Jakadan Sin A Najeriya Ya Gana Da Ministan Harkokin Wajen Najeriya
Published: 8th, May 2025 GMT
A jiya ne jakadan Sin a Najeriya Yu Dunhai ya gana da ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Tuggar. Jakada Yu ya bayyana cewa, ganawar da ta gudana tsakanin ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da mista Tuggar a kasar Brazil a baya-bayan nan, ta aike da sako mai karfi cewa, Sin da Najeriya na tsayawa tsayin daka kan bin ra’ayin bangarori daban-daban, da tabbatar da adalci da daidaici.
A nasa bangare, minista Tuggar, ya yi kyakkyawan nazari kan yadda huldar dake tsakanin kasashen biyu ke gudana, ya kuma jaddada cewa, Najeriya na fatan karfafa hadin gwiwa da kasar Sin a fannonin cinikayya, zuba jari, da hada-hadar kudi da dai sauransu, da zurfafa tuntubar juna da hadin gwiwa a harkokin da suka shafi bangarorin daban daban.
Bangarorin biyu sun amince cewa, daukar matakan kakaba harajin da Amurka ta yi ba bisa ka’ida ba, ya matukar yin illa ga ka’idojin cinikayya tsakanin bangarori daban daban, da kuma halaltattun hakkoki da muradun dukkan kasashe. Ya kamata kasashen duniya su hada kai tare da yin adawa da dabi’ar cin zarafin da Amurka ke yi bisa radin kai. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Babban Hafsan Sojan Nijeriya Ya Sha Alwashin Inganta Tsaro A Yobe
“Duk da cewa, ba zan iya yin cikakken bayani dangane da sabbin dabarun da muka dauka ba. Amma mutanen Yobe su kwantar da hankalinsu kuma abubuwa za su inganta.”
Har ila yau, ya yi karin haske dangane da wasu muhimman matakan da za a dauka don magance rashin tsaro a jihar, ciki har da tura karin sojoji tare da kayan aikin tsaro.
A nasa bangaren, Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya yaba wa COAS kan daukar matakan gaggawa wajen mayar da martani kan hare-haren kwanan nan, sannan ya yi wa sojojin da suka rasu addu’a.
Ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin farar hula da sojoji, inda ya bukaci karfafa hadin gwiwa wajen bayar da bayanan sirri don dakile matsalolin tsaro.
Gwamna Buni ya kara da cewa, “Dole mu hada kai mu yi aiki tare, tsakanin jami’an hukumomin tsaro wajen bayar da gudummawa tsakanin rundunonin tsaron Nijeriya.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp