2025-12-02@07:18:06 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3331

«wannan rahoto»:

    Jagoran ‘Yan Jam’iyyar Democrat na Majalisar Dattawa Chuck Schumer ya zargi Shugaban Amurka Donald Trump da shirya  yaƙi a ɓoye a kan kasar Venezuela, yana mai jaddada cewa ikon ayyana yaƙi ya rataya ne kawai a kan Majalisa, kuma dan majalisar ya bayyana cewa zai  gabatar da kuduri  don hana tura sojojin Amurka yaki a Venezuela. Schumer ya tabbatar da cewa Trump ba shi da ikon aika sojojin Amurka zuwa yaƙi ba tare da izinin Majalisa ba, yana mai bayyana  cewa wannan ikon an keɓe shi ne ga Majalisa kaɗai. A cikin wata sanarwa, Schumer ya zargi Trump da shirin yaƙi a ɓoye da Venezuela, yana mai gargadin cewa Majalisa za ta ɗauki mataki nan take don gabatar da kuduri...
    Daga Bello Wakili Ministan tsaron Najeriya, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya yi murabus daga mukaminsa nan take. Sanarwar da mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan yada labarai Bayo Onanuga ya fitar, ta ce wasikar da Badaru ya aika wa Shugaba Bola Tinubu mai dauke da kwanan watan 1 ga watan Disambar 2025, ta yi bayanin cewa, ya ajiye aikin ne saboda dalilan lafiya. Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu ya amince da murabus ɗin tare da gode wa Badaru Abubakar bisa irin gudummawar da ya bai wa ƙasa. Ana sa ran Shugaba Tinubu zai sanar da Majalisar Dattawa sunan wanda zai maye gurbin Badaru nan da ƙarshen wannan makon. Badaru Abubakar, mai shekara 63, ya taɓa zama gwamnan jihar Jigawa har...
    Daga Shamsuddeen Mannir Atiku  Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta karɓi daftarin kasafin kuɗin shekarar 2026 da ya zarce naira miliyan dubu dari tara da tamanin da biyar daga bangaren zartarwa jihar. Da yake gabatar da kasafin kudin a  zauren majalisar, Gwamna Malam Uba Sani ya bayyana kasafin a matsayin na sauye-sauye da ci-gaba wanda aka tsara domin bunkasa al’umma cikin tsarin da ya haɗa kowa da kowa. Ya ce gabatar da kasafin kuɗi muhimmin al’amari ne na dimokradiyya da ke bai wa gwamnati damar yin waiwaye, da tantance nasarorin da aka samu, da kuma fayyace hanyoyin ci gaba na shekara mai zuwa. Gwamnan ya bayyana cewa an ware sama da naira biliyan dari shida da casa’in da tara daidai...
    Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III, ya shawarci gwamnonin jihohin Arewa 19 su riƙa sauraron masu sukarsu tare da amfani da shawarwarin da ake ba su domin inganta salon mulkinsu. Ya bayar da wannan shawara ne a ranar Litinin, yayin taron haɗin gwiwar Gwamnonin Arewa da Sarakunan Gargajiya a Kaduna. ’Yan sanda sun gano zinaren N23m bayan shekara 13 da ɓacewarsu a Borno ’Yan bindiga sun sace fasto da matarsa  masu ibada a Kogi  Sarkin Musulmi, ya ce bai kamata shugabanni su yi biris da ƙorafin jama’a ba, musamman a wannan lokaci da Arewa ke fama da matsalolin rashin tsaro, talauci da matsin tattalin arziƙi. A cewarsa, babu wani gwamna ko shugaban ƙasa da zai nemi ƙuri’un jama’a sannan bayan ya...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta bayyana cewa Isra’ila na jinkirta aiwatar da mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma. Mai magana da yawun Hamas, ya bayyana cewa duk da cewa kungiyar ta na girmama yarjejeniyar tsagaita wuta sosai, gwamnatin mamayar Isra’ila na jinkirta aiwatar da mataki na biyu na yarjejeniyar, wanda ya tanadi dakatar da yaki da kuma cika alkawarinta. Hazem Qassem, ya fayyace cewa ci gaba da neman gawarwakin fursunoni, duk da wahalhalun da suke fuskanta, yana nuna cikakken jajircewar kungiyar ga yarjejeniyar. A wata hira da ya yi da Al Jazeera, ya kara da cewa Isra’ila na jinkirta aiwatar da mataki na biyu na yarjejeniyar, wanda ke kawo cikas ga aiwatar da ita. Kakakin...
    Daga Abdullahi Jalaluddeen  Gwamnatin Jihar Kano ta sha alwashin daukar mataki kan masu yin haya da  babura a fadin jihar. Mai bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Sufuri, Alhaji Danladi Idris Karfi, ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a Kano. Ya ce gwamnatin ta lura da yadda aka cigaba da yin haya da babura a cikin birnin Kano, lamarin da ya bayyana a matsayin barazana ga zaman lafiya a jihar. Danladi Karfi ya jaddada cewa dokar da ta haramta zirga-zirgar babura a matsayin sufuri na haya har yanzu tana nan daram, kuma za a aiwatar da ita sosai, inda ya gargadi masu karya doka da cewa za su fuskanci hukunci mai tsanani. Ya kara da cewa Kano...
    Jamhuriyar Nijar ta sanar da cewa za ta sanyar da sinadarin uranium dinta a kasuwar duniya ga wanda ta ga dama bayan da gwamnatin kasar ta mayar da hakar uranium ga kamfanin kasar a watan Yuni. Hakar ma’adinan uranium a Nijar na daga cikin batutuwan da suka fi daukar hankali tsakanin gwamnatin soji data kwace mulki a shekarar 2023, da kuma kamfanin Orano, mallakin kasar Faransa wacce ke da kashi 90% a arzikin urinum da ake fitawar shekarun baya. A wani rahoto da gidan talabijin din kasar ta Nijar ya watsa da yammacin ranar Lahadi, an ambato shugaban kasar, Janar Abdourahamane Tiani, na tabbatar da “hakkin kasar na baje hajarta da albarkatunta da kuma sayar da su ga duk wanda...
    ’Yan bindiga sun yi garkuwa da wani fasto da matarsa da mabiyansa a yayin da suke tsaka da ibada a coci da ke a  Jihar Kogi. Wani ganau da ke cikin cocin a lokacin da aka kai harin, Adegboyega Ogun, ya ce misalin ƙarfe 9.30 na safe ’yan bindigar suka kai harin suna bude wuta. “Mutane sun qarshe ta ko’ina, har da faston, wanda aka fi sani da Baba Orlando da matarsa da wasu masu ibada duk an yi garkuwa da su. Gaskiya harin ya yi muni, dukkanmu tserewa muka yi daga cocin.” Sace masu ibadar a ranar Lahadi a Cocin Cherubim and Seraphim ya auku ne bayan a kwanan nan Gwamna Usman Ododo, ya koka da cewa wasu  manyan...
    Ana ci gaba da ta ƙaddama kan Naira dubu ɗari bakwai da hamsin da Jami’ar Amurka ta Maryam Abacha  (MAAUN) da ke Jihar Kano ta wajabta wa ɗalibanta da suka kammala karatu biya a matsayin kuɗin bikin yaye ɗalibai. Jami’ar MAAUN ta sanya wa kowane ɗalibin da ya kammala karatu biyan Naira dubu ɗari bakwai da hamsin a matsayin kuɗin bikin yaye ɗalibai, kafin ta ba shi takardar shaidar kammala karatu da gabatar da bayanansa domin samun damar halartar aikin yi wa ƙasa hidima (NYSC). Sai dai kuma, Hukumar Karɓar Ƙorafi ta Jihar Kano (PCACC) ta umarci iyayen ɗaliban cewa su dakata da biyan kuɗin har sai ta kammala bincike kan ƙorafin da suka gabatar mata a kan lamarin. Sanarwar...
    Fira ministan HKI Benjamin natanyaho ya bukaci yafiyar shugaban kasa game da shari’a da aka dade ana yi kan zargin da ake masa na cin hancin da rashawa da mutane da sauran yan siyasa ke Allah wadarai da shi. Mazu zanga zanga sun mamaye gidan shugaban gwamnatin isra’ila Isaac Herzog inda suka yi tir da wanna mataki kuma suka bayyana shi a matsayin keta doka , suna ta daga ganyen Ayaba da aciki aka rubuta afuwa, wanda ke kwatanta wani shiri ne na jamhuriyar ayaba. Natanyaho mai shekaru 76 da haihuwa ya nemi afuwar shugaba Herzog a hukumance yana kokarin tsrewa daga gidan kaso idan aka yanke masa hukumci, shekaru da yawa ke nan natanyaho yake neman afuwa kamar yadda...
    Ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasdinu a Gaza ta sanar da cewa; An sami shahidai 3 da aka kai su asibitin a cikin sa’o’i 24 da su ka gabata.  Shi kuwa ofishin gwamnati dake Gaza ya sanar da cewa, daga tsagaita wutar yaki zuwa wannan lokacin, sau 591 Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta keta wutar yaki. Ofishin gwamnatin a yankin Gaza ya yi tir da hare-haren na Haramtacciyar Kasar Isra’ila, tare da yin kira ga kasashen duniya da su yi matsin lamba akan ‘yan mamaya masu keta dokokin kasa da kasa. Kididdiga ta bayyana cewa daga tsagaita wutar yaki a ranar 11 ga watan Oktoba 2025, adadin Falasdinawa da su ka yi shahada sun kai 356,yayin da wadanda su ka jikkata sun...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana halin da Falasdinu ke ciki da rauni mafi muni da aka aikata kan bil adama a doron kasa. A yayin bikin Ranar Falasdinu ta Duniya, Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta sake nanata goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke bai wa Falasdinawa, tana mai bayyana halin da suke ciki a matsayin “mafi munin rauni ga lamirin dan adam, Kamar yadda mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmail Baghai, ya bayyana. Kisan kare dangi, wanda ya fara a watan Oktoba na 2023, ya kashe Falasdinawa sama da 70,000, galibi mata da yara, kuma ya mayar da yankin kufai. Yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a farkon watan Oktoba tare da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa...
    Wata fitacciyar sinima a Faransa, Cinematheque Francaise, ta rufe ɗakunan kallonta na tsawon wata guda saboda yaɗuwar kuɗin cizo da aka gano a cikinta Cibiyar wadda ke gabashin birnin Paris ta ce rufe sinimar zai ba ta damar tabbatar da cewa masu kallo sun samu “aminci da kwanciyar hankali” bayan ƙorafe-ƙorafen da aka yi na cewa ƙwarin suna cizon mutane a lokacin kallon fina-finai. Tinubu ya sake aike wa majalisa ƙarin sunayen jakadu 32 Dalilin da na koma jam’iyyar ADC — Atiku A farkon watan Nuwamba, wasu daga cikin masu kallo sun shaida wa kafafen yada labarai cewa ƙwarin sun cije su bayan wani taro da aka yi da shahararriyar ’yar fim ɗin Hollywood, Sigourney Weaver. Wani daga cikinsu ya...
    Antonio Guterres babban sakataren majalisar dinkin duniya yayi kira da a kawo karshen mamayar yankunan falasdinawa da isra’ila ke yi da ya sabama doka, kuma yace babu ja da baya game da kudurin kafa kasashe biyu masu cin gashin kai Sakataren ya sake yin kira ne saboda ya nuna irin bukatar da ake da ita wajen kare hakkin falasdinawa da kuma matsa kaimi wajen warware rikicin ta hanyar siyasa, adaidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare a yankin Gaza da labanon da kuma kasar siriya, Wannan bayanin yana zuwa ne adaidai lokacin da zaman dar-dar da cin zarafin dan adam ke kara Kamari a yankin Gaza da kuma gabar yammacin kogin Jodan, inda hankalin duniya ya tashi...
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya sake aike wa Majalisar Dattawa ƙarin sunayen mutum 32 domin tantance su a matsayin jakadu. Sunayen sun haɗa da manyan mutane kamar tsohon shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Femi Fani-Kayode, da Reno Omokri. Muna buƙatar taimakon ƙasashen waje kan tsaro a Najeriya — Obasanjo Yadda aka horar da mata 100 sana’o’in dogaro da kai a Gombe An raba sunayen zuwa kashi biyu; na farko yana ɗauke da sunan mutum 15 waɗanda suke da gogewar aikin jakadanci da kuma waɗanda ba su gogewar aikin jakadanci mutim 17. Wasu daga cikin fitattu da suka shiga jerin sun haɗa da tsofaffin gwamnonin kamar Ifeanyi Ugwuanyi da Victor Okezie Ikpeazu, matan tsofaffin gwamnoni kamar Angela Adebayo da Florence Ajimobi, da...
    Gwamnatin kasar Iran ta bada sanarwan cewa ta kakkabo jiragen yakin HKI fiye da 196 a cikin yakin kwanaki 12 da aka dora mata a cikin watan Yunin da ya gabata. Daga ciki har da jiragen yaki samfurin Heron da Hermes -900 wadanda ke aiki da kayakin zamani. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto wata tashar talabijin ta cikin gida tana fadar haka a yau Asabar ta kuma kara da cewa Sashen garkuwar sararin samaniya na sojojin sama sun nuna hutunan lokacin da suke kakkabo jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa na HKI a lokacinda suka shigo sararin samaniyar kasar kafin su kai ga bararsu. Burgediya Janar Reza Khajeh mataimakin kwamandan garkuwar sararin samaniya na sojojin...
    Iran da wasu kasashen yankin Tekun Fasha sun yi Allah wadai da sabon kutse da farmakin da sojojin Isra’ila suka kai ta kasa da kuma ta sama a birnin Beit Jinn da ke kudancin Siriya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 13, ciki har da yara. A cikin wata sanarwa, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmail Baghai ya jaddada ‘yancin da kasashen Yammacin Asiya ke da shi na kare ‘yancinsu da kuma ‘yancin yankinsu daga harin Isra’ila. Ya kuma soki rashin daukar matakin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya kan take ‘yancin kai na kasashen yankin, musamman Siriya da Lebanon. A nata bangaren, Qatar ta yi gargadin cewa wannan “yana kara ta’azzara tashin hankali kuma yana kawo cikas ga...
    Ofishin Babban Kwamishinan Kare Hakkin Dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira da a gudanar da cikakken bincike bayan kisan gillar da sojojin Isra’ila suka yi wa Falasdinawa biyu a ranar Alhamis a Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, bayan sun daga hannayensu suka mika wuya. “Mun firgita da kisan gillar da ‘yan sandan kan iyaka na Isra’ila suka yi wa Falasdinawa biyu a Jenin, a Yammacin Kogin Jordan ” in ji mai magana da yawun Babban Kwamishinan Jeremy Laurence ga manema labarai. “Babban Kwamishinan (Volker Türk) ya yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa, cikin gaggawa, kuma ya bukaci a hukunta wadanda suka aikata wadannan laifukan,” Bidiyon da ke yawo a shafukan sada zumunta...
    Ma’aikatar Harkokin Wajen Lebanon ta sanar a ranar Juma’a cewa ta shigar da kara a kan Isra’ila gaban kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya dangane da gina katanga biyu na siminti a cikin yankin Lebanon da ke kudu da garin Yaroun (yankin Bint Jbeil). A cikin wata sanarwa da ta fitar, Ma’aikatar ta ce tawagar Jakadancin Lebanon ta Dindindin a Majalisar Dinkin Duniya da ke New York ne ta shigar da ƙarar gaban membobi 15 na kwamitiin Tsaron. Labanon ta yi kira ga kwamitin Tsaro da Sakatariyar Majalisar Dinkin Duniya da su ɗauki matakan gaggawa don hana Isra’ila keta hurumin Lebanon. A cewar ƙarar, keta hurumin ya kunshi gina katanga biyu da Isra’ila ta yi a kudu maso yamma da kudu...
    Pars Today – Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran ya jaddada cewa ayyukan Isra’ila, ciki har da kisan kai da ayyukan ta’addanci, ba komai ba ne illa wauta, domin “muna da dubban ƙwararrun nukiliya a Iran.” Ali Larijani, Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran, ya ce a ranar Juma’a a wata hira da HUM News a Islamabad cewa ra’ayin da Amurka da gwamnatin Isra’ila ke da shi game da lalata ƙarfin nukiliyar Iran abin dariya ne kuma wauta ne, domin masana’antar nukiliya kimiyya ce ta asali da Tehran ke bi da gaske. A cewar Pars Today, yana ambaton Fars News, Larijani ya ƙara da cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya yi iƙirarin cewa an dakatar da ayyukan nukiliyar Iran kuma...
    Rahotanni sun bayyana cewa kasashen larabawa na tekun fasha da kuma kasar Iran sun yi tir da hare-hare  ta kasa da sojojin isra’ila suka kai a wasu yankuna dake kudancin kasar Siriya kamar su bait jinn da ya kai ga mutuwar mutane 13 ciki har da yara kanana. A cikin bayani da ya fitar a jiya jumaa kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Esmail Baghai ya jadda game da hakkin kasashe a yammacin asiya na kare martabar su da yankunansu game da wuce gona da irin Isra’ila. Har ila yau yayi suka game da kasa tabuka komai da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya kan hare haren da isra’ila ke kai wa kan wasu kasashe kamar labanon da siriya wanda...
    Rahotanni sun bayyana cewa hukumar kwallon kafa ta kasar iran ta sanar cewa  za ta kauracewa taron da za’a yi  a makon gobe a birnin Washington bayan da kasar Amurka ta ki yarda ta bada shedar izinin shiga kasar ga wasu daga cikin wakilanta Kakakin hukumar kwallon kafa ta kasar iran yace mun riga mun sanarwa da hukumar kwallon kafa ta duniya fifa cewa wannan matakin ba shi da wata alaka da wasanni , kuma wakilan kasar iran din ba za su halarci gasar kofin duniya ba . Wannan yazo ne bayan da hukumar kwallon kafa ta kasar iran ta sanar cewa Amurka ta hana wasu daga cikin jami’anta visa shiga Amurka ciki har da shugaban hukumar Mahdi Taj, Ana...
    Hukumar ƙwallon ƙafa ta Afrika (CAF), ta sanar da cewa daga yanzu kowace ƙasa da za ta taka leda a Gasar Cin Kofin Afrika za ta je da ’yan wasa 28, maimakon 23 da ake amfani da su a baya. CAF, ta ce ta ɗauki wannan matakin ne domin rage matsalar samun raunin da ’yan wasa ke samu a lokacin gasar, tare da bai wa masu horaswa damar samun zaɓin ’yan wasa. Gwamnatin Kano ta nemi a binciki Ganduje kan zargin kalaman ta da hankali Yadda mutane suka yi cikar ƙwari don halartar jana’izar Sheikh Dahiru Bauchi Haka kuma, an amincewa kowace ƙasa za ta je gasar da mutum 17 daga cikin masu horaswa da likitoci. Hukumar ta bayyana cewa...
    Kasar Portugal ta kafa tarihi a birnin Doha na Qatar bayan da ta lashe Kofin Duniya na ’yan ƙasa da shekaru 17 (U-17) a karon farko, inda ta doke Austria da ci 1-0 a wasan ƙarshe. An jefa ƙwallon da ta bai wa Portugal nasara ne ta hannun Anisio Cabral, wanda ya ci a minti na 32 da fara buga wasan a filin wasa na Khalifa. Gwamnatin Kano ta nemi a binciki Ganduje kan zargin kalaman ta da hankali Yadda mutane suka yi cikar ƙwari don halartar jana’izar Sheikh Dahiru Bauchi A hanyarta ta kaiwa  wasan ƙarshen, Portugal ta doke Brazil a wasan kusa da na ƙarshe, yayin da Austria ta fitar da Italiya bayan lallasa ta da ci 2-0....
    Rundunar “Sarayal-Quds” ta kungiyar Jihadul-Islami ta sanar da shahadar  mayakanta biyu a yammacin kogin Jordan sanadiyyar harin da sojojin mamaya na Haramtacciyar Kasar Isra’ila su ka kai. Daya daga cikin shahidan shi ne Yusuf Ali Asa-Asa, dan shekaru 37, da kuma Mahmud Abdullah dan shekaru 26, sun kuma yi shahadar ne a jiya Alhamis.  Sanarwar ta kuma ce,an yi batakashi a tsakanin shahidan biyu da kuma ‘yan mamaya gabanin su kwanta dama a unguwar Abu Dhahir dake Jenin a yammacin Kogin Jordan. Wasu rahotanni daga yankin da lamarin ya faru sun ce, sojojin Haramtacciyar kasar Isra’ila sun kutsa cikin unguwar tare da shiga cikin wani gidan sannan kuma su ka kama wani saurayi Bapalasdine daya. Gabanin su yi awon gaba...
    Jagoran juyin musulunci na kar iran Ayatullah sayyid Ali Khamna’i ya bayyana cewa kasar Amurka bata ji da dadi ba a yakin kwanaki 12 da ta kaddamar a kan kasar iran a watan yuni, duk da amafani da ta yi da manyan makaman yaki na zamani da suka hada da jiragen yaki da kuma makaman kariya . Har ila yau jagoran yace Amurka da isra’ila sun sha kashi a yakin kwanaki 12 da suka kaddamar kan kasar iran, sun kai harin ne don su ci blus, sai suka koma da borin kunya, basu iya tabuka komai ba, wannan babban shan kashi ne a garesu, Yace wasu rahotanni sun nuna cewa gwamnatin sahyuniya ta shirya yakin shekaru 20, ta shirya tunzura...
    Gammayar ministocin harokin wajen kungiyar tarayyar Turai sun fitar da wata sanarwa da aciki suka soki hare haren da yahudawa yan share wuri zauna suke kai wa falasdinawa a gabar yammacin kogin Jodan da isra’ila ta mamaye kuma yake kara ci gaba fiye da kowanne lokaci a baya, Sanarwar ta fito ne daga minsitocin kasashen birtaniya, jamus , faransa da kuma italiya inda manyan jami’an diplomsiyarsu suka bayyana hare-haren a matsayin mataki ne na tada fitina da kuma ta’addanci. Haka zalika sun yi kira ga fira ministan isra’ila Benjamin na tanyaho da yayi aiki da nauyin da ya rataya a wuyansa karakshin dokokin kasa da kasa, kuma ya kiyaye hakkin falasdinwa dake zaune a bangarorin da aka mamaye. Daga karshe...
    Babban Sufeton ’yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya ce sun janye ’yan sanda 11,566 da ke rakiyar manyan mutane kamar yadda Shugaban Ƙasa ya ba da umarni a kwanakin baya. Ya kuma ce an sake tura waɗannan jami’an zuwa muhimman wuraren da aka fi buƙatars su don kare al’ummomi masu rauni a fadin ƙasa. NAJERIYA A YAU:Waiwaye Kan Irin Gudunmawar Da Sheikh Dahiru Bauci Ya Bayar Ga Cigaban Addini An gano gawawwakin mata uku ’yan Kamaru da aka sace a Anambra Aminiya ta rawaito cewa Shugaba Bola Tinubu, a ranar Lahadi, ya bayar da umarnin janye jami’an ‘yan sanda daga aikin tsaron manyan mutane tare da umartar a sake tura su zuwa ayyukan tsaro na asali. Umarnin ya biyo bayan...
    Ministan yakin Isra’ila ya yi barazanar kai wa kasar Lebanon hari gadan-gadan, inda ya bukaci kungiyar Hizbullah ta kwace damarar makamai. Ministan yakin Isra’ila, Isra’ila Katz, ya yi gargadin cewa Tel Aviv a shirye take ta kaddamar da wani sabon yaki kan kasar Labanon matukar kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta ki mika makamanta zuwa  karshen shekarar 2025. Da yake jawabi ga Knesset na Isra’ila, Katz ya yi ikirarin cewa Washington ta ba Beirut wa’adin kwance damarar Hezbollah zuwa karshen shekara, amma ya ce ba ya tsammanin kungiyar za ta mika makamanta. “Ban yi imani cewa Hizbullah za ta mika makamanta bisa radin kanta ba,” kamar yadda ya shaida wa ‘yan majalisar. “Idan Hezbollah ba ta yi watsi da makamanta a karshen...
    Ana fargabar cewa wata mata mai suna Success ta kashe wata yarinya mai shekaru bakwai, Alicia Olajumoke, a unguwar Rumueme da ke birnin Fatakwal na Jihar Ribas. Mazauna yankin sun shaida wa Aminiya cewa matar da ake zargin tana da kusanci da dangin mahaifiyar yarinyar, wacce ita kaɗai ce a wurin iyayenta. El-Rufai ya koma jami’yyar haɗaka ta ADC An janye ’yan sanda 11,566 daga gadin manyan mutane a faɗin Nijeriya Bayanai sun ce ita ma matar ta caka wa kanta wuƙa a wuya bayan kashe yarinyar, kuma bayan an garzaya da duk su biyun asibiti, likitoci suka tabbatar da cewa sun riga mu gidan gaskiya. Lamarin wanda ya faru a ranar Talata ya ɗimauta mazauna yankin, la’akari da zargin...
    Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya sauka sheƙa daga jam’iyyar SDP zuwa jami’yyar haɗaka ta ADC. Komawar El-Rufai jam’iyyar ADC a hukumance wani mataki ne da ake ganin zai kawo sabon salo a siyasar adawa wajen ƙalubalantar jam’iyyar APC mai mulki a Zaɓen 2027. An janye ’yan sanda 11,566 daga gadin manyan mutane a faɗin Nijeriya Mbappe ya ci ƙwallaye 4 rigis a wasan Madrid da Olympiacos A wannan Alhamis ɗin ce El-Rufai ya kammala rajistar zama mamba na jam’iyyar ADC a mazaɓarsa ta Unguwar Sarki da ke birnin Kaduna, inda ya yi alƙawarin amfani da jam’iyyar ADC wajen fuskantar abin da ya kira rashin ƙwarewa a jagorancin gwamnatin jihar. “Ina da cikakkiyar rajista a jam’iyyar African Democratic...
    Ɗan wasan gaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid, Kyalian Mbappe ya samu nasarar zura kwallaye huɗu rigis a ragar Olympiacos a wasan mako na biyar na kofin zakarun nahiyyar turai da suka buga a yammacin jiya Laraba. Real Madrid dai caskara Olympiacos 4-3 ne a wasan, lamarin da ya ba ta damar haɗa maki 12 cikin fafatawa biyar. Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi ta bar babban gibi a Najeriya – Tinubu An rantsar da sabon shugaban kasa a Guinea-Bissau bayan juyin mulkin sojoji Kawo yanzu dai Mbappe ya shiga gaban Victor Osimhen na Galatasaray wajen yawan zura ƙwallaye a raga a gasar ta kakar nan, inda Mbappe ya ke da 9, yayin da Osimhen wanda ke fama da rauni...
    Daga Usman Muhammad Zaria  Shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kudu a Jihar Jigawa, Dr. Builder Muhammad Uba, ya aiwatar da wani aiki na da naira miliyan biyar domin tallafa wa aiwatar da Shirin Tallafawa Yara Mata  (AGILE) a yankin. Aikin ya hada da gyaran ajujuwa biyu da samar da muhimman kayan aiki, ciki har da injunan dinki, injin yin surfani wato (monogram) da shirin AGILE ya bayar kyauta wanda Dr. Uba ya shirya, ya taimaka wajen ganin an fara amfani da shi, tare da samar da janareta da tabarmi domin inganta koyarwa da horo. Wannan ci gaban ya biyo bayan wani bincike da tawagar AGILE ta jihar Jigawa ta gudanar a baya, inda ta bayyana cewa wuraren koyon sana’o’in na...
    Sojojin Guinea-Bissau sun naɗa Janar Horta Nta Na Man a matsayin sabon shugaban ƙasar na rikon kwarya, kwana ɗaya bayan sun yi juyin mulki tare da kama shugaban ƙasar, Umaro Sissico Embalo. Sojojin dai sun kwace mulkin ne yayin da ake shirin bayyana sakamakon zaɓen kasar mai cike da takaddama. Majalisar Wakilai ta nemi gwamnati ta gaggauta dauko Jonathan daga Guinea Bissau Abubuwa 20 da ya kamata ku sani game da Sheikh Dahiru Bauchi “Na rantsar da kaina a matsayin shugaban Babban Kwamandan Soja,” in ji Janar Horta bayan ya karbi rantsuwar aiki a wani biki da aka gudanar a hedkwatar sojoji a ranar Alhamis, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito. Daruruwan sojoji dauke da makamai sun...
    Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Bauchi, a matsayin babban rashi ga al’umma. Gwamnan ya bayyana malamin a matsayin jagoran haɗin kai, zaman lafiya, da fahimtar juna tsakanin Musulmi da mabiya addinai daban-daban. ’Yan sanda sun gano harsasai 210 a kan titin Zariya-Funtuwa Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa A cikin saƙon ta’aziyya da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Mukhtar Gidado, ya sanya wa hannu, gwamnan ya ce Gwamnatin Jihar Bauchi tana alhinin rasuwar malamin. Dahiru Bauchi, ya rasu da safiyar ranar Alhamis, 27 ga watan Nuwamba, 2025 a Bauchi, yana da shekara 102. Gwamnan, ya ce Sheikh Dahiru Bauchi babban malami ne na addinin...
    Fitaccen malamin addinin Musulunci nan daga Jihar Bauchi, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya rasu. Ɗansa, Sayyadi Ali Dahiru Usman Bauchi ne,  ya tabbatar wa Aminiya rasuwar malamin. Juyin mulki ya rutsa da Jonathan a Guinea-Bissau Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban Amurka Ya ce sun karɓi wannan ƙaddara tare da gode wa Allah bisa rayuwar da malamin ya yi. “Tabbas Sheikh ya koma ga Mahaliccinsa. Daga Allah muke, kuma gare Shi za mu koma,” in ji Sayyadi. “Lokacin Sheikh ya yi. Mun gode wa Allah Maɗaukaki. Ya bai wa Sheikh tsawon rai, kuma rayuwarsa ta yi kyau. Alhamdulillah,” in ji shi. Sayyadi, ya ce zuwa yanzu ba su yanke inda za a yi jana’izar malamin ba.
