Likitocin Sin Sun Ba Da Jinya Kyauta A Yankunan Karkara Na Saliyo
Published: 10th, May 2025 GMT
Daga ranar 7 zuwa ta 8 ga watan Mayun nan, tawagar likitocin kasar Sin a kasar Saliyo karo na 26 ta shiga cikin yankunan karkara da dama na kasar Saliyo, inda ta kammala ayyuka hudu na bayar da jinya kyauta cikin kwanaki biyu, tare da bayar da hidimar jinya ga mazauna kauyakan da ma’aikatan kamfanoni.
A gun gudanar da ayyukan jinyar kyauta, kwararrun likitocin kasar Sin daga bangaren aikin tiyata na gama-gari, da aikin kasusuwa, da aikin kula da mata da na sauran sassa sun gudanar da gwaje-gwajen lafiya da gano cututtuka da kuma ba da jinya cikin tsari a wurin bayar da jinya na wucin gadi da rarraba magunguna kyauta, tare da ba da cikakken jagora kan yadda za a yi amfani da magunguna da rigakafin cututtuka. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
NNPC Ya Ƙara Kuɗin Fetur, Duba Sabon Farashin
Wani hari da Sojojin Amurka da Isra’ila suka kai kan wuraren Nukiliyar Iran ya kara tsoratar da kasuwar mai, wanda ke nuna cewa farashin na iya haura sama da $80 a kowace gangar mai. Masana sun yi hasashen cewa farashin fetur na iya haura sama da N1,000 a litar cikin ‘yan makonnin nan idan ba a dauki mataki ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp