Sauya sheƙa bayan cin moriyar jam’iyya butulci ne — Kwankwaso
Published: 10th, May 2025 GMT
Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya soki ’yan siyasar da ke sauya sheƙa daga jam’iyyar da a ƙarƙashinta suka samu nasarar lashe zaɓe zuwa wata.
Kwankwaso ya bayyana lamarin a matsayin cin moriyar ganga, yana mai cewa hakan babban kuskure ne a siyasance.
HOTUNA: An ƙaddamar da tashin sahun farko na maniyyatan Nijeriya zuwa Saudiyya JAMB ta saki sakamakon jarrabawar 2025Sanata Kwankwaso ya bayyana hakan ne a gidansa da ke Miller Road a Kano yayin da yake karɓar wasu ’yan siyasar da suka sauya sheƙa zuwa NNPP daga Ƙaramar Hukumar Takai.
Kwankwaso ya ƙara jaddada irin juriya da haɗin kai da ke tafiyar Kwankwasiyya duk kuwa da cewa an ta ƙoƙarin ganin an kawar da hankalin mabiya.
“Duk mun ga abin da ya riƙa faruwa a tarihi, musamman a shekarar 2015 lokacin da wasu ’yan siyasa suka dawo cikinmu amma ashe mayaudara ne masu mugun nufi a zuciyarsu.
“Waɗannan ’yan siyasa sun yi ƙoƙarin kawo hargitsi a cikin jam’iyyarmu amma ba su yi nasara ba.
“Haka ma lokacin da zaɓen 2019 ya zo duk kowa ya san abin da ya faru. Amma abin da yake faruwa a bayan nan ya koya mana darasi sosai.
“Wannan tafiyar tamu ta Kwankwasiyya tana tare da talakawa a kodayaushe, saboda haka duk wani mai kwaɗayi ba zai iya zama a cikinta ba.
Furucin Kwankwaso na zuwa ne yayin da bayan nan wasu jiga-jigan siyasa a NNPP da tafiyar Kwankwasiyya suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC — ciki har da Sanata Kawu Sumaila da Kabiru Alhassan Rurum da sauransu.
Kodayake a baya-bayan nan shi ma dai Kwankwason ana raɗe-raɗin cewa zai koma jam’iyya mai mulki ta APC.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Sanata Rabi u Musa Kwankwaso Sauya Sheƙa Kwankwaso ya
এছাড়াও পড়ুন:
Martanin Kwankwaso Ga Kawu Sumaila Da Sauran Masu Ficewa Daga NNPP
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp