2025-09-17@21:52:27 GMT
إجمالي نتائج البحث: 143
«Zaɓen 2027»:
Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi zargin cewa gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ba ta da niyyar gudanar da sahihi kuma ingantaccen zaɓe a 2027. Galadima ya bayyana hakan ne ranar Talata a wata hira da aka yi da shi a shirin Prime Time na gidan talabijin na Arise TV, inda ya ce...
Ɗan takarar jam’iyyar Labour a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Peter Obi, ya ziyarci tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, da kuma sabon Olubadan na Ibadan, Rashidi Ladoja, a wani zagayen ganawa da manyan ’yan siyasa gabanin zaɓen 2027. Obi, wanda ke ƙoƙarin ƙara yauƙaƙa zumunci da manyan shugabanni a fadin ƙasar, ya bayyana cewa ziyarar...
Jagoran jam’iyyar NNPP na kasa kuma dan takararta na shugaban kasa a 2023, Rabiu Kwankwaso, a ranar Talata ya gana da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a jihar Kuros Ribas domin tsara dabarun tunkarar babban zabe na 2027. Da yake jawabi a babban birnin jihar, Kalaba, Kwankwaso ya bukaci ‘ya’yan jam’iyyar da su ba...
“Don haka, Ma’aikatar Yaɗa Labarai tana aiki kafada da kafada da Ma’aikatar Harkokin Ƙananan Hukumomi, Hukumar Harkokin Addinai, tare da haɗin gwiwar manyan shugabannin gargajiya da na addini, domin tabbatar da cewa wayar da kai da kuma tura saƙon rajista ya isa kowace mazaba, ƙauye, da unguwa a fadin Jihar Kaduna,” in ji Maiyaki. ...
Firaministan Japan, Shigeru Ishiba, ya sanar da murabus dinsa a matsayin shugaban jam’iyyar Liberal Democratic Party (LDP), watanni kaɗan bayan jam’iyyarsa ta sha mummunan kaye a zaɓen watan Yuli. Ishiba ya sanar da matakin ne a ranar Lahadi, duk da cewa a baya ya yi ƙoƙarin kaucewa matsin lambar ‘yan jam’iyyarsa da ke neman ya...
Ya kuma nuna damuwa kan rikicin magoya bayan wasu ‘yan siyasa a kafafen sada zumunta, yana mai cewa hakan na iya tayar da hankali a jihar. Game da tsaro kuwa, Gwamna Sule ya bayyana cewa gwamnati na ɗaukar matakai don shawo kan matsalolin da ke tasowa a wasu sassan jihar. Ya ce sun ƙarfafa haɗin...
Wata mata mai tabin hankali da ba a iya gano danginta ba, ta haihu a bainar jama’a a cikin kasuwar garin Aarinoye a karamar hukumar Itesiwaju ta Jihar Oyo. Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa matar ta haihu ne da misalin karfe 5:00;na yammacin ranar Laraba, kuma ta haifi jaririnta namiji lami lafiya ba...
Tun kafin zaɓen 2023 PDP ke fama da rikici, matsalar da ake ganin ta taimaka wajen hana jam’iyyar samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da...
Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana ƙwarin gwuiwar cewa Shugaba Bola Tinubu zai sake lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027, inda ya ce ya shirya yin “alwashi” akan wannan nasara. Wike ya yi wannan bayani ne a yayin wata tattaunawa da manema labarai a Abuja, yana mai ƙaryata hasashen tsohon gwamnan...
Jam’iyyar APC ta yi nasarar lashe ƙananan hukumomi 20 daga cikin 23 a zaɓen ciyammomi da kansiloli da aka gudanar ranar Asabar. Jam’iyyar PDP wadda ke mulki a jihar ta samu nasara a ƙananan hukumomi uku ne kacal, a zaɓen da Hukumar Zaɓe ta Jihar Ribas (RSIEC) ta gudanar. Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram...
Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana cewa Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara da ’yan majalisar dokokin jihar za su koma kujerunsu a ranar 18 ga Satumba, lokacin da dokar ta-ɓaci a jihar za ta ƙare. Wike, ya bayyana haka ne a ranar Asabar bayan ya kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen ƙananan hukumomi da ake...
A yau Asabar ake gudanar da zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin Jihar Ribas. Hotuna: Bassey Willie
Ya ƙara da cewa jam’iyyarsu ta ADC za ta iya fito da ‘yan takara daga kowace shiyya, duk da cewa APC da PDP sun nuna cewa daga Kudu za su fito da ɗan takara a 2027. Duk da cewa wasu na ganin tasirinsa ya ragu a Jihar Ribas saboda rikicin siyasa tsakaninsa da Nyesom Wike,...
