gafara ta hanyar wallafa bayani a manyan jaridu biyu na ƙasa. Amma a zaman kotu na ranar Litinin, wanda ya shigar da ƙarar da lauyansa ba su halarci zaman kotu ba. Lauyan da ke kare Emefiele da CBN, Mista Chikelue Amasiani, ya sanar da kotu cewa tun da aka shigar da ƙarar, mai ƙarar da lauyansa ba su nuna wata alama ta son ci gaba da shari’ar ba. Ya roƙi kotun da ta kori ƙarar. Mai shari’a Ekwo ya amince da buƙatar kuma ya...
Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa kuskure ne abin da jami’anta ke yi na cin zarafi da cin zalin fararen hula saboda sun sanya kayan sojoji. Shugaban Sashen Hulɗar Sojoji da Fararen Hula na rundunar, Manjo-Janar Gold Chibuisi, bayyana cewa rundunar tana hukunta duk jami’inta da aka kama da laifin cin zalin farar hula saboda sanya kayan sojoji. Ya ce duk da haka doka ta haramta wa fararen hula sanya kayan sojoji ba bisa ka’ida ba, kuma laifi ne da zai iya kai su gidan yarin. Manjo-Janar Gold Chibuisi, ya ci gaba da cewa doka ba ta ba ta ba sojoji ikon hukuntawa balantana cin zalin masu aikata hakan ba. Sai kuma ta ba su ikon kama masu sojan gona...
Ministan harkokin cikin gidan Iran Askandar Mumini wanda ya kai Ziyara zuwa wurin da gobarar ta tashi ya sanar da cewa adadin wadanda su ka jikkata sun kai 750 da kuma wadanda su ka rasa rayukansu zuwa 14. Sai dai kuma daga baya ma’aikatar shari’a ta kasar Iran din ta ta sanar da karuwar wadanda su ka kwanta dama zuwa 21 Mai shigar da kara na gundumar Hurzumgan, Mujtaba Kahraman ya sanar da cewa; Daya daga cikin aikin da suke yi shi ne tantance wadanda su ka su ka rasa rayukansu. Haka nan kuma ya kara da cewa; Ya zuwa yanzu sun tabbatar da mutuwar mutane 21. Har ila yau ya bayyana cewa bayan tantance gawawwakin wadanda su ka rasa...
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya EFCC, ta ayyana neman wasu jami’an CBEX waɗanda take zargi da hannu a damfarar ’yan kasar miliyoyin kuɗaɗe a wani tsarin zuba kuɗi. Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da EFCC ta wallafa a shafinta ranar Juma’a. An gano tsohuwar da ake nema a cikin maciji A soma laluben watan Zhul Qi’da — Sarkin Musulmi Sanarwar ta ambato EFCCn tana zargin mutanen takwas da yaudarar jama’a su zuba kuɗi don samun riba – daga bisani suka tsere da kuɗaɗensu. Hukumar ta bayyana sunayen mutanen da Seyi Oloyede da Emmanuel Uko da Adefowora Oluwanisola da Adefowora Abiodun Olaonipekun. Sauran sun waɗanda ta ce ’yan ƙasashen waje ne sun haɗa da Johnson Otieno...
Koton tsarin Mulki ta kasar Gabon din ta tabbatar da nasarar da Brice Clotaire aOligui Nguema a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi. Sakamakon zaben dai ya nuna cewa Nguema ya sami kaso 94.85.% da hakan ya mayar da shi akan gaba a tsakanin dukkanin ‘yan takara. Nguema dai tsohon janar ne wanda ya yi juyin Mulki a cikin watan Ogusta na 2023 da ya kifar da gwamnatin Ali Bongo Odnimba. Magoya bayan Nguema sun yi bikin hukuncin da kotun ta yanke na samun nasarsa. Zaben ya kawo karshen matakin rikon kwarya bayan kifar da gwamnatin iyalan Bongo da su ka yi kusan rabin karni akan karagar Mulki. Zababben shugaban kasar ta Gabon ya yi alkawalin...
Ya koka kan halin da kasar ke ciki, kuma ya bukaci ‘yan arewa da su yi taka-tsantsan da ‘yan siyasa masu rarraba kawunan mutane da yaudara, gabanin babban zabe mai zuwa. “Muna son gwamnati da za ta fahimci matsalolinmu kuma ta magance su. Bayan shekaru takwas na mulkin Muhammadu Buhari, mun dauki darasi. ”Yanzu haka muna cikin wata gwamnati, kuma har yanzu muna kuka. Kuka kadai ne muka san yadda za mu yi?” Baba-Ahmed ya tambaya. Baba-Ahmed ya ce arewa ta sha wahala sosai a lokacin Boko Haram, wanda ya shafi dukkan kungiyoyi, ciki har da Musulmi da Kiristoci da Fulani da Baju, da sauransu, yana mai jaddada bukatar hadin kai. “Kafin Buhari ya zama shugaban...

‘Yan Sama Jannati 3 Na Kumbon Shenzhou-20 Na Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniyar Sin Cikin Nasara
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Bankin Zenith ya kasance a kan gaba tare da samun ribar naira tiriliyan 1.32 kafin a biya haraji, wanda hakan ke nuna karin kashi 67 cikin 100 daga naira biliyan 796 da aka samu a shekarar 2023. Bankin GTCO ya bi sahu, inda ya fitar da ribar kashi 107.8 kafin a fara biyan haraji zuwa naira tiriliyan 1.266, daga naira biliyan 609 na bara. Har ila yau, Access Corp da UBA sun taka rawar gani sosai, inda suka samu ribar naira biliyan 867 da kuma naira biliyan 803.7, wanda ya zarce adadin da suka samu a shekarar 2023 na naira biliyan 729 da kuma naira biliyan 757.6. First HoldCo ya kuma samu ribar kashi 124 cikin 100...
Sashin ma’adinai da ba na karfe ba ta kashe kudin makamashi da kashi 33.7 zuwa naira biliyan 118.49, kuma masana’antar yadi, tufafi da takalmi kudin da ya kashe ya karu sau hudu, wanda ya kai naira biliyan 26.45 a shekarar 2024, idan aka kwatanta da naira biliyan 6.97 a shekarar 2023. Rahoton ya ce duk da an samu karin wutar lantarki a cikin masana’antu a shekarar 2024, da adadin karin wuta na awa 13.3 a kwace ranar da ya karu daga awa 10.6 a shekarar 2023. Kazalika karin kudin wuta ya karu da kaso 200 ga wadanda suke amfani da rukunin A, don haka kudaden da masana’antun ke kashewa wajen biyan kudin wuta nan ma ya karu sosai....
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa ba tabbas ko za’a iya kawar da cutar zazzabin cizon sauro nan da shekarar 2030, musamman a nahiyar Afrika. Fiye da mutane miliyan 263 ne suka kamu da cutar a cikin 2023, kuma kusan 600,000 ne suka mutu sanadin cutar a cewar alkalumman na MDD. Musamman a wannan lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ya rage kashe kudaden tallafi na kasa da kasa, inji rahoton. A cikin shekaru 25, zuba jari a yakin da ake yi da zazzabin cizon sauro ya hana kamuwa da cutar ga mutane biliyan 2 da kuma mutuwar mutane miliyan 13, musamman a Afirka. “Akwai babbar barazana, da kuma bukatar jajircewa wajen samar da magunguna in ji Philippe Duneton, darektan...
Sabbin ‘yan sama-jannatin da aka tura, za su gudanar da gwaje-gwaje da bincike game da yanayin rayuwa a sararin samaniya, da kimiyyar karamar fizgar kasa ko jazibiyya (micro-gravity physics) da sabbin fasahohin sararin samaniya. Kazalika, za su kuma yi tafiye-tafiye mabambanta a sararin samaniya don kakkafa shingayen kariya daga baraguzai da tarkacen sararin samaniya, da kuma girkewa da dawo da na’urorin da aka makala a wajen tashar. Ya zuwa yanzu dai, ‘yan sama jannatin kasar Sin 26 ne suka yi nasarar zuwa sararin samaniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere). Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da...

Shugaba Xi Ya Jaddada Aniyar Kasarsa Ta Goyon Bayan Kudurorin Kyautata Yanayi Da Ci Gaba Marar Gurbata Muhalli
Ya ce, “Muddin muna da kwarin gwiwa, da karfin goyon bayan juna da hadin kai, za mu kai ga kawar da manufofi masu illa, da wanzar da daidaito da ci gaba a manufofin jagoranci a fannin kare yanayi da samar da ci gaba. ” (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Mutane 47 ne suka rasa rayukansu tare da jikkatan wasu da dama a harin da aka kai da jirgin sama kan birnin El-Fasher na kasar Sudan Runduna ta 6 da ke yankin El- Fasher ta sanar da mutuwar fararen hula 47 tare da jikkata wasu da dama sakamakon kazamin lugudan wuta da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces suka yi kan birnin El- Fasher, fadar mulkin jihar Darfur ta Arewa. A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce: Dakarun Kai Daukin Gaggawa na Rapid Support Forces na ci gaba da kai hare-hare kan fararen hula, inda suka yi amfani da harsasai masu yawa a yayin da suka yi ruwan wuta a kan unguwannin birnin El-Fasher a...

Rohoton Kwamitin Kare Hakkin Dan Adam Ya Tabbatar Da Tafka Manyan Laifukan Cin Zarafin Bil-Adama A Siriya
Wani rahoton kare hakkin bil adama ya tabbatar da aikata manyan laifuka a gabar tekun Siriya tare da yin kira da a kare fararen hula Kwamitin da ke bin diddigin kare hakkin bil adama a kasar Siriya karkashin jagorancin dan gwagwarmaya Haitham Al-Manna, ya fitar da wani cikakken rahoton take hakkin dan Adam mai shafuka 72 da ke kunshe da jerin munanan laifukan da aka yi wa fararen hula a gabar tekun Siriya, yana mai bayyana shi a matsayin “neman shafe wata al’ummar daga kan doron kasa a kan tubalin sabanin Mazhaba”. Rahoton wanda masu fafutuka 12 suka shirya, ya zo ne bayan kisan kiyashin da aka fara a ranar 6 ga Maris. Rahoton ya yi nuni da wani tsari...
A shekarar 2024, an kammala jigilar fasinjojin da yawansu ya kai biliyan 1.46 a filayen jiragen sama na kasar Sin yayin da yawan tashi da saukar jiragen sama ya wuce miliyan 12.4, adadin sun karu da kashi 15.9 bisa dari da kuma kashi 5.9 bisa dari, idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara. Hakan ya nuna cewa, duka alkaluma masu alaka da harkokin sufuri sun kafa tarihi. Kazalika, a ranar 21 ga wata, kungiyar filayen jiragen sama masu daukar fasinja ta kasar Sin, da kwalejin nazarin kimiyya da fasahar jiragen sama masu daukar fasinja ta kasar Sin, da sauransu sun fitar da “Rahoton kimanta ingancin hidimar filin jirgin sama na shekarar 2024”, inda rahoton ya ce, akwai daidaito...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kungiyar kare farar hula ta Falasdinu ta zargi sojojin da ” kashe-kashe masu yawa” a yayin farmakin da ya kashe ma’aikatan jinya 15 a cikin watan Maris a zirin Gaza, wanda ya saba wa sakamakon wani rahoton bincike na cikin gida da sojojin Isra’ila suka fitar. Wani jami’in tsaron farar hula a Gaza Mohammed al-Moughair ya shaidawa AFP cewa “Bidiyon da daya daga cikin ma’aikatan jinya ya dauka ya tabbatar da cewa rahoton da sojojin Isra’ila suka fitar akwai karairayi a ciki saboda ta aiwatar da hukuncin kisa. Al-Moughair ya kuma zargi Isra’ila da neman kaucewa abinda ya wajaba kanta a karkashin dokokin kasa da kasa. Tunda farko dama Kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu ta yi watsi da...
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Burnley United tare da takwararta ta Leeds United sun samu nasarar dawowa gasar Firimiya bayan samun nasara a mabanbantan wasannin da suka buga. Burnley ta doke Sheffield United da ci 2-1 da yammacin yau domin samun wannan nasarar, hakazalika Leeds United ta samu nasara akan Stoke City da ci 6-0 a daya wasan na yau, dukkan kungiyoyin biyu zasu buga gasar Firimiya Lig ta badi. Alex Iwobi Ya Kafa Tarihi A Gasar Firimiya Salah Ya Kafa Tarihi Yayin Da Liverpool Ke Dab Da Lashe Gasar Firimiya Yayinda kungiyoyin Firimiya Southampton da Leicester City suka koma gasar Championship su kuma Burnley da Leeds United sun samu nasarar tsallakawa zuwa gasar Firimiya a kakar wasa ta badi....
A ranar Litinin ɗin nan aka wayi gari da fastocin takarar shugaban ƙasa a Zaɓen 2027 na Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed. An liƙa fastocin wuri-wuri da suka haɗa da shataletale da turakun wutar lantarki da allunan tallace-tallace daban-daban a wasu manyan tituna da ke ƙwaryar birnin na Bauchi. HOTUNA: An yi zanga-zangar adawa da matsalar tsaro a Filato Bikin Ista: Hatsarin mota ya laƙume rayuka 5 a Gombe Aminiya ta ruwaito cewa fastocin masu ɗauke da saƙon “Kaura for President” an manna su a wasu manyan hanyoyi da suka haɗa da titin jirgin ƙasa, Sabon Titin Karofi da kuma Ƙofar Dumi. Ɗaya daga cikin matasan da ke aikin manna fastocin, Aminu Auwal, ya shaida wa Aminiya cewa wasu...
Har ila yau, rahoton ya nuna cewa, yayin da adadin yabanya ke karuwa a cikin gida, kuma karuwar bukatunsu ke raguwa, akwai hasashen raguwar bukatar shigo da nau’o’in amfanin gona cikin kasar daga ketare. (Mai Fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Amurka ta sake kai wani hari ta sama kan babban birnin kasar Yemen, Sana’a, inda ta kashe fararen hula akalla 12 tare da jikkata wasu fiye da 30 na daban. Mummunan harin na Amurka an kai shi ne a wata kasuwa mai cike da cunkoson jama’a a unguwar al-Farwa da ke gundumar Sha’ub a safiyar ranar Litinin. Ana fargabar adadin wadanda suka mutu zai karu yayin da mutane da dama ke makale a karkashin baraguzan gine-gine da aka wargaza a harin. A gefe guda kuma, Amurka ta kai hare-hare a yankunan lardin Sa’ada, a arewa mai nisa na kasar, da tsakiyar Ma’rib, da yammacin Hudaydah. Dama kafin hakan a ranar Lahadi, Amurka ta kai wasu hare-hare ta sama a Yemen,...