    Ma’aikatar Ma’adinai da wutan lantarki a yankin Kurdistan na kasar Iraki ta bada sanarwan cewa an dakatar da tura iskar gas zuwa cibiyoyin samar da wutan lantarki a yankin saboda hare-haren da aka kai kan wata cibiyar hakar iskar gas a yankin. Tashar talabijan ta Almayadeentv ta kasar Lebanon ta bayyana cewa wani jirgin yaki wanda ake sarrafashi daga nesa ne ya fada kan cibiyar hakar iskar gas ta Kurmur, ta kuma jawo dakatar da tura iskar gas din. Labarin ya kara da cewa jirgin ya fada kan cibiyar hakar iskar gas ta kurmur a bangaren Chemchel na lardin Sulaimaniyya ne, ya kuma haddasa barna mai yawa, wanda mai yuwa har da rasa rai ko rayuka. A halin yanzu dai...
    An kulle Fadar Shugaban Kasar Amurka ta White House tare da wasu gine-ginen gwamnati da dama, sakamakon harbin ɗan bindigar da ya raunata sojoji biyu a kusa da fadar. A yayin, an harbe masu tsaron fadar biyu har lahira. Gwamna Patrick Morrisey da farko ya ce an kashe sojojin, amma daga baya ya ce yana samun “rahotanni masu karo da juna” game da halin da suke ciki, yana mai da cewa za a fitar da ƙarin bayani idan an tabbatar. A cikin wani rubutu a shafin X, ya ce, “Yanzu muna samun rahotanni masu cin karo da juna game da halin sojojin biyu, kuma za mu bayar da ƙarin bayani idan mun samu cikakken rahoto. “Addu’o’inmu suna tare da waɗannan...
    ’Yan wasan tawagar ƙwallon ƙafar Nijeriya ta Mata, Super Falcons, sun yi barazanar ƙaurace wa wasannin sada zumunta da Najeriya za ta buga a watan Disamba mai kamawa. ’Yan wasan sun ce za su ƙaurace wa wasannin ne idan har Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) ta ci gaba da jinkirta biyan kuɗaɗen alawus-alawus da suke biyo tun na Gasar Olympics da aka yi a birnin Paris a 2024. Andrea Thompson ta zama mace mafi ƙarfi a duniya Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro Wasu majiyoyi daga ƙungiyar sun tabbatar cewa ’yan wasan na ci gaba da jiran a biya su haƙƙoƙinsu na wasannin da suka buga, ciki har da alawus na nasarar da suka samu a gasar...
    Rahotanni sun bayyana cewa kididdigar da ma’aikatar harkokin wajen yankin falasdinu ta fitar ya nuna cewa sojojin Isra’ila sun kashe akalla yan mata 33000 a ci gaba da yakin kare dangi da take yi kan alummar Gaza. Ma’aikatar fa fitar da wannan sanarwar ce a wajen taron ranar kawo karshen hare-hare kan mata ta duniya . kuma tayi kaca-kaca da gwamnatin sahayuniya game da irin muggan laifukan yaki da ta tafka, inda ta rika amfani da makamai na zamani kan alummar falasdinu Kididdigar ta nuna cewa sama da mata 12500 da kuma yara 20,000 ne Isra’ila ta kashe a harin da ta kai tun daga watan oktoban shekara ta 2023. Har ila yau ma’aikatar ta bayyana cewa lallai a kwai...
    A yammacin nan ne ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid za ta kece raini da Olympiacos a ci gaba da Gasar Zakarun Turai, duk da rashin wasu manyan ’yan wasanta biyu. Babban mai tsaron ragar Madrid, Thibaut Courtois, da ɗan wasan baya Dean Huijsen, na fama da jinya, lamarin da zai hana su buga wannan muhimmin wasa. Sojoji sun yi juyin mulki a Guinea-Bissau Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa sunayen jakadu Yanzu haka jerin ’yan wasan Madrid da ke jinya sun haɗa da: Thibaut Courtois, Dean Huijsen, Antonio Rüdiger, David Alaba, Franco Mastantuono, da Éder Militão. Tun bayan zuwan sabon kocin Real Madrid, Xabi Alonso, Courtois ya riƙe ragamar tsaron raga a dukkan wasanni 17 da suka buga a...
    Jakadan kasar Aljeriya a kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya yayi tir da abin da ya kira zalunci isra’ila da kuma ci gaba da kai hare-hare kan mutane kasashen labanon, Syria, da Gaza da kuma gabar yammacin kogin jodan , yayi kira ga majalisar dinkin duniya da ta dauki mataken gaggawa wajen dakatar da wadannan hare haren, kuma akwai dubban laifuffukan da Isra’ila ta aikata da ba’a manta ba kuma ba’a dauki wani mataki a kai ba. Aljeriya ta yi wannan bayanin  ne bayan karuwar sukar da ake yi a kwamitin tsaro game da mataken da isra’ila ke dauka a daidai lokacin da ake cikin matsala game da isar da taimakon agaji ga alummar gaza. A taron da kwamitin tsaro...
    Hukumar tsaro ta DSS ta zargi dan jarida kuma mai shiga tsakani da ’yan ta’addar da suka sace fasinjojin jrigin kasan Kaduna-Abuja a shekarar 2022, Tukur Mamu, da karbar Naira miliyan 50 daga kudin fansar fasinjojin. Ana zargin Tukur Mamu da karbar kudin ne daga jagoran ’yan bindigar da ake kira da “Shugaba”. Zulum ya ba kowanne ɗalibin Borno da ke karatu a Indiya tallafin N500,000 Ko sisi ba a biya ’yan bindiga ba kafin su saki ɗaliban da suka sace – Gwamnan Kebbi Mamu na fuskantar tuhumar laifukan ta’addanci, ciki har da karɓar kuɗin fansa daga iyalan waɗanda aka yi garkuwa da su a harin jirgin Kaduna na ranar 28 ga Maris, 2022, hulɗa da kuɗaɗen ’yan ta’adda, hana...
    Shugaban Iran ya sanar da cewa gwamnati na aiki don inganta juriya da ingancin tattalin arzikin kasar. Masoud Pezeshkian, Shugaban Iran, ya yi jawabi a taron Kasuwar Jarin Iran na shekara-shekara mai taken “Juriya, Kirkire-kirkire, Ci gaba,” yana mai jaddada gyare-gyaren manufofin tattalin arziki, kula da albarkatu, da kuma tallafawa masu zuba jari. Ya bayyana cewa gwamnati na aiki don rage cikas ga samar da kayayyaki da ciniki. Pezeshkian ya nuna muhimmancin yin tarurruka na wata-wata tare da masu zuba jari da masu samar da kayayyaki don nemo hanyoyin magance matsalolin da ake fuskanta. Ya kara da cewa, “Tanadin kashi 10% na iya adana ganga 800,000 zuwa 900,000 na mai a kowace rana.” Ya kuma nuna cewa samar da wutar...
    Pars Today – Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran, yana mai jaddada muhimmancin Pakistan a yankin, ya ce haɗin gwiwa tsakanin Tehran da Islamabad a fannoni daban-daban yana taimakawa wajen kawo kwanciyar hankali da zaman lafiya a yankin Ali Larijani, Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran, ya ce da sanyin safiyar Talata da ya isa Islamabad cewa Pakistan muhimmiyar ƙasa ce a yankin kuma tana da matsayi mai kyau wajen tasiri ga yanayin tsaro na yankin. A cewar Pars Today, ya ƙara da cewa a matsayinta na maƙwabciyar gabas ta Iran, Pakistan ma tana taka rawa a al’adu, kuma dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu ta daɗe tana da zurfi kuma ta tarihi. Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Jamhuriyar Musulunci...
    Babbar Kotun Jihar Oyo da ke Ibadan, babban birnin jihar, a ranar Litinin ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga mutum biyar da ta samu da laifin kashe wani direban tasi. Kotun dai ta sami mutanen ne da laifin kashe direban mai suna Akeem Shittu a lokacin mummunan rikici a shekarar 2024. DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane? An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a Kebbi Yayin yanke hukunci, alkalin kotun, Mai Shari’a Oyeyemi Ajayi ya bayyana cewa Segun Taiwo (36), Kehinde Ademola (46), Yahaya Adeniyi (45), Chinonso Samson (41), da Opadotun Michael (32) sun yi tarayya wajen yin hadin baki da kuma kisan Shittu. “Na yi la’akari...
    Shugaban kungiyar Ansar Allah a Yemen, Sayyed Abdul-Malik al-Houthi, ya aika da sakon ta’aziyya ga Sakatare Janar na Hezbollah, Sheikh Naim Qassem, kan shahadar babban  kwamandan dakarun kungiyar Haitham Ali al-Tabtabai da abokansa. Huthi ya jaddada cewa laifin da aka aikata a kansu, tare da hare-haren da ake kai wa Lebanon da Zirin Gaza, yana nuna irin girman kai da Isra’ila ke da shi ne. Sayyed al-Houthi ya kara da cewa shahid al-Tabtabai ya yi kokari matuka wajen cimma manyan-manyan nasarori, kuma ya ba da gudummawa ga hanyar gwagwarmaya don taimakon  gaskiya da wadanda aka zalunta, ya kara da cewa tasirin rawar da ya taka a cikin gwagwarmaya zai ci gaba da wanzuwa a cikin lamirin gwagwarmaya da zaluncin Isra’ila...
    Wani mai magana da yawun rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya (UNIFIL) ya tabbatar da cewa Isra’ila ta gina katanga kan iyakar da ta ratsa zuwa cikin yankin kasar Lebanon kusa da garin Yaroun, abin da tawagar ta bayyana a matsayin keta kudurin Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 1701. “Isra’ila ta shafe shekaru da dama tana gina katanga a gefen Layin da aka Shata da ya raba yankunan Falastinu da Isra’ila ta mamaye da Lebanon, amma a cikin wannan yanayi katangar Isra’ila ta ratsa layin da ya raba bangarorin biyu,” in ji mai magana da yawun UNIFIL. “Don haka muna nuna rashin amincewa da wannan mataki, Wannan, a bayyane ya keta kuduri mai lamba 1701...
    Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya gabatar da kasafin kuɗi na shekarar 2026 na sama da naira biliyan 900 ga Majalisar Dokokin jihar. Yayin gabatar da kasafin da aka lakaba wa suna “Kasafin Kirkire-kirkire da Sauyi Don Cigaban Jigawa II,” Gwamna Namadi ya ce za a ware sama da naira biliyan 693.4, wanda ya kai kimanin kashi 76 cikin 100, don ayyukan raya kasa. Gwamnan ya kuma ce sama da naira biliyan 208 za su tafi ne ga ayyukan yau da kullum. A cewarsa, an ware sama da naira biliyan 310 ga bangaren ilimi da lafiya, yayin da kimanin naira biliyan 186 za su tafi ga hanyoyi da sufuri. Malam Umar Namadi ya ƙara...