Wata ƙungiyar siyasa da ke goyon bayan masu fafutikar nan ta “Bring Back Our Goodluck” ta buƙaci tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan, da ya tsaya takara a Zaɓen 2027. Ƙungiyar ta ce a Zaɓen 2015 an yaudari ‘yan Najeriya da suka dage wajen ganin bai yi nasara ba a ƙoƙarinsa na neman wa’adi na...
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) a jihar Kano ta bayyana cewa akwai katin zaɓe na dindindin (PVC) sama da dubu 367,000 da jama’a ba su karɓa ba har yanzu a jihar. Kwamishinan INEC na Kano, Ambasada Abdu Zango, ya bayyana haka ne yayin da ya karɓi tawagar kwamitin gwamnatin jihar kan rajistar...
Mutum 333 sun shiga hannu kan zargin aikata laifuka a yayin zaben cike gurbi da aka kammala a Jihar Kano. A ranar Asabar aka gudnar da zaben na cike gurbi a mazabun Majalisar Tarayya da akamaimaita a ranar Asabar a mazabar Ghari/Tsanyawa da kuma zaben cike gurbi na Bagwai/Shanono. Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kano,...
Jam’iyyar NNPP a Jihar Kano, ta ƙi amincewa da sakamakon zaɓen ɗan majalisar jiha da aka gudanar a mazaɓar Ghari/Tsanyawa. Jam’iyyar ta ce Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da wasu ’yan siyasa sun yi maguɗi. Jauro Jatau: Al’umma sun roƙi gwamnati ta samar musu da wutar lantarki APC ta lashe zaɓen cike...
An bayyana sakamakon zaɓen cike gurbi da aka gudanar a Ƙaramar Hukumar Zariya da kewaye, da kuma Mazabar Basawa da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Gari, jihar Kaduna. Zaɓen ya gudana cikin kwanciyar hankali ba tare da rahoton tashin hankali ba. Isa Haruna Ihamo na APC ya yi nasara A zaɓen da aka gudanar a Zariya,...
Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar, ya sha kaye a rumfar zaɓensa yayin zaɓen cike gurbi na mazabar Garki-Babura a Jihar Jigawa ranar Asabar. Ministan ya kaɗa ƙuri’arsa a rumfar Ɓaɓura Ƙofar Arewa Primary School 001, inda sakamakon da aka bayyana, jam’iyyar APC ta samu ƙuri’u 112, yayin da PDP ta samu 308 a rumfar zabensa....
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi nasara a zaɓen cike gurbi na Ghari/Tsanyawa da aka gudanar ranar Asabar a Jihar Kano. Da yake sanar da sakamakon da misalin karfe 6:10 na safiyar Lahadin nan, babban jami’in da ya tattara sakamakon zaɓen, Farfesa Muhammad Waziri na Jami’ar Bayero, ya bayyana Garba Ya’u Gwarmai na jam’iyyar...
Jam’iyyar NNPP wato New Nigeria Peoples Party, ta lashe zaɓen cike gurbi na majalisar dokokin tarayya da aka gudanar a ƙananan hukumomin Bagwai da Shanono da ke Jihar Kano. Babban jami’in da ya tattara sakamakon zaɓen, Farfesa Hassan Adamu ne ya bayyana hakan da misalin ƙarfe 12:36 na daren Asabar wayewar gari Lahadi. Farfesa Hassan...
Jam’iyyar APC ta buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), da ta soke zaɓen cike gurbi na Shanono/Bagwai da kuma na mazaɓar Ghari a Jihar Kano. Jam’iyyar ta buƙaci a soke zaɓen saboda ta zargi cewar an samu tashe-tashen hankula a yankunan da zaɓen ya gudana. An kama ’yan daba 288 yayin zaɓen...
Aƙalla mutum 164,390 ake sa ran za su kaɗa ƙuri’a a zaɓen cike gurbi na ɗan majalisar dokokin Jihar Kaduna a mazaɓar Zariya da kewaye. Sai dai yawancin masu zaɓe ba su fito ba. APC ta buƙaci a soke zaɓen cike gurbi a Kano An kama ’yan daba 288 yayin zaɓen cike gurbi a Kano...
Jam’iyyar APC ta buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), da ta soke zaɓen cike gurbi na Shanono/Bagwai da kuma na mazaɓar Ghari a Jihar Kano. Jam’iyyar ta buƙaci a soke zaɓen saboda ta zargi cewar an samu tashe-tashen hankula a yankunan da zaɓen ya gudana. An kama ’yan daba 288 yayin zaɓen...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta kama mutum 288 da ake zargin ’yan daba ne a lokacin zaɓen cike gurbi da aka gudanar a jihar. Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an kama mutanen da makamai masu hatsari, ciki har da bindigogi ƙirar gida, wuƙaƙe da adduna. Zaɓen cike gurbi: An kama ’yan...
