HausaTv:
2025-05-07@19:56:05 GMT

Kasar Sudan Ta Yanke Huldar Jakadancinta Da Kasar Hadaddiyar Daular Larabawa

Published: 7th, May 2025 GMT

Kasar Sudan ta yanke huldar jakadancinta da kasar Hadaddiyar Daulart Larabawa tana mai ayyana UAE a matsayin ‘kasa mai cin zali’

Kamfanin dillancin labaran Sudan (SUNA) ya watsa rahoton cewa: Kwamitin tsaro da kula da matakan tsaron kasar Sudan ya sanar a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Talata cewa: Sudan ta yanke huldar diflomasiyya da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma kiran hanzarta dawowar ma’aikatan ofishin jakadancin Sudan gida daga Abu Dhabi.

Kwamitin tsaro da kula da matakan tsaron Sudan ya bayyana cewa: Fiye da shekaru biyu, daukacin duniya take bibiyar laifuffukan wuce gona da iri kan kasar Sudan, da tabbatar da tsaron yankunanta, da tsaron ‘yan kasarta daga hadaddiyar daular Larabawa ta hanyar wakiliyarta na cikin gida, ‘yan ta’adda, masu tayar da kayar baya na kungiyar Rapid Support Forces ta dakarun kai daukin gaggawa, kuma masu goyon bayan siyasarsu.

Ya kara da cewa: “Lokacin da Hadaddiyar Daular Larabawa ta tabbatar da rushewar wakilayarta na cikin gida, wanda sojojin Sudan suka fatattake su, sai Hadaddiyar Daular Larabawar ta kara ba da goyon bayanta tare da bayar da karin karfinta wajen baiwa ‘yan tawayen makamai na zamani.”

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: Hadaddiyar Daular Larabawa kasar Sudan

এছাড়াও পড়ুন:

UEFA: An Kai Ruwa Rana Yayin Da Inter Ta Koro Barcelona Gida

 

Wannan nasara da Inter Milan ta samu ya sa ta kai wasan karshe na gasar Zakarun Turai a karo na biyu cikin shekaru 3, a shekarar 2023 Manchester City ta doke Inter Milan a wasan karshe na gasar, wannan rashin nasara da Barcelona ta yi ya bata mata burinta na lashe gasar a karon farko cikin shekaru 10.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sudan ta katse  hulda da Hadaddiyar Daular Larabawa bisa goyon bayan dakarun RSF
  • Nijar Ta Soke Yarjejeniyar Tattara Bayanai Da Rasha Da Turkiyya, Ta Fara Neman Sabbin Abokan Hulɗa
  • Sudan ta katse dangantakar diflomasiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa
  • UEFA: An Kai Ruwa Rana Yayin Da Inter Ta Koro Barcelona Gida
  • AU, ta yi tir da harin baya bayan nan a tashar ruwan Sudan
  • Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Batun Samun Hadin Kai Tsakanin Al’ummar Kasar
  •  Kotun Duniya Ta Wanke HDL Akan Zargin Kisan Kiyashi A Sudan
  • Yau Kotun ICJ ke yanke hukunci kan zargin da Khartoum ke wa UEA
  • Sojojin Sudan Da ‘Yan Tawayen Kasar Suna Ci Gaba Da Gwabza Fada A Wasu Saasan Kasar