JAMB ta saki sakamakon jarrabawar 2025
Published: 9th, May 2025 GMT
Hukumar JAMB mai shirya jarrabawar neman shiga makarantun gaba da sakandire a Nijeriya, ta sanar da sakin sakamakon jarrabawar da ɗalibai suka zana a bana.
Wata sanarwa da shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede ya fitar ranar Juma’a, ta ce an riƙe sakamakon ɗalibai 39,834 wanda a cikin wannan adadi tana bincike kan sakamakon ɗalibai 1,426.
A ranar Litinin ne JAMB ta fitar da alƙaluman sakamakon bana tana mai cewa yawancin ɗaliban da suka zauna jarabawar sun gaza samun maki 200 daga cikin maki 400.
JAMB ta ce ɗalibai miliyan 1.95 ne suka rubuta jarabawar daga cikin 2,030,862 da suka yi rajista, amma cikin wannan adadi, miliyan 1,534,654 ne wanda ya kai kaso 78 cikin 100 suka samu maki ƙasa da 200.
Alƙaluman sakamakon ya nuna cewa kashi 0.63 ne na ɗalibai ƙalilan da suka samu makin da ya haura 300, wanda a jimlace suka kai ɗalibai 12,414.
A matakin maki tsakanin 250 zuwa 299 kuma, an samu ɗalibai 73,441 yayin da ɗalibai 334,560 suka samu maki tsakanin 200 zuwa 249.
Rukunin da ya fi yawan ɗalibai shi ne na maki 160 zuwa 199, inda aka samu ɗalibai dubu 983,187 wato kashi sama da 50 cikin 100 ke nan.
Haka kuma, ɗalibai dubu 488,197 suka samu maki tsakanin 140 zuwa 159, sannan dubu 57,419 suka samu tsakanin 120 zuwa 139.
Ɗalibai 3,820 kuma sun samu maki tsakanin 100 zuwa 119, sannan ɗalibai dubu 2,031 sun gaza samun ko da maki 100.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Mutane A Fadin Duniya Sun Soki Ayyukan Neman ‘Yancin Kan Taiwan
Wasu jerin shirye-shiryen neman ‘yancin kan Taiwan da hukumomin yankin suka gudanar a baya bayan nan, sun sha suka sosai daga al’ummomin kasa da kasa. Wani nazari da kafar CGTN ta Sin ta gudanar ya nuna cewa adadin mai rinjaye na wadanda suka shiga nazarin, watau kimanin kaso 89.8 sun yi ammana cewa, manufar kasar Sin daya tak ta zama wata matsaya da kasashen duniya suka amince da ita, inda suka soki hukumomin yankin Taiwan bisa shirinsu na neman ‘yanci da takala.
Kafar CGTN ta wallafa nazarin ne cikin harsunan Ingilishi da Spaniyanci da Faransanci da Larabci da Rashanci, inda mutane 13,650 suka bayar da amsa cikin sa’o’i 24. (Fa’iza Mustapha)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA