Me Ya Sa ‘Yan Kasuwar Kasashen Afirka Rungumar Kudin RMB?
Published: 8th, May 2025 GMT
Tsohon ministan kudin kasar Amurka John Connally ya ce, dala kudi ne na Amurka, amma matsala ce ga sauran kasashen duniya. Yanzu haka tsarin kudin na haifar da karin radadi ga kasashe daban daban, sakamakon matakan kasar Amurka na kashin kai, lamarin da ya sanya dimbin kasashe neman kauracewa tsarin dalar Amurka.
Kudi wani nau’in kayan aiki ne. Idan ana iya amfani da shi cikin sauki, kuma za a iya dogaro a kan sa ba tare da samun hasara ba, to, za a so a yi amfani da shi. Amma idan wani kudi ya kan haifar da matsaloli, to, tabbas za a guji yin amfani da shi. Wannan batu yana cikin tsarin gudanar tattalin arziki, ba wani abu ne da za a iya sauya shi ta karfin siyasa ba. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Hannayen jarin kamfanonin fina-finan Amurka sun fadi sakamakon barazanar Trump na kakaba harajin kwastam
Bayanai daga Amurka na cewa Hannayen jari na kafofin watsa labaru da kamfanonin shirya fina-finai da harkokin nishadi na Amurka sun fadi kasa, bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa, yana shirin kakaba harajin kwastam da kashi 100 bisa 100 a kan fina-finan da ake shiryawa a ketare.
Hannayen jarin kamfanonin fina-finai irin su Netflix Inc. da Warner Bros. Discovery Inc. sun fadi da kusan kashi 3 cikin dari, inda na Paramount Global da Walt Disney Co. kuma suka fadi da kusan kashi 2 cikin dari yayin da aka bude kasuwa.
A wani sakon da ya wallafa kan shafinsa na manhajar True Social, shugaban na Amurka ya ce yana umurtar ma’aikatar kasuwanci da wakilinsa na cinikayya da su “yi maza-maza su fara aikin kakaba” harajin a kan fina-finan kasashen waje, inda ya kara da cewa, “Muna son kara ganin fina-finan da ake yi a Amurka”.
Shugaban ya kuma sanya fina-finan kasashen waje a cikin jerin abubuwan dake kawo barazana ga tsaron kasa.