Falasdinawa Sun Yi Shahada A Hare-Haren Da Sojojin Isra’il Suka Kai Gidan Cin Abinci Da Kasuwa A Gaza
Published: 8th, May 2025 GMT
Falasdinawa da dama ne suka yi shahada tare da jikkata sakamakon hare-haren bama-bamai da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wani gidan abinci da wata shahararriyar kasuwa a Gaza
Akalla Falasdinawa 20 ne aka kashe tare da raunata wasu da dama a jiya Laraba a wani sabon kisan kiyashi da jiragen saman yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai a wani gidan cin abinci na kasar Thailand da wata shahararriyar kasuwa a yammacin birnin Gaza.
Majiyoyi watsa labarai a Gaza sun rawaito cewa: Jiragen saman yakin mamayar Isra’ila sun kai wani hari kai tsaye kan gidan cin abinci na kasar Thailand da wata kasuwa mai farin jini da ke kusa, lamarin da ya yi sanadin shahadan mutane da dama da kuma jikkata wasu na daban yawancinsu fararen hula, a wani mummunan yanayi da ke nuni da yadda sojojin mamayar Isra’ila ke nuna rashin kula da rayukan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.
Wannan kisan kiyashi na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tabarbarewar zubar da jini, inda adadin wadanda suka mutu sakamakon hare-haren bama-baman da sojojin mamaya suka kai kan wasu makarantu uku a sansanin ‘yan gudun hijira na Bureij da kuma gabashin birnin Gaza a cikin ‘yan sa’o’in da suka gabata suka kai mutane 49, wadanda akasarinsu yara ne, mata da kuma tsofaffi.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kotun Indiya ta daure dan Najeriya shekara 10 kan safarar miyagun kwayoyi
Wata kotu ta musamman a Coimbatore da ke kasar Indiya, ta yanke wa wani dan Najeriya mai suna Samson Chukwunonso hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari kan laifin safarar miyagun kwayoyi.
Jaridar Times of India ta ruwaito cewa lamarin ya faro tun a watan Yuli na shekarar 2012, lokacin da jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta India (NCB), reshen Chennai, suka kama wasu fakiti guda uku a ofishin aika sakonni.
An kama ɗan sandan bogi a Kano Sanata Natasha ta koma Majalisar DattawaA cikin fakitin, an gano tabar wiwi mai nauyin kilo 1.195 da methaqualone giram 200, wanda darajarsa ta haura kimanin Dalar Amurka 240,000 a kasuwar duniya.
Bincike ya gano cewa fakitin na da alaka da Samson mai shekaru 40, wanda ake zargin yana zaune ba bisa ka’ida ba a kasar.
Jami’an na NCB sun kai samame gidansa inda suka gano ganja kilo 4, lamarin da ya kai ga cafke shi a watan Satumba 2012.
Bayan tambayarsa, an gano cewa Samson yana shirya aika miyagun kwayoyi zuwa kasashen waje ta hanyar kamfanonin aika sakonni, kuma yana da hannu a kungiyoyin safarar kwayoyi na duniya.
A ranar Asabar, 20 ga Satumba, an gurfanar da shi a gaban mai shari’a Rajalingam a kotun musamman da ke karkashin dokar hana safarar miyagun kwayoyi.
An same shi da laifin shirya aika kwayoyi zuwa kasashen waje a matsayin wani bangare na wata babbar kungiyar safarar kwayoyi ta duniya, kuma aka yanke masa hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari tare da tara ₹1 lakh.
Wannan hukunci na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da kama ’yan Najeriya da dama a kasashen Asiya kan laifukan da suka shafi safarar kwayoyi da aikata laifuka na kasa da kasa.
Ko a watan Agusta, sai da ’yan sanda a birnin Kozhikode na kasar ta Indiya suka kama ’yan Najeriya takwas kan zargin safarar kwayoyi.
Jaridar The Hindu ta ce ana zargin su da taka rawa a wata babbar kungiyar safarar kwayoyi da ke da rassa a fadin India.
A wani rahoto makamancin haka, wata kotu ta musamman a gundumar Bengaluru ta yanke wa wani dan Najeriya mai suna Kingsley Samuel hukuncin daurin shekaru 14 kan safarar kwayoyi, lamarin da ke kara nuna yadda ’yan Najeriya ke kara shiga harkar safarar kwayoyi a India.
Yawan kamawa da yanke hukunci ga ’yan Najeriya a kasashen waje na ci gaba da haifar da tambayoyi kan yadda ake kallon Najeriya a idon duniya.