An tabbatar da rasuwar mutum uku tare da asarar gonakin shinkafa da faɗinsu ya kai hekta dubu 10 a Jihar Neja a sakamakon mummunar ambaliyar ruwa. Wannan ibtila’i ya faru ne a Ƙaramar Hukumar Mikawa, sakamakon sakin ruwa daga Madatsar Ruwa ta Jebba. Shaidu sun bayyana cewa ambaliyar ta yi ɓarna sosai a gonakin yankin. Shugaban Ƙungiyar Raya Yankin Kede, Abdulraham Abdulƙadir Kede-Wuya, ya ce gonar shinkafarsa mai faɗin hekta uku na daga cikin waɗanda suka salwanta a ambaliyar. Gobara ta ƙone gidaje sama da 100 a sansanin ’yan gudun hijira a Borno An shiga ruɗani kan satar al’aurar maza a ƙasar Chadi Ya ce, “gonata mai faɗin hekta uku na daga cikin waɗanda ruwan ambaliyar ya shanye, Sannan akwai...
Wata gobara ta ƙone gidajen wuccin gadi sama da 100 ma ’yan gudun hijira a sansanin ’yan gudun hijira na hukumar ruwa da ke Ƙaramar Hukumar Monguno ta Jihar Borno. Shaidu sun ce ba a samu asarar rai ba a gobarar da ta tashi da misalin karfe 10.40 na safe na ranar Alhamis da ta gabata, kuma cikin sauri ta bazu a unguwar, inda ta ƙona kayan abinci, da sauran kadarori masu ɗimbin yawa. Majiyar da ke sansanin ta bayyana cewar an tura jami’an agaji zuwa wurin domin kula da jama’a da kuma hana sace-sacen kayayyakin jama’a da suka rage, yayin da jami’an kashe gobara tare da mazauna sansanin suka yi bakin ƙoƙarinsu wajen kashe wutar. Tashin gobarar dai ba...
Majiyar labarai daga kasar Lebanon sun bada sanarwa kama wasu mutane wadanda suke shirin Cilla Makamai kan HKI. Jaridar Arab News ta yanar gizo ta kuma kasar Saudiya ta bayyana cewa a makon da ya gabata ma an kama wasu mutane wadanda ake zargi da cilla makaman roka kan HKI daga kudancin kasar ta Lebanon. Amma dangane da kwance damarar kungiyar Hizbullah kuma shugaban kasar Lebanon Jesept Aun ya ce wannan al-amarin ba abu ne mai sauki ba, sai dai a jira lokacinda ya dace na yin hakan. Aun ya kara da cewa duk wani kokari na kwance damarar kungiyar hizbullah kawo karshen zaman lafiya a kasar Lebanon ne. Kafin haka dai shugaban kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kasim a jawabin...
Tsohon mashawarcin Shugaba Bola Tinubu kan harkokin siyasa, Dokta Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana cewa babu wani ɗan siyasa da zai iya lashe kujerar shugabancin Nijeriya a Zaɓen 2027 ba tare da goyon bayan yankin Arewacin ƙasar ba. Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana hakan a wata hira ta bidiyo tare da tsohon Babban Sakataren Hukumar Kula da Inshorar Lafiya (NHIS), Farfesa Usman Yusuf. NDLEA ta kama hodar iblis da aka ɓoye cikin littafai ana shirin kaiwa Saudiyya Zaɓen 2027: Me ya sa jam’iyyu ke neman tabarrakin Buhari? Ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba yankin Arewacin Nijeriya zai fuskanci alƙiblarsa ta siyasa. “Nan da watanni shida mutanen Arewacin Nijeriya za su fayyace inda suka dosa, saboda haka zaɓi ya rage wa...
Kungiyar Hamas ta yi watsi da kudirin baya bayan nan na Isra’ila na kwance damarar kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa domin tsagaita bude wuta a Gaza, tana mai kiran hakan a matsayin wani yunkuri na gurgunta ‘yancin Falasdinu. Tattaunawar da ake ci gaba da yi tsakanin Isra’ila da Hamas ta tsaya cik, inda Isra’ila ta matsa kaimi kan batun kwance damara, yayin da Hamas ta dage kan hakan a matsayin wani muhimmin hakki na kare Falasdinu. Mahmoud Mardawi na kungiyar Hamas ya jaddada cewa kwance damarar kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa abu ne da ba zai yiwu ba. Ya bayyana kudurin na Isra’ila a matsayin wani dabarun yahudawan sahyoniya da Amurka na kwacewa Falasdinawa karfin kare kansu da kuma tinkarar mamaya.
A shekarar 2017, aka dauki matakin fadada kasashen da za su halarci gasar 2026 zuwa 48 bayan duka mambobin Fita sun kada kuri’ar amincewa da matakin, sannan a ranar 15 ga watan Mayu mai zuwa ne za a gudanar da taron FIFA na 75, kuma a nan ne za a tattauna bukatar ta Conmebol. Idan har aka amince da bukatar, gasar ta 2030 za ta kunshi karawa 128, daga karawa 64 da ake yi tsakanin 1998 zuwa 2022. Masu sukar matakin dai na cewa fadada gasar zai rage darajar tsarin da ake bi wajen tantance cancantar shiga gasar, yayin da kungiyar kare muhalli ta FFF ta ce shawarar buga gasar a nahiyoyi uku barazana ce ga muhalli. Tuni dai a...
Wannan nasarar ta nona irin namijin kokarinda Bankin ya yi na kara habaka samar wa da kansa kudaden shiga duk da matsin tattalin arzikin da kasar nan ke fuskanta. Bugu da kari, kadarorin Bankin sun karu zuwa jimmlar kaso 47 daga Naira tiriliyan 20 a shekarar 2023 zuwa Naira tiriliyan 30, a shekarar 2024. Kazalika, abokan huddar Bankin sun karu zuwa kashi 45, wanda kudaden da suka ajiyarsu ya karu zuwa Naira tiriliyan 22 a shekarar 2024, sabanin yadda ya ke kan Naira tiriliyan 15, a shekarar baya. Duk da samun hauhawan farashin kaya a kasar, Bankin ya samu karin kudaden shigar Bankin, sun karu zuwa kashi 38.9, sabanin kashi 36.1. Bankin na da yakinin samun ribar shiyar da ta...
Sakatare-janar na kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem ya yi Allah wadai da kalaman da kiraye kirayen da ake na “kwance damarar” kungiyar Hizbullah, yana mai kiransa da cewa wani yunkuri ne na raunata kasar Lebanon da kuma ci gaba da fadada manufofin Tel Aviv. Sheikh Naim Qassem ya bayyya hakan ne a wani jawani da ya gabatar da kai tsaye ta talabijin jiya Juma’a. Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Isra’ila ke ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma a karshen shekarar da ta gabata da nufin kawo karshen kazamin rikicin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 4,000 a kasar Labanon. Sheikh Qassem ya jaddada cewa ci gaba da kokarin da...