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta tabbatar da kama aƙalla ’yan daba 100 da ake zargi da tayar da zaune-tsaye a lokacin zaɓen cike gurbi da aka gudanar a Ƙaramar Hukumar Bagwai a Jihar Kano. Kwamishinan INEC na Jihar Kano, Abdu Zango, ya shaida wa manema labarai a Bagwai cewa jami’an tsaro...
Ga hotunan yadda ake gudanar da zaɓen cike gurbi a sassan Najeriya.
Jami’an tsaro sun kama wani mutum da tsabar kuɗi Naira miliyan 25 da ake zargin kuɗin sayen kuri’a ne a zaɓen cike gurbin da ke gudana a Jihar Kaduna. Da misalin ƙarfe 3 na dare kafin wayewar garin safiyar Asabar da ake gudanar da zaɓen ne ’yan sanda da jami’an hukumar tsaro ta DSS suka...
Ahmed Maiyaki da Sadiq Mamman Legas a madadin gwamnatin jihar Kaduna sun ce ofishin babban lauyan gwamnati da kwamishinan shari’a zai yi nazari kan kalaman da kungiyar hadaka ta ADC ta yi tare da baiwa gwamnatin jihar shawara kan mataki na gaba. Tun da farko a wani taron manema labarai, jam’iyyar African Democratic Congress da...
Jam’iyyar ta naɗa Abdulrazaq Abubakar Isah Iko a matsayin shugaban riƙon ƙwarya, da Adamu Aliyu a matsayin sakataren riƙon ƙwarya har sai an gudanar da sabon zaɓe. ADC ta gargaɗi shugabannin da aka dakatar kada su ci gaba da kiran kansu a matsayin shugabannin jam’iyyar ko gudanar da harkokinta. Haka kuma ta soke tarukan siyasa...
“Duk da cewa jama’a suna da ‘yancin nuna sha’awarsu kan siyasa, shirye-shiryen amincewa, yunƙurin tattarawa, da tallace-tallace irin na kamfen da nufin tallata ‘yan takara kafin lokacin yaƙin neman zaɓe na hukumance ba a amince da su ba. “INEC tunin ta nusar da wannan batun a lokacin ganawarta da jam’iyyun siyasa, ta kuma gargaɗin dukkanin...
Jam’iyyar PDP ta ce za ta ɗauki mataki kan wasu mambobinta da ke aikata abubuwan da ke kawo wa jam’iyyar koma baya. Shugabancin jam’iyyar ya fi damuwa da mambobin da ke bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu don sake tsayawa takara a zaɓen 2027. Isra’ila za ta mamaye ilahirin Zirin Gaza ya koma...
Kotun tsarin mulkin Kamaru ta haramta wa jagoran adawar ƙasar, Maurice Kamto tsayawa takarar shugaban ƙasa, a babban zaɓe mai zuwa na watan Oktoba, kan abin da ta bayyana rashin cika ka’idojin tsayawa takara. Lauyansa, Hippolyte Meli Tiakouang ne ya tabbatar wa manema labarai hukuncin kotun wanda ba za a iya ƙalubalanta ba, bayan kammala...
Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani, ya gargadi ’yan siyasa da masu amfani da kafafen sada zumunta da su daina zagin malaman addini da a yanzu ya zama ruwan dare a ƙasar nan. Gwamnan ya bayyana cewa irin wannan mummunar ɗabi’a ta cin zarafi malaman addini na iya lalata zamantakewa da tubalin zaman lafiya a tsakanin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce idan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC suka sake lashe zaɓe a 2027, hakan zai lalata makomar ’yan Najeriya. El-Rufai, ya faɗi haka ne a Jihar Sakkwato yayin wani gangamin wayar da kan jama’a da jam’iyyar adawa ta ADC, ta shirya. Gwamnan Yobe ya naɗa Gadaka...
Bayan shekar 22 da kuɓutar da Nijeriya daga mulkin soja, dimokuraɗiyya na ci gaba da fama da rauni mai tsanani. Alamun cutar sun bayyana ne a cinikin baragurbin wakilai (delegates), amfani da kuɗin ƙasa da aka wawure ta hanyar haram wajen gudanar da yaƙin neman zaɓe, maƙudan kuɗin da ake ware wa Hukumar Zaɓe ta...
