Kungiyar gwagwarmaya ta Ansarullah ta bayyana cewa yarjejeniyar tsagaiat wutar da ta cimma da Amurka, ba ta sauya matsayin kasar ba na kai wa Isra’ila hari.

Kakakin kungiyar Ansarullah Mohammed Abdul-Salam ya jaddada cewa Dakarun Yeman za su ci gaba da kai hare-hare kan Isra’ila domin goyan bayan Falasdinawa a zirin Gaza.

Yarjejeniyar da Amurka ba ta da alaka da matsayinmu na goyan bayan Gaza, inji Abdul-Salam.

A jiya ne masarautar Oman ta sanar cewa Amurka da kungiyar Ansarullah da aka fi sani da ta ‘yan Houtshis a Yeman suka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Oman ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa: Bayan tattaunawa da tuntubar juna da aka yi a baya-bayan nan da kuma tuntubar juna tsakanin masarautar Oman ta Amurka da hukumomin da abin ya shafa a birnin Sana’a na jamhuriyar Yeman, an samu cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu.

Sanarwar ta kara da cewa: A nan gaba, ko wanne bangare ba zai kai hari kan daya ba, ciki har da jiragen ruwan Amurka a tekun Bahar Rum da Bab al-Mandab, domin tabbatar da ‘yancin zirga-zirgar jiragen ruwa da kuma tafiyar da harkokin kasuwancin kasa da kasa cikin sauki.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

 Hare-haren Hizbullah Sun Jazawa HKI A Fagen Gona Asarar Dala Miliyan 108

Wani rahoto na musamman da HKI ta gudanar akan asarar da ta fuskanta sanadiyyar yaki da Hizbullah, ya bayyana cewa, a fagen aikin gona kawai sun yi asarar dalar Amurka miliyan 108 wacce ta fara daga 8 ga watan Oktoba 2023.

Kungiyar ReGrow Israel” ta ce, yakin da aka yi da Hizbullah ya yi barna gagaruma a fagen aikin gona da asarar da ta kai ta dala miliyan 108 a kan iyaka da Lebanon.

Nazarin wannan kungiyar ya kuma kara da cewa; Tun daga ranar 8 ga watan Oktoba 2023 har zuwa lokacin tsagaita wutar yaki a karshen 2024, hare-haren Hizbullah sun lalata muhimmacin cibiyoyi a “Isra’ila” da kuma haddasa gobara mai girma, da hakan ya tilastawa mazaunan yankin, musamman manoma yin hijira.

Bugu da kari, binciken ya ce, barnar da yakin ya haddasa akan gonaki, ya haddasa koma baya a fagen samar da abinci, da kuma kawar da daidaito a kasuwanni.

Shugabar zartarwa ta kungiyar “ReGrow Isra’el” Danil Abraham,  ta sanar da cewa; Barnar da aka samu a kan iyaka da Lebanon tana da girman gaske, da kuma rikiritarwa, ta kuma shafi yanki mai girma fiye da fagen dagar Gaza.

Abraham ta kuma ce; Sai 9000 aka kai wa arewacin “HKI” hare-hare da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuki, da hakan ya sa gonaki masu yawa su ka kone. Haka nan kuma kaso 60% na manoman a Arewacin HKI, sun dakatar da ayyukansu baki daya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  •  Hare-haren Hizbullah Sun Jazawa HKI A Fagen Gona Asarar Dala Miliyan 108
  • Bukhaiti: HKI Ta Ketari Jan Layimmu, Ta Jira Maida Martanimmu
  • Jiragen Yaken HKI Sun Kai Hare-Hare A Kan Tashar Jiragen Sama Na Birnin San’aa Na Kasar Yemen
  • Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Jaddada Yin Allah Wadai Da Hare-Haren ‘Yan Sahayoniyya Kan Kasar Yemen
  • Amurka Da Haramtacciyar Kasar Isra’ila Sun Taron Dangi Kan Kasar Yemen
  • Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Janyo Shahadan Falasdinawa 50 A Yankin Zirin Gaza
  •  Sojojin HKI Sun Kai Hare-hare A Sassa Mabanbanta Na Kasar Yemen
  • Iran ta watsi da zargin Isra’ila da Amurka cewa ta na da hannu a harin ramuwar gayya na Yemen
  • Rundunar Yemen Zata Kakaba Takunkumi Kan Jiragen Saman Fasijan Haramtacciyar Kasar Isra’ila