Kungiyar Ansarullahi Ta Yemen Ta Ce: Sanarwar Trump Kan Batun Yemen Gazawa Ce Ga Netanyahu
Published: 7th, May 2025 GMT
Kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen ta mabiya Al-Houthi ta sanar da cewa: Sanarwar da shugaban Amurka ta fitar kan Yemen gazawa ce ga Netanyahu
Kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen ta sanar a jiya Talata cewa: Sanarwar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi dangane da kasar Yemen gazawa ce ga Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu.
Mohammed Ali al-Houthi mamba a majalisar koli ta siyasa ta kungiyar Ansarullahi ya bayyana cewa: Sanarwar Trump gazawa ce ga Netanyahu, kuma dole ne fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi murabus daga kan mukaminsa.
Ya kara da cewa: “Za su fara tantance sanarwar da Trump ya bayar na dakatar da hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yemen,” bisa la’akari da cewa “Sanarwar Trump wata nasara ce da ta raba goyon bayan da Amurka ke baiwa gwamnatin yahudawan sahayoniyya ‘yar mamaya.”
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Yemen
এছাড়াও পড়ুন:
Ansarullah: Yarjejeniya da Amurka ba za ta dakatar da hare-haren da Yemen ke kaiwa Isra’ila ba
Kungiyar gwagwarmaya ta Ansarullah ta bayyana cewa yarjejeniyar tsagaiat wutar da ta cimma da Amurka, ba ta sauya matsayin kasar ba na kai wa Isra’ila hari.
Kakakin kungiyar Ansarullah Mohammed Abdul-Salam ya jaddada cewa Dakarun Yeman za su ci gaba da kai hare-hare kan Isra’ila domin goyan bayan Falasdinawa a zirin Gaza.
Yarjejeniyar da Amurka ba ta da alaka da matsayinmu na goyan bayan Gaza, inji Abdul-Salam.
A jiya ne masarautar Oman ta sanar cewa Amurka da kungiyar Ansarullah da aka fi sani da ta ‘yan Houtshis a Yeman suka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Oman ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa: Bayan tattaunawa da tuntubar juna da aka yi a baya-bayan nan da kuma tuntubar juna tsakanin masarautar Oman ta Amurka da hukumomin da abin ya shafa a birnin Sana’a na jamhuriyar Yeman, an samu cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu.
Sanarwar ta kara da cewa: A nan gaba, ko wanne bangare ba zai kai hari kan daya ba, ciki har da jiragen ruwan Amurka a tekun Bahar Rum da Bab al-Mandab, domin tabbatar da ‘yancin zirga-zirgar jiragen ruwa da kuma tafiyar da harkokin kasuwancin kasa da kasa cikin sauki.