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), za ta fara rajistar ƙuri’a ta intanet a ranar 18 ga watan Agusta, 2025, domin tunkurar zaɓen 2027. Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar ban girma da Hukumar NOA ta masa a hedikwatar INEC da ke Abuja. Rundunar sojin ruwa za...
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana naɗin Saidu Yahya a matsayin sabon Shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafen Jama’a da yaƙi da cin hanci da rashawa (PCACC), bayan ƙarewar wa’adin tsohon shugaban, Barrister Muhuyi Magaji Rimin Gado, a watan Yuni. Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ta...
A wani ɓangare na shirin gudanar da zaɓen cike gurbi na Babura/Garki a Majalisar Tarayya, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) reshen Babura ta shirya muhimmin taron masu ruwa da tsaki domin tabbatar da sahihin zaɓe mai inganci da haɗin kai. A jawabinsa yayin taron, jami’in zaɓe na ƙaramar hukumar Babura, Malam...
Ɗaya daga cikin jigo da suka kafa Jam’iyyar PDP, Farfesa Jerry Gana ya yi iƙirarin cewa tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi zai kayar da duk wani ɗan takara a jihohin Arewacin Najeriya idan ya tsaya takara a PDP. Da yake bayabni a tashar talabijin ta Arise TV a ranar Laraba, Gana ya ce, “Ni...
Ya ce biyayyarsa ga doka da oda ya sa ya samu girmamawa daga abokan aikinsa da jama’a gaba ɗaya. Gwamnan ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalansa, ’yan uwansa, abokansa da ma al’ummar masarautar Hardawa da ta Misau. Ya roƙi Allah Ya gafarta masa, Ya jikansa, ya kuma sanya shi a Aljanna. LEADERSHIP Hausa ta gano cewa...
Sauran sun haɗa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro Nuhu Ribadu, tsoffin gwamnoni, ministoci da hafsoshin tsaro. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
Al’ummar Arewacin Najeriya na shirin kayar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027 saboda ƙuncin rayuwa da kuma tsare-tsaren gwamnatinsa da suka mayar da yankin saniyar ware. Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir David Lawal ne ya bayyana haka, yana mai cewa gamayyar shugabanni da ’yan siyasar Arewa na haɗa ƙarfi da ƙarfe domin...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba ’Yan Najeriya da dama ne dai aka bayyana ba sa fitowa kaɗa kuri’a a duk lokacin da zaɓe ya zagayo. Wasu daga cikin ’yan ƙasar sun bayyana rashin jin daɗin abun da hukumar zaɓe ke yi, rashin yarda da sakamakon zaɓuɓɓukan da suka gabata da dai sauransu a...
Sanata Dickson ya ƙara da cewa duk da wasu jami’an gwamnati ba su bi umarnin shugaban ƙasa ba, amma shi ya lashe zaɓen, kuma ya gode wa Buhari. Hakazalika, ya ce bayan ya kammala wa’adinsa a 2020, a lokacin da APC ke shirin karɓar mulki a Bayelsa, kotun ƙoli ta yanke hukunci cewa ɗan takararsu...
Olumekun ya ƙara da cewa, katunan zaɓe na rijistar da ta gabata ma za su kasance a shirye don karɓa. Ya ce da saura kwanaki 105 zuwa zaɓe, INEC ta san lokaci ya matse, amma tana tabbatar da cewa sabbin masu rijista a jihar Anambra za su samu damar karɓar katunansu kafin zaɓen. Daga...
Hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa a Nijeriya (NCDC) ta ce adadin mutanen da zazzaɓin lassa ya kashe bana sun kai 151 a fadin kasar. Cikin wata sanarwa da NCDC ta wallafa a shafinta na X ranar Litinin, ta ce yawan kisan da cutar zazzaɓin lassa ke yi ya ƙaru daga kashi 17.3 cikin 100...
Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Ɓarkewa (ATBUTH) da ke Bauchi zai fara gwajin rigakafin cutar zazzabin Lassa. Wannan shiri na da nufin tabbatar da ingancin rigakafin, kuma wani ɓangare ne na babban shiri mai kasashe da yawa mai suna “Background Rates of Adverse Events for Vaccine Evaluation in Africa (BRAVE).” ATBUTH na daga cikin...
Kotun Ƙoli ta tabbatar da Sanata Monday Okpebholo na jam’iyyar APC a matsayin sahihin Gwamnan Jihar Edo. Wannan hukunci ya kawo ƙarshen shari’ar da ake yi biyo bayan zaɓen gwamnan jihar da aka yi a ranar 21 ga watan Satumba, 2024. Jami’ar Tarayya ta Gashuwa za ta ba matar Tinubu digirin girmamawa Tinubu ne ya...