    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta samu nasara a wasan mako na 14 na Nigeria Premier Football League (NPFL), bayan da ta doke Ikorodu City da ci 2–1 a filin wasa na Muhammad Dikko, da ke birnin Katsina. Wannan ita ce nasara ta uku da Pillars ta samu a kakar bana, cikin wasanninta 14, inda ta yi kunnen doki uku, sannan ta sha kashi shida. ’Yan bindiga sun yi yi garkuwa da mutane 11 a Kwara Chelsea za ta kece raini da Barcelona a Gasar Zakarun Turai Kafin wannan wasan, Kano Pillars ta yi wasanni takwas a jere ba tare da samun nasara ba. Pillars ta zura kwallayenta ne ta hannun Rabiu Ali, wanda ya zura ta farko a...
    Kungiyar Hizbollah ta kasar Lebanon ta bayyana cewa Isra’ila na yin kuskure idan ta na tunanin kashe-kashe da kisan gillar da ake wa mambobi da kwamandojinta zai kawo karshen kungiyar. Wannan na zuwa ne bayan kisan gillar da Isra’ila ta yi wa babban kwamandan sojin kungiyar da wasu makusantansa a ranar Lahadi, a wani hari da ta kai a kudancin babban birnin Lebanon. Haitham Ali Al-tabataba’i  da aka fi sani da Abu Ali, ya yi shahada ne tare da wasu dakarun hizbullah guda 4 a wani mummunan hari  da Isara’ila ta kai a heret hareik dake kudancin birnin beirut. Tabataba’I yana daya daga cikin jajircaccen dakarun kungiyar hizbullah , kuma ya taka rawa sosai wajen tsarin tsaron kungiyar tun shekarun...
    ’Yan Majalisar Tarayya daga yankin Kudu sun yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi wa jagoran ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, afuwa bayan da kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai. Kungiyar ’Yan Majalisar Wakilai daga yankin Kudu maso Gabas ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya yi amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi, wajen yi wa Nnamdi Kanu afuwa wanda kotu ta same shi da laifin ta’addanci. Alƙali James Omotosho na Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ne ya yanke hukuncin, inda ya same shi da laifi a kan tuhumar da ake masa guda bakwai, sannan ya yanke masa hukuncin daurin rai da rai. Tuni aka tura Nnamdi Kanu...
    ’Yan Majalisar Wakilai daga yankin Kudu sun yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi wa jagoran ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, afuwa bayan da kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai. Kungiyar ’Yan Majalisar Wakilai daga yankin Kudu maso Gabas ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya yi amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi, wajen yi wa Nnamdi Kanu afuwa wanda kotu ta same shi da laifin ta’addanci. Alƙali James Omotosho na Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ne ya yanke hukuncin, inda ya same shi da laifi a kan tuhumar da ake masa guda bakwai, sannan ya yanke masa hukuncin daurin rai da rai. Tuni aka tura Nnamdi Kanu...
    Ana zargin wata amarya da yi wa angonta yankan rago kwana uku bayan ɗaurin aurensu a Jihar Katsina. Angon mai suna Abubakar Abdulkarim da aka fi sani da Dan Gaske, ana zargin ya rasa ransa bayan da amaryar ta yi amfani da wuƙa wajen halaka shi. Shaidu sun ce ta yi masa mummunan rauni a wuya wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa. Angon da amaryarsa suka daura aure ne a ranar Alhamis, 18 ga Nuwamba, 2025, amma farin cikin aure ya rikide zuwa makoki a ranar Lahadi da rana lokacin da lamarin ya faru. Gobarar tankar mai ta ƙone gidaje a Jihar Neja NAJERIYA A YAU: Irin Radadin Da Masu Cutar Amosanin Jini Ke Fuskanta Wani ɗan uwansa mai suna Aminu...
    Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon  na juyayin shahadar kwamanda haitham Ali Al-tabataba’i  da aka fi sani da Abu Ali wanda yayi shahada tare da wasu dakarun hizbullah guda 4 a wani mummunan hari  da Isara’ila ta kai a heret hareik dake kudancin birnin berut na kasar labanon. Tabataba’I yana daya daga cikin jajircaccen dakarun kungiyar hizbullah , kuma ya taka rawa sosai wajen tsarin tsaron kungiyar tun shekarun farko da aka kafata, kisan nasan ya kara nuna irin yadda isra’ila ke keta yarjejeniyar dakatar da tsagaita bude wuta da aka cimma, kuma kisan nasa zai kara karfafa jajircewa a turbar gwagwarmaya a yankunan labanon da falasdinu. Kungiyar hizbullah ta bayyana cewa babban kwamandan ya bi dan uwansa da yayi shahada...
    Fitaccen jarumin masana’antar fina-finan Indiya ta Bollywood, Dharmendra Deol da aka fi sani da Dharam Ji, ya mutu yau Litinin yana da shekaru 89 a duniya. Dharam ya riga mu gidan gaskiya ne kwanaki gabani cika shekaru 90 bayan fama da doguwar jinya mai alaƙa da numfashi kamar yadda kafofin labarai suka ruwaito. Slot na fuskantar matsin lamba saboda rashin kataɓus a Liverpool Ɗaya daga cikin ’yan matan da ISWAP ta sace a Borno ta tsere A watan Nuwambar nan ne labaran ƙanzan kurege suka riƙa yaɗuwa cewa jarumin ya mutu a daidai lokacin da ake jinyar sa a asibitin Breach Candy da ke birnin Mumbai na ƙasar ta Indiya. Bayanai sun ce tun dai cikin watan Oktoban da ya gabata,...
    Yundunar ’Yan Sandan Jihar Borno ta tabbatar da cewa ɗaya daga cikin ’yan mata 14 da ƙungiyar ISWAP ta sace a Ƙaramar Hukumar Askira-Uba ta kuɓuta, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin gano sauran 13. A sanarwar da ya fitar dangane da irin ƙoƙarin da Jami’an tsaron ke yi na ceto sauran ‘yan matan 13 da ke hannun ‘yan ta’addan, kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya ce, shugaban gundumar Huyum ya bayar da rahoto a ranar Asabar 22 ga Nuwamba cewa waxanda ake zargin mayaƙan Ƙungiyar ISWAP ne suka sace ‘yan matan, yayin da suke aiki a wata gona a gundumar Mussa. Tawagar ’yan sanda, sojoji, Sibiliyan JTF, da mafarauta da ’yan banga nan da nan suka fara...
    Babban magatakardar Majalisar koli ta tsaron kasar Iran Dr. Ali Larijani ya mika ta’aziyyar shahadar daya daga cikin kwamandojin kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Haisam al-Tabtabai wanda ya yi shahada a jiya Lahadi sanadiyyar harin Haramtacciyar Kasar Isra’ila. Dr. Ali Larijani ya wallafa sakon ta’aziyyar a shafina na X cewa; A daren shahadar Sayyidah Fatimah az-Zahrah ( a.s) daya daga cikin masu tafiyar gaskiya akan tafarkin jagorar matan duniya, dan’uwa, mujahidin Haisam Ali Tabtabai’ ya yi shahada, tare da wasu manyan kwamandoji sanadiyyar harin ‘yan sahayoniya.” Dr.Ali Larijani ya kuma ce; Har yanzu Netanyahu yana ci gaba da tarbar aradu da ka, da hakan yake sake tabbatarwa da duniya cewa babu abinda ya kamata a yi sai kalubalantar wannan tsarin...
    Ofishin Yada Labarai na Gwamnatin Gaza ya ce Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza da Amurka ta shiga tsakani akalla sau 497 cikin kwanaki 44, inda ta kashe daruruwan Falasdinawa tun lokacin da yarjejeniyar ta fara aiki a ranar 10 ga Oktoba. Ofishin ya ce Isra’ila ce ke da alhakin dukkan tabarbarewar al’amuran jin kai da tsaro sakamakon keta yarjejeniyar tsagaita wuta da ta yi akai-akai. An kashe fararen hula 342 a hare-haren, mafi yawansu yara, mata da tsofaffi ne. “Muna Allah wadai da ci gaba da karya yarjejeniyar tsagaita wuta mai tsanani da aka yi da hukumomin mamayar Isra’ila,” in ji ofishin a cikin wata sanarwa. Isra’ila ta ci gaba da takaita kwararar kayan agaji da magunguna...
    Babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya yi kira ga shugabannin kasashen duniya da suke taro a birnin  Johannesburg na kasar Afirka Ta Kudu da su warware matsalar rashin daidaito a cikin harkokin kasuwanci a tsakanin kasashe. Babban magatakardar MDD wanda ya gabatar da jawabi a wurin taron na G 20 ya yi Ishara da gibin kasuwanci da ake da shi a tsakanin kasashen da su ka ci gaba da masu tasowa wanda ya kamata a san yadda za a magance shi. Antonio Gutrres ya kuma ce: “Wani abu guda daya wanda zan iya bayar da tabbaci a kansa shi ne cewa ofishin babban magatakardar MDD zai yi duk abinda zai iya yi domin yin gyara a cikin rashin daidaito da...
    Rahotanni sun bayyana cewa an sanar da sunan brigadier janar Ali Jahanshashi a matsayin sabon kwamandan dakarun sojan kasar iran inda ya gaji brigadier janar Kiumars Haidari Bayanan da yayi jim kadan bayan sanar da nadin nasa a yau Asabar, Jahanshahi ya jaddada cewa dakarun sojin kasar a shirye suke su mayar da martani kan duk wata barazana ta hanyar amfani da kwarewarsu da makamai na zamani da kuma daukan darasi kan rikicin da ya faru abaya bayan nan musamman yakin kwanaki 12 da Israila ta kallafa mata. Haka zalika ya kara da cewa a halin yanzu sojoji sun bada fifiko ga kaidoji da dokoki guda 5 da jagoran juyin musulunci na iran Ayatullah imam khamnai ya sanya, wanda suka...
    Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya soki hukuncin da kotu ta yanke wa jagoran ’yan awaren ƙungiyar Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu. Obi ya bayyana hukuncin matsayin “abun takaici” kuma alamar gazawar jagoranci. Sace ɗalibai: An rufe makarantu a Katsina da Taraba Gobara ta lalata gidaje 40 a sansanin ’yan gudun a Borno A ranar Alhamis ne wata Kotun Tarayya da ke Abuja, ta yanke wa Kanu hukuncin ɗaurin rai da rai bayan samun sa da laifukan ta’addanci. Sai dai Obi ya ce Gwamnatin Tarayya ta yi kuskure tun daga farko wajen tafiyar da lamarin, kuma bai kamata ya kai wannan mataki ba. Ya ce Najeriya na fuskantar matsaloli da dama ciki har da...
    Kwamandan sojan kasa na Rudnunar sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran Birgerdiya Janar Ali Jahanshahi ya ce; Sojojin kasar a shirye suke su mayar da martani akan duk wata barazana daga abokan gaba saboda suna da zaratan mayaka da kuma sabbin makamai.” Har ila yau Ali Jahanshahi ya ce; Sojojin za kuma su yi amfani da kwarewar da tsofaffin sojoji suke da ita, haka nan kuwa darussan da su ka koya daga kallafaffen  yakin kwanaki 12 da HKI.  Janar Jahanshahi ya kuma ce; A wannan lokacin kwarewar da sojojin kasa na Iran suke da su, ta kai koli saboda wararrun masana da kuma amfani da fannoni mabanbanta na ilimomi, musamman kirkirarriyar Fasaha.” A dalilin hakan, sojojin suna cikin Shirin mayar wa...
    Gwamnatocin jihohin Katsina da Taraba sun ba da umarnin rufe makarantu sakamakon hare-haren ’yan bindiga da suka sace daruruwan ɗalibai a makarantu a cikin mako guda a jihohin Kebbi da Neja. Gwamnatin Jihar Taraba ta rufe makarantun kwana a fadin jihar, inda ta ba da umarnin a koma tsarin jeka-ka-dawo sakamakon tabarbarewar tsaro. Gwamnan Agbu Kefas, ya umarci duk makarantun sakandare na gwamnati da masu zaman kansu da dalibai su daina kwana a makarantu saboda fargabar tsaro a faɗin ƙasar. Sanarwar da kwamishinar ilimi ta jihar, Augustina Godwin, ya fitar ta ce garkuwa da ɗalibai a Kebbi da Neja ta sanya daliban makarantun kwana zama cikin hadari. Don haka gwamnati ta umarci komawa tsarin jeka-ka-dawo har sai tsaro ya inganta....
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyar mu a yau. Shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata wadanda suka shafi siyasa, tattalin, arziki, zamantakewa tsaro da sauransu, inda muke masu Karin bayani sannan daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane da su da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu nay au /////… Madalla, masu sauraro zamu fara shirimmu da labarimmu na farko wanda yake cewa majalisar gwamnoni a hukumar IAEA ta amince da wani kuduri na takurawa JMI a taron da ta yi a ranar Alhamis 22 ga watan Nuwamban da muke ciki. Kuduri wanda kasashen E3 ko Traiko na...
    Shugaban kasar Ukrain Volodymyr Zelensky ya fito fili ya bayyana cewa bai amince da sabon shirin shugaban kasar Amurka Donal Trump na kawo karshen yaki a kasarsa. Ya kuma bayyana cewa kasar Ukraine tana cikin mafi munin hali a tarihin kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa shugaban kasar Amurka yana takurawa kasarsa ta amince da al-amura guda 28 da ya gabatar wanda a fadinsa zai kawo karshen yakin shekari kimani 3 wanda kasarsa take fafatawa da kasar Rasha. Labarin ya kara da cewa daga cikin al-amuran da shugaban ya gabatar a wannan shirin kawo karshen yaki a Ukraine sun hada da amincewa da zaben...
    Yan wasan kasar Iran sun kammala gasar wasannin sada zumunci na kasashen musulmi wanda aka kammala a birnin Riyad na kasar Saudiya tare da lambobin yabo har 81. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa wannan ya nuna cewa kasar Iran na daga cikin kasashen musulmi wadanda suke da kwarewa a wasannin motsa jiki daban daban. Labarin ya kara da cewa an gudanar da wasannin ne daga ranar 6 ga watan Nuwamba zuwa 21 ga watan. Tare da fara wasu wasannin daga ranar 3 ga watan. Kasar Saudiya wacce ta dauki bakwancin wadan nan wasannin motsa jiki ta sami nasarar tattara yan wasannin motsa jiki na kasashen musulmi a duniya a cikin kwanaki kima 20 da suka...
    Hukumar DSS ta mayar d Shugaban ’Yan Awaren Biyafara (IPOB), zuwa gidan gyaran hali a Jihar Sakkwato. Wannan mataki ya biyo bayan hukuncin da kotu ta yanke masa na ɗaurin rai da rai kan laifukan ta’addanci. Sojoji sun bar makarantar Maga kafin ’yan bindiga su kai hari — Gwamna Kebbi  Zargi: Majalisar Kano ta dawo da shugaban ƙaramar hukumar Rano kan kujerarsa A ranar Alhamis ne, Alƙalin Kotun Tarayya da ke Abuja, James Omotosho, ya ce DSS za su kai Kanu kowace cibiyar gyaran hali da ke Najeriya. Lauyan Kanu, Aloy Ejimakor, ya tabbatar da mayar da shi Sakkwato aranar Juma’a. Ya ce: “DSS ta ɗauke Mazi Nnamdi Kanu daga gidan yari na Abuja zuwa  Sakkwato, sun nesanta shi da...
    Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya umarci Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, da ya koma jihar Kebbi da aiki sakamakon sace ɗalibai ’yan mata 25 da wasu ’yan bindiga suka yi a jihar. Tinubu ya umurci Matawalle, wanda tsohon Gwamnan Jihar Zamfara ne, da ya zauna a Kebbi domin sa ido kan dukkan matakan tsaro da ake ɗauka domin kuɓutar da ɗaliban da aka sace. Babu wani addini da matsalar tsaron Nijeriya ta ƙyale — Fafaroma Za a aurar da marayu 200 a Zamfara ’Yan bindiga sun sace ɗalibai 25 a Makarantar Sakandiren Mata da ke garin Maga na Jihar Kebbi da misalin ƙarfe 4 na Asubahin ranar Litinin. A cewar mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga wanda...
    Daga Bello Wakili Shugaba Bola Tinubu ya umurci Ministan  Tsaro, Alhaji Bello Matawalle, da ya koma Jihar Kebbi biyo bayan sace dalibai  ’yan mata 24  a jihar. An umurci Matawalle, wanda tsohon gwamnan Jihar Zamfara ne, da ya zauna a jihar domin sa ido kan ƙoƙarin  da ake yi na kubutar da ɗaliban da aka sace. ’Yan bindiga sun sace ɗalibai mata 24 na Makarantar Sakandare ta ’Yan Mata da ke garin Maga, Jihar Kebbi, da misalin  ƙarfe 4 na asubar ranar Litinin. Matawalle, wanda ake sa ran zai isa Birnin Kebbi a ranar Juma’a, ya samu ƙwarewa wajen fuskantar matsalar ’yan fashi da garkuwa da mutane a lokacin da yake gwamnan Jihar Zamfara daga shekarar 2019 zuwa 2023. Idan...
    Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da fitar da Naira Biliyan 3 a matsayin  tallafin hadin gwiwa na kowace shekara  domin inganta ilimi a matakin farko, wato UBEC 2025 Matching Grant. A wata sanarwa da Kwamishinan  Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na Jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya fitar ya bayyana cewa za a yi amfani da kudaden ne wajen gina sabbin azuzuwa, gyare-gyare, haka rijiyoyin burtsatse da kuma samar da kayan koyo da koyarwa ga dalibai da malamai. Ya ce, majalisar ta kuma amince da sama da Naira Miliyan 289 domin gina sabbin ofisoshin gudanarwa da gyare-gyare a kananan hukumomi 9 na jihar. A cewarsa, za a yi amfani da kudaden ne wajen gina ofisoshin...
    Iyalai da ‘yan uwan wadanda aka kashe a lokacin zanga-zangar da ta kawo karshen gwamnatin tsohuwar Firaminstar Bangaledash Sheikh Hasina a bara, sun yi maraba da hukuncin kisa da wata kotun birnin Dhaka ta yanke mata. An samu Sheikh Hasina da laifin cin zarafin bil adama tare da ba ‘yan sanda umurnin kashe masu zanga-zanga, inda aka yanke mata hukuncin a bayan idonta. Gwamnatin Bangaledash ta bukaci Indiya da ta tasa keyar Hasina da ke gudun hijira a can domin ta fuskanci hukuncin. Wakiliyar BBC ta ce  Hukumomin Indiya na cewa suna ci gaba da bibiyar lamarin tsakanin Sheikh Hasina da mahukuntan Bangaledash kuma hakan na nufin Indiya na neman wata hanyar diflomasiyya akan lamarin.   BBC
    Rahotanni sun bayyana cewa a zaman da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya yayi a baya bayan nan yayi kira a dauki matakin gaggawa don kawo kareshen yaduwa ayyukan ta’addanci a kasashen yammacin Afrika da kuma yankin sahel, yana gargadin cewa yankin na so ya zama cibiyar tsattsauran raayi da rikice- rikice Anasa bangaren babban sakatare janar din majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya bayyan cewa yanayin da yankin sahel da sauran kasahen dake makwabtaka da shi kullum yana kara yin tsananin sosai, kamar kai hare-haren ta’addanci da kuma matsalar da ta shafi mai a kasar mali suna mummunan tasiri a yankin. Haka zalika yayi gargadin cewa kungiyoyin masu iykirarin jihadi masu yankurin kafa daular musulunci a yankin sahara ISGS...
    Rahotanni daga birnin Tehran sun bayyana cewa ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi ya fadawa masana tattalin arziki cewa Tehran a shirye take na yi duk wata yarjejeniya idan dai za’a tsage gaskiya, kuma iran ta kara karfafa dakarunta wajen kasancewa cikin shirin ko ta kwana musamman ma bayan yakin kwanaki 12 da aka kallafa mata. Wadannan kalaman sun nuna kyakkyawar niyar iran na tattaunawa sai dai bata yarda da shirin Amurka na tattaunawa kai tsaye ba, bugu da kari dabarun siyasar iran shi ne ta amince da bin hanyoyin diplomasiya amma kuma tana ci gaba da nuna adawrta ga isra’ila Janyewar da Amurka ta yi a yarjejeniyar JCPOA a shekara ta 2018 tasa an shiga zaman dar-dar don...