Wasu ’yan ta’adda da ake kyautata zaton ’yan Boko Haram ne sun kai hari a sabuwar unguwar Yamtake da ke Ƙaramar hukumar Gwoza a Jihar Borno, inda suka kashe sojoji biyu tare da wasu fararen hula da ba a bayyana adadinsu ba. Majiyoyin tsaro da na cikin gida sun tabbatar da harin, inda suka ce maharan sun mamaye unguwannin ne da misalin ƙarfe 11:15 na daren Alhamis. Gwamnatin Yobe ta sayo hatsi don tunkarar kakar bana Matan da suka tsira daga Boko Haram na buƙatar tallafin musamman Ɗaya daga cikin majiyar sojojin ta ce, kafin a aike da wata tawagar sojoji daga Gwoza, maharan sun riga sun afkawa jama’a da sansanin sojan Yamtake. “Muna jiran tawagar masu ƙarfafa musu su...
Gwamnatin Jihar Yobe ƙarƙashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni ta sayo ton 2,000 na hatsi iri-iri domin ƙarfafa samar da abinci da kuma tabbatar da shirin tunkarar kakar bana a matsayin gudun ko ta kwana. A cikin wata sanarwa da Yusuf Ali, mai bada shawara ta musamman kan harkokin dabarun sadarwa na zamani (SSA) ga gwamna Buni ya ce, Kwamishinan ma’aikatar noma da albarkatun ƙasa, Ali Mustapha Goniri, ya kai ziyarar duba irin hatsin a shagunan bunƙasa noma na jiha da ke kan titin Gujba da ke Damaturu. ’Yan Najeriya miliyan 150 sun samu ingantacciyar wutar lantarki – Minista ISWAP sun ruguza gadar Mandafuma a Borno Da yake zantawa da manema labarai a yayin ziyarar, Ali Mustapha ya bayyana kyakkyawan fata...
Jami’an hukumar shiyyar Kaduna na hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, sun kama wasu mutane arba’in da ake zargi da damfarar yanar gizo a kananan hukumomin Bida da Minna na jihar Neja. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban hukumar EFCC, Dele Oyewale ya raba wa manema labarai a Minna babban birnin jihar Neja. A cewarsa an kama su ne biyo bayan sahihan bayanan sirri da ke alakanta su da ayyukan damfara na intanet. Kayayyakin da aka kwato daga hannunsu sun hada da motoci uku, na’urorin samar da wutar lantarki guda takwas, na’urar sanyaya daki samfurin Hisense guda daya, na’urorin sarrafa wutar lantarki guda biyu, babura 10, kwamfutocin...
Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya NBS ta ce hauhawar farashi ya ƙaru a ƙasar zuwa kashi 24.23 cikin 100 a watan Maris. Alƙaluman da hukumar ta fitar sun nuna an samu ƙarin kashi 1.05 daga kashi 23.18 cikin ɗari da aka samu a watan Fabrairu. EFCC ta gaza tabbatar da tuhumar Murja kan zargin wulaƙanta takardun kuɗi ’Yan Najeriya sun koka kan rashin ingancin shinkafar Gwamantin Tarayya Wannan ne karon farko da aka samu ƙarin hauhawar farashin tun bayan da hukumar ta NBS ta soma fitar da rahoton bisa sabon tsarin tattara alƙaluma da ta fara amfani da shi a farkon shekarar nan. Sai dai bayan soma amfanin da sabon tsarin fitar da ƙididdigar a watan jiya, NBS ta ce da...
Kasashe da dama sun bi sahu a wannan karnin, inda Saudiyya ta zama ta baya-bayan nan, wajen ba mata ‘yancin kada kuri’a a kananan zabukan kasar a shekarar 2015. (Ba su yin zaben shugaban kasa a Saudiyya.) A cewar Majalisar Dinkin Duniya, wannan ya sa yanzu mata a kowace kasa suna da ‘yancin yin zabe. Sai dai Afghanistan a karkashin mulkin Taliban, ta mayar da hannun agogo baya wajen kwace wa mata hakkin zabe. “Matan Afghanistan sun samu damar kada kuri’a ne kimanin shekaru 100 da suka gabata, amma yanzu a karkashin mulkin Taliban, an cire a tsarin dimokuradiya,” in ji tsagin mata na Majalisar Dinkin Duniya, sashen da aka ware domin karfafa gwiwar mata. Zuwa tsakiyar karni na 19,...
Rahotanni daga Nijar na cewa dakarun tsaron ƙasar sun yi nasarar kashe ‘yan ta’adda biyu tare da kama ‘yan bindiga 12 a yankunan Dosso da Diffa na ƙasar. Kafar watsa labarai ta ActuNiger ta ruwaito cewa a Boumba da ke yankin Dosso ne dakarun tsaron ƙasar suka yi nasarar kashe ‘yan ta’adda biyu bayan dakarun da ke sintiri sun yi arangama da ‘yan ta’addan da suka je daga yankin Falmey. Kotu ta tsare ’yan TikTok 2 a Kano An rantsar da shugabannin ƙananan hukumomi 34 na Katsina Kazalika ranar Alhamis ne dakarun tsaron ƙasar suka yi nasarar kama ‘yan bindiga 12 a ƙauyen Jagada da ke yankin Diffa. TRT ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a lokacin da ‘yan...
Wata mata mai suna Jennifer Castro ta shigar da ƙarar kamfanin jiragen sama na GOL da wata fasinja a kotu bisa wani faifan bidiyo aka wallafa da yake nuna matar ta ki barin kujerarta da ke kusa da taga saboda wani yaro da yake kuka. Matar ’yar ƙasar Brazil da ta ƙi barin kujerar kusa da taga saboda wani yaro mai kuka ta shigar da ƙara a kotu. Tsohon kocin Super Eagles Christian Chukwu ya rasu An kashe Uba da ’ya’yansa biyu a ƙauyen Filato Jennifer Castro, mai shekara 29 na daukar matakin shari’a a kan kamfanin jiragin sama na GOl da kuma fasinjar da ta ɗauki bidiyonta a lokacin da lamarin ya faru. Lamarin wanda aka yi ta...
Newcastle ta lallasa Leicester da ci 3-0 a ranar Litinin a gasar Firimiya Lig ta Kasar Ingila, wasan wanda ya kasance na 8 a jere da Leicester City ta buga ba tareda jefa kwallo a raga ba, Newcastle da Eddie Howe ke jagoranta na fatan ganin sun samu gurbi a gasar Zakarun Turai na badi, tun da farko dai sun lashe gasar League Cup a watan da ya gabata. Yanzu haka su na matsayi na biyar a kan teburin Firimiya, inda suke da maki daya da Chelsea da ta ke matsayi na hudu, Leicester City kuma a nata bangaren ka iya komawa gasar ‘yan dagaji ta Championship idan aka doke su a wasansu na gaba a gasar. Yadda Tashar...
Gwamnatin tarayyar Najeriya tace tana fatan samun dalar Amurka billiyon $200 a ko wace shekara, a ko wace shekara daga ayyukan sararin samani. Jaridar Premiun times ta Najeriya ta nakalto ministan kirkire-kirkira da fasahar sararin samaniya yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa kamfanonin sadarwan da suke cikin kasar kamar Starlink da DSTV. Banda haka yace jiragen ruwa masu shigowa kasa ba zasu kaucewa biyan haraji ko kudin foto ba, saboda kayakin aiki na sararin samaniya wanda kasar take da su. Ministan yace shugaba Tinubu ya bada umurni a yi amfani da fasahar sararin samaniya wajen ayyukan gas da man fetur. Uche Nnaji ya ce gwamnati tana fatan samun karin dala biliyon 20 a wannan bangaren.
Mata a Jihar Jigawa sun yi kira da gwamnati da kungiyoyin agaji masu zaman kansu da su samar da magungunan samun tazarar haihuwa kyauta domin inganta tsarin iyali. Matan da suka tattauna da wakilinmu a cibiyoyin kula da lafiya na Kudai da Kachi dake Dutse, a yayin bikin ranar Lafiyar Uwa ta duniya, wato “Safe Motherhood” a turance, sun bayyana damuwarsu kan rashin samuwar kayayyakin bada tazarar haihuwa. Wata uwa mai yara uku, Malama Karimatu Sani, ta ce duk lokacin da ta je siyan maganin samar da tazarar haihuwa, ana bata wadanda lokacin aikinsu ya wuce, wanda hakan na iya haifar da illa ga lafiyar mata. “Sau da dama sai na jira asibiti ya samu sababbin kaya, ina addu’ar...
A wannan rana a filin jirgin saman Legas, Babafemi ya ce jami’an ‘yansanda sun kama wata ‘yar asalin kasar Ghana mai shekaru 20, mai suna Parker Darren Hazekia Osei, mai shekaru 20 da haihuwa, dauke da fakiti 36 na Loud—wani nau’in tabar wiwi mai karfin gaske, a cikin wata katuwar jakar tafiya mai nauyin kilogiram 19.40. Ya ce wanda ake zargin wanda ya bayyana kansa a matsayin dalibin Kimiyyar Kwamfuta a Jami’ar Gabashin Landan, ya taso ne daga birnin Bangkok na kasar Thailand ta hanyar jirgin Ethiopian Airlines, ya kuma amince ya dauko kayan a Bangkok domin kai wa Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
A cewarsa, wadannan kudaden sun hada da biyan kudaden samar da kariya da na inshore da kuma sauran kudaden da ake biyan kamfanonin na waje. Ya sanar da cewa, wadanan kudaden da ake biya, na shafar ci gaban tattalun arzikin kasar, inda ya yi nuni da cewa, duk Jirgin ruwa daya da ya yi dakon Danyen Mai ana biyan dala miliyan 130, inda kuma ake cazar kudin da suka kai akalla dala 445,000. Kazalika, Osagie ya bayyana cewa, ana jigilar Kwantaina kuma ana biyan dala miliyan $150, wanda kuma ake cazar dala 525,000, kan kowacce jigila daya. Kamfanin Maersk, daya daga cikin manyan kamfanoni a duniya da ke dakon kaya, ya kirkiro kowacce Kwantaina na biyan dala 450, wanda kuma...
Tun daga farkon bana zuwa yanzu, sau da dama kasar Sin ta mai da martani kan matakai na rashin adalci da kasar Amurka ta dauka, domin tana da karfin fuskantar da kalubaloli tare da kiyaye bunkasuwar tattalin arzikin kasar yadda ya kamata, sakamakon bunkasuwar manyan kasuwannin cikin kasa, da manufofin da gwamnatin kasar ta fidda wajen kare karfin tattalin arziki da cinikayya. Kwanan baya, manyan jami’an kasar Sin sun yi shawarwari da takwarorinsu na kungiyar tarayyar kasashen Turai (EU) da na kungiyar tarayyar kasashen dake kudu maso gabashin nahiyar Asiya (ASEAN), inda suka bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da kara bude kofa ga waje. Masanan kasa da kasa suna ganin cewa, kasar Sin ita ce kasa...
Masu shigar da kara sun bukaci kotun da ta hana wadannan jami’an gudanarwa gudanar da taro, ko kuma jagorantar babban taron jam’iyyar na kasa, bisa hujjar cewa an kore su daga jam’iyyar NNPP. Ko da yake, alkali mai shari’a Justice MA Hassan ya yanke hukuncin cewa kotun ba ta da hurumin sauraren karar, inda ya bayyana cewa rikicin cikin gida na jam’iyyar kotun ba ta da hurumin sauyaran karar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku ya kasance mai fafutukar tabbatar da hadin kan ‘yan adawa, yana mai jaddada muhimmancin hadin gwiwa wajen kayar da Tinubu a zaben 2027. A ranar 8 ga watan Maris ne ya bayyana kokarinsa na hada kan ‘yan adawa da kafa kawancen korar jam’iyyar APC. Bayan sauya shekar El-Rufa’i daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PSP a ranar 10 ga watan Maris, tattaunawar da aka yi tsakanin shugabannin ‘yan adawa ta samu gagarumar nasara. Atiku da sauran ‘yan adawa sun bayyana cewa taron na ranar 20 ga watan Maris ya nuna kaddamar da kawancen a hukumance. A baya dai an ruwaito a ranar 23 ga watan Maris cewa ana jinkirin tattaunawa kawance tsakanin shugabannin siyasa saboda burin...
Wannan ya hada da darajar kayayyakin da ake shigowa da su daga waje da kuma fitar da su, wanda ke nuni da irin dimbin alakar kasuwanci da ke tsakanin kasashen biyu. Kayayyakin da Nijeriya ke fitarwa a cikin gida da na waje da jirgin ruwa ya kai dala miliyan 473.6 a watan Fabrairun 2025, kadan ya ragu daga dala miliyan 501 a watan Fabrairun 2024, wanda ke nuna raguwar kashi 5.5 cikin dari. A shekarar zuwa yau, fitar da kayayyaki na FAS ya ragu daga dala miliyan 792.8 a shekarar 2024 zuwa dala miliyan 687.4 a shekarar 2025, wanda ya nuna raguwar kashi 13.3 cikin dari. Amurka ta samu gibin ciniki a kan Nijeriya ne kawai a watan Janairun 2025,...
A ƙalla shaguna 12 sun ƙone ƙurmus sakamakon gobarar da ta tashi da daddare a Agodi Gate, birnin Ibadan, babban birnin Jihar Oyo. Lamarin ya faru ne a daren Alhamis a ginin Block A na kasuwar Siminti ta Mayegun, Araromi, kamar yadda hukumar kashe gobara ta Jihar Oyo ta tabbatar. Shugaban hukumar, Akinyemi Akinyinka, ya bayyana cewa jami’ansu sun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 11:02 na dare, inda nan take suka tura tawaga ƙarƙashin jagorancin Cfs Jimoh. Bayan isarsu, sun tarar da shaguna da dama na ci da wuta, amma cikin gaggawa suka dakile yaɗuwar gobarar zuwa sauran shagunan da ke kusa. Gobara Ta Kashe Yaro A Sansanin ‘Yan Gudun Hijira A Maiduguri Gobara Ta Ƙone Sabon Ginin...
An gurfanar da wani mutum a gaban Kotun Majistare ta 17 a Kano bisa zargin shi da karɓar kuɗi a hannun wasu fursunoni da alƙawarin cewa zai fitar da su daga gidan yari. Ana zargin wanda ake tuhumar, Kabiru Ahmed, da karɓar jimillar kuɗi naira dubu dari shida da goma daga Abdul Mukhtar, Bilkisu Shehu da kuma Muhammad Yahaya da sunan zai yi musu aiki a sako su daga gidan yari. Lauyar masu gabatar da ƙara, Barista Sadiya Sabo, ta tuhumi mutumin da laifin damfara da kuma cin amanar da aka ba shi. Wanda ake tuhuma ya amsa laifin, amma ya bayyana cewa ba shi kaɗai ya aikata wannan haramtaccen aiki ba. ’Yan kasuwa da dama sun mutu bayan kifewar...
Hukumar Kula Wutar Lantarki ta Ƙasa (NERC) ta ci kamfanonin rarraba lantarki tarar naira miliyan 628 kan laifin karɓar kuɗin wuta fiye da kima daga hannun kwastomomi marasa mita. Hukumar ta kuma ba wa kamfanonin rarraba lantarkin da hakan ta shafa wa’adin ranar 15 ga watan Mayu, 2025, sun tabbatar sun biya kwastomomin da suka canza fiye da kima, ta hanyar ba su wuta daidai da abin da suka ƙware su. NERC ta bayyana cewa ɗaukar wannan mataki ya zama dole saboda kamfanonin sun yi kunnen ƙashi bayan umarnin da ta ba su, wanda ya ƙayyade kuɗin da su caji kwastomomi da ba su da mita. Ta ce waɗanda aka ci tarar sun haɗa da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na...
Kasar Sudan ta kai kukan HDL a gaban kotun MDD cewa ta keta dokar hana kisan kiyashi ta hanyar taimakawa dakarun kai daukin gaggawa. A jiya Alhamis kasar ta Sudan din ta bukaci kotun ta kasa da kasa dake karkashin MDD da ta ta fitar da hukunci na gaggawa na bayar da umarni ga HDL da ta kawo karshen kisan kiyashin da aka yi wa kabilar Masalit da sauran al’ummu a cikin tsawon shekaru biyu na yakin basasar kasar. Ministan shari’a na kasar Sudan Muawia Usman ya bayyana cewa: Kisan kiyashin da dakarun kai daukin gaggawa su ka yi wa al’ummar Masalit da su ka kunshi larabawan yankin Darfur, ya faru ne ta hanyar taimakon kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.” Bayan...
Jakadan Sudan a Tehran, Abdul Aziz Hassan Saleh, ya tabbatar da cewa, za a gudanar da zaman farko na kotun kasa da kasa da ke birnin Hague a yau Alhamis, domin duba korafin da Sudan ta shigar kan kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, kan rawar da take takawa a yakin da ake ci gaba da yi a kasar, da kuma goyon bayan da take baiwa mayakan sa kai na Rapid Support Forces, tana mai kallonta a matsayin wani bangare na haddasa rikicin da ke faruwa a Sudan. A wani taron manema labarai da ya gudanar a wannan Laraba 9 ga watan Afrilu a ofishin jakadancin Sudan da ke Tehran, jakadan Sudan ya yi tsokaci kan laifukan da dakarun RSF suka aikata...
Gwamnatin Najeriya ta nuna damuwarta kan yadda masu safarar mutane ke ƙara amfani da kafafen sadarwa na zamani wajen yaudarar mutane da kuma yi musu cin zarafi, inda ta bayyana hakan a matsayin barazana wadda ba ta da iyaka kuma mai saurin yaɗuwa wadda ke buƙatar ɗaukar mataki cikin gaggawa. Da yake jawabi a taron masu ruwa da tsaki na ƙasa karo na 27 kan safarar mutane da aka gudanar a Abuja a ranar Laraba, Babbar Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi SAN, ya ce dole ne Najeriya ta ɗauki mataki ta hanyar zamani daidai yadda matsalar take saurin faɗaɗa. Ministan shari’an ya ce, “Safarar mutane ta koma ta intanet. Dole ne mu gaggauta ɗaukar mataki ko kuma...
Adadin wadanda suka yi shahada a zirin Gaza ya karu zuwa 58 a cikin ‘yan sa’o’i da suka gabata, yayin da wasu 213 suka jikkata sakamakon kazamin harin bam da Isra’ila ta kai a yankin. Jiragen yakin Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun kai hari kan fararen hula da gidajensu, a ci gaba da luguden wutar da suke yia kan fararen hula a yankuna da dama na Gaza. Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar da samun sabbin adadin wadanda suka yi shahada sakamakon hare-haren wuce gona da iri da Isra’ila ke kai wa zirin Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoban 2023, inda adadin shahidai ya kai 50,810 yayin da adadin wadanda suka jikkata ya kai 115,688. Adadin wadanda suka raa...
Kasashen Mali, Nijar, da Burkina Faso sun janye jakadunsu daga kasa Algeria bayan takaddamar da ta barke tsakaninta da Mali. Kasashen uku da ke karkashin mulkin soja sun sanar da daukar wannan matakin hadin gwiwa ne bayan Mali ta zargi sojojin Algeria da harbo wani jirginta mara matuki a sararin samaniyarta a karshen watan Maris. A ranar 1 ga Afrilu, Algeria ta sanar cewa ta harbo wani jirgin sama mara matuki mai dauke da makamai a sararin samaniyarta, amma ba ta yi karin bayanin ba. A cikin wata sanarwa, Ma’aikatar Harkokin Wajen Mali ta ce hukumomi sun tabbatar da “cikakken yakini” cewa an harbo jirgin ne a cikin “A matsayin harin makiya da aka shirya daga gwamnatin Algeria.” Gobara ta...
Wata gobara da ta ɓarke ta cinye garejin gyaran motocin kamfanin sufurin Borno Express na Gwamnatin Jihar Borno, inda ta lalata motocin bas sama da 10 masu daukar mutane 18 kowacce. Shaidu sun ce gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 12 na rana a ranar Litinin, bayan wani fashewa mai ƙarfi a harabar garejin. Ko da yake babu wanda ya rasa ransa a wannan lamarin, wani ma’aikacin hukumar kashe gobara ya samu raunuka yayin da yake kokarin kashe gobarar. Wani ganau ya ce, “Gobarar ta tashi ne sakamakon fashewar tukunyar gas — inda wani kara mai ban tsoro ya sa ma’aikata da matafiya a yankin suka yi ta gujegujen domin tsira.” Gobara ta laƙume ƙauyuka a Borno Mahara sun...
A wani mataki na mayar da martani da nuna fishi, kasar Aljeriya ta yi wa jakadunta a kasashen Mali, da Nijar kiranye, tare da jinkirta aikewa da jakadanta a Burkina faso, bayan da kasashen guda uku na kawacen sahel suka dau irin wannan matakin domin goyan bayan Mali, bisa takadamar dake tsakaninta da Aljeriya biyo bayan kakkabo jirginta marar matuki. Haka zalika ma’aikatar tsaron kasar Aljeriya ta sanar da rufe sararin samaniyarta ga dukkan jiragen da ke zuwa kasar Mali”, ba tare da bayar da wani karin bayani ba, wanda ke nuni da cewa jiragen farar hula na kasuwanci da kamfanonin jiragen sama na kasa da kasa su ma abin ya shafe su. Takaddama dai ta yi zafi tsakanin Aljeriya...