    Kafofin yada labarai na duniya sun mayar da hankali kan taron majalisar shugabannin kasashe mambobin kungiyar Shanghai SCO na 24 da aka gudanar kwanan nan a birnin Moscow na kasar Rasha.  Fira ministan kasar Sin Li Qiang ya yi kira ga kungiyar SCO da ta aiwatar da shawarar inganta tsarin shugabanci na duniya da  kasar Sin ta gabatar, da karfafa kungiyar SCO a bangaren hadin kai da harkoki da kuma tasirinta. Shekaru 24 da suka wuce bayan kafuwar kungiyar SCO, a karkashin jagorancin ruhin Shanghai, an samu habakar abotan kungiyar, da kara ingancinta, shi ya sa ma ta zama kungiyar yanki mafi girma a duniya, wadda ta kare muradun kasashe mambobin kungiyar, ta kuma inganta zaman lafiya da ci gaban...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Esmail Baghaei yayi tir da shigar isara’ila kasar Siriya ba bisa kaida ba, yayi gargadin cewa ci gaba da kai hare-hare da fadada siyasarta ta mamaya babbar barazana ce ga zaman lafiya da tsaron yanki. Haka zalika tahren ta yi gargadin cewa matakin baya bayan nan da isra’ila ta dauka wani bangare ne na nuna tsangwama da kai hare hare da aka dade ana yi ta sama da kasa da kuma mamaye kudancin Syria da zai iya jefa yankin cikin mawuyacin hali. Fira ministan isra’ila banjamin na tanyaho da wasu manyan jami’an gwamnati da suka hada da ministan harkokin wajen da na yaki sun shiga cikin kasar siriya kuma sun  zarta iyakar aka yi...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Yarjejeniyar Alkahira tsakanin Iran da IAEA ba ta da inganci Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya sanar da cewa: Iran ta sanar da Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) cewa: Yarjejeniyar Alkahira ba ta da inganci a martanin kudurin da ta bayar, yana mai nuni da cewa yarjejeniyar ta rasa rawar da take takawa a matsayin tsarin hadin gwiwa tsakanin Iran da IAEA. Da yake mayar da martani ga kudurin da kwamitin Gwamnonin IAEA ta dauka kan Iran, Araqchi ya ce: “Sun sanar da IAEA cewa Yarjejeniyar Alkahira ba ta da inganci a martanin kudurin da ta bayar.” Ministan harkokin wajen Iran ya kara da cewa: “Yarjejeniyar Alkahira ta rasa rawar da...
    Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, babban birnin Nijeriya, ta yanke wa fitaccen jagoran masu fafutukar kafa ƙasar Biafra Nnamdi Kanu, hukuncin ɗaurin rai-da-rai, bayan samunsa da aikata laifukan ta’addanci. Masu gabatar da ƙara sun buƙaci a yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin kisa, to amma Mai Shari’a James Omotosho, ya bayyana cewa a yanzu ba a amfani da hukuncin kisa, a maimakon haka ya yanke masa hukuncin ɗaurin rai-da-rai.
    Mai bai wa shugaban kasa shawara kan sha’anin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya jagoranci manyan jami’an Gwamnatin Nijeriya zuwa Amurka don tattaunawa game da zargin kisan ƙare dangi da ake yi wa Kiristoci. Lamarin ya samo asali ne bayan Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya goyi bayan kafa ƙasashe biyu na Isra’ila da Gaza. A farkon watan nan, Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi barazanar daukar matakin soji a kan Nijeriya, kuma ya bukaci ‘yan majalisar dokokin kasar, ciki har da dan majalisa Riley Moore, su binciki lamarin. Ko da yake Nijeriya ta karyata ikirarin, amma Amurka ta ci gaba da jadadda zargin kisan Kiristoci. A ranar Talata, mawakiyar Amurka, Nicki Minaj a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya ta...
    Gwamnatin Tarayya ta ɗora alhakin dawowar hare-haren ta’addanci, ciki har da sace dalibai mata a jihar Kebbi da kai hari a coci a jihar Kwara, kan kalaman da Amurka ta yi kwanan nan a kan Najeriya. Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya ce sakonnin da Shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa, inda ya zargi Najeriya da “kisan kiyasin Kiristoci” tare da barazanar tura sojojin kasarsa, sun kara wa wasu ƙungiyoyin ’yan ta’adda kaimin kai hare-hare. Babu addinin da ake yi wa kisan ƙare dangi a Binuwai — Gwamna Alia Yadda maganin sauro ya yi ajalin magidanci da iyalinsa a Kano “Kalaman da Amurka ta yi kwanan nan sun kara wa wasu ƙungiyoyin masu tayar da kayar baya da ke son...
    Shugaban majalisar dokokin kasar Labanon Nabih Berri yayi kira da a gudanar da taron gaggawa na kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya  domin tattaunawa kan ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da Israi’la ke yi kan kasar Labanon, wanda ya kashe mutane 14 , kuma ya jaddada game da muhimmancin shigar da kara a hukumance ga majalisar dinkin duniya. Wannan bukata ta zo ne adaidai lokacin da sojojin Isra’ila suke kai hare hare kan fararen hula dake jawo asarar rayuka, kuma yake jawo fargaba game da ci gaba da hara-haren israila na keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta mai lamba 1701, Isra’ila ta kai hare hare a lokuta daban daban a kudancin labanon kuma yayi sanadiyar mutuwar...
    An sanar da dan wasan Paris St Germain, Achraf Hakimi a matsayin wanda ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na 2025, mai tsaron baya da ya lashe kyautar karon farko bayan shekara 52. Dan wasan tawagar Masar Mohamed Salah shi ne na biyu mai taka leda a Liverpool da kuma Victor Osimhen na Super Eagles mai wasa a Galatasaray a mataki na uku. Mai tsaron bayan Morocco ya karbi kyautar sakamakon nasarorin da ya samu a 2025 tare da Paris St Geramin ciki har da lashe Champions League da Ligue 1 da Coupe de France da kuma UEFA Super Cup. Shi ne na farko daga Morocco da ya karbi kyautar tun bayan Mustapha Hadji a 1998, kuma...
    Wata Kotun Tarayya da ke Abuja, ta sanya ranar 15 ga watan Janairun 2026, don fara shari’ar shugabannin ƙungiyar ’yan ta’adda ta Ansaru; Mahmud Usman da Abubakar Abba. Ana zargin su da jagorantar ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru, kuma Hukumar DSS ce ta kama su tare da gurfanar da su a kotu. Ribadu ya jagoranci tawaga zuwa Amurka don ƙaryata zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi Hakimi ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana An tsara faea sauraren shari’ar a ranar Laraba, amma aka ɗage bayan lauyoyin waɗanda ake tuhuma sun nemi a ƙara musu lokaci. Lauyansu, B.I. Bakum, ya bayyana cewa har yanzu suna jiran takardun zargi da wajen DSS. Haka kuma, ya nemi a mayar da...
    Rahotanni daga Falasdinu na cewa Isra’ila ta kashe akalla Falasdinawa 28 tare da raunata wasu 77 a zirin Gaza, wanda ke nuni da ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma a shiga tsakanin Amurka. Rahotanni daga kafafen yada labarai na cikin gida sun nuna cewa mata da yara 17 suna cikin wadanda Isra’ila ta yi wa kisan gilla. Sojojin Isra’ila sun kuma tabbatar da kai hari kan al-Mawasi a Khan Younis, kudancin Gaza. Isra’ila ta kai hare-hare uku daban-daban a birnin Gaza da ke arewacin yankin Falasdinawa da kuma kudancin Khan Younis, a cewar hukumar Falasdinawa. Hukumomin lafiya na Falasdinawa sun ce sojojin Isra’ila sun kai hare-hare 393, inda suka kashe akalla Falasdinawa 290 tare da raunata...
    Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu, ya jagoranci wata tawagar gwamnati zuwa Amurka domin mayar da martani kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi a Najeriya. Wannan zargi ya samo asali ne bayan mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, ya nuna goyon bayansa wajen kafa ƙasashe biyu tsakanin Isra’ila da Gaza. Wardley ya zama zakaran damben boksin na duniya Hakimi ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana A farkon wannan watan ne Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ayyana Najeriya cikin jerin ƙasashen matsala ta musamman. Sannan Trump ya umarci wasu ’yan majalisar Amurka, ciki har da Ɗan Majalisa Riley Moore da su binciki lamarin. Duk da ƙoƙarin da Najeriya ta yi na bayyana...
    Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza kusan sau 400 Babban Daraktan Ofishin Yada Labarai na Gwamnati a Zirin Gaza, Ismail al-Thawabta, ya bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta aikata laifuka 393 da aka rubuta tun lokacin da yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki a Zirin Gaza. Ya jaddada cewa wadannan laifukan sun shafi rayukan fararen hula kai tsaye, da nufin tsoratar da su da kuma fadada barna, ta haka ne ke kara ta’azzara yanayin jin kai da kuma barazana ga makomar kwanciyar hankali. Al-Thawabta ya kara da cewa, a cikin sanarwar da ya bayar ga Al Jazeera Net, cewa: Yanayin jin kai a Gaza yana kara muni tare da rugujewar tsarin lafiya da kuma rufe...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da kasafin 2026 na kuɗi Naira tiriliyan 1.36 a Majalisar Dokokin jihar. Kasafin wanda aka yi laƙabi da “Kasafin Gine-gine, Ci Gaban Kowa da Ɗorewar Ci Gaba.” Dukiyar sama da miliyan 500 ta kone a gobarar kasuwar katako ta Gombe Tinubu ya fasa zuwa taron G20 saboda matsalar tsaro a Najeriya Yayin jawabi da ya gabatar a zauren majalisar a ranar Laraba, gwamnan ya ce an tsara kasafin ne don samar da sauye-sauye, kammala manyan ayyuka, inganta ilimi da harkar kiwon lafiya. Ya bayyana cewa za a kashe Naira biliyan 934.6 (kashi 68) a manyan ayyuka kamar hanyoyi, gine-gine da sauran muhimman ayyuka. Sauran Naira biliyan 433.4 (kashi 32), za su tafi...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da kasafin 2026 na kuɗi Naira tiriliyan 1.36 tiriliyan a Majalisar Dokokin jihar. Kasafin wanda aka yi laƙabi da “Kasafin Gine-gine, Ci Gaban Kowa da Ɗorewar Ci Gaba.” Dukiyar sama da miliyan 500 ta kone a gobarar kasuwar katako ta Gombe Tinubu ya fasa zuwa taron G20 saboda matsalar tsaro a Najeriya Yayin jawabi da ya gabatar a zauren majalisar a ranar Laraba, gwamnan ya ce an tsara kasafin ne don samar da sauye-sauye, kammala manyan ayyuka, inganta ilimi da harkar kiwon lafiya. Ya bayyana cewa za a kashe Naira biliyan 934.6 (kashi 68) a manyan ayyuka kamar hanyoyi, gine-gine da sauran muhimman ayyuka. Sauran Naira biliyan 433.4 (kashi 32), za su...
    Majalisar Dattawa ta shiga cikin jimami a ranar Laraba bayan mutuwar Sanata Okey Ezea, mai wakiltar mazabar Enugu ta Arewa. Bayanai sun nuna marigayin ya rasu ne a kasar Burtaniya inda yake jinya. ‘Yadda aka harbe mijina a gabana lokacin sace daliban Kebbi’ Mai taɓin hankali ya kashe soja a Legas Ezea, wanda aka zaɓe a ƙarƙashin jam’iyyar LP, shi ne kaɗai Sanatan da ya ci zabe daga Enugu karkashin jam’iyyar a Majalisar Dattawa ta 10. Rasuwarsa ta sa ya zama sanata na biyu daga yankin Kudu maso Gabas da ya rasu cikin shekaru biyu, bayan mutuwar Sanata Ifeanyi Ubah daga Jihar Anambra, wanda shi ma ya rasu a Landan a watan Yuli 2024 yana da shekara 52. Da labarin...
    pirme ministocin kungiyar hadin guiwa ta kasashen shangai SCO sun kawo karshen taron kungiyar karo na 24 a birnin mosko inda suka fitar da bayanin hadin guiwa na yi watsi da duk wani mataki na kasashen turai dake nuna adawa da kasar iran, musamman kan abin da ya shafi shirin ta na nukiliya na zaman lafiya. Bayanin karshe na taron da mamabobin kungiyar suka fitar ya yi tir da adawa da kasashen yamma ke nunawa kasar iran  da ya shafi takunkumin karya tattalin arziki da ya sabama dokokin kasa da kasa , shuwagabannin sun yi gargadin cewa daukar irin wannan matakai zai cutar da majalisar dinkin duniya wajen cimma kudurin ci gaban alumma. Kasashen Amurka da sauran kawayenta sun maka...
    Rahotanni sun nuna cewa hare-haren da Isra’ila ta kai a sansanin yan gudun hijira na Ainul Hilwa dake kusa da Sidon yayi sanadiyar shahadar falasdinawa 22 tare da jikkata wasu da dama, kana sun soki kasar Labanon game da rashin daukar matakin soji da na siyasa akai. Harin an kai shi ne kan sansanin yan gudun hijira mafi girma dake kasar Labanon  yanzu dai dubban gidaje ne suka shiga cikin fargaba saboda da hare haren da isra’ila ke kaiwa ba kakkautawa, Gwamnatin kasar labanon na fuskantar mummunar suka na rashin daukar matakan da suka dace da haka yasa isra’ila ke yawan kai hare-hare a kudancin kasar, yayain da jami’an gwamnatin ke cewa yanzu haka suna shirin mika wani korafi  ga...
    Wani mutum da ake zargin yana fama da matsalar tabin hankali ya kai hari tare da kashe wani soja a yankin Imota da ke Ikorodu a jihar Legas. Lamarin, wanda ya faru a fili da rana tsaka a ranar Lahadi, ya sa makwabtan wurin da dama guduwa don neman tsira. Gobara ta laƙume kasuwar Katako a Gombe Amurka za ta binciki zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Nijeriya ranar Alhamis Shaidu sun bayyana cewa wanda ya kai harin, wanda ba shi da makami sai sanda ta itace, ya kusanci sojan ya dinga dukan shi da sandar. Sojan da ya rasu, wanda aka ce yana aiki a karkashin Operation AWASE, rundunar haɗin gwiwa ta musamman da ke yaki da laifuka...
    A ranar Alhamis, 20 ga watan Nuwamban 2025, ake sa ran Majalisar Wakilan Amurka za ta gudanar da zama na musamman domin bincikar zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Nijeriya. Kwamitin Majalisar Wakilan kan Afirka ya sanya ranar domin bitar fasalin da Shugaba Donald Trump ya yi kwanan nan na sanya Nijeriya a matsayin kasar da ake sa wa ido na musamman, CPC, kan zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi. Gwamnan Taraba ya dakatar da ficewa daga PDP saboda sace ɗalibai a Kebbi Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai mata a Kebbi Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa, an gayyaci mambobin Kwamitin Harkokin Waje na majalisar, wanda aka shirya za a yi tattaunawar da...
    Fira ministan jamhuriyar Kalmykia mai kwarya-kwaryar cin gashin kai a tarayyar Rasha, Utshir Janibinov ya fada wa manema labaru a wurin taron gwamnonin gundumomin dake gabar ruwan “Caspian” cewa; Taron da aka yi wanda shi ne irinsa na farko yana da tasiri mai kyau wajen bunkasa alaka a tsakanin gundumomin gabar ruwan “Caspian”. Taron na gwamnonin gundumomin da suke a gabar ruwan “Caspian” an yi shi ne dai a garin Rasht a gundumar Gilan  dake nan Iran. Mataimakin Fira ministan jamhuriyar Kalmykia ta tarayyar Rasha, ya bayyana jin dadinsa na halartar wannan taron a nan Iran. A Yau Talata ne dai aka bude wannan taron wanda aka bai wa taken: ” Tekun Caspian A Matsayin Wata Gada Ta Bunkasa Alaka...
    Tsohon zakaran damben duniya a ajin masu nauyi, Anthony Joshua, zai fafata da tauraron YouTube, Jake Paul, a wani damben ƙwararru da za a yi a watan Disamba mai zuwa. Joshua, ɗan ƙasar Birtaniya mai shekaru 36, wanda ya lashe kambun duniya ajin masu nauyi sau biyu, zai kara da Paul a cibiyar Kaseya Center da ke Miami. ’Yan bindiga sun sako mutane 45 bayan sulhu a Katsina Barau FC ta doke Enugu Rangers a Firimiyar Najeriya Ana sa ran za a watsa damben kai tsaye a tashar Netflix a ranar 19 ga Disamba. Wadda za ta kasance fafatawa mai turmi takwas, kowanne na mintuna uku. Joshua, wanda ya yi fafatawa uku a baya da nauyin sama da kilogram 113,...
    Masu gabatar da kara a kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) a ranar Litinin din nan sun bukaci kotun da ta zartar da hukuncin daurin rai da rai kan Ali Muhammad Ali Abd-Al-Rahman, wanda aka fi sani da Ali Kushayb, kwamandan rundunar Rapid Support Forces (RSF), saboda rawar da ya taka a ta’asar da aka aikata a lokacin harin da aka kai a yankin Darfur na kasar Sudan. An samu Kushayb da laifuka 27 da suka hada da laifukan yaki da cin zarafin bil adama da suka hada da kisan kai, azabtarwa, fyade, da dai sauran manyan laifuka. Shari’ar dai ita ce shari’ar farko da aka shigar a gaban kotun ICC dangane da yakin  Darfur. A farkon...
    Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da daftarin kudurin Amurka, don ba da izinin kafa Rundunar Tsaro ta Kasa da Kasa (ISF) a Zirin Gaza. Mambobi 13 daga cikin 15 na Majalisar sun amince da kudurin, inda Rasha da China suka kaurace wa kada kuri’ar. Kudurin yana da nufin tura sojojin kasashen waje na wucin gadi don kula da tsaro, tallafawa sake ginawa da kuma kiyaye tsari a yankin. Daftarin ya yi kira ga rundunar ta yi aiki na tsawon shekaru biyu, tare da yiwuwar kara sabunta wa’adin aikinta wanda ya danganta ne da ci gaban da ake samu a kasa. Kudurin ya kunshi abubuwa da yawa,  ciki har da kare iyakokin Gaza, kare fararen hula, kare hanyoyin...
    Hukumar ƙwallon ƙafar Afirka CAF, ta bayyana cewa bayan tankade da rairaya da ta yi, a yanzu ’yan wasa uku kacal ne suka rage a takarar gwarzon nahiyyar na bana. A wata sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana Achraf Hakimi da Mohamed Salah da Victor Osimhen, a matsayin sauran ukun da suka rage a takarar gwarzon dan ƙwallon ƙafar Afirka na bana. Gobara ta laƙume rayukan yara biyu ’yan gida ɗaya a Ribas Mayaƙan ISWAP sun kashe kwamandan soji a Borno Hakimi, kyaftin din Morocco, ya lashe kofuna daga ciki har da Champions League a PSG — na farko a tarihin ƙungiyar — da Ligue 1, da European Super Cup, da kuma kai wa zagayen ƙarshe...
    Mataimakin shugaban kasar Iran na farko ya bayyana cewa: Iran tana da kyakkyawar alaƙa ta musamman da kuma al’adu da membobin ƙungiyar haɗin gwiwa ta Shanghai Mataimakin Shugaban Kasa na Farko na Iran ya ce, “Iran tana da alaƙar haɗin gwiwa na musamman da al’adu da dukkan ƙasashe membobin Ƙungiyar Haɗin Kan Shanghai (SCO), kuma abin farin ciki, ƙasar Iran ta shiga ƙungiyar SCO a hukumance cikin shekaru biyu da suka gabata.” Da yake jawabi a Filin Jirgin Sama na Mehr-abad kafin ya tashi zuwa Rasha don halartar taron kolin kungiyar Shaanghai ta SCO, Mataimakin Shugaban Kasa na Farko Mohammad Reza Aref ya ce, “Ƙungiyar SCO ƙungiya ce mai tasowa amma mai ƙarfi da cikakken iko. Jimillar yawan al’ummar ƙasashe...