Ya kuma kara da cewa, binciken farko ya nuna cewa, da sa hannun ma’aikatan hukumar ake tafka wannan aika-aika. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jirgin da ke ɗauke da mutane sama da 200 daga Bali a ƙasar Indonesia zuwa Ostireliya, ya yi juyawar dole bayan wani fasinja ya yi yunƙurin buɗe ƙofarsa yayin da jirgin kamfanin Jetstar ke shawagi a tekun Indiya. “Mun samu wani jirgin sama ya koma Denpasar (filin jirgin sama na Bali) a daren Talata bayan wani ruɗaɗen fasinja ya yi yunƙurin buɗe ɗaya daga cikin kofofin jirgin kuma ya ci zarafin ma’aikatanmu,” a cewar wata sanarwa da kamfanin jirgin sama ya fitar game da lamarin a daren Litinin, 31 ga Maris. Ɓarawo ya haɗiye ɗan kunnen Naira biliyan ɗaya Tsohon Gwamnan Oyo Olunloyo ya riga mu gidan gaskiya Hukumomin yankin Bali ne suka fitar da fasinjan daga cikin jirgin. A...
Direba da kwandastan motar bas sun tsere domin tsira da rayukansu, inda suka bar fasinjoji a ciki yayin da wata motar bas ta BRT ta kama wuta a Maryland da ke Jihar Legas da safiyar ranar Asabar. Majiyar Channels TV da ke wajen da lamarin ya faru, ta ce motar ta taso ne daga yankin Ikorodu tana kan hanyar zuwa CMS a lokacin da lamarin ya faru. Rashin tsaro a Filato ya wuce rikicin manoma da makiyaya – Muftwang An ceto fasinjoji 14 a hannun ’yan bindiga, 3 sun rasu a Benuwe Ya zuwa lokacin da aka gabatar da wannan rahoton, masu bayar da agajin gaggawa da suka haɗa da jami’an ’yan sandan Nijeriya, da hukumar kula da zirga-zirgar ababen...
An ceto yara takwas da aka yi safarar su daga Jihar Taraba ta hanyar haɗin gwiwar ma’aikatar mata da ci gaban ƙananan yara ta Jihar Taraba da Hukumar Hana Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP). Kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban yara ta jihar Taraba, Misis Mary Sinjen ta ce yaran da aka ceto sun fito ne daga ƙauyen Minda da ke Ƙaramar hukumar Lau a Jihar Taraba. Adadin waɗanda suka mutu a harin Filato ya kai 52 Boko Haram: An kashe ɗan sanda a sabon hari a Borno A yayin da take zantawa da manema labarai a Jalingo, ranar Juma’a ta ce an yaudari yaran daga unguwar su aka yi safarar su zuwa jihohin Kudu maso Gabas. Ta ce, sun...
Gwamna Umar Namadi ya amince da naɗin Dr. Jummai Ali Kazaure a matsayin sabuwar shugabar Kwalejin Ilimi, Shari’a da Nazarin Addinin Musulunci (JSCILS) da ke Ringim. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya fitar. A cewarsa, kafin wannan naɗi, Dr. Jummai ta kasance malama a Kwalejin Ilimi ta Jihar Jigawa da ke Gumel. Tana da digiri na uku (Ph.D.) a fannin Gudanarwa da Tsare-tsare, tare da gogewa a harkar koyarwa daga matakin firamare har zuwa manyan makarantu. “Dr. Jummai ta rike mukamai da suka gada da Darakta a Makarantar Sakandaren gwamnati ta ‘yan mata da ke Kazaure da kuma Darakta a Makarantar Sakandare ta larabci da ke Babura. Mace ce...
Gwamnatin Nijar ta saki kusan mutane 50 da suka hada da ministocin da aka tsare tun bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum a watan Yulin 2023. Baya ga tsaffin ministocin da akwai wasu sojoji da ake zarginsu da yunkurin juyin mulki a shekarar 2010 da suma aka sake su. “An sako wadannan mutane ne bisa ga shawarwarin da babban taro na kasar ya bayar,” kamar yadda sakataren gwamnatin kasar ya karanta a gidan talabijin din kasar a cikin daren jiya. Cikin tsaffin ministocin da aka saki har da tsohon ministan man fetur Mahamane Sani Issoufou, dan tsohon shugaban kasar Mahamadou Issoufou, da kuma tsohon ministan tsaro Kalla Moutari, da tsohon ministan kudi Ahmat Jidoud, da kuma tsohon...
Jamhuriyar Nijar ta ba da sanarwar ficewa daga Rundunar haɗin Kan Sojojin Kasashe Tafkin Chadi (MNJTF) da ke yaƙi da ta’addanci a yankin tafkin Chad. Sanarwar da aka fitar ta gidan talabijin na gwamnati kuma Reuters ta ruwaito, ta zo ne a lokacin da Nijar ke mai da hankali kan tsaron man fetur a cikin ƙasar, sakamakon tashin hankali na cikin gida. Rundunar MNJTF, wadda ta ƙunshi Sojoji daga Najeriya, da Chadi, da Kamaru, da Nijar (a baya), an kafa ta ne a shekarar 1994 don magance barazanar tsaro a yankin. An sake farfaɗo da rundunar ne a shekarar 2014 domin yaki da Boko Haram, kuma ta taka muhimmiyar rawa a yaƙi da ta’addanci. Ficewar Nijar, wadda ta kasance muhimmiyar...
Nijar ta fice daga rundunar tsaro ta haɗin gwiwa da ke yaƙi da masu iƙirarin jihadi a Tafkin Chadi da ke yammacin Afirka yayin da take ƙoƙarin inganta tsaro kan albarkatun mai a cikin gida. A shekarar 2015 ce Nijeriya da Chadi da Kamaru da Nijar suka sake farfaɗo da rundunar haɗin gwiwa ta Multinational Joint Task Force (MNJTF), wacce aka ƙirƙira a shekarar 1994 don yaƙi da ƙungiyoyin jihadi a kewayen Tafkin Chadi. NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Komawa Cin Abinci Yadda Ya Kamata Bayan Watan Ramadana Azumin Sitta Shawwal a Musulunci Sai dai har yanzu ana ci gaba samun rarrabuwar kai da matsalar rashin daidaito na hana rundunar samun nasara sosai, lamarin da ya sa ƙungiyoyin ‘yan bindiga a...
A shekarar 1468 wanda yake mulkin Sonni Ali Shugaban Songhai ya ci wurin da yaki.Shi ba wanda yake ya saki jikinsa bane musamman ma musulmai wadanda suke da ilimin musulunci,amma wanda ya gaje shi Askia Muhammad na daya (1) wanda ya yi mulkin kasar daga shekarar( zuwa 1493–1528)ya yi amfani ne da wadanda suka yi karatu a matsayin wadanda yake tuntuva dangane da abinda ya shafi shari’a da al’amura na yau da kullum. Bayan da kasar Morocco ta mamaye ta a shekarar 1591, daga nan sai Birnin ya fara komawa baya.Aka bada umarni na kama Malamanta a shekarar 1593 saboda ana yi masu kallon basu goyon bayan abinda aka yi; an kashe wasu daga cikinsu lokacin da aka yi wani...
Akwai yiwuwar Barcelona za ta yi asarar maki saboda saɓa wata dokar Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA) a wasan gasar La Liga wanda ta doke Osasuna. Rahotanni na cewa ƙungiyar Osasuna za ta shigar da ƙorafi kan wasan da Barcelona ta doke ta da ci 3-0, saboda zargin saɓa dokar FIFA kan amfani da ɗan wasan da bai cancanta ba. Girgizar ƙasa ta kashe mutum 150 a Myanmar da Thailand An sake harbe wani ƙasurgumin ɗan bindiga a Zamfara A jiya Alhamis ce Barcelona ta karɓi baƙuncin Osasuna a wani kwantan wasa na gasar La Liga, inda to doke baƙin nata da ci 3-0. Wannan nasarar ta bai wa Barcelona damar yin zaman faɗi da tazarar maki 3 a...
A ranar Juma’a kasuwar ta rufe a cikin makon makon inda masu zuba hannun jarin, suka yi asarar Naira biliyan 166.43. Duk a cikin makon, saye da sayawar da aka yi ta shiyar ta kai ta jimlar Naira biliyan 3.281 da kuma wata shiyar ta Naira biliyan 63.517, duk a cikin hada-hada guda 60,782 da masu zuba hannun suka yi. Wannan ya nuna, savanin jimlar shiyar da aka yi hada-hadar ta kasuwar da ta kai Naira biliyan 1.818 sai kuma wata shiyar da ta kai ta Naira biliyan 47.226, wato wacce aka yi musayarta a makon da ya wuce wadda ta kai 64,222. Misali, manyan kamfanonin da suka yi hada-hada a kasuwar sune, kamfanin Inshora na Sovereign Trust Insurance da...
Aƙalla mutum 24 ne suka rasu a wata gobarar daji mai muni da ta auku a tarihin Koriya ta Kudu baya ga mummunar ɓarna da ta haddasa. Mukaddashin shugaban ƙasar ya sanar a ranar Laraba cewa wutar dajin ta rabu kashi daban-daban har fiye da goma tun ƙarshen mako, inda ta laƙume wasu yankunan kudu maso gabashin kasar. Ribas: Za mu ɗauki matakan da za su shafi tattalin arzikin Nijeriya — ’Yan ƙwadago Ban sani ba ko zan tsaya takara a 2027 — Atiku Har ila yau, ta kuma tilasta wa kusan mutum 27,000 ƙaurar gaggawa bayan ta datse tituna da kuma na’urorin sadarwa kamar yadda mazauna yankunan da ke neman tsira da rayukansu suka sanar. Wani jami’in Ma’aikatar Kare...
Wani rahoto da aka fitar yau Talata, yayin zaman taron shekara-shekara na shekarar 2025, na dandalin tattaunawa na Asiya na Boao, ya nuna yadda kasar Sin ke ci gaba da kasancewa cibiyar rarraba hajojin da masana’antu ke sarrafawa. Rahoton mai taken “Nazarin tattalin arzikin Asiya, da hadadden rahoton ci gaba na shekarar”, ya nuna yadda tun daga shekarar 2017, hada-hadar cinikayya ta duniya a fannin rarraba matsakaitan hajoji, ke kara dogaro kan kasar Sin sama da dogaronta ga yankin arewacin Amurka. Kazalika a shekarar 2023, dogaron sassan kasa da kasa kan kasar Sin ta fuskar samar da matsakaitan hajoji ya kai kaso 16 bisa dari, sama da na yankin arewacin Amurka mai kaso 15 bisa dari. Bugu da kari, rahoton...
Ba wannan tarihi na kanfar iko da ayarin farko na “yan majalisun wannan kasa ke da shi ne abin kallo ko la’akari ba, cikakkiyar dama da suke da ita a yau, tare da turbude hancin bukatun masu zabe, shi ne babban abin nadama da kaico!!!. Idan a wancan lokaci za a ce Turawa sun rike musu kugu ne, ta yadda za a ga ba su da wani tasiri ko katabus, wajen zuwa da kyawawan manufofi, don ciyar da jama’arsu gaba. Yanzu kuwa, za a iya yi wa wadannan “yan majalisun uzuri?. Shin, suna da cikakken ikon gudanar da aiyukan nasu ko babu?. Babu shakka, duk wani irin iko da ake da bukata da tsarin mulki zai ba da, ya jima...
“SDP jam’iyya ce mai zaman kanta, kuma za mu ci gaba da bin tsarukanmu da dokokinmu wajen zaɓen ‘yan takara,” in ji shi. “Za Mu Fi Mayar da Hankali Kan Ci Gaban Jama’a” Shugaban jam’iyyar ya bayyana damuwa kan halin da ‘yan Nijeriya ke ciki, musamman matsalar tsadar rayuwa da rashin tsaro. Ya ce SDP ba za ta zama mafakar wasu ‘yan siyasa masu neman mulki ba tare da wani ingantaccen shiri ba. “Dole mu duba halin da ƙasa ke ciki. Tsadar rayuwa na ci gaba da ƙaruwa, mutane na fama da wahala, amma ana cewa tattalin arziki yana inganta. Dole ne a fuskanci gaskiya, a yi aiki don ci gaban jama’a, ba kawai neman mulki ba,” in ji Gabam....
Jami’iyyar adawa ta “Turkish National Party” ta bayyana cewa dan takararta a zaben shugaban kasa na 2028 shi ne magajin garin Istanbul Akram Imam Ugulu wanda a halin yanzu yake a gidan kurkuku. Imam Uglu dan shekara 53 shi ne muhimmin dan takarar shugaban kasa a tsakanin ‘yan hamayya da ake hasashen cewa zai iya bugawa da shugaba Rajab Tayyib Urdugan a zabe mai zuwa. ‘Yan jam’iyyar ta adawa sun kada kuri’ar tsayar da Imam Ugulu a matsayin dan takararsu a zabe mai zuwa, inda ya sami kuri’u miliyan 1.6 a tsakanin miliyan 1.7. Shugaban jam’iyyar ta “National Party” Uzgur Uzil wanda ya sanar da hakan, ya kuma bayyana cewa an yi zabe na gwaji da miliyoyin mutane su ka...
Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya naɗa Sarkin Kauru, Mai Martaba Alhaji Ya’u Shehu Usman, a matsayin Amirul Hajj kuma jagoran tawagar jami’an jihar don aikin Hajjin 2025. A cikin wata sanarwa, Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamna, Ibraheem Musa, ya bayyana cewa naɗin wannan basarake mai daraja ya biyo bayan sadaukarwarsa, da gaskiya, da jagorancinsa, da nagarta a harkokin mulki. A matsayinsa na Amirul Hajj, Sarkin zai yi aiki kafada da kafada da Kwamitin Hajj na Musamman na Jihar Kaduna tare da haɗin gwiwa da hukumomin Jiha, Tarayya, da na ƙasashen duniya, domin tabbatar da aikin Hajji cikin nasara ga maniyyatan Jihar Kaduna. Gwamnan ya kuma yi addu’a ga Allah da ya ma Sarkin jagora da kariya...